2025-04-16@23:13:30 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2827
«gwamnati»:
Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta amince da kudirin kafa sashen kula da masu fama da matsalar kwakwalwa a jihar ya zama doka. Dokar za ta samar da kariya da kuma bunkasa ‘yancin masu fama da matsalar kwakwalwa musamman masu tu’ammuli da muggan kwayoyi a fadin jihar Kaduna. Da yake jagorantar zaman majalisar, shugaban majalisar dokokin...
Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum, ya karɓi baƙuncin Majalisar Sarakunan gargajiya ta Arewa a wani taronta karo na bakwai da ta gudanar a ranar Talata. Taron wanda ya gudana a birnin Maiduguri, an yi shi ne domin lalubo hanyoyin ƙarfafa tsaro da haɓaka ci gaban yankin. ...
Yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ke ziyarar aiki a Vietnam, shugaban CMG Shen Haixiong, ya kulla yarjejeniyoyin hadin gwiwa da shugaban gidan radiyon Vietnam Nguyen Thanh Lam, da shugaban gidan rediyon na Voice of Vietnam Do Tien Sy, kana da shugaban kwalejin yada labarai da fadakarwa na Vietnam Pham Minh Son, a...
Hukumar Ƙididdiga ta Nijeriya NBS ta ce hauhawar farashi ya ƙaru a ƙasar zuwa kashi 24.23 cikin 100 a watan Maris. Alƙaluman da hukumar ta fitar sun nuna an samu ƙarin kashi 1.05 daga kashi 23.18 cikin ɗari da aka samu a watan Fabrairu. EFCC ta gaza tabbatar da tuhumar Murja kan zargin wulaƙanta takardun...
Ban da haka, Wang ya ce matakan kasar Amurka sun karya ka’idojin kungiyar WTO na rashin nuna bambanci, da takaita karbar haraji, kana suna girgiza tsarin tattalin arzikin duniya, da tushen tsarin cinikayya da ya shafi bangarori daban daban. Ganin haka ya sa kasar Sin daukar matakan ramuwar gayya kan kasar Amurka, don kare halaltacciyar...
’Yan Najeriya da suka rabauta da sayen shinkafar kasar waje da Gwamnatin Tarayya ta karya farashinsa sun koka bisa rashin ingancin wata wadda ake sayarwa a Jihar Kogi. Wadanda suka sayi rukunin farko na shinkafar sun yaba da ingancinta da dandanonta, wasu kuma na korafi a kan yanayi da kuma dandanon wadda suka samu daga...
’Yan Najeriya da suka rabauta da sayen shinkafar kasar waje da Gwamnatin Tarayya ta karya farashinsa sun koka bisa rashin ingancin wata wadda ake sayarwa a Jihar Kogi. Wadanda suka sayi rukunin farko na shinkafar sun yaba da ingancinta da dandanonta, wasu kuma na korafi a kan yanayi da kuma dandanon wadda suka samu daga...
Rahoton Kungiyar Kasashe Masu Samar da Man Fetur (OPEC) ya nuna cewa Nijeriya ta ci gaba da riƙe matsayinta na ƙasa mafi yawan samar da ɗanyen man a nahiyar Afirka a watan Maris. OPEC ta ce hakan ya faru ne duk da raguwar yawan man da ƙasar ta samar a watan da ya gabata. Sabon...
Ta bayyana cewa gwamnatin jihar ta bayyana ayyana dokar ta-ɓaci a harkar ilimi, kuma ta kashe biliyoyin Naira wajen gyara da sabunta makarantun kwana, inda ta ce “nan ba da jimawa ba za a sake buɗe su don yara mata su ci gaba da samun ilimi.” Ta kuma ƙara da cewa wasu daga cikin makarantun...
Ya ce sama da mutane 150 ne aka kama da laifin faɗan ɗaba da tashin hankali, tare da ƙwato makamai, miyagun ƙwayoyi da kayan sata. Ya ƙara da cewa matsalolin faɗan ɗaba da shaye-shaye barazana ce ga zaman lafiyar jama’a da makomar matasa. Duk da yake kame na da muhimmanci, Bakori ya ce dole ne...

Kwamishinan ‘Yansandan Kano Ya Nemi Taimakon Sarakunan Gargajiya Wajen Kawo Ƙarshen Faɗan Daba A Jihar
Ya ce sama da mutane 150 ne aka kama da laifin faɗan ɗaba da tashin hankali, tare da ƙwato makamai, miyagun ƙwayoyi da kayan sata. Ya ƙara da cewa matsalolin faɗan ɗaba da shaye-shaye barazana ce ga zaman lafiyar jama’a da makomar matasa. Duk da yake kame na da muhimmanci, Bakori ya ce dole ne...
Hukumar Bunƙasa Noman Sukari a Najeriya (NSDC) ta sanya hannu kan yarjejeniyar Dala biliyan guda da kamfanin SINOMACH na ƙasar China kan bunƙasa noman rake da sarrafa shi da nufin samar da sukari da kudina ya kai metrik ton miliyan guda. Kulla yarjejeniyar wani ɓangare ne na shirin Kawancen Najeriya da China, na Gwmanatin Shugaba...
Isra’ila ta kashe Palasdinawa 17 tare da jikkata wasu 69 a cikin awa 24 a yankin Gaza, inda ta kai harin sama a wani asibiti da ke yankin Khan Younis. Ma’aikatar Lafiyar Gaza ta sanar cewa jiragen Isra’ila sun kashe wani jami’in lafiya tare da jikkata wasu tara a Asibitin Kuwaiti da ke yankin Al-Musawi...
Majiyar Falasdinawa a Gaza sun bada labarin kissan wasu sojojin HKI a unguwar Shuja’iyya kusa da Gaza a jiya Litini, inda wasu kuma suka ji rauni. Kafafen yada labarai da yahudawan da kuma larabawa sun bayyana cewa kungiyar Jihadul Islami a Gaza ta ce nayakanta masu farautar yahudawa daga nesa sun bayyana cewa suk halaka...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Bagaei ya bayyana cewa kokari da JMI a tattaunawarta da kasar Amurka kan shirin Nukliyar kasar shi ne ganin an dauke mata takunkuman tattalin arzikin da aka dora mata, ko amurka da dora mata.. Tashar talabjin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar...
A zantawarsa ta wayar tarho da tokwaransa na kasar Kuwait, ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya ce tattaunawarsa da Abdullah Ali Al-Yahya ya fi bada karfi kan al-amuran yankin Asiya ta kudu musamman tattaunawa tsakanin Iran da Amurka kan shirinta na makamshin nukliya da kuma dagewa kasar takunkuman tattalin arzikin da aka dora...
Ministan harkokin noma na JMI Ghulan Reza Noori Ghezelji ya jagoranci wata tawagar jami’an gwamnatin kasar zuwa kasar Brazil don halattan taron ministocin noma na kungiyar BRICS da kuma tattauna al-amura masu muhimmanci wadanda suka shafi ayyukan noma a duniya. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa gwamnatin JMI ta fara aiki...
Bayan da hukumar zaben kasar Gabon ta tabbatar da nasarar da Brice Oligui yayi a zaben shugaban kasa na karshen makon da ya gabata, shugaban ya gabatar da jawabinsa na farko ga mutanen kasar, inda ya bayyana masu kan cewa, babu jin dadi sai tare da wahala. Shafin tanar gizo na labarai ‘Africa News” ya...
Kotu ta yanke wa wani matashi hukuncin ɗaurin shekara biyu a gidan yari kan laifin yunƙurin soka wa mahaifinsa makami a unguwar Fagge da ke Jihar Kano. Kotun da ke zamanta a yankin Mai Alluna ta yanke wa matashin hukuncin ne bayan bayan alƙali ya kama shi da laifin yunƙurin soka wa mahaifinsa almakashi saboda...
A kalla tsoffin sojojin rundunar “Gulani” ta HKI 150 ne su ka rattaba hannu akan takardar yin kira da a dawo da fursunoni gida daga Gaza. Ita dai rundunar “Gulani” ce mafi karf a tsakanin rudunonin sojan HKI,kuma tun da aka kafa ta, ta shiga dukkanin yake-yaken da HKI ta yi. Wadanda su ka rattaba...
Wasu masu dauke da makamai sun kai hari a wasu kauyuka biyu dake jihar Filato inda su ka kashe mutane 52. Rahotannin da suke fitowa daga jihar ta Filato sun ambaci cewa wasu makiyaya ne su ka kai harin na ranar Litinin din da ta gabata an kai shi ne a kan yankin Bassa. Kamfanin...
Sojoji a Jihar Filato sun ceto wasu mutum 16 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a kan titin Jos zuwa Mangu. Dakarun Rundunar Operation Safe Haven ne suka ceto mutanen a cikin wata mota da a aka jefar da ita a yankin Mararabar Kantoma da ke Ƙaramar Hukumar Manngu. Jami’in Hulɗa da Jama’a...
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na Kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin al-kur’ani mai girma ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da Littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawi na maulana Jalaluddin Rumi, ko...
A jiya Litinin daruruwan yahudawa ‘yan share wuri zauna sun kutsa cikin masallacin kudus, suna masu bayar da take na tsokana ga Musulmi. Har ila yau ‘yan share wuri zauna din sun kuma gudanar da na’u’oin ibadu na addinin yahudanci a cikin farfajiyar masallacin na Kudus. Ma’aikatar da take kula da wuraren ‘wakafi’ na musulunci,...
Gwamnatin kasar Ajeriya ta bayyana jami’an diflomasiyyar Faransa da suke kasar su 12 a matsayin ‘wadanda ba a bukatar ganinsu” a cikin kasar, tare da yin kira a gare su da su fice a cikin sa’oi 48. Bugu da kari kasar ta Aljeriya ta yi suka da kakkausar murya akan ministan harkokin wajen Faransa Bruno...
’Yan bindiga sun kai hari a kan taron masu ibada inda suka yi awon gaba da mutane da dama da ba a tantance ainihin yawansu ba. Mutane suna tsaka da gudanar da ibadar dare ne a kan wani tsauni a lokacin da ’yan bindigar suka kai musu farmakin suka yi garkuwa da su. Lamarin ya...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A yanzu haka, al’ummar Filato na cikin fargaba da tashin hankali sakamakon jerin hare-haren da suka afku a wasu sassan jihar, inda daruruwan mutane suka rasa rayukansu, wasu kuma suka tsere daga muhallansu. Ko mene ne dalilin sake dawowar rikice-rikicen da suka dabaibaye yankin da ake ganin an...
Wasu kafofin yada labarai a duniya na ganin cewa, idan gwamnatin Amurka ta ci gaba da saka shingayen haraji, to sauran kasashe za su maye gurbinta a bangaren samar da hidimomi. Abin da gwamnatin ta yi biris da shi yayin da take kididdigar harajin da za ta kakabawa sauran sassa, har yanzu wannan bangare na...
Gwamnatin Jihar Kebbi ta kammala shirye-shiryen daukar nauyin dalibai 70 zuwa Masarautar Saudiyya domin karatun digiri a fannoni na addini da na zamani. Wannan na daga cikin shirin “Kaura Capacity Building Project 2025“ karkashin ma’aikatar kula da harkokin addinai ta jihar. A yayin wani taron manema labarai, mai bai wa Gwamna shawara kan harkokin addinali,...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaba Bola Tinubu ya bayyana bakin cikinsa kan harin da aka kai Jihar Filato wanda ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da 40. A cikin wata sanarwa, Shugaban kasa ya la’anci wannan tashin hankali tare da mika ta’aziyyarsa ga Gwamna Caleb Mutfwang, Gwamnatin Jihar, da al’ummar Filato. Sanarwar da Mai ba Shugaban Kasa shawara na...
Tsangayar Ilimi na Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK) ya shirya wani taron bikin cika shekaru 50 da kafuwa tare da gudanar da taron kasa karo na uku. Taron wanda aka yi wa take da “Ilimi Mai Sauya Rayuwa Don Gaba: Fuskantar Sabbin Kalubale da Buɗe Damar Samun Ci gaba” ya samu halartar manyan masu...
Babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya zai ziyarci Tehran a ranar Laraba mai zuwa. Ziyarar ta Grossi na zuwa ne gabanin sabuwar tattaunawar da za’ayi tsakanin Iran da Amurka a ranar Asabar mai zuwa kan batun shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya. Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin...
Rikicin diflomasiyya tsakanin Paris da Algiers na dada kamari, inda Aljeriya ta bukaci wasu jami’an diflomasiyyar Faransa 12 da su fice daga kasar cikin sa’o’i 48. Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Noël Barrot ya sanar cewa, Aljeriya ta bukaci jami’an diflomasiyyar Faransa da su fice daga kasar bayan kama wasu ‘yan kasar Aljeriya uku a Faransa....
Wata Kotun Majistire mai lamba 7 a Kano, ta bayar da umarnin tsare wasu ’yan TikTok biyu kan zargin wallafa wasu bidiyon batsa a shafukansu na dandalin sada zumunta. Hukumar Tace Fina-Finai ta Kano ce ta gurfanar da ababen zargin biyu — Isa Kabir Brigade da Fatima Adam Kurna — kan wallafa bidiyon da suka...
Rundunar ‘Yansandan Jihar Adamawa ta kama Umar Shaibu bisa zargin cin zarafin wata mata a yankin Jimeta a jihar. An kama Shaibu ne bayan wani bidiyo mai tayar da hankali ya yadu a kafafen sada zumunta, kamar yadda Jami’in hulda da Jama’a na ‘Yansandan Jihar Adamawa, SP Suleiman Nguroje, ya bayyana. Salamatu Yakubu, matar...
Wata ’yar kasar Jamus mai suna Alexandra Hildebrandt mai shekara 66 ta ja hankalin jama’a bayan ta haifi ɗanta na 10 ba tare da maganin haihuwa ba. Haihuwar ta faru ne a ranar 19 ga Maris a Asibitin Charité da ke Berlin da taimakon likita. Bello Turji ya kashe manoma 11 a Sakkwato ’Yan bindiga...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kasurgumin dan ta’addar nan da ke addabar yankin Sakkwato ta Gabas da Zamfara, Kacalla Bello Turji ya kashe manoma 11 a garin Lugu cikin Karamar Hukumar Isa ta Jihar Sakkwato. Dan gwagwarmaya da ke biye da lamarin rashin tsaro a yankin Sakkwato ta Gabas Bashiru Altine Guyawa ya sanar wa manema labarai cewa, Turji ya...
Sai dai har yanzu rundunar ‘yansandan jihar ba ta fitar da wata sanarwa ba kan lamarin, kuma ƙoƙarin da samun martaninsu ya ci tura. A gefe guda kuma, gwamnatin jihar Filato ta nuna damuwa kan hare-haren da ake samu a wasu sassan faɗin jihar, lamarin da ke ƙara haifar da damuwa a zuƙatan jama’a....
Gwamnatin jihar Jigawa ta bada kwangilar sanya kwalta akan hanyar Dolen kwana zuwa Garin Gabas zuwa Hadejia, kan naira miliyan dubu bakwai da miliyan dari takwas. Gwamna Umar Namadi ya bayyana hakan a wajen bikin kaddamar da aikin sanya kwaltar. Ya ce aikin hanyar mai tsawon kilomita 29, ana sa ran kammalawa nan da...

Shugaban Kasar Iran Ya Mika Ta’aziyyar Ta Rasuwar Wanda Ya Assasa Hukumar Makamashin Nukiliya Ta Iran
Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya bayyana alhininsa akan rasuwar Dr. Akbar I’itimadi wanda shi ne na farko da ya kafa hukumar makamashin Nukiliya ta Iran. Wasikar ta’aziyyar da shugaban kasa ta kunsa ta ambaci cewa: Shakka babu hidima mai kima da wannan masanin ya yi, ya share fagen gina da ci gaban fasahar makamashin...

Tsoffin Ma’aikatan Hukumar Leken Asiri HKI Mosad Sun Shiga Cikin Masu Kiran A Kawo Karshen Yaki Da Gaza
A daidai lokacin da ake ci gaba da takaddama a HKI dangane da wasikar da wasu sojojin sama su ka rubuta na sukar yakin Gaza, wasu tsoffin ma’aikatar hukumar leken asiri ta “Mosad” sun bi sawunhu. Kafafen watsa labarum HKI sun ambaci cewa, fiye da tsoffin jami’an leken asirin kungiyar MOSAD 200 ne su ka...
Majiyar asibiti a yankin Gaza, ta ambaci cewa an sami karuwar shahidai a cikin sassa mabanbanta na zirin Gaza zuwa 38, 3 daga cikinsu a yankin Deir-Balah. Jiragen yakin HKI sun kai wasu hare-hare akan wata mota da take dauke da wasu ‘yan’uwa shakikai su 6, da hakan ya yi sanadiyyar shahadarsu baki daya. ‘Yan’uwan...
Rundunar ‘yansandan jihar Yobe ta kama wasu mutane biyu da ake zargin barayin wayar wutar lantarki ne a Damaturu babban birnin jihar. Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar, SP Dungus Abdulkarim, a wata sanarwa da ya fitar, ya bayyana cewa, rundunar ‘yansanda ta Karasuwa ce ta kama wadanda ake zargin – Yahaya Mustapha,...
’Yan bindiga sun kashe mutane arba’in a wani hari suka kai a ƙauyen Zike, a yankin Kwall da ke Ƙaramar Hukumar Bassa a Jihar Filato. Wani shugaban al’ummar Kwall, Wakili Tongwe, ya ce maharan sun shiga ƙauyen ne da sanyin safiyar ranar Litinin suna harbi kan mai uwa da wabi, lamarin da ya sa mazauna...
Rundunar ‘yansandan Nijeriya ta gano wani haramtaccen wurin hada makamai a jihar Kano, lamarin da ya kai ga kama wasu mutane uku tare da kwato bindigogi kirar gida guda 15 tare da harsashi 102. Wadanda ake zargin sun hada da Abdul Sadiq mai shekaru 43; Ahmad Muazu, 22; da Aliyu Sharif, mai shekaru 40, an...
Sanatan Kudancin Borno, Ali Ndume, ya bayyana cewa a halin yanzu mayaƙan Boko Haram sun ƙwace yankunan ƙananan hukumomi uku a jihar. Ndume ya bayyana cewa mayaƙan kungiyar sun kashe fararen hula sanda a 200 da sojoji 100 a sabbin hare-haren da suka kai a sassan jihar a baya-bayan nan. A wata zantawar da aya...
Da yake jawabi a madadin shugaban kasa, Gwamna Uba Sani ya bayyana mahimmancin hanyar wadda ta hada babban birnin tarayya da jihohi sama da 12 dake fadin shiyyar Arewa ta tsakiya, Arewa maso Yamma, da Arewa maso Gabas. A yayin taron da aka yi a Jere a karamar hukumar Kagarko a ranar Lahadin da...
Fursunoni a gidajen yarin daban-daban a sassan Najeriya sun koka game da munin irin abincin da ake ba su, wanda suka ce na karnuka ya fi shi. Da dama daga cikin fursunonin da muka zanta da su sun bayyana cewa takwarorinsu sun sha mutuwa a sakamakon yunwa. Wannan zargi na zuwa ne bayan da Hukumar...