2025-04-13@08:46:08 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2700

«Ruwan Sama»:

      Kazalika, mahalarta taron sun jaddada muhimmancin inganta samar da ayyukan yi, da karfafa tattalin arziki, da kyautata zaman rayuwar ’yan Najeriya, ta hanyar kulla huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare da kasar Sin. (Mohammed Yahaya) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura...
    Tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriya kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a 2023, Alhaji Atiku Abubakar ya ziyarci tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari a Kaduna. Atiku ya samu rakiyar tsofaffin gwamnoni da suka haɗa da tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai da tsohon Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal da wasu jiga-jigan ’yan siyasa. An gano gawar makiyayi...
    Kudin biyan bashin cikin gida na shekarar 2024 ya kai naira tiriliyan 5.97, wanda hakan ke nuna karin kashi 14.15 cikin 100 daga naira tiriliyan 5.23 da aka samu a shekarar 2023. Karuwar ana danganta shi da karuwar kudin ruwa da karin lamuni na cikin gida. Nijeriya dai ta kashe dala biliyan 4.66 (kwatankwacin naira...
    Dakarun rundunar ‘Operation Safe Haven’ da ke aikin tabbatar da zaman lafiya a Jihar Filato, sun nemo gawar wani makiyayi mai shekaru 16 da ya ɓace tare da ƙwato shanu sama da 50 da aka sace.  Daily Trust ta rawaito cewa, sojojin sun gano gawar makiyayin da ya ɓace tare da wasu Fulani makiyaya a...
    Tun daga farkon bana zuwa yanzu, sau da dama kasar Sin ta mai da martani kan matakai na rashin adalci da kasar Amurka ta dauka, domin tana da karfin fuskantar da kalubaloli tare da kiyaye bunkasuwar tattalin arzikin kasar yadda ya kamata, sakamakon bunkasuwar manyan kasuwannin cikin kasa, da manufofin da gwamnatin kasar ta fidda...
    Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta sanar da cewa, bisa gayyatarsa da sakatare janar na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Vietnam kuma shugaban jamhuriyar gurguzu ta Vietnam ya yi, shugaban kasar Sin Xi Jinping, zai kai ziyarar aiki kasar daga ranar 14 zuwa 15 ga wata.   Haka kuma, bisa gayyatarsa da firaministan...
    Masu shigar da kara sun bukaci kotun da ta hana wadannan jami’an gudanarwa gudanar da taro, ko kuma jagorantar babban taron jam’iyyar na kasa, bisa hujjar cewa an kore su daga jam’iyyar NNPP. Ko da yake, alkali mai shari’a Justice MA Hassan ya yanke hukuncin cewa kotun ba ta da hurumin sauraren karar, inda ya...
    Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya yi wata muhimmiyar ganawar sirri da shugabannin sojojin Nijeriya a Abuja ranar Alhamis. Taron wanda ya gudana daban-daban tare da babban hafsan sojin ƙasa, Laftanar Janar Olufemi Olatubosun Oluyede da babban hafsan sojin ruwa, Vice Admiral Emmanuel Ikechukwu Ogalla da babban hafsan sojin sama, Air Marshal Hasan Bala...
    ’Yan bindigan da suka sace Fasto Samson Ndah Ali na cocin ECWA da ke Mararaba Aboro a Ƙaramar Hukumar Sanga ta Jihar Kaduna, sun sake shi sannan sun tsare wanda ya kai kuɗin fansar, Yusuf Shehu Ambi, wanda shi ne sakataren cocin. Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Aminiya...
    Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku ya kasance mai fafutukar tabbatar da hadin kan ‘yan adawa, yana mai jaddada muhimmancin hadin gwiwa wajen kayar da Tinubu a zaben 2027. A ranar 8 ga watan Maris ne ya bayyana kokarinsa na hada kan ‘yan adawa da kafa kawancen korar jam’iyyar APC. Bayan sauya shekar El-Rufa’i daga jam’iyyar...
    Wannan ya hada da darajar kayayyakin da ake shigowa da su daga waje da kuma fitar da su, wanda ke nuni da irin dimbin alakar kasuwanci da ke tsakanin kasashen biyu. Kayayyakin da Nijeriya ke fitarwa a cikin gida da na waje da jirgin ruwa ya kai dala miliyan 473.6 a watan Fabrairun 2025, kadan...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ba kamar kayayyakin manyan kamfanoni irin su Ajinomoto, Bedan wadanda aka zuba su a cikin kwali, ana sayar da su cikin lafiyayyen mazubi kuma NAFDAC ta amince da su ba, wadannan danyun kaya ne da ba su da wata alama. Babban abin ban tsoro shi ne ba za a iya gano masana’antunsu don bincikar sahihancinsu...
    ’Yan bindiga sun kai hari garin Mahuta da ke Ƙaramar Hukumar Kafur a Jihar Katsina, inda suka harbi wani alkali, Rabiu Mahuta, a hannu da kuma dansa. A lokacin harin na daren Talata, maharan sun raunata mutane uku tare da yin garkuwa da wasu mutane 13, ciki har da matar alƙalin da kuma biyar daga...
    Hukumar ilimin bai daya ta kasa wato UBEC ta yabawa Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa bisa jajircewar sa wajen inganta ilimi a matakin farko a Jihar. Shugabar Hukumar, Hajiya Aisha Garba, ta bayyana hakan a yayin ziyarar gwamnan zuwa hedikwatar UBEC a Abuja. Hajiya Aisha Garba ta bayyana jihar Jigawa a matsayin abin...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmaeil Baqaei ya bayyana cewa, ma’a, kwana guda gabanin tattaunawar da ake jira a kasar Oman tsakanin Amurka da Iran kan shirin nukiliyar kasar Iran, damammaki da daman a diflomasiyya da Amurka za ta iya tabbatar da aniyarta a kansu Baqaei ya rubuta a dandalin  X, “Ya kamata Amurka...
    Wata kungiya mai zaman kanta da ke dauke da sunan Kauru Emirate Consultative Initiative (KECI) ta nisanta da yunkurin da wasu ke yi na saka Masarautar Kauru cikin sabon tsarin Jihar Gurara da ake kokarin kirkira daga Jihar Kaduna. Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Shugaban kungiyar, Malam Isah Mukhtar, ya sanya...
    Jami’an Kongo da masu shiga tsakani na M23 sun isa Qatar domin tattaunawa don cimma yarjejeniyar tsagaita wuta. Jami’an Kongo da masu shiga tsakani na kungiyar M23 sun isa Doha babban birnin kasar Qatar domin tattaunawa da nufin cimma tsagaita bude wuta da kuma kawo karshen fadan da aka shafe watanni ana gwabzawa a yankin,...
    Namibiya ta janye bayar da biza ga Amurka, Burtaniya, da wasu kasashe sama da 30. Matakin, wanda majalisar ministocin Namibiya ta yanke tun a watan Yuli, ya fara aiki ne a ranar 1 ga Afrilu. Ya zuwa yanzu, galibin kasashen Turai, ciki har da Jamus, babbar tushen yawon bude ido a Namibiya, sun ci gajiyar...
    Wakilin kungiyar Hizbullah a majalisar dokokin kasar Labanon ya yi kira ga gwamnatin kasar da ta ba da fifiko wajen dakatar da hare-haren wuce gona da iri da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi wa kasar Labanon. A cewar Al-Mayadeen Hassan Fadlallah mamba a bangaren Hizbullah a majalisar dokokin kasar Labanon ya ce: Dakatar da...
    A ƙalla shaguna 12 sun ƙone ƙurmus sakamakon gobarar da ta tashi da daddare a Agodi Gate, birnin Ibadan, babban birnin Jihar Oyo. Lamarin ya faru ne a daren Alhamis a ginin Block A  na kasuwar Siminti ta Mayegun, Araromi, kamar yadda hukumar kashe gobara ta Jihar Oyo ta tabbatar. Shugaban hukumar, Akinyemi Akinyinka,...
    Wani jirgi mai saukar ungulu ya faɗa cikin kogin Hudson da ke birnin New York a Amurka.   Kafafen yaɗa labaran ƙasar sun bayyana cewa mutum shida da ke cikin jirgin – fasinja biyar da direban jirgi guda sun mutu.   Magajin garin New York Eric Adams ya ce jirgin na ɗauke da wani iyali...
      -Mun lura da ilimomin harkokin zamaninmu a cikin Alkur’ani Cikin godiyar Allah, muna mika ziyara ga Shehu Isma’ila Umar Almadda (Mai Diwani) da kuma ban gajiya da gabatar da Tafsirin Alkur’ani mai girma na Azumin Ramadan na bana. Allah ya kai mu na badi albarkar Annabi (SAW) da Shehu (RTA). Ya Shehi, a Tafsirinka...
    Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da dokar albashi na naira 70,000 a ranar 29 ga watan Yuli na 2024, bayan shafe watanni ana muhawara da kungiyoyin kwadago. Sabon mafi karancin albashin na wata-wata ya karu da kaso 133 daga naira 30,000 zuwa naira 70,000, sakamakon matsin tattalin arziki da ake fama da shi a...
    Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana gamsuwarta da yadda ake ci gaba da gudanar da ayyukan gina tituna da gyare-gyare a fadin jihar.   Kwamishinan ayyuka da samar da ababen more rayuwa na jihar Alhaji Lawal Barau Bungudu ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Gusau babban birnin jihar.  ...
    Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara, ta ce an shirya shirye-shirye domin karfafa tsaro a jihar da kuma tabbatar da mazauna yankin suna rayuwa cikin yanayi na zaman lafiya da tsaro.   Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Adekimi Ojo ne ya bayyana haka da yake zantawa da manema labarai a hedikwatar ‘yan sanda da ke Ilorin.  ...
    Sama da gidaje dari biyu da arba’in ne aka lalata a daren Talatar da ta gabata, ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka shafe sa’o’i ana yi a unguwar Garin Kestu Atuwo dake karamar hukumar Shanga ta jihar Kebbi.   Da yake jajantawa wadanda abin ya shafa, Gwamna Nasir Idris ya shawarci gidajen da...
    Sanata Oluremi Tinubu yt gana da sarakunan Taraba, ta kuma ba da gudummawar naira miliyan 50 don tallafa wa mata 1,000, da kayan aiki dubu 10,000 ga ma’aikatan lafiya   Uwargidan shugaban Najeriya, Sanata Oluremi Bola Ahmed Tinubu, ta bukaci shugabannin gargajiya da su marawa shirin ta na sabon fata ta hanyar wayar da kan...
    Mataimakin shugaban kasar wanda ya samu wakilcin Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Na Musamman Kan Ayyuka Na Ofishin Mataimakin Shugaban Kasa, Aliyu Modibbo Umar ya ce, “Kalubalan Nijeriya ya ta’allaka a tsarin tarayyarmu,” in ji Shettima. “Ba batu ne na wai nawa ne kowace rukunin tarayya ke samu ba, magana ce ta yadda ake amfani...
      Amfanuwa Da Mamakon Arziki Da A Ka Yi Mana Baiwarsu Babu shakka, mutuwar zuciya ce ta mai da jama’ar wannan Kasa tamu ta Nijeriya dogara kacokan da sabgar man fetur, a matsayin wata hanya daya tilo da za ta rika samar mana da sama da kashi tamanin ga tattalin arzikinmu na Kasa!. Hakika akwai...
    An gurfanar da wani mutum a gaban Kotun Majistare ta 17 a Kano bisa zargin shi da karɓar kuɗi a hannun wasu fursunoni da alƙawarin cewa zai fitar da su daga gidan yari. Ana zargin wanda ake tuhumar, Kabiru Ahmed, da karɓar jimillar kuɗi naira dubu dari shida da goma daga Abdul Mukhtar, Bilkisu Shehu...
    Rahotanni daga kasar Yemen sun ambaci cewa jiragen yakin Amurka sun kai jerin hare-hare a yankuna mabanbanta na kasar Yemen da su ka hada da birnin San’aa. Tashar talabijin din al-masirah ta ambaci cewa; jiragen yakin Amurka sun kai hare-haran ne har sau 7, biyu a cikin yankin Hamadan, da Banu Hashish sai kuma babban...
    Fira ministan HKI Benjamine Netanyahu ya yi suka cikin fushi saboda Fira ministan kasar Mark Carney  Canada ya bayyana cewa abinda yake faruwa a Falasdinu kisan kiyashi ne. Shi dai Fira ministan kasar Canada Mark Carney wanda ya halarci taron yankin neman zabe a garin Calgary, yayin da wani daga cikin mahalarta, ya daga murya...
    Hukumar Kula Wutar Lantarki ta Ƙasa (NERC) ta ci kamfanonin rarraba lantarki tarar naira miliyan 628 kan laifin karɓar kuɗin wuta fiye da kima daga hannun kwastomomi marasa mita. Hukumar ta kuma ba wa kamfanonin rarraba lantarkin da hakan ta shafa wa’adin ranar 15 ga watan Mayu, 2025, sun tabbatar sun biya kwastomomin da suka...
    Mahukunta a kasar Syria sun kafa dokar hana zirga-zirga a yankin Dar’a dake kudancin kasar Syria. Tashar talabijin din ‘almayadin’ ta ambato cewa; jami’an tsaron kasar ta Syria sun kafa dokar ta baci a yankin “Basra-sham’ dake yankin Dar’a. Sai dai har yanzu babu wani cikakken bayani akan dalilin da ya sa aka kafa wannan...
    Sojojin HKI suna ci gaba da yin kiyashi a sassa mabanbata na Gaza, da a bayan nan su ka yi wa mutane 30 kisan kiyashi a unguwar Shuja’iyya dake birnin Gaza.  Majiyar asibitin Falasdinawa ta ambaci cewa; Harin da sojojin HKI su ka kai da manyan bindigogi sun yi sanadiyyar shahadar mutane 17 a unguwar...
    Kasar Sudan ta kai kukan HDL a gaban kotun MDD cewa ta keta dokar hana kisan kiyashi ta hanyar taimakawa dakarun kai daukin gaggawa. A jiya Alhamis kasar ta Sudan din ta bukaci kotun ta kasa da kasa dake karkashin MDD da  ta ta fitar da hukunci na gaggawa na bayar da umarni ga HDL...
    Kazalika, a wani binciken kwanan baya na gama gari kan yawan alummar kasar, ya gano cewa, kaso 53 na wasu matasan kasar, a kullum suna rungumar wannan dabi’ar. Sai dai, muna sane da cewa, wasu ‘yan Nijeriya, na kallon yin cacar tamkar wata aba ce, ta nishadi kawai, amma wasu bincike sun bayyana cewa, wani...
    Ana fargabar matafiya da dama sun rasu bayan kifewar wani  kwalekwale ɗauke da ’yan kasuwa a yankin Kogin Neja. Hatsarin kwalekwalen ya auku ne ƙauyen Sokun da ke yankin Ƙaramar Hukumar Lapai, a sakamakon iska mai ƙarfi da ta haddasa juyawar igiyar ruwan. Shaidu sun ce hatsarin ya auku ne a yayin da kwalekwalen ke...
    Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta yi hasashen za a yi ruwan sama mai ƙarfi da ambaliya a jihohi 30 da kuma babban birnin tarayya Abuja. Jihohin da ake fargabar fama da ambaliyar ruwan sun haɗa da: Abia, Adamawa, Akwa Ibom, Anambra, Bauchi, Bayelsa, Benue, Borno, Cross-Riɓer, Delta, Ebonyi, Edo, Gombe, Imo, Jigawa, Kebbi, Kogi, Kwara, Lagos,...
      Daga nan sai ya ce, kasar Sin na aiwatar da matakan ramuwar gayya na wajibi game da cin zalin Amurka, ba kawai don kare ikon mulkin kanta, da kare tsaro da muradun ci gabanta ba ne, har ma da tabbatar da gaskiya da adalci tsakanin sassan kasa da kasa, da wanzar da tsarin cinikayyar...
    Gwamnatin Yobe ta bayyana shirinta na mayar da tubabbun mayaƙan Boko Haram cikin al’ummarsu da aka yi wa shirin kawar da tsattsauran ra’ayi, gyara da sake haɗewa da iyalansu ƙarƙashin rundunar Operation Safe Corridor (OPSC). Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ne ya bayyana haka a ranar Alhamis a Damaturu lokacin da ya karɓi baƙuncin...
    Wani muhimmin abun lura ma shi ne ita kanta Amurka ba za ta tsira daga mummunan tasirin wannan yaki na cinikayya da take rura wutarsa ba. Ko shakka babu matakin zai haifarwa Amurka matukar koma bayan tattalin arziki, da hauhawar farashi a cikin gida, da dakile guraben ayyukan yi da sauransu. Tuni ma kasuwannin Amurkan...
    Ƙungiyar Ƙwadago a Jihar Sakkwato (NLC), ta musanta iƙirarin da shugaban ƙungiyar ma’aikatan ƙananan hukumomi ta ƙasa (NULGE), Ali Kankara, ya yi cewa gwamnatin jihar ba ta fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi na Naira 70,000 ba. Shugaban NLC na jihar, Kwamared Aliyu Abdullahi, ya bayyana wa manema labarai a ranar Laraba cewa Gwamnatin Sakkwato...
    Sojojin kasa na kasashen Iran ta Armenia sun fara atisayen soje na hadin guiwa a tsakaninsu, don kyautata tsaro na kan iyakar kasashen biyu na kuma tsawon kwanaki biyu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa dakarun kare juyin juya halin musulunci na kasar Iran ne suke jagorantar wannan atisayen. Da nufin...
    Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bada sanarwan cewa yana kokarin cimma matsaya da kasar Chaina dangane da kamfanin sadarwa da kuma yanar gizo na TIK Tok. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto shugaban yana fadar haka a shafinsa na ‘Trump Social, Labarin ya kara da cewa shugaban yana fadar haka a...
    Sojojin HKI wadanda suka yi ritaya da kuma masu jiran aiki ko Reserv sun watsa wata bukata da suka rubuta ta kawo karshen yakin da Benyamin Natanyahu yake jagoranta a Gaza. Sojojin sun kara da cewa a halin yanzu yakin yana cimma manufar Natanyahu ne kawai, ba don manufar HKI ake yins a ba. Kamfanin...
    Kasashen China da Tarayyar Turai sun maida martani kan kudaden fiton da Amurka ta kara masu. Kamfanin dillancin labaran Rauter ya bayyana cewa kasashen Turai 27 sun kara kashi 25% ga wasu zababbun kayakin kasar Amurka masu shigowa kasashen su. Wannan dais hi ne maida martani na farko wanda kasashen turan suka yi tun bayan...