2025-02-22@22:01:17 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1174
«Sanata Marshal»:
Wasu ’yan bindiga da ake zargin ’yan fashi ne sun harbe wasu jami’an ’yan sanda biyu a ofishinsu da ke Kolere a Ƙaramar Hukumar Fune ta Jihar Yobe. Aminiya ta ruwaito cewa, a watan Janairun da ya gabata ne gungun wasu ’yan ta’adda suka harbe DSP Ali Pindar, wani jami’in ɗan sanda da ke ofishin....

’Yan Wasan Motsa Jiki Na Asiya Sun Yi Murnar Bikin Sabuwar Shekara Bisa Kalandar Gargajiya Ta Sin A Harbin
An gabatar da bikin mu’ammalar al’adu a jiya Litinin a birnin Harbin da ake wa lakabin “Birnin kankara”, yayin da ake gudanar da gasar wasannin motsa jiki na lokacin hunturu ta Asiya karo na 9 a birnin. An yi wannan gaggarumin biki ne bisa jigon “bikin sabuwar shekara ta kalandar gargajiya ta kasar Sin, wato...
A ci gaba da kokarinta na samun tagomashi a fannin tattalin arziki da ci gaban jihar ta hanyar kawo sauyi a harkar noma, gwamnatin jihar Jigawa na shirin hada gwiwa da wani kamfani da ke samar da dabino da bayar da shawarwari a harkar noma, wanda ke da ofishi a Najeriya a kasar Saudiyya domin...
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka. Sharhin bayan labarammu zai yi magana ne dangane da barazanar shugaban kasar Amurka ga JMI “Ko ta yarda da ta zauna kan teburin tattaunawa da ita kan shirinta na makamashin nukliya ko kuma ya tura HKI ta fermata da yaki’. Wanda ni tahir amin zan karanta. ///… A...
Shugaban Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya gargaɗi Hamas da ta yi gaggawar sakin Isra’ilawan da take tsare da su a hannunta. Netanyahu ya ce ya bai wa ƙungiyar wa’adin zuwa ranar Asabar da ta saki Isra’ilawan da take garkuwa da su kamar yadda aka amince a yarjejeniyar tsagaita wuta da ke tsakaninsu ta tanada. Gwamnatin Kano...
Masu zanga-zangar wadanda ke dauke da alluna da rubuce-rubuce daban-daban sun ce, dole ne kamfanin ya samar da mafita mai dorewa tare da maido da wutar lantarki a tashar wutar lantarki ta ‘Kwara Poly feeder’ da ke rarraba wutar ga al’ummomin yankin.
Kungiyar masu samar da motoci ta kasar Sin CPCA, ta ce bangaren fitar da motoci daga kasar Sin zuwa kasashen ketare, ya ci gaba da samun tagomashi a shekarar 2024. A cewar CPCA, kasar Sin ta fitar da jimilar motoci miliyan 6.41 zuwa kasashen waje a bara, adadin da ya karu da kaso 23 bisa...
Har kullum, na kan ce, ci gaban kasar Sin wata dama ce ba kalubale ba. A matsayin ’yar Afrika, ci gaban kasar Sin daidai yake da ci gaban nahiyar Afrika domin duk wata nasara da ta samu, ba ta kyashin kai wa Afrika, kuma burinta shi ne ta ga nahiyar ta amfana, ta samu ci...
Tafida, ya bayyana godiyar Gwamna Nasir Idris ga Sakatarorin kan irin gudunmuwar da suka bayar ga inganta bangaren Ilimi a matakin kananan hukumomi da kuma goyon baya ga gwamnatinsa a kan jagorancin al’ummar jihar. Daga karshe, Gwamnan ya gode wa Sakatarorin kan irin yadda suka sadaukar da kansu wajen kawo cigaba a bangaren Ilimi...
Kungiyoyin da suke dauke da makamai sun kashe fararen hular da ba su gaza 55 ba a wani hari da su ka kai wa wasu kauyuka da sansanin ‘yan hijira a Arewacin DRC. Mahukunta a yankin na Arewacin DRC sun ambaci cewa wasu masu dauke da makamai na kungiyar CODECO sun kai wa wasu kauyuka...
Da marecen jiya Litinin ne aka yi tattaunawa ta wayar tarho a tsakin ministocin harkokin wajen Iran da na Saudiyya akan shirin Donald Trump na korar Falsdinawa daga Gaza,inda kasashen biyu su ka ki amincewa da shi. Ministan harkokin wajen na Iran Abbas Arakci, da takwaransa na Saudiyya Faysal Bin Farhaan, sun nuna kin amincewarsu...
Gwamnatin Kano ta bayyana aniyarta na kafa Hukumar Kula da Masu Buƙata ta Musamman a wani mataki na tabbatar da adalci a tsakanin al’ummar jihar. Kwamishiniyar Mata da Yara masu bukata ta musamman, wacce Daraktar Jin Daɗi ta ma’aikatar, Binta Muhammad Yakasai, ta wakilta, ta bayyana hakan yayin wani taron tattaunawa na yini guda da...
Nijeriya ta zama ƙasa ta 140 a cikin jerin ƙasashen da aka fi tafka cin hanci da rashawa a duniya a shekarar 2024 a cewar ƙungiyar Transparency International. A cikin rahoton wanda ta fitar a yau, Transparency ta ce Denmark ce ƙasar da ta kasance wadda ba ta fuskantar matsalar ta cin hanci da rashawa....
Nijeriya ta zama ƙasa ta 140 a cikin jerin ƙasashen da aka fi tafka cin hanci da rashawa a duniya a shekarar 2024 a cewar ƙungiyar Transparency International. A cikin rahoton wanda ta fitar a yau, Transparency ta ce Denmark ce ƙasar da ta kasance wadda ba ta fuskantar matsalar ta cin hanci da rashawa....
An ce, tsakanin shekarar 2000 zuwa 2023, kasar Sin ta samar da rance da yawansa ya kai kimanin dalar Amurka biliyan 43 ga kasashen Afirka, don su raya bangaren samar da wutar lantarki. Kana a shekarun nan, kamfanonin kasar Sin sun gudanar da dimbin ayyukan samar da wutar lantarki a nahiyar Afirka, kamarsu madatsar ruwa...
Gwamnatin Jihar Jigawa ta kara jaddada kudurinta na yin hadin gwiwa da wani kamfanin sarrafa dabino da kayan marmari domin inganta noman dabino da alkama a jihar. Gwamna Umar Namadi ya bada wannan tabbaci a lokacin da tawagar Babban Daraktan kamfanin, Dakta Abubakar Musa Bamai ta ziyarci shi a gidan Gwamnati dake Dutse, Babban...
Honorbaul Isika Ibrahim ya zama sabon Mataimakin Mai Tsawatarwa na Majalisar Wakilai. Majalisar Tarayya ta nada shi ne bayan rasuwar Honorabul Oriyomi Onanuga, mai rike da mukamin. Shugaban Majalisar, Honorabul Tajuddeen Abbas ne ya sanar da haka a yayin zaman majaliasr a safiyar Talata. A watan Janairu ne Allah Ya yi wa Onanuga rasuwa. Dukkansu...
ATM da ke cikin shalƙwatar banki: Za a caji N100 kan duk wani cire kuɗi na N20,000. ATM da ke wajen shalƙwatar banki: Za a caji N100 kan N20,000 da kuma ƙarin haraji har zuwa N500. Cire kuɗi a ƙasashen waje: Za a yi caji bisa ga yawan kuɗin da mai ATM ya buƙata. CBN...
Kafafen watsa labarun HKI sun ce; Barazanar da ake yi wa kungiyar Hamas ba ta wani tasiri a gare ta. Kafafen watsa labarun na HKI suna yin tambaya akan yadda Hamas din take isar da sakwanni a fakaice ga Isra’ila a yayin bikin mika fursunoni da take shiryawa. Tashar talabijin din ta 12: ta ambaci...
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi barazanar cewa matukar Falasdinawa ba su saki fursunonin Isra’ila ba daga nan zuwa Asabar, to za a kawo karshen tsagaita wutar yakin da aka yi, da komawa yaki. Shugaban kasar ta Amurka ya shata wa’adin 12: 00 Na ranar Asabar a matsayin lokacin karshe na mika fursunonin. Shugaban...
Ɗan Majalisar PDP Ya Sauya Sheka Zuwa APC
Gidauniyar tunawa da Sir Ahmadu Bello ta sanar da cewa za a gudanar da taron Karrama Sir Ahmadu Bello karo na 11 a ranar Asabar, 22 ga Fabrairun 2025, a Bauchi. Wannan taron, wanda ke tunawa da rayuwa da gado na Sir Ahmadu Bello KBE, Sardaunan Sokoto da Firaministan tsohuwar Yankin Arewa,...
Jami’ar Bayero Ta Shirya Bikin Yaye Ɗalibai Karo Na 39
Dan Majalisar Tarayya mai Wakiltar Zangon Kataf/Jaba daga Jihar Kaduna, Honorabul Amos Gwamna Magaji ya sauya sheka daga jam’iyyar adawa ta PDP zuwa APC mai mulki. A safiyar Talata Shugaban Majalisar, Abbas Tajuddeen ya sanar da sauya shekar, yana mai bayyana rikicin cikin gidan PDP a mastayin dalilin ficewar dan majalisar daga jam’iyyar. Dan majalisar ya ...
Dalibai 179 za su samu shaidar Digiri Mai Daraja ta Ɗaya a yayin bikin yaye ɗalibai na Jami’ar Bayero ta Kano (BUK). Shugaban Jami’ar Bayero, Farfesa Sagir Abba, ya bayyana cewa dalibai 4,402 ne za a yi bikin yaye su a ranar farkon, inda a za a ba su shaidar kammala Digirin farko da Difloma...
Honorbaul Isika Ibrahim ya zama sabon Mataimakin Mai Tsawatarwa na Majalisar Wakilai. Majalisar Tarayya ta nada shi ne bayan rasuwar Honorabul Oriyomi Onanuga, mai rike da mukamin. Shugaban Majalisar, Honorabul Tajuddeen Abbas ne ya sanar da haka a yayin zaman majaliasr a safiyar Talata. A watan Janairu ne Allah Ya yi wa Onanuga rasuwa. Dukkansu...
Honorbaul Isika Ibrahim ya zama sabon Mataimakin Mai Tsawatarwa na Majalisar Wakilai. Majalisar Tarayya ta nada shi ne bayan rasuwar Honorabul Oriyomi Onanuga, mai rike da mukamin. Shugaban Majalisar, Honorabul Tajuddeen Abbas ne ya sanar da haka a yayin zaman majaliasr a safiyar Talata.
Abin Kunya Ne Nijeriya Har Yanzu Ba Ta Iya Ciyar Da Kanta – Gwamna Bala
’Yan sanda sun kama gungun wasu makiyaya 47 ɗauke da makamai kan zargin kutse da yunƙurin aikata kisa a Kwalejin Kimiyya da Ƙere-kere ta Tarayya ta Umaru Waziri da ke Shinkafi a Jihar Kebbi. Kakakin ’yan sandan Jihar Kebbi, CSP Nafi’u Abubakar ya ce makiyayan sun haɗa baki ne da wani mutum wajen rusa katangar...
Dalibai 179 za su samu shaidar Digiri Mai Daraja ta Ɗaya a yayin bikin yaye ɗalibai na Jami’ar Bayero ta Kano (BUK). Shugaban Jami’ar Bayero, Farfesa Sagir Abba, ya bayyana cewa dalibai 4,402 ne za a yi bikin yaye su a ranar farkon, inda a za a ba su shaidar kammala Digirin farko da Difloma...
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Sirrin nasarar da Iran ta samu shine haɗin kai da kasancewar mutane a cikin kowane fagen neman ci gaba Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa juyin juya halin Iran ya samu nasarar korar azzalumai daga kasar Iran ce, kuma sirrin ire-iren nasarorin da aka samu bayan nasarar...
Bikin zagayowar cikan shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a Iran ya jaddada kare tushen tsarin kasar da gwagwarmaya Dukkanin sassan kasar Iran sun gudanar da zanga-zanga da dukkanin bangarori na al’umma suka halartar domin tunawa da zagayowar cikan shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar. Tun daga...
Shugaban kasar Amurka ya bayyana cewa: Akwai yiwuwar nan gaba kasar Ukraine ta iya zama wani bangare na tsarin tsaron kasar Rasha Shugaban Amurka Donald Trump ya fada a ranar Litinin cewa: Dole ne kasar Ukraine ta tabbatar da tsaron kudaden Amurka da aka zuba a cikinta, saboda zata iya zama karkashin kasar Rasha wata...

Sojojin Mamayar Isra’ila Suna Ci Gaba Da Murkushe Falasdinawa A Birnin Tulkaram Da Ke Gabar Yammacin Kogin Jordan
Sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da rusa ababen more rayuwa a birnin Tul-karam da sansanoninsa na Falasdinu tare da kama Falasdinawa da tilasta wa jama’a yin gudun hijira Sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da kai hare-hare kan birnin Tul-Karam da sansanoninsa guda biyu Tul-karam da Nourul- Shams a rana ta 16 a jere,...
Wani sanatan Amurka yana barazana ga shugaban kasar Tunisiya da neman rusa nasarar dimokuradiyyar kasar Sanatan Amurka Joe Wilson, dan majalisar wakilai daga shiyar kudancin jihar Carolina, ya kaddamar da hari kan shugaban kasar Tunusiya Qais Sa’id, inda ya dauke shi a matsayin “dan mulkin kama karya” tare da yin kira da a kakabawa Tunisiya...
Kamfanin Dangote na Peugeot Automobiles Nigeria Limited (DPAN), wanda ke kera wa da tallata motocin Peugeot a Nijeriya, ya fara tarawa da haɗa sabuwar Peugeot 3008 GT a masana’antarsa da ke Kaduna. Peugeot 3008 GT, mai injin 1.6-lita turbo mai ƙarfi, ya ƙara yawan jerin motocin da ake haɗawa a masana’antar DPAN, wanda ya ya...
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta jinkirta sakin sauren karin ‘yan Isra’ila da take garkuwa dasu “har sai an ga abinda hali ya yi”, saboda keta dokar da Isra’ila ta yi na tsagaita wuta a Gaza. Sanarwar da bangaren soji na Hamas ta fitar bakin kakakinta Abu Obeida, ta bayyana cewa ‘’fiye da mako uku...
Iran, ta la’anci kalaman foraministan Isra’ila dake cewa a kasa kasar Falasdinu a cikin kasar Saudiyya. Ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi ya yi kakkausar suka ga kalaman na Benjamin Netanyahu da ke nuna cewa a kafa kasar Falasdinu a Saudiyya, yana mai danganta hakan da tsokana da kuma barazana ga zaman lafiya da tsaro...
Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa shirin korar al’ummar Zirin Gaza zai hada da kwace ‘yancinsu na komawa kasarsu. Trump ya fada a wata hira da tashar Fox News cewa shirin da yake yi a kan Gaza ya kunshi fitar da daukacin al’ummar yankin da kuma sake gina abin da ya kira ‘’Sake farfado...
Gungun aiki na Majalisar Dinkin Duniya kan tsare mutane ba bisa ka’ida ba, ya yi kira da a gaggauta sakin hambararen shugaban kasar Nijar, Mohamed Bazoum da matarsa Hadiza. Tun a watan Yulin 2023 ne ake tsare da Bazoum a wani reshe na fadar shugaban kasar da ke Yamai, inda Likitansa ne kawai aka yarda...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Dakta Zainab Muhammad na daga cikin matan Arewacin Najeriya da ta jajirce tare da ƙudirin cika burinta na karantar kimiyya duk da ƙalubalen da wasu matan yankin ke bayyana cewa suna fuskanta wurin karantar fannin. Dakta Zainab ba kimiyya kawai ta karanta ba, ta karanci ɗaya daga cikin...
Kamfanin kula da sufurin layin dogo na kasar Sin, ya ce jarin manyan kadarori da kasar ta zuba a bangaren layin dogo ya kai yuan biliyan 43.9, kwatankwacin dala biliyan 6.12, a watan Janairun bana. A cewar kamfanin, adadin ya karu da kaso 3.7 bisa dari idan aka kwatantan da makamancin lokacin a bara. A...
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya rantsar da sabon Sakataren Gwamnatin Kano, Umar Farouk Ibrahim. An dai rantsar da sabon Sakataren Gwamnatin ne a wani ƙwarya-ƙwaryan biki da aka gudanar ofishin gwamnan. ’Yan bindiga sun kashe fasto a Gombe An shiga nuna wa juna yatsa tsakanin Hamas da Isra’ila Aminiya ta ruwaito cewa, Kwamishinan Shari’a kuma...
Kungiyar kula da harkokin jigilar kayayyaki da sayen kayayyaki ta kasar Sin ta samar da adadin sana’o’in adana kayayyaki na Sin a watan Janairun da ya gabata cewa, wanda ya nuna cewa, yawan bukatun ajiye kaya a Sin ya bunkasa cikin sauri duba da karuwar bukatun sayayya a lokacin bikin sabuwar shekara, kuma sana’o’in adana...
A kokarinta na karfafa hadin gwiwa da tabbatar da gaskiya da rikon amana, hukumar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Jigawa (JG-PCACC) ta kai ziyarar ban girma ga takwararta da ke Abuja. Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban sashen hulda da jama’a na JG-PCACC Alhaji Yusuf Suleiman...
’Yan bindiga sun kashe wani fasto, Rabaran Bala Galadima yayin harin da suka kai garin Lubo da ke Ƙaramar Hukumar Yamaltu Deba a Jihar Gombe. Aminiya ta ruwaito cewa, ’yan bindigar sun kuma yi fashin kuɗi har Naira dubu 300 a yayin harin da suka kai cikin dare wayewar gari Lahadi. Wani mazaunin garin ya...
NUC Ta Dakatar Da Bayar Da Lasisin Gina Sabbin Jami’o’i Masu Zaman Kansu
Hamas ta sanar da yanke shawarar jinkirta sakin fursunonin Isra’ila nan gaba har sai abin da hali ya yi. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da ƙungiyar gwagwarmaya ta Falasɗinu ta fitar tana mai cewa an ɗauki matakin ne a matsayin mayar da martani ga keta yarjejeniyar tsagaita wuta da Isra’ila ta yi. Dalilin da...
A yau Litinin, kasar Sin ta sanar da sabbin ka’idojin kyautata kare sirrikan jama’a yayin kare tsaron al’umma. Firaministan kasar Sin Li Qiang ne ya rattaba hannu kan wata dokar majalisar gudanarwar kasar, domin fitar da ka’idojin, wadanda za su fara aiki daga ranar 1 ga watan Afrilu. Ka’idojin na da nufin tafiyar da harkokin...