2025-03-22@08:01:21 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2343

«Harin bam»:

    Gwamnatin Jihar Yobe ta kafa cibiyoyin bayar da abinci 85 domin samar wa almajirai abinci a dukkanin Ƙananan Hukumomin 17 na jihar, a lokacin azumin Ramadan. Sakataren zartarwa na Hukumar Ilimin Larabci da Addinin Musulunci ta Jihar Yobe, Malam Umar Abubakar ne, ya bayyana hakan a wata hira da Daily Trust a ranar Alhamis. Sanƙarau...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya bayyana cewa, Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta mayar da martani ga wasikar shugaban Amurka Donald Trump a cikin kwanaki masu zuwa ta hanyoyin da suka dace. Araghchi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi kai tsaye a gidan talabijin na Jamhuriyar Musulunci ta Iran (IRIB)...
    Gwamnatin Isra’ila ta sanar da korar shugaban hukumar liken asiri ta cikin gidan kasar Ronen Bar, wanda Firaministan kassar Benjamin Netanyahu ya ce bai gamsu da kwarewarsa ba hasali ma ba’a yarda da shi.  “Gwamnati baki daya ta amince da shawarar Firaminista Benjamin Netanyahu na kawo karshen wa’adin” Ronen Bar, wanda zai bar ofis idan...
    Iran ta yi Allah wadai da Kwamitin Sulhun na MDD na rashin tabaka komai wajen  dakatar da ayyukan Amurka da Isra’ila wanda Iran din ta bayyana da abin kunya. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya yi tir da munanan hare-haren da jiragen yakin Amurka suka kai kan kasar Yemen da kuma yadda gwamnatin Isra’ila...
    Shugaba Kaïs Saïed na Tunisiya ya kori firaministan kasar Kamel Madouri,  da aka nada a watan Agustan da ya gabata yayin wani gagarumin garanbawul a majalisar ministocin kasar a daren jiya Alhamis. Wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar ta ce an maye gurbin firaministan kasar Madouri nan take inda aka maye gurbinsa da...
    Martanin da Fadar Shugaban Kasar ta mayar, ya biyo bayan nuna damuwa a kan matakin da Majalisar Dokokin Amurka ta dauka na amincewa da takunkumin da aka kakaba wa Nijeriya, bisa zargin kashe Kiristoci. Da yake goyan bayan wannan matsaya, Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Kasa (CAN) reshen Arewa, Rabaran Yakubu Pam ya bayyana a baya...
    Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya yi caccaki Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan ayyana dokar ta-baci a Jihar Ribas. Kwankwaso ya ce matakin da Tinubu ya ɗauka ya saɓa doka kuma barazana ne ga dimokuraɗiyya. Gobara ta ƙone gidaje tare da asarar dukiya a Gombe NAJERIYA A YAU: Illar Sare Itatuwa Ga...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tsawon lokaci, hukumomi a duniya suna gudanar da taruka don nemo hanyoyin daƙile ɗumamar yanayi kan irin illar da ke haifar wa rayuwar al’umma. Ɗumama ko sauyin yanayi yana barazana ga duniya, yana haifar da sauye-sauye da masana ke cewa zai iya tsananta idan ba a ɗauki matakin...
    Ramadan lokaci ne da ke hada kan iyalai da al’ummomi a fadin duniyar Musulmi. Lokaci ne da masoya ke haduwa tun daga lokacin sahur har zuwa buda-baki, ta hanyar kasancewa tare domin cin abinci mai gina jiki. A wannan lokacin, ba a yin abinci don nishadi kawai, lokaci ne na inganta rayuwa da bayar da...
    Wasu da ba a san ko su wanene ba sun yi awan gaba da kayayyakin wata mota ɗauke da kayan abinci na Hukumar abinci ta duniya (WFP) a garin Gubio, yayin da take kan hanyarta ta zuwa Damasak a Jihar Borno. Majiyar leƙen asiri ta shaidawa Zagazola Makama cewa, lamarin ya faru ne da misalin...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
        Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna ta roƙi Hukumar Kula da Sararin Samaniyar Najeriya (NAMA) ta ci gaba da ba da goyon baya domin tabbatar da nasarar gudanar da aikin Hajjin bana.   A ziyarar ayarin hukumar ƙarƙashin jagorancin Sakataren Gudanarwa, Malam Baba Mohammed Rufa’i, wanda ya wakilci Shugaban Hukumar, Malam Salihu...
    (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Tsohon mataimakin shugaban Nijeriya, Atiku Abubakar ya bayyana cewa yanzu haka ’yan adawar siyasa a ƙasar nan a shirye suke su ƙalubalanci shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027. Tun bayan da ya sha kaye a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, Atiku ya riƙa yin taro da ’yan adawa don neman karɓe...
    Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Mao Ning ta bayyana cewa, kakaba haraji da sauran shingayen kasuwanci ba za su amfani kowa ba, kuma suna matukar haifar da illa ga samar da wadatar tattalin arzikin duniya, da tafiyar da shi cikin kwanciyar hankali.  Jami’ar wacce ta bayyana haka a yau Alhamis yayin...
    Wannan hazaka, da hangen nesa na kasar Sin, sun ci gaba da zama ginshiki na ingiza jagorancin dukkanin manufofin kare hakkin bil Adama a duniya, kana hakan zai ci gaba da zama muhimmiyar gudummawar kasar Sin ga duniya, a bangaren kare hakkin rayuwa da walwalar daukacin al’ummar duniya.(Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare....
    “Wannan mataki na dokar ta-ɓaci wata dama ce ta kare rayuwar al’umma, tabbatar da tsaron muhimman kadarori, da dawo da tsarin mulkin dimokuraɗiyya,” in ji Tinubu. Shugaba Tinubu ya buƙaci dukkanin ɓangarori su mara baya ga ƙoƙarin dawo da zaman lafiya a Jihar Ribas tare da jaddada ƙudirin gwamnatinsa na bunƙasa tattalin arziƙi da haɗin...
    Wata gobara mai muni ta laƙume gidaje uku a unguwar New GRA, a birinn jihar Gombe, a ranar Laraba inda ta bar iyalai cikin rashin matsuguni tare da asarar dukiya ta miliyoyin Naira. Waɗanda abin ya shafa sun koka kan rashin damar ceto komai daga kayan su, kuma yanzu haka suna neman tallafin gaggawa domin...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira ga lardin Yunnan dake kudu maso yammacin kasar Sin, da ya mayar da hankali kan karfafa samar da ci gaba mai inganci, da warware tarnakin tafakkuri, da aiwatar da gyare-gyare da kirkire-kirkire, da kokarin ci gaba da azama, da daukar matakai masu inganci, da kuma kafa sabon...
    Masu yi wa ƙasa hidima (NYSC), za su fara jin daɗin sabon alawus ɗin gwamnatin tarayya na N77,000.00 wanda aka sake duba shi da za a fara biya daga watan Maris, 2025. Babban Darakta Janar (DG) na NYSC, Birgediya Janar Olakunle Oluseye Nafiu ne ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga masu...
    Tun lokacin da Donald Trump ya hau mukaminsa na shugaban kasar Amurka a watan Janairu na bana, sau da dama gwamnatinsa ta dauki matakan kakaba harajin kwastan kan abokan cinikinta. A ganinsa, matakan za su tilasta kamfanoni da su maido da tsarin samar da kayayyaki zuwa Amurka, matakin da zai gaggauta bunkasuwar masana’antun kasar. Ko...
    A shekarar 2004, lokacin da Olusegun Obasanjo ya ayyana dokar ta-ɓaci a Filato, matakin ya fuskanci suka daga jama’a da ɓangaren shari’a. Masana doka da ‘yan siyasa sun yi Allah-wadai da matakin da Tinubu ya ɗauka, inda Dokta Reuben Abati ya bayyana shi a matsayin “laifi da za a iya tuhumar Tinubu a kai”. Ya...
    Mece ce Dokar Ta-ɓaci? Dokar ta-ɓaci tana bai wa shugaban ƙasa damar ɗaukar matakan gaggawa a wani yanki na ƙasa idan ana fuskantar barazanar tsaro ko zaman lafiya. Sai dai kundin tsarin mulkin Nijeriya ya tanadi cewa dole ne a bi tsari na doka kafin a aiwatar da hakan. Mece Ce Ma’anar Wannan Mataki A...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya taya al’ummar Iran murnar zagayowar lokacin bukukuwan Nowruz na sabuwar shekarar hijira shamsiyya da ake amfani da itya a hukumance a kasar Iran. Ayatullah Khamenei ya bayyana hakan ne a wani sako da ya aikewa al’ummar kasar ta gidan telebijin na murnar shiga sabuwar shekara...
    Kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta duniya ta fitar da wata sanarwa inda ta yi Allah wadai da sake dawo da hare-haren wuce gona da irin da Isra’ila ke yi a zirin Gaza tare da yin kira da a dauki matakin gaggawa na kasashen duniya domin dakile wadannan laifuka. Kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta...
    Dakarun Falasdinawa sun mayar da martani ga kisan kiyashin da Isra’ila ke yi wa fararen hula bayan sake dawo da yakin Isra’ila a kan al’ummar Gaza, inda suka harba rokoki zuwa Tel Aviv. Al-Qassam Brigades, reshen soji na kungiyar gwagwarmayar Islama ta Hamas, ta sanar a wannan  Alhamis cewa, ta yi ruwan makamai masu linzami...
    ’Yan Najeriya na iya fuskantar karin farashin man fetur bayan da Matatar Man Dangote ta bayyana cewa ta daina sayar wa ’yan kasuwa man fetur a kudin Naira. Matatar, wacce ke siyan danyen mai da Naira bisa yarjejeniyar gwamnati, yanzu ta koma sayan danyen mai da dalar Amurka. An kirkiro yarjejeniyar siyan danyen mai da...
    Sabon Gwamnan riƙon ƙwarya na Jihar Ribas, Vice Admiral Ibok-ete Ibas (mai ritaya), ya isa jihar domin ci gaba da aiki. Ibas ya isa filin jirgin saman Fatakwal da misalin ƙarfe 11:25 na safiyar ranar Alhamis inda ya samu tarba daga manyan jami’ai da jami’an tsaro. ’Yan Boko Haram 7 sun miƙa wuya ga sojojin...
    Rundunar ‘yansandan babban birnin tarayya Abuja ta tabbatar da mutuwar mutane shida a fashewar tankar man fetur da ya afku a yankin Karu da ke Abuja a daren Laraba. Rundunar ta kuma ce motoci 14 ne suka kone a mummunan hatsarin. Jami’an Tsaro Sun Ceto Mutane 84, Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 3 A Katsina Cikar...
    Majalisar Wakilai ta amince da ayyana dokar ta-ɓaci da Shugaba Bola Tinubu ya yi a Jihar Ribas. Majalisar ta yanke wannan shawara ne a ranar Alhamis, ta hanyar kaɗa ƙuri’a da baki, inda ’yan majalisa 243 suka halarta. Muhimman ayyuka 8 a goman ƙarshe na Ramadan Fashewar Tanka: Asibitoci sun cika da mutane a Abuja...
    A yayin da aka shiga kwana goman ƙarshe a watan Ramadan, ga tunarwar wasu muhimman ayyukan lada da ya kamata a dage da su a cikin watan mai alfarma. Fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya bayyana cewa riƙo da su yana da muhimmanci saboda tarin lada da aka tanadar wa mai aikata su:...
    A yayin da aka shiga kwana goman ƙarshe a watan Ramadan, ga tunarwar wasu muhimman ayyukan lada da ya kamata a dage da su a cikin watan mai alfarma. Fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya bayyana cewa riƙo da su yana da muhimmanci saboda tarin lada da aka tanadar wa mai aikata su:...
    Darakta mai kula da al-amuran mata da kuma kare hakkin bil’adama a ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, Forouzandeh Vadiati, ta hadu da jakadan kasar Jamus a nan Tehran da kuma mataimakin jakadan kasar Burtania a Tehrana a ma’aikara. Inda ta bayyana masu bacin ranta da yadda kasashen biyu suka shigar da wata daftari ta tuhumar...
    Yan tawayen M-23 na kasar Kongo wadanda suke samun goyon bayan gwamnatin kasar Ruwanda sun kara nosawa zuwa gaba a mamayar da sukewa gabancin kasar ta Kongo. Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa yan tawayen sun kama garin Walikale a jiya Laraba kuma a halin yanzun sun kokarin zuwa sauran garuruwa a yankin. Labarin...
    Rahotannin da suke fitowa daga yankin Gaza na kasar Falasdinu da aka mamaye sun nuna cewa, a cikin sa’o’ii 24 da suka gabata Falasdinawa 71 ne suka yi shahada a yayinda wasu da dama suka ji rauni. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa a wannan karon jiragen yakin HKI da...
    Sojojin kasar Yeman sun bada sanarwan cilla makamai masu linzami kan tashar jiragen sama ta Bengerion a birnin Tel’aviv na HKI a daren jiya laraba don tallafawa falasdinawa a gaza wadanda sojojin HKI suke kashewa bayan yi masu kofar rago ta shigo da abinci da abinsha cikin yankin na kimani wata guda. Tashar talabijin...
    Mutane fiye da 30 ne aka tabbatar damutuwarsu a  jiya Laraba a Abubja babban birnin tarayyar Najeriya sanadiyyar bindigan da wata motar daukar iskar gas ta yi a kan gadar Karo da misalign karfe 7:15 a jiya Laraba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa hatsarin na jiya ya aukune a dai...
    A cewar Kwamishinan, sojojin sun yi artabu da ‘yan ta’adda a kauyukan Malori da Matalawa, inda suka kara tura su cikin tsaunukan.   Mua’zu ya ci gaba da bayanin cewa, yayin da jami’an tsaron suka isa sansanin Sanusi Dutsin-Ma, sun yi nasarar tarwatsa jama’arsa tare da kashe ‘yan ta’adda uku, yayin da wasu da dama...
      Ƙungiyar bada agaji ta Civil defence a zirin Gaza ta ce hare-hare ta sama da Isra’ila ta kai cikin dare sun yi sanadin mutuwar mutum aƙalla 50 ciki harda yara ƙanana.   Hamas wadda zirin Gaza ke ƙarƙashin ikonta ta ce ta yi alla wadai da farmaki ta kasa na sojoji Isra’ila kuma ta...
    Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya umarci daukacin masarautun Jihar hudu da su fara shirye-shiryen Bikin Sallah Daba domin ganin jama’a da maziyarta sun ji dadin bukukuwan Sallah.   Wannan umarni na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, bayan wani taron...
    Aƙalla mutum 55 ne suka rasu sakamakon ɓarkewar cutar sanƙarau a ƙananan hukumomin Jega, Gwandu, Aliero, Bunza, da Birnin Kebbi da ke Jihar Kebbi. Hukumar Lafiya ta Jihar ta tabbatar da ɓullar cutar bayan gwaje-gwajen da aka yi a Abuja. Ƙungiyoyin ƙwadago sun buƙaci Tinubu ya mayar da Fubara kan kujerarsa Shugaban Dattawan Arewa ya...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi rangadi a birnin Lijiang na lardin Yunnan dake kudu maso yammacin kasar Sin da yammacin jiya, inda ya ziyarci lumbunan samar da furanni masu aiki da sabbin fasahohi na zamani da tsohon garin Lijiang, don fahimtar yadda ake raya aikin gona na musamman mai la’akari da yanayin wurin,...
    Sabon kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Bakori, ya sha alwashin yin aiki da gaskiya domin inganta tsaron rayuka da dukiyoyi.   CP Bakori ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a hedikwatar hukumar dake Bompai Kano.   CP Bakori, wanda kwanan nan ya karbi mukamin kwamishinan ‘yan sanda...
    Dakarun Sashe na 2 tare da hadin gwiwar sojojin sama na rundunar hadin gwiwa ta Operation Fansan Yamma sun ceto mutane 101 da aka yi garkuwa da su a fadin Kankara a jihar Katsina da Shinkafi a jihar Zamfara a ranakun 17 da 18 ga watan Maris 2025.   A cewar sanarwar mai Magana da...
    Wata gobara da ta tashi da sanyin safiya ta kone wani shago a wani gini mai daki 13 da ke rukunin gidajen Ile-Lodo a cikin garin Etan a karamar hukumar Ekiti a jihar Kwara.   A cikin wata sanarwa da kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, Hassan Adekunle ya fitar, ya ce bayan an...
    An dakile fashewar wata babbar tankar mai a Sokoto bayan da jami’an tsaro da jami’an kwana-kwana da masu bayar da agajin gaggawa suka yi gaggawar kai dauki bayan da tankar ta kife a hanyar Gagi-Nakasari a karamar hukumar Sokoto ta Kudu.   Wani shaidan gani da ido, Magaji Shanono ya shaidawa gidan rediyon Najeriya cewa...
    Gwamnatin jihar Kebbi, ta tabbatar da mutuwar mutane 56 a sakamakon barkewar cutar sankarau a jihar inda 25 a Gwandu, 16 a Jega, 14 kuma suka mutu a kananan hukumomin Aliero na jihar.   Da yake zantawa da manema labarai, babban sakatare a ma’aikatar lafiya ta jihar, Dakta Nuhu Koko, ya ce an samu jimillar...
    Jakadan Amurka a Najeriya, Richard Mills Jr, ya ziyarci mai martaba Sarkin Zazzau Malam Ahmad Bamalli domin ingantawa da karfafa hadin kan al’adu.   Jekadan ya ce Amurka ta jajirce sosai kan alakar da Najeriya ya kara da cewa; ‘ muna so mu zurfafa shi kuma mu ƙarfafa shi.”   A cewarsa, hanyar da ta...
    Ya kuma nuna jin daɗinsa da irin nasarorin da aka samu a ƙarƙashin jagorancin Kwamared Alhassan Yahayan, inda ya ce an ɗora ƙungiyar kan kyakkyawan turbar da ya kamata don ta ci gaba da taka rawar gani wajen bunƙasa aikin jarida a Nijeriya.   Yahaya ya jaddada cewa akwai kyakkyawar dangantaka tsakanin gwamnatin Jihar Gombe...
    Sojojin Amurka sun kai sabbin hare–hare kan kasar Yemen a safiyar yau Alhamis inda suka lalata gine-gine a garuriwa Al-Hudaida da kuma  Sa’ada. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban kasar Amurka Donal Trump kafin haka ya na fadar cewa, sai ya shafe kungiyar Ansarullah wacce take iko da kasar Yemen daga...