2025-04-01@17:08:54 GMT
إجمالي نتائج البحث: 15

«rika kwaikwayon»:

    Ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS), ta kammala gyara wata cibiya don kula da masu fama da shan miyagun ƙwayoyi a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano (AKTH) da ke Kano, tare da miƙa ta ga asibitin domin amfanin jama’a. Jami’in ECOWAS mai kula da shirin hana yawaitar shan miyagun ƙwayoyi, Dokta Daniel Akwasi Amankwaah, ya ce wannan cibiya na daga cikin ƙoƙarin ƙungiyar wajen rage yawaitar shan ƙwayoyi da kuma tabbatar da samun ingantacciyar kulawa ga masu buƙata. Tinubu zai sake zama shugaban ƙasa a 2027 — Akpabio ’Yan sanda sun ƙwato wa mutumin da aka sace kuɗin fansarsa a Kano A yayin bikin miƙa cibiyar, Dokta Amankwaah, ya jaddada aniyar ECOWAS na yaƙi da matsalar shan...
    Har ila yau, masu bincike sun gano wasu tsoffin dabarun hana koguna da madatsun ruwa ambaliya da yadda aka tsaga manyan hanyoyin ruwa da aka yi amfani da su shekaru 5,000 da suka gabata, a wani tsohon yanki na Zhejiang ta hanyar amfani da kayan binciken muhalli. Binciken ya fayyace wayewar kai na tsara birane da kula da koguna da hanyoyin ruwa irin na Liangzhu a tsohon zamani. Babu shakka, amfani da wayewar kan magabata a zamaninmu na yanzu yana daga cikin sirrin nasarorin da Sinawa ke samu ta fuskar wayewar kai da bunkasa ci gaban kimiyya da fasaha da kere-kere da kirkire-kirkire. Ina fatan kasashenmu na Afirka su dau hannu domin jifar tsuntsu biyu da dutse daya, tabbatar da...
    An yi kira ga gwamnati a dukkan matakai da su hada kai da sauran masu ruwa da tsaki a harkar rage karuwar amfani da magungunan ba bias ka’ida ba a tsakanin matasa.   Babban Daraktan Kula da Lafiya (CMD,) a Babban Asibitin Neuro-Psychiatric na Tarayya, Budo Egba, Jihar Kwara, Dokta Issa Awoye, ya yi wannan kiran ne a cikin jawabinsa mai taken, Sakamakon Neuropsychiatric na Maganganun Magani: Ra’ayin Clinical a taron masu ruwa da tsaki na Kwara na biyu kan Kariya da Sarrafa miyagun kwayoyi, wanda aka gudanar a Ilorin.   A cewarsa an samu karuwar noma da fataucin miyagun kwayoyi a kasar, musamman a tsakanin matasa.   Ya jera magungunan da aka saba amfani da su sun hada da...
    Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya nuna damuwarsa kan yadda sarautar gargajiya ke rasa martabarta a ƙasar nan. A cikin sabon littafinsa mai suna ‘Nigeria: Past and Future’, ya bayyana cewa yanzu akwai masu laifi, ’yan daba, da masu safarar miyagun ƙwayoyi da suka zama sarakuna a wasu yankuna na Najeriya. Afirka ta Kudu ta yi martani kan korar jakadanta daga Amurka Trump ya dakatar da kafar watsa labarai ta VOA “A yau, akwai ’yan daba, masu safarar miyagun ƙwayoyi, ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane da ake kira sarakuna,” in ji Obasanjo. “Wannan abu ne mai matuƙar ban takaici, kuma yana daga cikin matsalolin da ke addabar Najeriya.” Ya ce dole ne a dawo da mutunci da ƙimar sarautar...
    Fitaccen mai barkwancin nan wanda yake kwaiwayon maganganun tsohon Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, Obinna Simon wanda aka fi sani da ‘MC Tagwaye’ wanda yake mai nishaɗantarwa, ɗan kasuwa, kuma ɗan siyasa ya sauya sheƙa daga Jam’iyyar APC zuwa SDP. Ya sanar da hakan ne a cikin wani saƙon da ya wallafa a dandalin sada zumunta na zamani a ranar Juma’a, ya danganta sauya jam’iyyar ne bayan tuntuɓa da yin shawarwari. Wata mata ta faɗa ruwa ta mutu a Legas Direba ya murƙushe yarinya ta mutu a artabu da jami’an tsaro a Edo “Bayan tsawon watanni na tuntuɓar juna, ni Obinna Simon da aka fi sani da MC Tagwaye, na yanke shawarar ficewa daga Jam’iyyar APC na koma SDP.” “Wannan gagarumin...
    ’Yan sanda sun cafke wasu mutum uku bisa zargin lalatawa da kuma satar wayoyin lantarki a ƙauyen Bororo da ke Ƙaramar Hukumar Michika ta Jihar Adamawa. An cafke ababen zargin ne da wayoyin lantarkin yayin wani sintiri da jami’an ’yan sanda suka gudanar a ranar 9 ga wannan wata na Maris. Abin da ya sa na sauya sheƙa daga APC zuwa SDP — El-Rufai ’Yan bindiga sun yi garkuwa da matashi a Kano Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan, Suleiman Yahaya Nguroje, ya ce ababen zargin da ke hannu sun yi iƙirarin aikata laifin da ake zarginsu da shi. Sai dai ya ce za a ci gaba da gudanar da bincike gabanin ɗaukar matakin da ya ce nan gaba...
    Babbar Kotun Tarayya da ke Jihar Legas da ta Yola, da Jihar Adamawa, sun yanke wa wasu dillalan miyagun ƙwayoyi huɗu da aka kama da safarar ƙwayoyi da darajarsu ta kai Naira biliyan 4.6 hukuncin ɗaurin shekaru 95 s gidan yari. Ɗaya daga cikinsu, Ogbuji Christian Ifeanyi, jami’an hukumar NDLEA sun kama shi a filin jirgin saman Murtala Muhammad da ke Legas a bara, yana ƙoƙarin shigowa da hodar iblis ɗauri 817 mai nauyin kusan kilogram 20, wadda kuɗinta ya kai biliyan 46. Tinubu ya bai wa Farfesa Jega muƙami a gwamnatinsa PDP ta soki dakatar da Natasha, ta nemi a binciki Akpabio Sauran da aka kama sun haɗa da Iloduba Augustine Chinonye, Shuaibu Nuhu Isa (wanda aka fi sani...
    Kamar yadda ba a lokaci guda a ke gina dabi’u ba, haka nan ba zai yiwu a rusa su a lokaci guda ba. mutum na gina dabi’a ne ta hanyar yin mu’amala da mutane. Gina dabi’un na farawa daga shekarun yarinta, saboda a sannan ne a ke koyon al’adu, tarbiyya da girmama manya. Har zuwa mutuwan mutum ya na mu’amala ne da mutane ya na gina sabbin dabi’u. Iyaye su ne ke ginawa yara dabi’un farko, shi ne ma ya sa a ke so su rika kiyaye irin maganganun da za su rika yi a gaban yaransu, sannan su tsaftace mu’amalolinsu ta yadda yaran ba za su rika kwaikwayon abubuwan da ba su dace ba. hatta da yin dakuwa da...
    Shugaban Majalisar Wakilai, Tajuddeen Abbas, ya bayyana cewa mutum hudu a cikin kowane mata 10 a Jihar Kano sun fuskanci cin zarafi a gidajensu.  Tajuddeen Abbas ya bayyana cewa akalla kashi 35 na matan Najeriya sun fuskanci cin zarafi, lamarin da ya ce ya fi muni a yankin Arewa maso Yamma. Ya bayyana wa taron wayar da kai game da illar ta’ammali da miyagun kwayoyi da kuma cin zarafi a cikin gidaje cewa, “abin ya fi muni a yankin Arewa maso Yamma, inda a Jihar Kano matan da ake cin zarafinsu a cikin gidajensu sun kai kashi 40 cikin 100.” Game da yawa masu ta’mmali da miyagun kwayoyi kuwa, Shugaban Majalisar Wakilan, wanda dan yankin ne, ya bayyana cewa an...
    Kiyaye taruwar maiƙo da kwayoyin cuta a fuska da kirji. Wannan kan dan yi wahala amma ta wadannan dabaru za a samu nasara: 1- Rage maiƙo a cikin abinci. Misali, idan aka soya wani abinci, yana da kyau a tsane mai da mayanin kicin wafif ko tawul ko tushu mai tsabta kafin a ci. Idan an yi haka an rage man kusan da kashi hamsin cikin dari ko ma fiye. 2- Yin amfani da sabulu mai kashe kwayoyin cuta wajen wanke fuskar safe da yamma. 3- Shan kayan itatuwa da cin ganyayyaki a kai –a-kai ya kan tsane maikon cikin jini ya kara karfin garkuwar jiki wajen yakar kwayoyin cuta. 4- Ga wanda wadannan Dabaru ba su yi musu aiki...
    In an taba rarrauna a gabanka, kana da ikon kare masa, to ka kare masa, kin kare masa sakaci ne ba hakuri ba ne. An ruwaito cewa, Annabi (SAW) bai taba dukan wata daga cikin Matansa ba ko kuma cikin masu masa hidima a gida ko a waje. An kama wani Mutum da yake shirin kashe Annabi (SAW), aka gurfanar da shi gaban Annabi (SAW), sai jikinsa ya fara makyerkyata, Annabi (SAW) ya ce masa, kar ka firgita, ko da ka yi niyyar kashe ni, Allah ba zai dora ka a kaina ba. Zaidu dan Sa’anatal Yahudi ya zo wurin Annabi (SAW) kafin ya Musulunta yana neman Annabi (SAW) ya biya shi bashin da ya karba a wurinshi. Sai ya...
    “Sauran abubuwan baje kolin da aka kwato daga hannun mutanen biyu sun hada da: bindigogi guda uku da aka kera a cikin gida; bindiga guda da aka yi a gida guda biyu; bindigar zamani guda daya; bindigar gida guda daya; cartridges guda uku da 9mm mara komai da gatari mai kan karfe. “Wani farmakin da aka kai Legas, ya kai ga kama skunk mai nauyin kilogiram 47, wani nau’in tabar wiwi, da kuma Nitrous Odide mai nauyin kilogiram 25.46 da aka fi sani da dariya a unguwar Akala da ke Mushin,” Babafemi ya kara da cewa. A Jihar Ekiti, Babafemi ya ce jami’an NDLEA sun kama wani matashi dan shekara 26 mai suna Adepoju Taiwo, dauke da kilo 1.950 na...
    Hukumar yaƙi da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi (NDLEA) reshen Jihar Yobe ta ce ta kama wasu haramtattun ƙwayoyi da nauyinsu ya kai kilo 537 tare da kama wasu mutum 46 da ake zargi da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi a shekarar 2024. Kwamandan hukumar ta NDLEA a Jihar Yobe, Mista Abdulazeez Ogungboye ne ya bayyana hakan a Damaturu yayin da yake bitar ayyukan hukumar na shekara guda da ta gabata. Kiristoci sun yi addu’ar ɗorewar zaman lafiya a Kudancin Kaduna DAGA LARABA: Dalilan Da Mutane Suke Son Haihuwar Maza Fiye Da Mata Ya ce magungunan da aka kama sun haɗa da kilo 396.526 na tabar wiwi da kilo 141.2 na sauran kayayyakin maye. Ogunboye ya ce hukumar ta miƙa mutane 21...
    An gudanar da gwajin wasan kwaikwayo karo na biyar na shirye-shiryen bikin sabuwar shekarar Sinawa na CMG na 2025 jiya Lahadi. Ya zuwa yanzu, an kammala dukkanin ayyukan share fagen shirye-shiryen bikin sabuwar shekarar Sinawa na CMG na 2025. (Safiyah Ma)
    Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke Fagge ’Yan Alluna a Jihar Kano, ta yanke wa wani matashi hukuncin ɗaurin shekara biyu, a gidan yari bayan samun sa da laifin satar wayoyin salula. An gurfanar da Aliyu Rabi’u Rijiyar Lemo a gaban kotun, bayan kama shi a kan titin Ibrahim Taiwo tare da wasu biyu, inda suke amfani da Adaidaita Sahu wajen satar wayoyin hannun fasinjoji. ’Yan bindiga sun sace matashiya bayan karɓar kuɗin fansa a Kano ’Yan bindiga sun sace mutum 22 a ƙauyukan Kaduna A wajen da aka kama shi, wasu fusatattun mtsne sun ƙone Adaidata Sahun da suke amfani da shi wajen aikata laifin. An tuhume shi da haɗa baki don aikata laifi, sata, da tayar da hankalin...
۱