2025-04-02@01:29:48 GMT
إجمالي نتائج البحث: 265
«Majalisar Wakilan Najeriya»:

An Tsamo Gawakin Mutane 30 A Karon Da Wani Jirgin Fasinja Ya Yi Da Wani Jirgi Mai Saukar Ungulu A Birnin Washinton
Kamfanin dillancin labaran BBC ya bayyana cewa mutane 64 ne suke cikin jirgin fasinja na kamfanin American Airline, sannan mutane 3 ne a cikin jirgin yaki mai saukar ungulu samfurin Black Hawk suka yi karo a birnin washinton a safiyar yau Alhamis. Labarin ya kara da cewa, a halin yanzu sun tashi daga kubutar da...
Shugaban Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa ya mika gaisuwar sabuwar shekara da fatan alheri ga kasar Sin yayin da ta shiga sabuwar shekarar gargajiya. Cikin sakonsa a jiya Laraba, Cyril Ramaphosa ya bayyana kwarin gwiwar shekarar Maciji za ta ci gaba da karfafa matsayin Sin na karfin samar da kyawawan abubuwa da hikima da wadata...
Sanarwar ta kuma bayyana cewa, jami’an hukumar tsaron farin kaya daga jamhuriyar Nijar ne suka biyo wanda ake zargin ɗan bindigar ne a kan babbar hanyar Zurmi/Kauran Namoda a jihar Zamfara. Da yake duba makaman da aka kama, Gwamna Dauda Lawal ya bayyana kyakkyawar haɗin gwiwa tsakanin sojojin da gwamnatin jihar Zamfara wajen yaƙi...
Kungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’a (SSANU) ta bayyana cewa jami’o’in gwamnati da dama a Najeriya sun shafe sama da watanni uku ba tare da wutar lantarki ba da za su gudanar bincike ko darussa ba. Kungiyar ta kuma yi barazanar ɗaukar tsattsauran mataki kan gwamnatocin jihohi da kamfanoni da suka ki fara biyan sabon mafi ƙarancin...
Jaridar “Le Monde” ta kasar Faransa ta dauki labarin da yake cewa iyalai masu yawa sun fice daga HKI baki daya zuwa kasashen Portugal,Cyprus, da kuma Girka. Rahoton ya ci gaba da cewa; Dalilan yin hijirar daga HKI zuwa kasashen waje sun kunshi yaki, rashin tsaro da kuma siyasar gwamnatin Benjemine Netanyahu. Har ila yau,...
Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Dole ne kasashen duniya su gane irin wahalhalun da al’ummar Iran ta sha wajen yaki da ta’addanci Jakadan kasar Iran na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya Amir Sa’id Irawani ya aike da wasika ga kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya dangane da laifukan da kungiyar ta’addanci ta...
Duk da ficewarsu daga ECOWAS, ƙasashen AES sun yanke shawarar cewa ‘yan ƙasashen ECOWAS za su iya shiga ƙasashensu, domin ƙarfafa dangantakar hada-hadar kasuwanci a tsakanin yankin. Wannan ficewa na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasashen Sahel ke fama da matsalolin tsaro, wanda ya haifar da juyin mulki a ƙasashen uku. Yanzu haka, suna...
Ɗan wasan Nijeriya kuma gwarzon ɗan ƙwallon ƙafar Afrika, Ademola Lookman, ba zai buga wasan da Atalanta za ta kara da Barcelona a gasar cin kofin Zakarun Turai yau Laraba ba, sakamakon rauni da ya ji a gwiwarsa. A wata sanarwa da kulob ɗin Atalanta ya fitar, ya ce ɗan wasan mai shekaru 27 ya...

Aragchi Yace Duk Wani Harin Da Aka Kaiwa Cibiyoyin Nukliyar Kasar Iran Hakan Wata Musiba ce Ga Yankin Asiya Ta Yamma
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa duk wani hari kan daya daga cikin cibiyoyin Nukliyar kasar Iran daga HKI ko Amerika, wannan wata musiba ce da yankin, kuma wadanda suka kai harin zasu gamu da maida martani ba tare da jinkiri ba. Tashar talabijin ta Presstva nan Tehran ta nakalto Abbas...
Runduna daya ta sojojin Najeriya ta gudanar da bikin jana’izar marigayi Mascot, Sajan Dalet Danfari Akawala, a shalkwatar rundunar dake jihar Kaduna. Wanda dokin sojojin ne. A wata sanarwa da mukaddashin Daraktan hulda da jama’a na rundunar soji ta daya, Laftanar Kanar Musa Yahaya ya fitar, ya ce Kanar Akabike ne ya jagoranci jana’izar,...
A cim ma burin Gwamna Umar Namadi na ci gaban bil’adama a cikin ajandar mai dauke da abubuwa 12, majalisar zartaswar jihar Jigawa ta kafa wani kwamiti mai mambobi 10 domin samar da hanyoyin da za a bi wajen nemo masu hazaka domin karfafa kirkire-kirkire a tsakanin matasa masu tasowa a jihar. Kwamishinan yada...
A ranar 25 ga wata, agogon Najeriya, ofishin karamar jakadiya kasar Sin dake Legas, da tawagar Sinawa wadanda ke kasar, sun gudanar da jerin ayyuka don yin maraba da murnar bikin Bazara na shekarar maciji bisa kalandar gargajiyar Sinawa. An gudanar da bikin nune-nunen abinci, da nune-nunen kayayyaki, da liyafar maraba bi da bi, wanda...
Rundunar Sojin Najeriya ta 8 da ke Sokoto ta bayyana ayyukanta na zamantakewar jama’a na yammacin Afirka WASA, a matsayin muhimmin kayan aiki don wanzar da hadin kai da ci gaba a yankin yammacin Afirka. Babban Kwamandan Rundunar, Manjo Janar Ibikunle Ajose ya bayyana haka a wajen taron na bana da aka gudanar a...
“Baya ga tsarin Daidaiton Jinsi, muna kuma ƙaddamar da Dokar Kare Al’umma a jihar Zamfara. Waɗannan matakai suna da muhimmanci don tabbatar da cewa tsarin zamantakewarmu yana da ƙarfi kuma ya dace da buƙatun mutanenmu, musamman ma masu rauni. “Dokar kare haƙƙin yara da dabarun aiwatar da ita sun ƙarfafa ƙudurinmu na kare haƙƙin yara...
Dan takarar zaben maye gurbin Dan Majalisar Tarayya da ke wakiltar Mazabar Chikum da Kajuru a jam’iyar APC Arc Sani A Abbas Sardaunan Chikum ya nada kwamitin mutane 7 domin raba tallafin karatu ga daliban yankin sa su 100 da suke karatun kimiyya da fasaha a manyan marantun Gwamnati. Wannan wata manuniya ce game da...