2025-02-20@09:14:28 GMT
إجمالي نتائج البحث: 431
«Yan fashi da makami»:
Kungiya mai gwagwarmaya ta Falasdinawa Hamasa ta bayyana cewa tana iya sakin fursinoni yahudawa wadanda suke hannunta gaba daya a lokaci guda a marhala ta biyu ta musayar fursinoni tsakaninta da tare da sharadin ta cika al-kawulan da ta nauyi alhakin aiwatar da shi a wannan karon. Daga cikin har da maida tsagaita wutan na...
Dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran ( IRGC) ta yaye kallabin sabbin makamai a atisayen soja mai yaken “Rasulul-A’azam” da suke ci gaba da yi a halin yanzu. Daga cikin makaman da aka kaddamar da akwai makamai masu linzami dake cin dogon zango, sai kuma jiragen sama marasa matuki da kuma makaman Atilare....

Trump Na Amurka Ya Zargi Shugaban Kasar Ukiraniya Da Kama –Karya Da Kuma Rusa Kasarsa Ba Tare Da Wani Dalili Ba
Shugaban kasar na Amurka Donald Trump ya wallafa wani sako a shafinsa na “Truth Social” da a ciki ya bayyana Volodymyr Zelenskyy dad an kama-karya, kuma abinda ya fi yi masa alheri shi ne ya yi wani abu da sauri, domin idan ba haka ba,zai yi asarar kasarsa baki daya. Shugaban na kasar Amurka ya...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tun bayan sanarwar shirin kafa gwamnatin bibiya ko kuma ‘shadow government’ a turance da wata kungiya ƙarƙashin Jam’iyyar APC a Jihar Kano tace za ta yi ne ne dai al’umma da dama ke ta jefa ayar tambaya kan halascinta. Kungiyar dai ta bayyana cewa za ta kafa wannan...
A karshe dai, ya nanata muhimancin raya karfin kasa da kasa ta hanyar aiwatar da ayyuka masu alaka da hakan. Wang Yi ya jaddada cewa, kasar Sin tana fatan yin hadin gwiwa da sassa daban daban, domin bude sabon babin raya huldar cude-ni-in-cude-ka, tare da kafa tsarin gudanar da harkokin kasa da kasa mai inganci....
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada Dokta Danjuma Adamu Ismaila a matsayin shugaban kwalejin koyon tukin jiragen sama ta Najeriya (NCAT) da ke Zariya. Sanarwar da mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga ya fitar, ta ce Dakta Ismaila, kwararre kan harkokin sufurin jiragen sama, da manufofin tattalin arziki, ya...

Shugaban Kasar Iran Ya Tattauna Da Sarkin Kasar Qatar Kan Muhimmancin Hadin Gwiwa Da Taimakekkeniya Tsakaninsu
Shugaban kasar Iran da Sarkin kasar Qatar sun jaddada muhimmancin hadin gwiwa da taimakekkeniya tsakanin kasashen yankin Gabas ta Tsakiya Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian da sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hamid Al Thani sun gudanar da taron manema labarai na hadin gwiwa a birnin Tehran, inda suka jaddada karfin dangantakar da ke tsakanin kasashen...
Ofishin Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF da ke Kano, ya ce zai ci gaba da hada gwiwa da gwamnatin jihar Jigawa a bangarori da dama da suka hada da kiwon lafiya, da ilimi, da samar da abinci mai gina jiki, da kare yara, da al’umma. Shugaban ofishin , Mista Rahama...
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila ta fuskanci cewa dole ta mika wuya tare da amincewa da sulhu da ‘yan gwagwarmaya da ta nemi murkushe su Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Yahudawan sahayoniyya ba su cimma ko daya daga cikin munanan manufofinta ba, kuma daga karshe...
Kungiyar Hamas ta ki amincewa da sabbin sharuddan fira ministyan gwamnatin mamayar Isra’ila na yarjejeniyar Gaza kashi na biyu Fira ministan gwamnatin mamayar Isra’ila Benjamin Netanyahu a hukumance ya yanke shawarar fara tattaunawa kan mataki na biyu na yarjejeniyar Gaza, tare da sanya sabbin sharudda. A nata bangaren kungiyar Hamas ta ki amincewa da sharadin...
’Yan bindiga sun kashe mutum biyu tare da yin awon gaba da aƙalla wasu 10 a hare-haren da suka kai Ƙananan Hukumomin Wushishi da Rafi a Jihar Neja. Wani jami’in tsaro da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Aminiya cewa waɗanda aka kashe sun haɗa da ɗan sa-kai da wani mutum mai saran...
Shugaba Tinubu, a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, ya fitar, ya yaba da irin hazakar da Ishiekwene ke da ita a fannin sharhi da nazari kan harkokin siyasa, tattalin arziki da halin da Nijeriya ke ciki. Shugaban ya yaba da gudummawar da ya ke bayarwa wajen bunkasa yanayin kafafen yada...
’Yan bindiga sun kashe wasu mazauna ƙauyen Gwargwada da ke Ƙaramar Hukumar Kuje a saboda jinkirin biya musu kuɗin fansa. Mutanen da aka kashe, sun haɗa da Mohammed Danladi da Nasiru Yusuf, wanɗanda aka sace su ne a ranar Laraba tare da wani makiyayi da wata mata a mahaɗar Gwombe, a kan hanyar Gwargwada zuwa...
“Kungiyar malaman jami’o’i, reshen KASU na son sanar da jama’a cewa, majalisar zartaswarta ta kasa ta amince da bukatar reshen kungiyar na tsunduma yajin aikin sai baba-ta-gani daga ranar, 18 ga Fabrairu, 2025. “Majalissar ta yi watsi da alkawuran da gwamnatin jihar Kaduna ta dauka na rashin tabbaci, da cikakkun bayanai, da kuma lokacin...
Kamfanin dillancin labarun Qatar ( Qana) ya sanar da cewa, sarkin kasar Sheikh Tamim Bin Hamad ali-Sani ya baro Doha akan hanyarsa ta zuwa Tehran. Majiyar ta kara da cewa, sarkin na Qatar zai zo da tawagar tattalin arziki da kuma siyasa. Baya ga batun tattalin arziki, bangarorin biyu za su tattauna batutuwan da su...
Shugaban kungiyar Hamas Khalilul-Hayyah, ya fadi cewa; A ranakun Alhamis da Asabar masu zuwa ne za a mikawa ‘yan mamaya fursunoni rayayyu da kuma wasu gawawwaki a cikin bude wani shafin na musaya. A jiya Talata ne dai Khalilul-Hayyah ya sanar da cewa, a bisa yadda aka cimma matsaya a musayar farko da aka yi,...
Dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran sun sanar da gano da kuma rusa wata kungugun masu yi wa Amurka da Isra’ila leken asiri a yankin Arewacin Iran. Kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci a yankin Mazandaran dake arewacin Iran ne ya sanar da bankado da kuma rusa gungun masu yi wa abokan...
Rundunar sojan kasar Sudan ta sanar da kwace iko da hanyoyin da suke isa al-Fasha, kamar kuma yadda su ka killace fadar shugaban kasa dake birnin Khartum. Sanarwar sojojin na Sudan ta kuma tabbatar da cewa, killace wannan hanyar da su ka yi, ya yanke duk wata dama da dakarun “Rundunar Kai Daukin Gaggawa” suke...
Sakataren harkokin waje na kasar Amurka Marco Rubio ya bayyana cewa kasashen Amurka da Rasha sun kuduri anniyar kawo karshen yakin Ukrai, banda haka zasu kara kyautata dankon zumunci da tattalin arziki a tsakaninsu. Shafin yanar gizo na labarai, Arabnews ta gwamnatin kasar Saudiya ya bayyana cewa, ya nakalto Rubio yana cewa kasashen biyu sun...

Ma’aikatar sharia ta kasar Iran Ta bada sanarwan Kama Yan Kasar Burtaniya 2 Tare Da Tuhumar Leken Asiri
Kakakin ma’aikatan shari’a a kasar Iran ya bayyana cewa jami’an tsaro na kasar Iran sun kama mutane biyu yan kasar Burtaniya tare da tuhumar aikin liken asiri a lardin Kerman na kasa. Kamfanin dillancin labaran (IP) na kasar Iran ya bayyana cewa mutanen biyu suna tafiye-tafiye zuwa lardunan kasar Iran suna tattara bayanai a cikin...
Jagoran juyin juya halin Musulunci A nan Iran Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya gana da shuwagabannin kungiyar Jihadul Islami na kasar Falasdinu da aka mamaye a jiya Talata. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ya bayyana cewa Ziyad Nakhalah shugaban kungiyar ne ya jagoranci tawagar kungiyar zuwa ganawa da jagoran. Labarin ya nakalto Jagoran...
Gwamnatin Jumhuriyar Nijer daga jiya Talata ta fara aikin hana yan Najeriya dauke da Passport na kungiyar ECOWAS shiga kasar. Kafin haka dai mutane daga kasashen ECOWAS suna shiga kasashen kungiyar ba tare da bukatar visar shiga ko wace kasa daga cikin kasashe kungiyar ba. Amma bayan da kasashe 3 Nijer, Burkina Faso da kuma...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Yanayin tattalin arziki da ma wasu dalilai kan tilasta wa mutane da dama, ciki har da masu karɓar albashi a karshen wata, neman wata hanya ta daban dake kawo Karin kudade. Shin mene ne yake kawo hakan, kuma mene ne tasirinsa a kan rayuwar masu buga-bugar da ma...
Yawan kudin tikitin kallon fim din “Ne Zha 2” na kasar Sin da aka saya ya zarce dala biliyan 16 a daren jiya, abin da ya sa ya shiga sahun fina-finai 9 mafi samun yawan kudin tikitin kallon fim dake sahun gaba a duniya. Dalilin da ya sa fim din samun wannan ci gaba shi...
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewa: Barazanar makiya a kan kasar Iran da al’ummarta ba ta yi nasara ba Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa: Gagarumar zanga-zamga da al’ummar Iran suka gudanar a ranar 22 ga watan Bahman ta tabbatar da cewa barazanar makiya a...

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Bayyana Irin Gagarumar Rawar Da Iran Ta Taka A Fegen Tsaro Yakin Tekun Pasha
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa; Iran tana taka rawa ta musamman wajen wanzar da kwanciyar hankali da tsaron yankin Tekun Pasha Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta hanyar mallakar mafi yawan layukan kan iyaka da tekun Pasha da kuma iko da mashigar Hormuz, ta...
Babban kwamandan sojojin kasar Iran ya bayyana cewa: Sun sabunta hanyoyin da sojojin Iran zasu mayar da martani kan duk wani harin wuce gona da iri kamar yadda Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bada umarni Babban kwamandan sojojin kasar Iran Manjo Janar Abdur-Rahim Mousawi ya bayyana cewa: Tun tsawon kwanaki da suka gabata jagoran...
Shugaban kasar Amurka ya bayyana cewa: Fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ya aikata duk abin yake so Shugaban Amurka Donald Trump ya yi nuni da wa’adin da ya bayar dangane da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kuma sakin fursunonin, yana mai cewa ya shaidawa fira ministan gwamnatin mamayar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya aika duk...

Jaridar Maariv Ta Isra’ila Ta Bayyana Wasu Daga Cikin Hasarorin Da Yakin Gaza Ya Janyo Wa Gwamnatin ‘Yan Sahayoniyya
Jaridar Ma’ariv ta Isra’ila ta bayyana adadin wadanda suka jikkata a cikin sojojin mamayar Isra’ila da kuma miliyoyin yahudawan sahayoniyya da suka samu matsalar tabin hankali a lokacin yakin Gaza Jaridar “Ma’ariv” ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta bayyana a jiya litinin, adadin wadanda suka mutu a cikin jerin sojojin mamayar Isra’ila a yayin mummunan ayyukan...

Ministan Harkokin Waje Iran Ya Jaddada Cewa Iran Ba Zata Tattauna Da Amurka A Karkashin Takunkumai ba
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Arazgchi ya kara jadda cewa JMI ba zata zauna a teburin tattaunawa da kasar Amurka ba a karkashin takunkuman tattalin arziki ba. Ya kuma kara da cewa Amurka ba zata iya tursasawa kasar Iran zama da ita ba. Ministan ya kara da cewa, ba zakin baki mukeso ba, sai...
Wasu daga cikin mutanen kasar Afirka ta kudu da suke dauke da cutar HIV suna yin koken cewa janye tallafin da Amurka ta yi a karkashin hukumar nan ta USAID, zai jefa rayuwarsu a tsakanin mutuwa da rayuwa. Da akwai miliyoyin mutane a kasar ta Afirka Ta Kudu da suke dauke da cutar HIV da...
Mataimakin kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran “IRGC” ya sanar da cewa; Iran za ta kai farmakin “Wa’adus-Sadik 3” a lokacin da ya dace. Laftanar janar Ali Fadwi ya kuma yi ishara da yakin Gaza, yana bayyana cewa, su kansu ‘yan sahayoniya sun bayyana cewa Hamas ta yi nasara, su kuma ba...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A kwanakin baya ne dai Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙirƙiro sababbin hukumomin raya shiyyoyin ƙasar nan da nufin kawo musu ci-gaba. Gabanin ƙirƙirar waɗannan hukumomin, gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ce ta fara kirkirar hukumar raya yankin Neja Delta bayan wasu ƙalubale da suka dabaibaye...
A ranar 15 ga watan Fabrairu, ministocin harkokin waje na kasashen Amurka, Japan, da Koriya ta Kudu sun yi shawarwari a Munich na kasar Jamus. A cikin sanarwar hadin gwiwar da suka fitar, a karon farko, sun bayyana goyon bayansu ga yadda Taiwan za ta shiga cikin kungiyoyin kasa da kasa da suka dace, tare...
Ya ce harin da aka kai ta sama ya yi sanadin kashe ‘yan ta’adda da dama tare da dakile harin da suka kai wa jami’an rundunar ‘yansanda (PMF) da jami’an tsaro na cikin unguwanni (Community Watch Corps, CWC) na jihar Katsina. AVM Akinboyewa ya bayyana cewa, an kaddamar da harin ne a matsayin martani...
Kakakin Majalisan ya amince da kudirin dan majalisa mai wakiltar mazabar Keana kuma shugaban Kwamitin Majalisar kan Muhalli, Hon. Muhammed Adamu Omadefu, wanda ya bukaci dakatarwar a yayin tantance kwamishinan a zauren Majalisar da ke Lafiya, babban birnin jihar. Hon. Jatau ya ce, Majalisar za ta sake duba batun tantance shi ne kawai idan...

Yawan Tikitin Kallon Fim Din “Ne Zha 2” Da Aka Sayar a Karshen Mako Ya Shiga Sahun Gaba Na Fina-Finai 5 A Arewacin Amurka
Kamfanin dake gudanar da nazari na Comscore na Amurka ya ba da kididdiga cewa, yawan tikitin da aka sayar a karshen mako na kallon fim din kasar Sin mai suna “Ne Zha 2” ya shiga sahun gaba na fina-finai 5 a arewacin Amurka. An yi kiyasin cewa, yawan kudin da aka samu a kwanaki 3...
Ya ce: “A bara, na wakilci Nijeriya a Indonesiya, kuma na gano cewa akwai manyan kamfanoni hamsin daga Indonesiya da ke aiki a Nijeriya, amma ba mu da ko kamfanoni biyar daga Nijeriya da ke aiki a Indonesiya. “Idan suna son zuwa ƙasar mu su yi kasuwanci saboda yawan mutanen mu da kuma damar...
Nijar ta bayyan fatanta na ganin ta kulla yarjejeniya da kafofin yada labarai na Iran. Wannan bayanin na kunshe ne a bayyannin da jakadan Nijar a Tehran Malam Seydou Ali Zataou, ya yi a ganawarsa da shugaban hukumar gidan radiyo da talabijin sashen kasashen waje na Iran, Ahmad Norozi a wannan Litinin. Bangarorin sun bayyana...
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa kokarin da makiya suke yi na haifar da sabani a tsakanin al’ummar kasar ta hanyar yi musu barazana ya ci tura. Babban tattakin da al’ummar kasar suka yi a ranar 10 ga watan Fabrairu ya nuna cewa barazanar makiya ba ta...
Kungiyar Hamas ta jinjinawa kungiyar tarayyar Afrika ta AU kan yin Allah wadai da kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a Gaza bayan da kungiyar ta soki Isra’ila da keta dokokin kasa da kasa a jawabin rufe taron da ta yi na kwanaki biyu a Addis Ababa. Hamas ta ce tana matukar godiya da matsayin...
Ministan tattalin arziki na kasar Iran Abdunnaser Himmati yana halatan taro dangane da matsaloli da kuma dammakin da kasashen masu tasowa suka fama da su a birnin Riyad na kasar Saudiya. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa Himmati yana halattan wannan taro na kwanaki biyu ne tare da gayyatar tokwaransa na...
Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana cewa kasashen Turai basa cikin tattaunawar tsagaita wuta a Ukraine. Jaridar Daily Mail ya bayyana cewa hankalin shuwagabannin kasashen turai ya tashi a lokacin da JD Vance mataimakin shugaba Trump ya fada masu cewa ba wani shugaba daga cikin shuwagabannin kasashen Turai da zasu halarci taron tsagaita wuta...
Shugaban kasar Sin kuma babban sakataren kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta kasar, Xi Jinping ya halarci wani taron tattaunawa na kamfanoni masu zaman kansu a yau Litinin. Xi, wanda har ila yau shi ne shugaban kwamitin tsakiya na sojin kasar, ya gabatar da muhimmin jawabi bayan sauraron ra’ayoyin wakilan ‘yan kasuwa masu zaman kansu....
Gwamna Umar Namadi ya kaddamar da aikin gina titin Kanya Babba (Kwanar Duzau) zuwa Kankare zuwa Ballada zuwa Duzau zuwa Danhill zuwa Kyambo zuwa Mundu zuwa Goron Maje. Aikin wanda aka bayar da shi kan kudi naira biliyan 6 da miliyan 300, wani muhimmin mataki ne a yunkurin gwamnatin jihar na inganta ababen more rayuwa...
Gwamnatin Amurka ta fara aiwatar da matakan korar ‘yan Nijeriya daga ƙasar, inda ake sa ran mutane 85 za su iso Lagos, yayin da wasu 116 ke tsare. Jakadan Amurka a Nijeriya, Richard Mills, ya bayyana haka yayin wata ziyarar ban girma da ya kai wa Ministan harkokin wajen Nijeriya, Ambasada Bianca Odumegwu-Ojukwu, a Tafawa...
Kungiyar da Hansi Flick ke jagoranta ta tsallake zuwa matakin zagaye na 16 a gasar zakarun Turai, amma kuma sabon kocin na fatan ganin ya lashe babbar gasar ta kasar Sifaniya.
Gwamnan Kano Ya Gargaɗi Malamai Kan Sa Yara Aikin Wahala
Wani matashi da aka kama kan yin gunduwa-gunduwa da budurwarsa da suka haɗu a Facebook bayan ta je ɗakinsa ya bayyana dalilinsa na aikata hakan. Matashin mai shekaru 29 da ke iƙirarin malumtar addini ya amsa a wurin ’yan sanda masu bincike cewa shi ne ya yi wa gawar budurwar tasa gunduwa-gunduwa. Ya shaida musu...
Da farko za ku zuba Fulawa a wata roba haka sannan ku kawo Baikin Fauda ko Yis duk dai wanda za ku yi amfani da shi ku zuba, sai ku zuba madara sannan sai Gishiri kadan haka sai Qwai shima ku fasa a ciki, amma kada ya yi ruwa ko kauri kwabin. Sannan sai ku...