2025-03-04@16:35:17 GMT
إجمالي نتائج البحث: 576

«Tara»:

    Majalisar bayar da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin (CPPCC), ta kaddamar da taronta na shekara-shekara yau Talata, a nan birnin Beijing. Shugaban kasar Sin Xi Jinping da sauran shugabannin kasar ne suka halarci taron bude zaman na 3 na kwamitin CPPCC karo na 14 da ya gudana a babban dakin taron jama’a. (Fa’iza...
    A yau ne za a gurfanar da yan adawar siyasa guda 40 da ake tuhumarsu  da aikata laifukan dake barazana ga tsaron kasa, a shari’ar da ƙungiyoyin kare hakkin bil adama suke daukarta a matsayin bi ta da kullin siyasa. Wadanda ake tuhumar sun hada da jami’an diflomasiyya da yan siyasa da lauyoyi da kuma...
    Gwamnatin jamhuriyar  Nijar ta bayyana aniyarta ta yin garambawul ga dokar tsarin amfani da shafukan sada zumunta irin su Whatsapp da Facebook da dai sauransu  a kasar. Ministan sadarwa na kasar Nijer sidi Mohammad Raliyu shi ne ya bayyana hakan, yana me cewa duk wani zaure na Whattsapp ko Facebook da ya kunshi mutanen  50...
    Masarautar Katsina ta ba wa dagattai da masu unguwaninta horo a kan sasanta jama’a a matsayin ginshikin samun dauwamammen zaman lafiya. An gudanar da taron ilmantarwar na tsawon kwanaki uku ne a kan yadda za a assasa zaman lafiya a tsakanin al’umma ta hanyar sasanci don samun aminci mai dorewa. Shugaban kamfanin tuntuba na Green...
    Tsohon Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA), Sepp Blatter, da tsohon shugaban UEFA, Michel Platini, za su sake gurfana a gaban wata kotu a Switzerland kan zargin cin hanci da rashawa. Kotun ɗaukaka ƙara da ke Muttenz za ta saurari buƙatar ofishin babban mai shigar da ƙara na ƙasar, wanda ke son sake dawo...
      Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya bayyana kasafin kuɗin bana, wanda Shugaba Tinubu ya rattaba wa hannu kwanan nan, a matsayin tsari mai karfi da zai daidaita tattalin arziki da kwanciyar hankali a zamantakewa, da kuma cigaban ƙasa.   Ya bayyana hakan ne a yayin taron da ake da...
    A karon farko manazarta a Iran sun yi nasarar samar da maganin farfadiya da kuma ciwon rabin kai Gabanin wannan lokacin ana amfani da maganin “Topiramate” wanda ake shigo da sanadari mafi muhimmanci na hada shi daga waje, domin yinsa a matsayin kwayoyi da kuma kafso. Wannan maganin ya sami karbuwa a matsayin na uku...
    Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Nasarawa da Toto daga Jihar Nasarawa, Honorabul Abdulmumin Ari ya ba da cekin Naira miliyan 45 don biyan kuɗin jarabawar WAEC ga daliban sakandare a mazaɓarsa. Da yake jawabi a wajen taron a garin Keffi, Abdulmumin Ari ya bayyana cewa kimanin shekara biyar ke nan yake aikin agaza wa...
    Kotu ta tsare wani magidanci a gidan yari kan zargin barazana ga rayuwar matarsa da yake zargin ta da maita. Babbar Kotun Musulunci da ke Gazawa a Jihar Kano ta tsare mutumin ne bayan ya yi barazana tare da yunƙurin kai wa matar tasa farmaki da adda. Mai gabatar da ƙara, Sadiq Yusuf ya shaida...
    Aikin titin Abuja zuwa Kano dai yana da matuƙar muhimmanci ga tafiye-tafiye da kasuwanci a Arewacin Najeriya, kuma jama’a sun daɗe suna ƙorafi kan jinkirin kammala shi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Baghaei ya yi kira ga gwamnatin kasar Turkiya ta sake tunani kan kalamanta dangane da JMI. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Baghaei ya na fadar haka a jiya Litinin, a taron mako mako da ya saba gabatarwa a ko wace litinin. Ya yi...
    A wani rahoto wanda ba’a tantance ba kungiyar kasashe masu arzikin man fetur da kawayenta a wajen kungiyar OPEC +  za su kara yawan man fetur da suke haka da ganga 138,000 a cikin watan Afrilu mai zuwa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto wasu majiyoyin kungiyar wadanda ba’a bayyana ba suna...
    Hukumar kare hakkin bil’adama ta MDD ta bada sanarwan cewa, sauye –sauye na asasi dake faruwa a kasar Amurka, zai shafi hukumar da ma MDD. Kwamishinan hukumar Volker Turk ya bayyana cewa fadar ‘White House’ a halin yanzu ta na gudanar da sauye-sauye na asasi a cikin hukumomi da ma’aikatu a Amurka, wadanda kuma za...
    Jami’an tsaro sun hana mutane zuwa kwasar man fetur daga wata tankar mai da ta yi hatsari a Jalingo, hedikwatar Jihar Taraba. A safiyar ranar Litinin ne ’yan sanda da jami’an hukumar tsaro ta Sibil Difens (NSCDC), suka ɗauki wannan mataki bayan faɗuwar tankar man a kan babban hanyar Jalingo zuwa Wukari. Rahotanni sun bayyana...
    A ranar 28 ga watan Fabarairun da ya shude ne aka saki wani fim din kasar Sin mai lakabin “Creation of the Gods II: Demon Force”, a gidajen kallon sinima 39 dake sassan tarayyar Najeriya, da kuma wasu 2 dake kasar Ghana, da sinima 1 a Laberiya. Wannan ne dai karon farko da aka saki...
    Majalisar Dattawa ta sanar da cewa a halin yanzu ba ta da hurumin gudanar da bincike kan zargin cin zarafi da Sanata Natasha Akpoti-Uduagha ke yi wa Sanata Godswill Akpabio. A bayan nan dai ana ci gaba da samun ƙarin kiraye-kirayen gudanar da cikakken bincike kan zargin da Sanata Natasha ta yi wa Shugaban Majalisar...
    Majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin (CPPCC) za ta gudanar da taron shekara-shekara daga ranar 4 zuwa ta 10 ga Maris a nan birnin Beijing, a cewar wani kakaki a yau Litinin. (Mohammed Yahaya) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban...
    Da yammacin yau Litinin ne aka gudanar da taron manema labarai na taro na uku, na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin ko CPPCC karo na 14, inda mai magana da yawun taron Liu Jieyi, ya gabatar da yanayin taron ga kafofin watsa labarai na kasar Sin da na waje, tare...
    Kasashen larabawa sun yi kakkausar suka ga matakin da Isra’ila ta dauka na dakatar da shigar da duk wani kayan agaji a zirin Gaza, suna masu bayyana hakan a matsayin keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kungiyar Hamas da kuma dokokin kasa da kasa. Ma’aikatar harkokin wajen Saudiyya a cikin wata sanarwa ta ce “Masar...
    Kungiyar ECOWAS, ta sanar da cewa tawagarta da ta je Guinea Bissau, ta bar kasar bayan barazanar data fuskanta daga shugaban kasar. A wata sanarwa da ta fitar, tawagar ta ce ta bar kasar “da sanyin safiyar Asabar sakamakon barazanar korar da shugaba Umaro Sissoco Embalo ya yi.” Tawagar kungiyar ECOWAS ta ziyarci kasar Guinea-Bissau...
    Ministan harkokin wajen Masar Badr Abdelatty ya ce shirin sake gina Gaza wanda ya baiwa Falasdinawa yancin ci gaba da zama a kasarsu, za a gabatar da shi a taron gaggawa na kasashen Larabawa da za a yi a wannan mako. Abdelatty a wani taron manema labarai a ranar Lahadin nan ya jaddada cewa shirin...
    Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce Paris da London na aiki kan shirin tsagaita wuta na wata guda a Ukraine. A wata hira da jaridar Le Figaro ta Faransa, Emmanuel Macron ya ce London da Paris suna ba da shawarar tsagaita wuta na wata guda da kuma samar da makamashi.” Daga baya a cikin jawabin...
    Karamar hukumar Malam Madori da ke jihar Jigawa, ta yi barazanar daukar matakin hukunta malaman makaranta da ba sa  zuwa aiki. Shugaban karamar hukumar, Alhaji Salisu Sani Garun-Gabas ya bayyana haka a wata hira da manema labarai bayan raba kudi dubu hamsin a matsayin tallafin karatu ga dalibai ashirin da biyar a yankin. A cewarsa,...
    Ƙungiyar Kwadago ta Nijeriya, NLC, ta yi fatali da yunƙurin ƙara kuɗin wutar lantarki a daidai lokacin da ’yan ƙasar ke fama da ƙuncin rayuwa. NLC ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta dakatar da yunƙurin ƙara kuɗin lantarki da masu amfani da layin A da B da C. Hakar ma’adanai: ILO ta horas...
    Gwamna Umar Namadi ya kaddamar da shirin noman rani ta hanyar amfani da rijiyoyin burtsatse a karamar hukumar Maigatari. Hakan wani muhimmin mataki ne  na samar da abinci da zamanantar da noma a jihar Jigawa. A cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labarai na gwamnan Hamisu Mohammed Gumel ya rabawa gidan rediyon Najeriya...
    Babban sakataren dakarun Asa’ibu Ahlul Hakki na kasar Iraki ya karyata zancen cewa za’a kwance damarar dakarun Hashdu sha’abi na kasar ta Iraki Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Qais Al-Khaz’ali ya na karyata wannan labarin, ya kuma bayyana haka ne a wani shiri a tashar talabijin ta Al-Irakiyya na kasar ta...
    Archbishop Okoh ya buƙaci jama’a da su zauna lafiya tare da bin hanyoyin doka domin shawo kan lamarin. Ya ce CAN ba za ta yi ƙasa a gwuiwa ba wajen ganin an samar da daidaito a tsarin ilimi, ba tare da nuna bambancin addini ba.   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Babban jami’in diplomasiyyar kasar Masar ya sanar da cewa; Shirin da kasarsa take da shi na sake gina Gaza, abu ne mai yiyuwa a aikace, kuma za a aiwatar da shi ba tare da an kori mutane su bar Gaza ba. Badr Abdul’adhy,  ya bayyana hakan ne a yayin ganawa da fira ministan gwmanatin kwarya-kwaryar...
    Hukumar wayar da kan jama’a ta kasa NOA, ta yi kira ga al’ummar Musulmi da su yi amfani da wannan lokaci na watan Ramadan wajen tunanin abubuwan da za su amfani kasa baki daya. Kodinetan hukumar na jihar Jigawa Mallam Ahmed Tijjani Ibrahim ya yi wannan kiran a wata sanarwa da ya raba wa manema...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    ‘Yan majalisar dokokin kasar Iran sun kada kuri’ar tsige ministan harkokin tattalin arziki da kudi Abdonnasser Hemmati daga mukaminsa saboda matsalolin tattalin arziki da kuma faduwar darajar kudin kasar. Hemmati ya rasa kuri’ar amincewa a zaman majalisar na wannan Lahadi inda ‘yan majalisa 182 daga cikin 273 suka kada kuri’ar tsige shi. ‘Yan majalisa tamanin...
    Bisa labarin da shafin intanet na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin NPC ya fitar, za a gudanar da taron manema labarai na taro na uku na NPC karo na 14, a zauren taron manema labarai na babban dakin taron jama’a, da karfe 12 na safiyar ranar 4 ga watan Maris, inda mai magana da yawun...
    Wasu ’yan bindiga sun yi basaja a matsayin jami’an Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), tare da sace mutum 10 a Otal ɗin White Hill da ke kan titin Shiroro a Ƙaramar Hukumar Chanchaga a Jihar Neja. Wani masani kan harkokin tsaro, Zagazola Makama, ya ce harin ya faru da misalin ƙarfe 4:58...
    Wadannan ayyuka suna tunatar da duniya hakikanin fuskar Musulunci. Kuma ko da yaushe na kan zama mafi samun kwarin gwiwa da kwanciyar hankali a wannan lokaci. A cikin wannan wata mai alfarma, dukkkanmu muna samun daukaka ta hanyar dabbaka wadannan dabi’u kuma muna rungumar ‘yan uwantaka don gina duniya mai adalci da zaman lafiya ga...
    Wadannan ayyuka suna tunatar da duniya hakikanin fuskar Musulunci. Kuma ko da yaushe na kan zama mafi samun kwarin gwiwa da kwanciyar hankali a wannan lokaci. A cikin wannan wata mai alfarma, dukkkanmu muna samun daukaka ta hanyar dabbaka wadannan dabi’u kuma muna rungumar ‘yan uwantaka don gina duniya mai adalci da zaman lafiya ga...
    Kafafen watsa labarun HKI sun sanar da cewa sojoji a shirye suke su shiga cikin rikicin da ya barke a garin Jarmana dake kusa da birnin Damascuss na kasar Syria domin kare ‘yan Duruz. Ofishin Fira ministan HKI Benjemine Netanyahi ya fitar da sanarwa a jiya Asabar da marece, yana ce; Netanyahu da ministansa na...
    A wani bidiyo mai ban mamaki da Hukumar Kashe Gobara ta yankin Tulsa da ke kasar Amurka ta fitar ya nuna yadda wani kare ya yi sanadin tashin wuta a wani gida ta hanyar tauna fakitin batirin Lithium. Hukuma ta kama karen bayan gano hakan a bidiyon mai ban mamaki, wanda ya nuna shi yana...
    Wata kungiyar kare hakkin bil’adama ta kasa da kasa ta bada rahoton cewa sojojin HKI sun kashe akalla yara 16 tun farkon wannan shekara ta 2025 a yankin yamma da kogin Jordan. Tashar talabijin ta Presstv  a nan Tehran ta nakalto Ayed Abu Eqtaish, daraktan kungiyar ‘ The Defense for Children International’ a yankin yamma...
    Gwamnatin kasar masar ta tabbatarwa gwamnatin Falasdinawa kan cewa tana goyon bayan falasdinawa a cikin dawo da hakkinsu, na kafa kasarsu mai cikekken yanci wacce take da gabacin birnin Qudus a matsayin babban birnin Kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Mostafa Madbouly ministan harkokin wajen kasar Masar yana fadar haka a...
    Malamai daga makarantun firamare 116 dake karamar hukumar Zaria sun gudanar da taron addu’o’i na musamman ga shugaban majalisar wakilai, Abbas Tajuddeen da gwamnatin jihar Kaduna. Malaman sun gudanar da addu’o’in ne domin nuna farinciki da godiya bisa yadda suke matukar kula da ilimi,wanda hakan ya inganta harkokin ilimin kuma ya kara bunkasa jin dadin...
    Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta gamu da cikas a kokarinta na darewa kan teburin gasar Laliga ta kasar Sifaniya, bayan rashin nasarar da ta yi a hannun Real Betis a filin wasa na Benito Villamarin da ke Seville. Tsohon dan wasan Real Madrid, Isco Alacon ne ya lashe kyautar gwarzon dan wasa a...
    Shugabar kasar Tanzaniya Samia Suluhu Hassan ta bayyana a jiya Juma’a cewa, tashar jirgin ruwa ta Tanga da kasar Sin ta inganta yanzu tana jigilar sama da tan miliyan 1.2 na kaya a duk shekara, adadin da ya karu daga jigilar tan 400,000 a kowace shekara. “Habaka tashar ta Tanga ya inganta ayyukanta.” a cewa...
    A jiya Juma’a ne mai magana da yawun ma’aikatar tsaron jama’a ta kasar Sin ya bayyana rashin amincewa da barazanar da Amurka ta yi ta sanya karin harajin kashi 10 cikin dari kan kayayyakin da kasar Sin ke fitarwa. Ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani ga wata tambayar manema labarai kan...
    Ana fargabar cewa wata gobara ta laƙume aƙalla shaguna 100 a Kasuwar Kara da ke Jihar Sakkwato. Gobarar wadda ta tashi tun da Asubahin wannan Asabar ɗin ta shafe sa’o’i 9 tana ta’adi. An raba wa ma’aikatan gona babura 200 a Yobe Yadda farashin kayan abinci ya sauka a kasuwannin Arewa Wani ɗan kasuwar da...
    Farashin kayayyakin abinci kamar masara da shinkafa da gero da dawa da wake da gari da waken soya da dai sauransu sun ragu, musamman a manyan jihohin da ake nomawa, kamar yadda wani bincike da Aminiya ta gudanar ya nuna. Wannan na faruwa ne gabanin watan Ramadan, wanda aka fara yau Asabar. Yadda ake ‘Spring...
    Wata gobara ta sake tashi a fitacciyar Kasuwar Kara da ke Sokoto, wacce aka fi sani da sayar da hatsi da kayan abinci, inda ta cinye gaba ɗaya kasuwar tare da mayar da shaguna da wuraren ajiyar kaya toka. Gobarar ta fara ci ne da safiyar Asabar, inda jami’an kwana-kwana suka yi ƙoƙarin shawo kanta...
    Dabi’un Da Suke Sa Malamin Makaranta Ya Ke Zama Nagartacce Ko dai su kasance suna koyar da manyan dalibai ne ko kuma lamarin ya zama suna koyar da kirga ce daga daya zuwa goma Azakakuran Malamai suna da wadansu dabi’u da suka yi kama da juna. Alal misali sanin kowa ne duk dai masu ilimi...
    A yau daya ga watan Maris ne dokar haramta amfani da tankunan dakon man fetur masu daukar lita 60,000 saboda yawan hatsarin da suke yi, wanda kuma yake lakume rayukan daruruwan mutane a ko wace shekara a duk fadin kasar. Jaridar Weeken Trust ya bayyana cewa hukumar ‘ The Nigerian Midstream and Downstream Petroleum Regulatory...
    Wata gobara da ta tashi cikin ta lalata wani ɓangare na Asibitin Ago da ke kan titin Ago Palace, Okota, a Jihar Legas. Gobarar ta fara ne da misalin ƙarfe 8:30 na daren ranar Juma’a, inda ta shafi wani sashe na ginin mai bene hawa ɗaya, inda asibitin yake. Gobara ta hallaka mutum 2 a...