2025-03-21@19:26:57 GMT
إجمالي نتائج البحث: 16
«miyagun kwayoyi»:
An yi kira ga gwamnati a dukkan matakai da su hada kai da sauran masu ruwa da tsaki a harkar rage karuwar amfani da magungunan ba bias ka’ida ba a tsakanin matasa. Babban Daraktan Kula da Lafiya (CMD,) a Babban Asibitin Neuro-Psychiatric na Tarayya, Budo Egba, Jihar Kwara, Dokta Issa Awoye, ya yi wannan kiran ne a cikin jawabinsa mai taken, Sakamakon Neuropsychiatric na Maganganun Magani: Ra’ayin Clinical a taron masu ruwa da tsaki na Kwara na biyu kan Kariya da Sarrafa miyagun kwayoyi, wanda aka gudanar a Ilorin. A cewarsa an samu karuwar noma da fataucin miyagun kwayoyi a kasar, musamman a tsakanin matasa. Ya jera magungunan da aka saba amfani da su sun hada da...
Dalilin wannan doka shi ne rikice-rikicen addini tsakanin Musulmai da Kiristoci a watan Satumba 2001, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 2,000. A Jihar Borno Ma An Taɓa Sanya Dokar, Amma Ba A Jihar Baki Ɗaya Ba A shekarar 2011, Shugaba Goodluck Jonathan ya ayyana dokar ta-ɓaci a wasu ƙananan hukumomin jihohin Borno, Adamawa, da Yobe saboda yawaitar hare-haren Boko Haram. A 2013, Jonathan ya faɗaɗa dokar ta-ɓacin zuwa ɗaukacin jihohin Borno, Yobe, da Adamawa sakamakon tsanantar matsalar tsaro. Wannan mataki ya bai wa jami’an tsaro ƙarin iko domin dawo da zaman lafiya. Sai Kuma Jihar Ribas a Yanzu Shugaba Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a Jihar Ribas saboda rikicin shugabanci...
Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya nuna damuwarsa kan yadda sarautar gargajiya ke rasa martabarta a ƙasar nan. A cikin sabon littafinsa mai suna ‘Nigeria: Past and Future’, ya bayyana cewa yanzu akwai masu laifi, ’yan daba, da masu safarar miyagun ƙwayoyi da suka zama sarakuna a wasu yankuna na Najeriya. Afirka ta Kudu ta yi martani kan korar jakadanta daga Amurka Trump ya dakatar da kafar watsa labarai ta VOA “A yau, akwai ’yan daba, masu safarar miyagun ƙwayoyi, ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane da ake kira sarakuna,” in ji Obasanjo. “Wannan abu ne mai matuƙar ban takaici, kuma yana daga cikin matsalolin da ke addabar Najeriya.” Ya ce dole ne a dawo da mutunci da ƙimar sarautar...
Fitaccen mai barkwancin nan wanda yake kwaiwayon maganganun tsohon Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, Obinna Simon wanda aka fi sani da ‘MC Tagwaye’ wanda yake mai nishaɗantarwa, ɗan kasuwa, kuma ɗan siyasa ya sauya sheƙa daga Jam’iyyar APC zuwa SDP. Ya sanar da hakan ne a cikin wani saƙon da ya wallafa a dandalin sada zumunta na zamani a ranar Juma’a, ya danganta sauya jam’iyyar ne bayan tuntuɓa da yin shawarwari. Wata mata ta faɗa ruwa ta mutu a Legas Direba ya murƙushe yarinya ta mutu a artabu da jami’an tsaro a Edo “Bayan tsawon watanni na tuntuɓar juna, ni Obinna Simon da aka fi sani da MC Tagwaye, na yanke shawarar ficewa daga Jam’iyyar APC na koma SDP.” “Wannan gagarumin...
’Yan sanda sun cafke wasu mutum uku bisa zargin lalatawa da kuma satar wayoyin lantarki a ƙauyen Bororo da ke Ƙaramar Hukumar Michika ta Jihar Adamawa. An cafke ababen zargin ne da wayoyin lantarkin yayin wani sintiri da jami’an ’yan sanda suka gudanar a ranar 9 ga wannan wata na Maris. Abin da ya sa na sauya sheƙa daga APC zuwa SDP — El-Rufai ’Yan bindiga sun yi garkuwa da matashi a Kano Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan, Suleiman Yahaya Nguroje, ya ce ababen zargin da ke hannu sun yi iƙirarin aikata laifin da ake zarginsu da shi. Sai dai ya ce za a ci gaba da gudanar da bincike gabanin ɗaukar matakin da ya ce nan gaba...
“Wadanda aka samu da laifi doka za ta hukunta su. “Ayyukan sun kai ga kwato tarin muggan makamai, haramtattun abubuwa, da abubuwan da ke da alaka da aikata laifuka. Wadannan sun hada da busasshen ganyen da ake zargin tabar wiwi ne, gatari uku da adduna uku, wadanda galibi ake amfani da su wajen aikata munanan laifuka. “Kananan bututu guda shida na manne, bongs din hannu guda biyar, kayan da aka fi hadawa da abubuwan maye, almakashi guda takwas, katunan ID guda biyar, kananan kwantena na filastik da yawa da wasu kwayayen da ake zargin haramun ne. “Rundunar ta kuma kara sanya ido kan gine-ginen da aka yi watsi da su da kuma wuraren da aka gano a matsayin maboyar masu...
Babbar Kotun Tarayya da ke Jihar Legas da ta Yola, da Jihar Adamawa, sun yanke wa wasu dillalan miyagun ƙwayoyi huɗu da aka kama da safarar ƙwayoyi da darajarsu ta kai Naira biliyan 4.6 hukuncin ɗaurin shekaru 95 s gidan yari. Ɗaya daga cikinsu, Ogbuji Christian Ifeanyi, jami’an hukumar NDLEA sun kama shi a filin jirgin saman Murtala Muhammad da ke Legas a bara, yana ƙoƙarin shigowa da hodar iblis ɗauri 817 mai nauyin kusan kilogram 20, wadda kuɗinta ya kai biliyan 46. Tinubu ya bai wa Farfesa Jega muƙami a gwamnatinsa PDP ta soki dakatar da Natasha, ta nemi a binciki Akpabio Sauran da aka kama sun haɗa da Iloduba Augustine Chinonye, Shuaibu Nuhu Isa (wanda aka fi sani...
Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Nijeriya (NDLEA) ta bayyana cewa ta kama wani mutum da take zargin madugun fataucin ƙwayoyi ne, Ogbonnaya Kevin Jeff, a maɓoyarsa da ke Jihar Legas. Sanarwar da mai magana da yawun NDLEA, Femi Baba Femi, ya fitar ta ce kamen mutumin mai shekaru 59 na zuwa ne bayan shafe shekaru 17 yana ɓuya, inda yake fataucin miyagun ƙwayoyi na biliyoyin nairori a faɗin duniya. Sanarwar ta ambato Shugaban NDLEA, Birgediya Janar Muhammad Buba Marwa mai ritaya yana bayyana hakan yayin taron manema labarai a Abuja a yau Litinin. Shugaban NDLEA ya kuma bayyana yadda jami’an sashen ayyukan musamman na hukumar suka riƙa bin diddigin Ogbonnaya biyo bayan nemansa ruwa a jallo...
Shugaban Majalisar Wakilai, Tajuddeen Abbas, ya bayyana cewa mutum hudu a cikin kowane mata 10 a Jihar Kano sun fuskanci cin zarafi a gidajensu. Tajuddeen Abbas ya bayyana cewa akalla kashi 35 na matan Najeriya sun fuskanci cin zarafi, lamarin da ya ce ya fi muni a yankin Arewa maso Yamma. Ya bayyana wa taron wayar da kai game da illar ta’ammali da miyagun kwayoyi da kuma cin zarafi a cikin gidaje cewa, “abin ya fi muni a yankin Arewa maso Yamma, inda a Jihar Kano matan da ake cin zarafinsu a cikin gidajensu sun kai kashi 40 cikin 100.” Game da yawa masu ta’mmali da miyagun kwayoyi kuwa, Shugaban Majalisar Wakilan, wanda dan yankin ne, ya bayyana cewa an...
An bukaci Majalisar Dokoki ta Kasa da ta kafa doka wacce za ta tanadi hukuncin kisa ga masu safarar da kuma masu shan miyagun kwayoyi, domin kare rayuwar ‘yan kasa. Wannan kiran ya fito ne daga shirin KAKAKI na FRCN Kaduna FM, inda masu kira suka bayyana ra’ayoyinsu a yayin tattaunawa da mai gabatar da shirin. Masu magana sun nuna damuwa kan illar safarar miyagun kwayoyi a kasar, musamman yadda yake shafar matasa, wadanda ake kallon su a matsayin shugabannin gobe. Alhaji Gaddafi Rigasa da Hajiya Aisha Mando sun jaddada bukatar hukumomin tsaro su kara zage damtse wajen yaki da wannan matsala, domin inganta ci gaban tattalin arziki da zamantakewa. Sai dai sun kuma ba da shawarar a farfado...
Kiyaye taruwar maiƙo da kwayoyin cuta a fuska da kirji. Wannan kan dan yi wahala amma ta wadannan dabaru za a samu nasara: 1- Rage maiƙo a cikin abinci. Misali, idan aka soya wani abinci, yana da kyau a tsane mai da mayanin kicin wafif ko tawul ko tushu mai tsabta kafin a ci. Idan an yi haka an rage man kusan da kashi hamsin cikin dari ko ma fiye. 2- Yin amfani da sabulu mai kashe kwayoyin cuta wajen wanke fuskar safe da yamma. 3- Shan kayan itatuwa da cin ganyayyaki a kai –a-kai ya kan tsane maikon cikin jini ya kara karfin garkuwar jiki wajen yakar kwayoyin cuta. 4- Ga wanda wadannan Dabaru ba su yi musu aiki...
In an taba rarrauna a gabanka, kana da ikon kare masa, to ka kare masa, kin kare masa sakaci ne ba hakuri ba ne. An ruwaito cewa, Annabi (SAW) bai taba dukan wata daga cikin Matansa ba ko kuma cikin masu masa hidima a gida ko a waje. An kama wani Mutum da yake shirin kashe Annabi (SAW), aka gurfanar da shi gaban Annabi (SAW), sai jikinsa ya fara makyerkyata, Annabi (SAW) ya ce masa, kar ka firgita, ko da ka yi niyyar kashe ni, Allah ba zai dora ka a kaina ba. Zaidu dan Sa’anatal Yahudi ya zo wurin Annabi (SAW) kafin ya Musulunta yana neman Annabi (SAW) ya biya shi bashin da ya karba a wurinshi. Sai ya...
Hukumar yaƙi a sha da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA) reshen Jihar Kano ta kama wani tsoho mai shekaru 75, Nuhu Baba, bisa zargin sayar da miyagun ƙwayoyi ga matasa. Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Sadiq Muhammad-Maigatari, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata a Kano, inda ya ce wanda ake zargi ya amsa laifinsa, yana mai cewa ya rungumi sana’ar ne domin rayuwa a unguwarsu da ke ƙaramar hukumar Gezawa. NDLEA Ta Cafke Masu Ta’ammali Da Ƙwayoyi 18,500 A 1 – Marwa NDLEA Ta Gargadi Iyaye Kan Bayyanar Alawar Ƙwaya A Kano Hukumar ta kwato nau’ikan kwayoyi daban-daban, ciki har da Tramadol, wiwi, Diazepam, Exol-5 da man shafawa mai sa maye. Kakakin hukumar...
Sin: Kasar Amurka Ce Ta Haifar Da Matsalar Miyagun Kwayoyi A Cikin Gidanta
“Sauran abubuwan baje kolin da aka kwato daga hannun mutanen biyu sun hada da: bindigogi guda uku da aka kera a cikin gida; bindiga guda da aka yi a gida guda biyu; bindigar zamani guda daya; bindigar gida guda daya; cartridges guda uku da 9mm mara komai da gatari mai kan karfe. “Wani farmakin da aka kai Legas, ya kai ga kama skunk mai nauyin kilogiram 47, wani nau’in tabar wiwi, da kuma Nitrous Odide mai nauyin kilogiram 25.46 da aka fi sani da dariya a unguwar Akala da ke Mushin,” Babafemi ya kara da cewa. A Jihar Ekiti, Babafemi ya ce jami’an NDLEA sun kama wani matashi dan shekara 26 mai suna Adepoju Taiwo, dauke da kilo 1.950 na...
Hukumar yaƙi da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi (NDLEA) reshen Jihar Yobe ta ce ta kama wasu haramtattun ƙwayoyi da nauyinsu ya kai kilo 537 tare da kama wasu mutum 46 da ake zargi da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi a shekarar 2024. Kwamandan hukumar ta NDLEA a Jihar Yobe, Mista Abdulazeez Ogungboye ne ya bayyana hakan a Damaturu yayin da yake bitar ayyukan hukumar na shekara guda da ta gabata. Kiristoci sun yi addu’ar ɗorewar zaman lafiya a Kudancin Kaduna DAGA LARABA: Dalilan Da Mutane Suke Son Haihuwar Maza Fiye Da Mata Ya ce magungunan da aka kama sun haɗa da kilo 396.526 na tabar wiwi da kilo 141.2 na sauran kayayyakin maye. Ogunboye ya ce hukumar ta miƙa mutane 21...