2025-03-26@11:30:40 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2497

«Sanata Marshal»:

    Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya sanya hannu kan dokar majalisar gudanarwar kasar Sin, mai kunshe da matakan dakile takunkuman kasashen waje ta janhuriyar jama’ar kasar Sin. Tanadin dokar zai fara aiki ne tun daga ranar kaddamar da ita. Dokar ta tanadi matakai da aka inganta na dakile takunkumai daga kasashen waje, da tsararrun matakan...
    A yau Litinin ne kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Guo Jiakun, ya jagoranci taron manema labarai na yau da kullum, inda wani dan jarida ya yi tambaya game da ko Sin za ta shiga tattaunawa da Amurka, game da hakan Guo Jiakun ya ce, a ko da yaushe kasar Sin na da imanin cewa, kiyaye...
    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Juventus ta raba gari da mai horas da ’yan wasanta, Thiago Motta, yayin da ko kaka ɗaya bai cika ba a kwantaragin da ya ƙulla da ƙungiyar ta Italiya. A cewar Jaridar wasanni ta La Gazzetta dello da Gidan Talabijin na Sky Sport, Juventus ta maye gurbin Thiago Motta da tsohon...
    Rundunar ‘yan sandan Birnin Tarayya ta ce ta kama damin alburusai 488 da aka ɓoye a jarkar manja a tashar mota. Mataimakin kwamishinan ‘yan sandan da ke kula da sintiri na musamman a Abuja, DCP Ishaku Sharu, ne ya bayyana hakan lokacin da yake holen wanda ake zargin a ofishin rundunar a ranar Litinin. Matasa...
    “Lokacin da aka samu rahoton faruwar lamarin, jami’an ‘yansanda ƙarƙashin jagoranci babban baturen ɗansanda (DPO) sun ziyarci wurin inda suka ɗauki gawar zuwa babban asibitin Darazo, a nan ne likita ya tabbatar da mutuwarsa,” Wakil ya shaida.   Yayin da bincike ya ci gaba da gudana, a ranar 20 ga watan Maris, ‘yansanda suka kama...
    Wasu fusatattun matasa sun daka wawa kan kayan abincin tallafin azumi da ɗan Shugaba Nijeriya, Seyi Tinubu zai raba a Jihar Gombe. Aminiya ta ruwaito cewa duk da cewa bai kai ga zuwa jihar ta Gombe ba, amma kayan abinci da zai raba tuni sun isa jihar. Gwamnonin PDP sun garzaya Kotun Ƙoli kan dakatar...
    Sojojin HKI sun kai wasu hare-hare akan sansanin sojan Sanamain dake gundumar Dara’a a kudancin kasar Syria. Tashar talabijin din da “ Akhbariyyah” ta Syria ta sanar a yau Litinin cewa; sojojin Isra’ila sun kai hari akan sansanin soja na “Sanamain” wanda yake a gundumar Dar’a, kuma an ga jiragen sama na ‘yan mamaya masu...
    Jami’iyyar adawa ta “Turkish National Party” ta bayyana cewa dan takararta a zaben shugaban kasa na 2028 shi ne magajin garin Istanbul Akram Imam Ugulu wanda a halin yanzu yake a gidan kurkuku. Imam Uglu dan shekara 53 shi ne muhimmin dan takarar shugaban kasa a tsakanin ‘yan hamayya da ake hasashen cewa  zai iya...
    Babban kamfanin fasahar nan na Amurka wato Apple, ya sanar da shirinsa na zuba jarin da ya kai kudin Sin yuan miliyan 720, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 100.31, a fannin samar da makamashi mai tsafta da ake iya sabunta amfani da shi a kasar Sin. Wata sanarwa da kamfanin ya fitar a Litinin din nan,...
    Kafafen watsa labarun HKI sun ambaci cewa; An kai hari nau’i biyu, da ya hada amfani da motar take mutane da kuma bude wuta daga bindiga. Harin da aka kai a kusa da yankin “Yukna’am Iliyat” dake gabashin garin Haifa, ya yi sanadiyyar halakar wani dan share wuri zauna da kuma jikkata wani guda daya....
    Babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin, wato CMG ya gabatar da taron tattaunawar kasa da kasa mai taken “Sin a lokacin bazara: More damammakin da take gabatarwa ga duniya” a ran 20 ga watan nan da muke ciki a kasar Rasha. Kuma Shugaban CMG Shen Haixiong ya gabatar da jawabi ta kafar...
    Shugaban majalisar dokokin kasar Lebanon Nabih Barri ya jaddada cewa; HKI tana kokarin jefa Lebanon cikin tarkon kulla alaka da ita, yana mai jaddada cewa; Ko kadan Lebanon ba ta kama wannan hanyar ba. Nabih Barri ya bayyana yadda wasu rahotanni daban-daban suke Magana akan cewa Amurka tana kai gwauro da mari, domin ganin an...
     Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa; Iran tana cikin shirin ko-ta-kwana akan duk wani abu da zai iya bijirowa, kuma a halin yanzu ba batun yaki ake yi ba. A wata ganawa da ministan harkokin wajen na Iran ya yi da tawagar kungiyar agaji ta “Red Cross” a karkashin jagorancin shugabanta Koliband, ministan harkokin...
    Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya naɗa Sarkin Kauru, Mai Martaba Alhaji Ya’u Shehu Usman, a matsayin Amirul Hajj kuma jagoran tawagar jami’an jihar don aikin Hajjin 2025. A cikin wata sanarwa, Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamna, Ibraheem Musa, ya bayyana cewa naɗin wannan basarake mai daraja ya biyo bayan  sadaukarwarsa, da gaskiya, ...
    Shirin ya fuskanci suka sosai a shafukan sada zumunta, inda suke ganin cewa, Arewa ta cancanci kulawa fiye da haka, yayin da wasu kuma ke ganin tallafin ya dace.   A wani faifan bidiyo da Daily Trust ta gani, an ga wasu fusatattun matasa suna kwashe kayan abinci a wata babbar mota da aka ajiye...
    Mataimakin firaministan kasar Sin He Lifeng ya bayyana a jiya Lahadi cewa, kasar Sin za ta ci gaba da bude kofa ga kasashen waje, kuma tana maraba da kamfanonin kasashen duniya da su fadada zuba jari a kasar Sin, domin zurfafa samun moriyar juna da samun nasara tare. He ya bayyana hakan ne a wata...
    A cewar takardun kotun, gwamnonin suna neman a bayyana cewa, hukuncin da shugaban kasa ya zartar ya saɓa wa sashe na 1 (2), 5 (2), da 305 na kundin tsarin mulkin 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima).   Sun kuma kara da cewa, shugaban kasa ba shi da wani iko ko kadan na dakatar da...
    Wasu daga cikin gwamnonin jam’iyyar adawa ta PDP sun maka Shugaba Bola Tinubu a Kotun Ƙoli kan dakatar da Gwamnan Ribas, Similanayi Fubara. Gwamnonin sun garzaya kotun ne domin neman fatawa game da abin da sashe na 305 na kundin mulkin ƙasar ke nufi. Ban bai wa majalisa haƙuri ba — Natasha Juventus za ta...
    Sanata mai wakilatar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta musanta batun da ake yaɗawa cewa ta bai wa Majalisar Dattawa haƙuri. A wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, Natasha ta ce tana na kan batunta, kuma ba za ta taɓa bai wa majalisar haƙuri a kan gaskiyarta ba. Fursunoni 12 sun tsere bayan fasa...
    Al’ummar duniya mai kyakkyawar makomar bai daya na nufin makomar kowace al’umma da kowace kasa tana da nasaba da juna. Hakan na nufin ya kamata mu yi rayuwa tare duk rintsi duk wuya, muna more daukaka da wahala tare da kuma kokarin mayar da duniyarmu al’umma guda mai jituwa, inda za mu mai da burin...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Cristiano Ronaldo ya zura ƙwallo a wasan da Portugal ta doke abokiyar karawarta ƙasar Denmark a daren ranar Lahadi, ƙwallon ita ce ta 929 da tsohon ɗan wasan na Manchester United ya jefa a tarihinsa na ƙwallon ƙafa, duk da cewar ya ɓarar da bugun daga kai sai mai tsaron gida a wasan da Portugal...
    Hukumar yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) ta kama wata mata ‘yar ƙasar Indiya mai suna Neetu Neetu, mai shekara 42, a filin jirgin saman Mallam Aminu Kano, ɗauke da hodar iblis mai nauyin kilo 11 da aka ɓoye a cikin ledojin da ke kama da kwallon alawar cakulati. An cafke...
    Aƙalla fursunoni 12 ne suka tsere baya sun fasa wani gidan yari da ke garin Kotonkarfe a Jihar Kogi. Kwamishinan watsa labarai na jihar, Kingsley Fanwo ya tabbatar da aukuwar lamarin. Za mu farfaɗo da Madatsar Ruwa ta Biu — Zulum Wasu manyan ’yan Nijeriya sun yi wa Gwamna Radda ta’aziyya a Saudiyya Mista Fanwo...
    Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya jaddada kudirin gwamnatinsa na sake farfaɗo da Madatsar Ruwa ta Biu da aka daɗe da watsi da ita domin bunƙasa noman rani da nufin samar da wadataccen abinci a Kudancin Borno da ma Jihar ta Borno gaba ɗaya. Zulum ya yi wannan alkawarin ne a yayin wata ziyarar...
    Iran ta yi gargadin cewa zaluncin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi wa kasar Labanon na da matukar hadari kuma barazana ga zaman lafiya da tsaron kasa da kasa, inda ta bukaci kasashen duniya da su dauki matakin da ya dace. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmaeil Baghaei ya yi kakkausar suka kan hare-haren...
    Ebrahim Rasool, jakadan Afirka ta Kudu da gwamnatin Trump ta kora, ya samu tarba a wannan Lahadin daga daruruwan magoya bayansa da suke rera wakoki  domin karrama shi a filin jirgin sama na Cape Town. Jama’a sun kewaye Rasool da matarsa ​​Rosieda bayan isowarsu, yayin da ‘yan sanda suka yi musu rakiya har zuwa tashar...
    Wani Sufeto Dansandan da ke aiki a Jihar Kuros Ribas, ya harbe matar abokin aikinsa har lahira tare da jikkata wasu mutane biyu a harbe-harben da ya yi a ranar Lahadi. Mai magana da yawun rundunar, SP Irene Ugbo, ta tabbatar da faruwar lamarin ga Labarai a birnin Kalaba, inda ta bayyana cewa jami’an Dansandan...
    Dubban mutane ne a birnin Amman babban birnin kasar Jordan suka gudanar da zanga-zanga bayan sallar Juma’a domin yin Allah wadai da sake dawo da laifukan da Isra’ila ke aikatawa a Gaza. A rahoton factjo, dubban mutane sun bayyana goyon bayansu ga al’ummar Gaza a wani gagarumin maci na wannan Juma’a. Mahalarta tattakin sun yi...
    Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Turai sun ce, tsagaita bude wuta nan take a Gaza ya zama dole. Da yake magana a wani taron kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, mataimakin babban sakataren majalisar kan  harkokin siyasa Khaled Khari, ya ba da rahoto game da tabarbarewar al’amura a Gaza bayan da Isra’ila ta karya yarjejeniyar...
    Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya sanar da cewa, yara a Gaza suna fuskantar matsakar kwakwalwa da ba a taba ganin irinsa ba a kan kananan yara. “Ba mu da wani bayani a tarihin wannan zamani dangane da ke bukatar tallafin lafiyar kwakwalwa kamar yaran Gaza,” in ji mai magana...
    Ƴansandan sun gayyaci Sanata Sunday Karimi domin bayani kan zarginsa na cewa ƙungiyar leƙen asirin ƙasar Rasha ta KGB ta samu shiga cikin Majalisar Dokoki, wanda ke barazana ga tsarin dimokuraɗiyya a Nijeriya. Zargin ya samo asali ne daga rahoton da Sanata Karimi ya raba akan ƙungiyar ta WhatsApp a Majalisar Dattijai a ranar 23...
    Wasu manyan ’yan Nijeriya da suka tafi Umarah sun yi wa Gwamnan Katsina Dikko Umar Radda ta’aziyya a Saudiyya. A safiyar Lahadi ce dai Allah Ya karɓi rayuwar mahaifiyar Gwamnan, Hajiya Safara’u Umaru Baribari bayan shafe tsawon lokaci tana jinya a Jihar Katsina. Wata mata ta haifi jaririn da ba nata ba NAJERIYA A YAU:...
    Wata mata mai suna Krystena Murray ’yar Amurka, wadda ta ɗauki ciki tare da haife jariri namiji ba tare da sanin cewa ba ɗanta ba ne, ta fara ɗaukar matakin shari’a a kan wani asibitin da ke taimaka wa mata samun ciki ta hanyar dashen ɗantayi (IBF). Matar tana zargin asibitin da yi mata dashen...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya yi kira ga kasashen duniya da su kawo karshen rikicin da Isra’ila ke ci gaba da haifarwa a yankin gabas ta tsakiya. A wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Masar Badr Abdelatty, Araghchi ya yi Allah wadai da sabbin hare-haren da Isra’ila ke kai wa...
    Kungiyar gwagwarmayar Falastinawa ta Hamas ta fitar da wata sanarwa dangane da shahadar Salah al-Bardawil, mamba a ofishin siyasa na kungiyar kuma wakilin majalisar dokokin Falasdinu. A rahoton tashar Al-Alam, bayanin Hamas yana cewa: Dr. Salah Al-Bardawil, wanda ya yi fice a fagen siyasa, kafofin watsa labarai, da fagage na kasa da kasa, kuma ake...
    Kungiyar da ke sa ido da kare hakkin dan adam ta Syria (SOHR) ta fitar da fayafan bidiyo guda hudu da ke dauke da hotunan azabtarwa da kisa da jami’an tsaron sabuwar gwamnatin kasar  karkashin kungiyar Tahrir Sham  suke aiwatarwa a kan fararen hula tsiraru marasa rinjaye a kasar. Kungiyar da ke sa ido kan...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Hausawa sun yi gaskiya da suka ce ‘yawan mutane su be kasuwa’. Yawan hada hadar da ake yi tsakanin ‘yan kasuwa da abokan cinikinsu na ɗaya daga cikin abun da zai tabbatar maka kasuwanci na gudana kamar yadda ake so. Sai dai da zarar an ce watan Ramadana...
    A yau Lahadi, kwararren masanin tattalin arziki dan kasar Amurka Jeffrey Sachs ya bayyana cewa, matakan kariyar cinikayya da Amurka ke aiwatarwa babban kuskure ne. Jeffrey wanda ya halarci dandalin bunkasa kasa na Sin na shekarar nan ta 2025 a birnin Beijing, ya kara da cewa Amurka na kara karkata ga salon kariyar cinikayya karkakin...
    A yau Lahadi firaministan kasar Sin Li Qiang, ya gana da dan majalisar dattawan Amurka sanata Steve Daines, tare da wasu ‘yan kasuwan Amurka da suka zo kasar Sin, don halartar dandalin bunkasa kasa na Sin na shekarar nan ta 2025 wanda ya gudana a nan birnin Beijing. (Mai fassara: Saminu Alhassan) Daga kanmu,...
    A yau Lahadi ne aka bude taron shekara-shekara na dandalin tattauna raya kasa na kasar Sin na 2025 a nan birnin Beijing, taron da cibiyar binciken raya kasa ta majalisar gudanarwar kasar Sin ta shirya tare da hadin gwiwar asusun binciken raya kasa na kasar Sin. Firaministan kasar Sin Li Qiang ya halarci bikin bude...
    Wata tanka ɗauke da man fetur ta kama da wuta yayin da ta ke sauke mai a gidan mai na A.A. Rano da ke Kontagora, a Jihar Neja. Lamarin ya faru ne da da misalin ƙarfe 7 na daren ranar Lahadi kusa da Asibitin Gaba. Gwamnonin Arewa sun yi wa Radda ta’aziyyar rasuwar mahaifiyarsa ’Yan...
    4 – Kar ki kasance kullum a cikin bacin rai ko fushi da mijinki, domin fushi kofa ce ta kowane sharri. 5 – Kar ki kasance mai girman kai wajen bashi hakkokin zamanku, abin da yake so ko da baki so matukar bai saba wa addini ba ki yi masa. 6 Ki nuna wa mijinki...
    Shugqbqn kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen sayyed Abdulmalik Badaruddin Huthi ya bayyana cewa tura wani kataparen jirgin ruwan yaki zuwa gabas ta tsakiya wanda shugaban kasar Amurka yayi wata gazawace. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalti Alhuthi yana fadar haka yau Lahadi a wani jawabin da ya gabatar ,inda yake bayyana irin...
    Shugaba hukumar makashin Nukliya na kasar Iran Mohammad Islami ya bada sanarwan cewa a ranar 8 ga watan Afrilu mai zuwa. Yace hukumarsa za ta kaddamar da sabbin magunguna da ta samar tare da amfani da makamashin Nukliya, a dai dai na ranar makamashin Nukliya ta kasar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ta...
    A gobe Litinin 24 ga watan Maris ne tawagogin masu tattaunawa na kasashen Amurka da Rasha zasu hadu a birnin Rayida na kasar Saudiya don ci gaba da tattaunawan da suka fara a yan makonnin da suka gabata dangane da yakin da ke faruwa a Ukraine, shekaru fiye da 3 da suka gabata, da kuma...
    A jiya Asabar 22 ga watan nan, jakadan kasar Sin a Amurka Xie Feng, ya amsa gayyatar halartar taro na 2 na tattaunawar sassan Sin da na Amurka game da batun tattalin arziki karkashin cibiyar Jimmy Carter, inda ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo.  A cikin jawabinsa, jakada Xie Feng ya ce ko kadan,...
    Ma’aikatar kasuwanci ta kasar Afganistan ta bada sanarwan cewa kasar Iran ce a gaba da dukkan kasashen makobta da kasar Afganisatan wacce tafi shigo da kayakinta cikin kasar a shekara ta 1403 ta kalandar Iraniyawa da ta kare. Kamfanin dillancin labaran Parstoday na kasar Iran ya nakalto kakakin ma’aikatar kasuwanci ta kasar Afganistan Abdussalam Jawad...
    Hukumar birnin istambul ta bada sanarwan dakatar da Akram Imamoglu daga matsayinsa na magajin garin birnin Istambul na wucin gadi, har zuwa lokacinda za’a tabbatar da kubutarsa daga abubuwan da aka zarginsa da su. Tashar talabijin ta Almayaddeen ta kasar Labanon ta nakalto mahukunta a birnin Istambul na bada labarin cewa za’a zabi wanda zai...
    Ya sanar cewa karamar hukumar ta kuduri aniyar daukar tsauraran matakai don dakile wannan barazana ta hanyar tura jami’an GOSTEC da Operation Hattara don inganta tsaro.   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don...