2025-04-26@04:54:28 GMT
إجمالي نتائج البحث: 212

«a shekarar 2024»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Wani katafaren wurin zubar da shara da aka tanada a wajen Kaduna ya koma wata babbar sana’ar kasuwanci inda ‘yan gwangwan ke amfani da gurbataccen ruwan najasa domin amfanin Noma.     Wata Kungiyar ‘yan jarida ta ziyarci al’ummar Katanga da ke karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna inda aka fara gudanar da wannan aiki inda suka gano cewa kimanin ‘yan gwangwan 150 ne suka tsunduma kansu domin karfafa tattalin arziki a wurin da ake jibge sharar.   Jama’a na yin tururuwa zuwa wurin zubar da sharar na Katanga wanda shi ne babban wurin da gwamnatin jihar ta amince da sharar don tabbatar da tsaftar muhalli.   Mallam Zubairu shi ne shugaba, ya shaidawa tawagar ‘yan jarida da sauran kungiyoyin...
    An gudanar da gwajin wasan kwaikwayo karo na biyar na shirye-shiryen bikin sabuwar shekarar Sinawa na CMG na 2025 jiya Lahadi. Ya zuwa yanzu, an kammala dukkanin ayyukan share fagen shirye-shiryen bikin sabuwar shekarar Sinawa na CMG na 2025. (Safiyah Ma)
    A yau Litinin ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da katin murnar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, a matsayin martani ga abokai a jihar Iowa ta kasar Amurka, inda ya ce, Sin da Amurka na da manyan muradun bai daya, da damar yin hadin gwiwa, kuma suna iya zama abokan hulda da aminai. Ya yi fatan jama’ar kasashen biyu za su kara cudanya da juna, da kara yin mu’amala da juna, da yin aiki tare wajen rubuta labarin abokantaka a tsakanin jama’ar kasashen biyu, da ba da sabbin gudummawa ga ci gaban dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka. (Mohammed Yahaya)  
    A yau Litinin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, kasar ta samu ci gaba mai inganci wajen zurfafa raya zamanantarwarta a cikin “yanayoyi masu sarkakiya da kalubale” a tsakanin watanni 12 da suka gabata. Ya furta hakan ne yayin gudanar da wata kasaitacciyar liyafar maraba da sabuwar shekara ta kasar Sin. Ana Shirin Kiranye Ga Ɗan Majalisar Da Ya Bar Kwankwasiyya Hisbah Ta Ceto Ƴanmata 16 Daga Hannun Masu Safarar Mutane A Kano Shugaba Xi wanda har ila yau shi ne babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin (CPC) kuma shugaban kwamitin tsakiya na sojojin kasar ya kara da cewa, “a cikin shekarar dabbar Dragon, mun nuna kuzari da ruhi mai karfi na iya aiwatarwa. Mun...
    “Dole ne iyaye su ɗauki nauyi kuma su kare ’ya’yansu. Yarda da fataucin su wani nau’in bauta ne na zamani wanda ke da mummunan sakamako,” in ji shi. ‘Yan matan da aka ceto yanzu haka suna hannun hukumar Hisbah, inda suke aiki da hukumomin da abin ya shafa domin tabbatar da tsaron lafiyarsu da kuma gyara su.
    Jagoran kungiyar Ansarullah ya bayyana cewa: A shirye suke su tunkari duk wani harin Amurka kuma ya gargadin sojojin haya Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyed Abdul-Malik Badruddeen al-Houthi ya tabbatar da cewa: Amurka ta yi amfani da dukkan karfinta wajen tallafawa haramtacciyar kasar Isra’ila da kuma kokarin murkushe al’ummar Falasdinu, yana mai jaddada tsayin daka da matsayarsa da ke tafiya a kan tubalin gaskiya, ikhlasi da ke gudana a tsakanin al’ummar Falastinu da ‘yan gwagwarmayarsu. Sayyid Abdul-Malik Badruddeen al-Houthi ya bayyana a yayin zagayowar ranar shahadar Sayyid Hussein Badruddeen al-Houthi, cewa: Abin da hukumomi suka yi a shekara ta 2004 kan shahidi wanda shi ne ya kafa tattakin Alkur’ani, kuma shugaba shahidi Hussein Adwan, ba a yi adalci...
    Ministan kiwon lafiya na kasar Lebanon ya bada sanarwan cewa sojojin HKI a kudancin kasar sun kashe fararen hula 15 sannan wasu 83 suka ji rauni a safiyar yau. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana cewa mutanen kudancin kasar Lebanon sun komawa gidajensu da suke kudancin kasar kan iyaka da kasar Falasdinu da aka mamaye ne, sai sojojin yahudawan, suka bude masu wuta suka kashe wannan adadin. A yau Lahadi ne 26 ga watan Jeneru ne, wa’adin ficewar sojojin HKI daga kasar Lebanon yake cika kamar yadda ya zo cikin yarjeniyar da suka sanyawa hannu da kasar Lebanon watanni biyu da suka gabata. Wannan bas hi ne kate hurumin yarjeniyar da aka sanyawa hannu da...
    An tabbatar da mutuwar aƙalla mutum 18 sakamakon hatsarin wata tankar mai da ta yi bindiga a Jihar Enugu. Alƙaluman da mahukunta suka fitar ya nuna cewa hatsarin ya rutsa da mutum 31 ciki har da mutum 10 da suka samu raunuka daban-daban yayin da aka ceto wasu uku da suka tsallake rijiya da baya sai kuma mutum 18 ɗin da suka ƙone ƙurmus. An yi taron Maulidin ƙasa duk da gargaɗin harin ’yan ta’adda a Kano An saki Falasɗinawa 200 da ke ɗaure a Isra’ila Hakan na ƙunshe cikin sanarwa da mai magana da yawun rundunar hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa reshen Jihar Enugu, Olusegun Ogungbemide ya fitar da yammacin ranar Asabar. Sanarwar ta bayyana cewa hatsarin wanda ya...
    Daga cikin yara ‘yan makaranta miliyan 242 da matsanancin yanayi ya raba da muhallansu a kasashe 85 a shekarar 2024, dalibai  miliyan 2 da dubu 200 ne a Najeriya suka rabu da muhallansu, lamarin da ya kawo cikas ga harkokin ilimi a shekarar. Rahoton wanda Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya fitar a daidai lokacin da duniya ke bikin ranar ilimi ta duniya ta shekarar 2025, ya nuna cewa a Najeriya baki daya dalibai miliyan 2,200,200 ne suka daina makaranta sakamakon ambaliyar ruwa. Da take gabatar da jawabi kan tasirin da sauyin yanayi ke da shi ga ilimin yara, shugaban ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahama Farah ya bayyana cewa, ambaliyar ruwa da ta...
    Hukumar Kula Da Taswira Ta Jihar Kebbi (KEBGIS), ta tsara wani gagarumin shiri na samar da kudaden shiga na sama da Naira biliyan daya a shekarar 2025.   Babban Manajan Hukumar, Bashiru Saidu Bakuwai, wanda ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a kan tabbatar da nadinsa a matsayin babban Manaja, ya ce hakan ya nuna kwazon hukumar a karkashin ma’aikatar filaye da gidaje na tallafa wa tattalin arzikin jihar.   Malam Saidu Bakuwai, ya ba da karin haske kan ayyukan hukumar da suka hada da alhakin duk wasu takardu da suka shafi filaye, tsarawa da bayar da takaddun kowane gida, sake tantancewa, daidaitawa, da kuma tsarin rajistar kadarorin.   Sauran su ne Gudanarwa da Rajista...
    Babban kwamandan sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Atisayen soji na “Manzon Allah Mai Girma na 19” ya cimma gagarumar nasara Babban kwamandan sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Admiral Ali Reza Tangsiri ya sanar da cewa: Atisayen soji mai take “Manzon Allah Mai Girma na 19” ya cimma gagarumar nasara da burin da ake son kai wa bayan samun nasarar gwada sabbin na’urori da gudanar da ayyuka daban-daban, tare da samun nasarar gwajin kai hari kan wuraren abokan gaba. A wata hira da ya yi da manema labarai a yau Lahadi, Admiral Tangsiri ya bayyana cewa: A rana ta biyu ta atisayen “Manzon Allah Mai Girma na 19”...