2025-03-29@08:26:04 GMT
إجمالي نتائج البحث: 15
«Sayyid Hassan nasaralla»:
Gwamnatin Tarayya ta kama mutum 347 da ake zargi da haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba a sassa daban-daban na Najeriya, inda aka gurfanar 143 a kotu. Kama mutanen ya biyo bayan kafa wata runduna a shekarar 2024 don daƙile ayyukan haƙar ma’adanai ba ƙa’ida ba. Kotun ƙoli ta tabbatar da Anyanwu a matsayin sakataren PDP Kwankwaso ya yi Allah-wadai da ayyana dokar ta-ɓaci a Ribas Ministan Ma’adanai, Dele Alake, ya ce gwamnati na ƙoƙarin tabbatar da an hukunta mutum 327 da ke gaban kotu. “A wannan watan, Babbar Kotun Tarayya da ke Ilorin ta yanke wa wasu ‘yan kasashen waje guda biyu, Yang Chao da Wu Shan Chuan, hukuncin ɗaurin gidan yari kan haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba....
Jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya bayyana cewa; Amurkawa su kwana da sanin cewa, babu wani abu da za su samu, ta hanyar yi wa Iran barazana, kuma waninsu ma ya sani cewa, idan har su ka aikata wani abu maras kyau akan Iran, to za su fuskanci mayar da martani mai tsanani. Ayatullah Sayyid Ali Khamnei wanda ya gabatar da jawabi a yau Juma’a dangane da bikin sabuwar shekara ta Noruz a Husainiyyar Imam Khumaini dake nan Tehran, ya bayyana cewa; Babban kusakuren ‘yan siyasar Amurka da kuma na Turai , shi ne daukar ‘yan gwagwarmaya a wannan yankin da cewa ‘yan koren Iran, da hakan batunci a gare su.” Jagoran juyin musuluncin...
Shugaban kungiyar Ansarullah na kasar Yemen Sayyid Abdulmalik Husi ya bayyana cewa; Matukar Amurka ta ci gaba da kai wa Yemen hare-hare, to suna da hanyoyi da za su iya gasa mata aya a hannu masu yawa. Sayyid Abdulmalik al-Husi ya yi ishara da yadda dubun dubatar mutanen Yemen su ka fito a cikin birnin San’aa da kuma sauran biranen kasar domin raya da tunawa da rana da aka yi yakin Badar, yana mai cea; hakan yana a matsayin wani sako ne zuwa Amurka da Isra’ila, kuma tabbas idan su ka ci gaba da kai wa Yemen hari, to muna da zabi na hanyoyin da za mu yi amfani da su domin dandana musu kudarsu. Sayyid Husi wanda ya gabatar...
“Muna kokarin kawar da bangaren dala. Abin da muke so mu yi shi ne mu biya a cikin kudin gida na duk kamfanonin jiragen sama. Kuma za a biya kudin ne daidai da farashin dala a halin yanzu a lokacin da ake biya. “Kason da ya dace ya ba ku damar gudanar da ayyukanku dukkan ne za a biya ku, bayan kammala aikin za a karasa biyanku sauran,” ya shaida. Tun da farko, shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Usman Saleh, ya ce, ayyukan jirage na sufuri na daga cikin muhimman ayyukan da ke gabansu wajen sauke nauyin aikin hajji. “Lamarin na bukatar kwarewa matuka gaya da kuma himma da azama. Wannan lamarin ba kawai ga batun sufuri ba ne, ya shafi...
A lokacin ganawar ta su, Dantsoho ya shedawa Daraktar yin ayyukan da ake gudanarwa a Hukumar ta Tashoshin Jiragen Ruwa ta Kasa. Da take mayar da jawabi Daraktar Janar ta Cibiyar ta bayyana tawagar ta NPA shawarar ta kan yadda za a kara inganta ayyukan NPA, musamman a bangaren samar da saukin yin kasuwanci, domin a kara habaka gasar yin kasuwanci da kuma kara tara kudaden shiga. Kazalika, Hukumomin biyu, sun bayyana fatan kan hadakar a tsakaninsu, domin a samar da sauye-sauyen da a za su samar da sakamako mai kyau. Hukumar ta NPA, ita ce aka dorawa nauyin tafiyarwa da kuma tafiyar da ayyukan Tashoshin Jirgen Ruwan Kasar. Ana sa ran wannan hadakar a tsakanin NPA da PEBEC, za...
Sanarwar ta ƙara da cewa, ziyarar wani bangare ne na tsarin Gwamna Dauda Lawal na tabbatar da ingantattun ayyuka a faɗin jihar da kuma tabbatar da kammala ayyukan a kan lokaci. “A ranar Talata ne Gwamna Dauda Lawal ya fara ziyarar aiki domin duba ɗimbin ayyukan da gwamnatinsa ta fara aiwatarwa. “An fara ziyarar ne da Babban Asibitin Gusau, ɗaya daga cikin manyan asibitocin da aka gyara, tare da samar mata da kayan aiki a faɗin ƙananan hukumomi 14 na jihar.” A lokacin da yake duba aikin filin jirgin sama na Zamfara, Gwamna Lawal ya ce, gwamnatinsa ba wai kawai tana gina kowane irin filin jirgin saman ba ne, amma ana ginin ne na zamani wanda zai...
Gwamna Umar Namadi ya kaddamar da shirin noman rani ta hanyar amfani da rijiyoyin burtsatse a karamar hukumar Maigatari. Hakan wani muhimmin mataki ne na samar da abinci da zamanantar da noma a jihar Jigawa. A cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labarai na gwamnan Hamisu Mohammed Gumel ya rabawa gidan rediyon Najeriya ya ce, gwamnan ya bayyana cewa, aikin da ake amfani da shi ta hanyar amfani da hasken rana da kuma amfani da dabarun noman rani, yana yana taimakawa wajen yin noma a kowane lokaci na shekara tare da bunkasa tattalin arzikin manoma. A cewarsa, shirin mai fadin hekta 10 wanda aka samar da rijiyoyin burtsatse na zamani guda hudu do tallafa wa kananan manoma...
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka, sharhin bayan labarammu zai yi magana dangane da ‘Sayyid Haassan Nasarallah’ shahidin Al-umma’ wanda aka yi jana’izar sa a ranar lahadin da ta gabata. Wanda ni tahir amin zan karanta. A ranar lahadi 23 ga watan Fabrayrun shekara ta 2025 ne aka gudanar da Jana’izar babbsan sakataren kungiyar Hibullah, sayyid Hassan nasaralla, da kuma magajinsa na tsawon kwanaki 6 Sayyid Hashim safiyyuda deen, kafin haka shi ne shugaban majalisar zartarwa na kungiyar Hizbullah. An haifi sayyid Hassan nasaralla (r ) a ranar 31 ga watan Augustan shekara ta 1960 a wani kauye a kudancin kasar Lebanon, Sayyid ya tashi a cikin gida mai saukin rayuwa, ya fara karatu kamar yadda ko wani...
Kwamatin lura da kananan hukumomi na majalisar dokokin jihar Jigawa ya kaddamar da rangadi na yini biyu a karamar hukumar Jahun, domin tantance kwazon karamar hukumar ta fuskar gudanar da ayyukan raya kasa da sha’anin mulki da kashe kudade. Shugaban kwamatin kuma wakilin mazabar Gwiwa, Alhaji Aminu Zakari, ya ce ziyarar na daga cikin ayyukan majalisa da suka hada da duba kasafin kudi da yin doka da kuma tantance abubuwan da gwamnati ta ke gudanarwa kamar yadda tsarin mulki ya tanadar. Ya ce a lokacin wannan ziyara, kwamatin zai tantance kundin bayanan ayyukan raya kasa da rahoton zangon shekara da bayanan tarukan kwamatin tsaro da na gudanarwa. Ya ce kwanitin zai kuma tantance bayanan ayyukan majalisar kansiloli da kuma alkaluman...

Tashar Jiragen Sama Ta Rafikul Hariri Int. Na Birnin Beirut Yana Ciki Da Masu Shiga Kasar Saboda Jana’izar Shaheed Nasarallah
Tashar jiragen sama ta birnin Beirut tana cike da masu shiga kasar daga kasashen daban-daban don halattar jana’izar Shahidai kuma shuwagabannin kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasarallah da kuma Magajinsa Shahid Sayyid Hashimi Safiyyuddeen wanda za’a gudanar a ranar 23 ga watan Fabarairu da muke ciki. Kamfanin tafiye-tafiye na “Ajuz Travillin Agency’ ya fadawa tashar talabijin ta Almanar kan cewa tun yawan jiragen sama masu zuwa daga kasashen waje suka nin nink tafiye-tafiyensu zuwa Beiru, daga cikinsu, akwai Iraq Air wanda yake zuwa Beiru har sau biyu. Amma daga yau ya kara shi zuwa har sau ukku. Kamama Egypt Air ya ninka zuwasa Beirut har sai yu. Da kuma Tarksih Air shi ya ninninka ta fiyasa zuwa kasar. Labarin ya kara...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’el Baghae ya ce gwamnatin kasar Iran zata aika tawaga mai karfi zuwa kasar Lebanon don halattar Jana’izar Sayyid Hassan Nasarallah wanda za’a gudanar a cikin yan kwanaki masu zuwa. Bakha’I ya kara da cewa, zamu halarci Jana’izar a kasar Lebanon, kuma zamu aika da tawaka wacce zata kunshi manya-manyan jami’an gwamnati da kuma malaman addini. A ranar Talatan da ta gabata ce wani jami’an kungiyar ta Hizbullah, ya bada sanarwan cewa baki daga kasashe 79 ne zasu halarci jana’izar. Sheikh Ali Daher shugaba kwamitin gudnar da jana’izar ya kara da cewa, ranar zata kasashen ranar sabonta bai’a da marigayin da kuma wanda ya gaje shi. A ranar 27 ga watan Satumba shekara ta...
Babban jami’in jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin Cai Qi, ya yi kira a ranar Laraba, da a ci gaba da yin kokari wajen kawar da ayyukan da ba su da ma’ana, da rage nauyin da ke wuyan jami’an kananan matakai, don tabbatar kyakkyawan salon aiki tsakanin ’yan jam’iyya da jami’ai wajen cimma burin da aka sa a gaba a cikin shirin shekaru biyar-biyar karo na 14 wato daga shekarar 2021 zuwa ta 2025. Cai, wanda kuma mamban zaunannen kwamitin kula da harkokin siyasa na kwamitin kolin JKS ne, kuma mamba a sakatariyar kwamitin kolin JKS, ya bayyana hakan ne a wani taro na matakin koli game da wannan batu. Taron ya bayyana cewa, ya kamata a mayar da hankali wajen...
Tashar Talabijin din “ Almanar” ta sanar da cewa, da marecen yau Lahadi ne babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sheikh Na’im Kassim sai yi jawabi akan muhimman abubuwan da suke faruwa a Lebanon da kuma wannan yankin. Har ila yau, Almanar ta ce babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah Sheikh Na’im Kassim zai yi bayani akan lokacin da za a yi jana’izar Shahid Sayyid Hassan Nasrallah. Babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrallah ya yi shahada ne a sanadiyyar hare-haren masu muni da jiragen yakin HKI su ka kai wa unguwar Dhahiya dake birnin Beiruta. Majiyar ‘yan sahayoniya ta ce sun jefa bama-bamai da su ka nai nauyin tan 85 akan ginin da Shahid Sayyid Hassan Nasrallah yake ciki.
Gwamnan ya kara jaddada Gwamnatinsa ta maida hankalin ta ne kan irin ayyukan da za ta yi wa al’umma, inda ya yi kira kamata ya yi koda wane lokaci Shugabanni su rika tunawa da al’umman da suka zabe su, suna yi ma su aiki. Da yake kara yin bayani Gwamna Ododo ya ba kungiyar mataimakan Shugabannin Kananan Hukumomi kan kudurin sa na ci gaba da kammala duk bada wadansu mukamai na magoya bayan sa fda suke a Karkara. Ya yi kira da mambobin kungiyar da wadanda suka amfana da taimakon kungiyar,su ci gaba da aiwatar da abubuwan da suka sa a gaban su, saboda ayyukan alkahairin da suka fara zai samar da babbar gudunmawar ci gaba a wasu shekaru ma...
A na sa jawabin Ministan Bunkasa Hakar Ma’adanai Dakta Dele Alake, ya godewa Gallezot, kan yin aikin da ya yi dashi, wajen tabbatar da rattaba hannun wannan yarjejeniyar, duk da karancin lokacin da ake dashi na lokacin da yake da shi, a lokacin da Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya ziyarci Shugaban kasa Bola Tinubu. Adeleke ya yi nuni da cewa, sake sabunta wannan yarjejeniyar ta kawo karshen yunkurin ‘yan adawar siyasa na kasar nan, kan yunkurinsu na gayawa ‘yan Nijeriya bayanan karya kan manufar wannan yarjejeniyar. Ministan ya ci gaba da cewa, Kungiyar ta Makomar Ma’adanan Kasa, za ta bai wa kasashen biyu damar fahimtar yadda za a samar da tsare-tsare da dabaru da kuma ayyukan da ya kamata...