2025-02-22@22:27:32 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1174
«Farfesa Fagge»:
“Duk da cewa an dan samu raguwar kai hare-hare amma har yanzu ana samun wasu su shiga su kashe mutane sannan su tafi da wasu domin kuɗin fansa” in ji ɗan majalisar. Sannan ya kuma kalubalanci rashin hanya mai kyau a yankunan wanda a cewarsa hakan ma yana kawo tsaiko wajen fatattakar yan ta’adda. Danlami...
Sannan dadin abin aka fada amma mene ne illar da ka iya biyo bayansa? Shin hakan ma batun yake a ilmance ko kuwa? Wannan ta sa da zarar haihuwa ta gabatowa mace kowa sai ka ga shawara yake ba ta akan komai ma, musamman ma atsakaninsu mata, Eh munsan kuna yi ne bisa kyakkyawar manufa...
Wannan bayanin da Babangida ya yi a kan zaɓen ya haifar da maganganu a kan irin rawar da Abacha ya taka wajen soke zaɓen da yadda ya hana Nijeriya komawa mulkin dimokuraɗiyya a wancan lokacin. Marigayi Sani Abacha dai ya yi mulkin soja a Nijeriya daga shekara ta 1993 zuwa 1998 da ya rasu.
Jam’iyyar PDP mai ci a Jihar Osun ta lashe zaɓen dukkan kujerun ƙananan hukumomi jihar guda 30 da na kansiloli 332 da aka gudanar yau Asabar. Shugaban hukumar zaɓen jihar OSSIEC, Hashim Abioye ne ya sanar da sakamakon a wani taron ganawa da manema labarai da ya yi a jihar. Wani mutum ya yi wa...
Rundunar ’yan sandan Jihar Legas ta cafke wani mutum mai shekaru 28, Samuel Alfred bisa zargin yi wa wata agolarsa fyaɗe har ta samu juna biyu. An cafke mutumin ne tare da wani abokinsa, Ikechukwu Obi mai shekaru 30 kan zargin wannan aika-aikar. An haifi alade mai fuskar mutum a Philippines Ko Real Madrid za...
Ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi ya bayyana a jiya Jumma’a cewa, kasar Sin tana goyon bayan tsarin ciniki cikin ‘yanci tare da zaman kungiyar ciniki ta duniya, watau WTO a matsayin wadda za ta yi uwa-ta-yi-makarbiya a kan tsarin, kuma za ta ci gaba da mara baya ga yin garambawul a kungiyar ta...
Mansa Mūsā, ko dai shi jikan ko kuma abokin wasan Sundiata wanda shi ne ya kirkiro Daular Mali yah au kan karagar mulkin ne a shekarar. A karni na 17 (1324),lokacin ne ya tafi aikin Hajjin wanda ya zama abinmagana saboda dalilai masu dama. Aikin Hajjin da ya tafi ne ya sa idon duniya ya...
Mamallakin aladiyar da ta haihu mai suna Alfredo Cardinas Junior, ya firgita bayan da ɗaya daga cikin aladun nasa ta haihu yana kallo, inda ya ji sautin kukan ɗan aladen kamar na dan-adam kuma yake kama da na jaririn ɗan-adam. Jaririn aladen mai siffar mutum yana daga cikin jarirai takwas da aladiyar Mista Cardinas ta...
Jagoran kula da harkokin tattalin arziki da kasuwanci na kasashen Sin da Amurka a bangaren Sin, wanda kuma shi ne mataimakin firaministan kasar Sin, He Lifeng, ya zanta da sakataren baitulmalin Amurka, Scott Bessent, ta kafar bidiyo jiya Jumma’a 21 ga wata, inda suka yi musanyar ra’ayoyi kan wasu muhimman batutuwan da suka shafi tattalin...
Kungiyar Hamas ta saki yahudawa 6 a marhala ta 7 na musayar fursinoni tsakaninta da HKI karo na 6 a yau Asabar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar Falasdiawan na fadar cewa, bayan wannan musaya ta 7, suna dakon a fara marhala ta biyu na yarjeniyar da ke tsakaninta da HKI....
Mutane 12 Sun Rasu A Hatsarin Mota A Neja

Amurka Ta Ce Zata Gabatar Da Nata Shawara Dangane Da Kawo Karshen Yakin Ukraine Ga Babban Zauren MDD
A karon farko tun bayan fara yaki a Ukraine tsakanin Rasha da Ukraine a shekara 2022 Amurka bata taba goyon bayan wani kuduri dangane da dakatar da yaki a Ukraine a babban zauren MDD wanda Ukraine da kuma kasashen Turai suka gabatar ba. Amma a halin yanzu ta ce zata tsara nata shawarar dangane da...
Sojojin kasa na jumhuriyar Musulunci ta Iran sun hada guiwa da sojojin ruwa don atisayen hadin guiwa wanda suka sanyawa suna Zulfikar 1403. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakain atisayen Brigadier General Alireza Sheikh yqana cewa a cikin wannan atisayen suna son gwada aiki tare da sojojin masu aiki a sama...

Yake-Yaken Kasa Da Kasa Ne Suka Mamaye Taron G20 Na Ministocin Harkokin Wajen Kungiyar A Afirka Ta Kudu
A jiya Jumma’a ce aka kammala taron kungiyar kasashen G20 a birnin johanasboug na kasar Afrika ta Kudu, kuma inda batun yake-yake a yankunan daban-daban na duniya ne suka mamaye taron. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa yakin Ukraine da Rasha Hamas da HKI, Congo da sauransu ne suka mamaye taron...
Jakadan Kasar Sin Ya Bukaci Dakatar Da Duk Wani Tashin Hankali A Gabashin Kongo
An shawarci shugabanni da aka zaba da su girmama hukuncin kotu domin tabbatar da dimokuradiyya a ƙasar. Wani malami a Jami’ar Bayero ta Kano, Farfesa Kamilu Fagge, ya bayar da wannan shawara a Kaduna, yana nuna damuwarsa kan zargin karya dokokin kotu a harkokin siyasa. Ya bayyana damuwarsa kan matakin da Gwamna Ademola Adeleke na...
A jiya Juma’a ce aka fitar da jadawalin zagayen ’yan 16 na Gasar Zakarun Turai ta bana a birnin Nyon. Hukumar Ƙwallon Ƙafar Turai, UEFA, ta tsara yadda zagayen na ‘yan 16 da zagayen dab da na kusa da na ƙarshe da zagayen dab da ƙarshe da kuma zagayen ƙarshe za su kasance. Haɗarin mota...
Manufar ita ce a kawo karshen wannan tashin hankalin ta hanyar adalci, mai dorewa, wace dukkanin bangarorin da abin ya shafa za su aminta da ita” in ji Rubio ga menema labarai, duk da cewa babu jami’an Yukiren ko na Turai a wurin tattaunawar. A wani labarin kuma, shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa ya shaida wa...
Kocin Manchester United Ruben Amorim ya bayyan cewar Kocin ƙungiyar ƙwallon kafa ta Everton David Moyes ba mutum ne wanda za a raina iyawarshi a harkar kwallon ƙafa ba, David Moyes ya na yin aiki mai kyau na farfado da Everton fiye da yadda na ke yi cikin ƙanƙanin lokaci a Old Trafford inji Amorim....
Aƙalla mutum 12 — ciki har da mata huɗu da maza takwas — sun riga mu gidan gaskiya a sanadiyyar wani mummunan haɗarin mota da ya auku a kan hanyar Lapai zuwa Agaie da ke Jihar Neja. Wani da lamarin na safiyar wannan Asabar ɗin ya faru a kan idonsa, ya shaida wa Aminiya cewa...
Sanata Sunday Marshall Katung, mai wakiltar Kudancin Kaduna a Majalisar Dattawa, ya bayyana damuwarsa kan yadda wasu mazauna yankin ke taimaka wa miyagu wajen aiwatar da ayyukan ta’addanci. Da yake magana a taron manema labarai na Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Kudancin Kaduna (SKJF) a Zonkwa, hedikwatar Ƙaramar Hukumar Zangon Kataf, Sanata Katung, ya jaddada cewa...
Premier League ranar Asabar 22 ga watan Fabrairu Eberton da Man United Premier League ranar Laraba 26 ga watan Fabrairu Man United da Ipswich English FA Cup ranar Lahadi 2 ga watan Maris Man United da Fulham.
Gwamnan Jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke, ya kaɗa ƙuri’arsa a zaɓen ƙananan hukumomi da aka gudanar a faɗin jihar a ranar Asabar. Gwamnan ya isa rumfar zaɓensa da ke Sagba/Abogunde, Ƙaramar Hukumar Ede, inda aka tantance shi kafin ya kaɗa kuri’arsa. Zaɓen, wanda ake gudanarwa don zaɓen sabbin shugabanni a ƙananan hukumomi 30 na jihar,...
Sadiq S. Abacha, ɗan Tsohon Shugaban Mulkin Soji na Najeriya, Janar Sani Abacha, ya bayyana mahaifinsa s matsayin mutum mai nagarta duk da sukar da ake yi masa har yanzu. A wani rubutu da ya wallafa a shafukan sada zumunta, Sadiq, ya ce an jima ana cin amanar mahaifinsa, amma tarihi zai yanke masa hukunci...

Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci Sun Jaddada Cewa: Zasu Kai Harin Daukan Fansa Na Alkawarin Gaskiya Kan Isra’ila
Mai ba da shawara ga kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Tabbas za a aiwatar da harin daukan fansa na “Alkawarin Gaskiya na 3” Mai ba da shawara ga babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Birgediya Janar Ibrahim Jabbari ya jaddada cewa: Tabbas za a gudanar da...

Kungiyar Hizbullah Ta Lebanon Ta Jaddada Rashin Amincewarta Da Mika Kan Kasar Ga Amurka Da Haramtacciyar Kasar Isra’ila
Kungiyar Hizbullahi ta bayyana cewa: Ba su yarda kasar Lebanon ta mika kai ga haramtacciyar kasar Isra’ila da Amurka ba Mataimakin shugaban majalisar zartaswar kungiyar Hizbullah Sheikh Ali Damoush ya jaddada cewa: Ba zasu amince kasar Lebanon, mai cin gashin kanta ta kasance karkashin dokar haramtacciyar kasar Isra’ila da Amurka a karkashin matsin lamba da...

Sojojin Gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila Suna Ci Gaba Da Luguden Wuta Kan Gabar Yammacin Kogin Jordan
Fira ministan gwamnatin mamayar Isra’ila ya ba da umarnin tsananta kai hare-hare kan yankunan yammacin gabar kogin Jordan biyo bayan hare-haren bama-bamai da aka kai a birnin Tel Aviv Fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya bada umarnin kai hare-haren wuce gona da iri kan sansanin ‘yan gudun hijira na Tulkaram da ke...
“Idan ba a dau matakin da ya dace akan abin da ke faruwa a DRC ba, al’amarin zai faskara. Ba batun fitar da takardar jawabin bayan taro ne kawai muke yi ba. Dole a biyo bayan hakan da wasu muhimman matakai ko tsare tsare da zasu tabbatar da cewa an gabatar da wadannan al’amura kan...
Bayan shekaru 47, Faransa ta janye daga sansanin sojinta mafi girma a kasar Ivory Coast A hukumance Faransa ta mayarwa kasar Ivory Coast babban sansanin soji da ta mamaye kusan shekaru hamsin a kusa da birnin Abidjan, a wani bangare na yarjejeniyar da kasashen biyu suka kulla. Filin tashar jiragen ruwa na Port Bouet, wanda...
Saudiyya Za Ta Haramta Shan Giya Lokacin Gasar Kofin Duniya
Hukumar Tsaron Farin Kaya ta Sibil Difens (NSCDC), a Jihar Yobe, ta kama wasu mutum 17 da ake zargi da satar kayayyakin lantarki, na’urorin sadarwa a jihar. Kwamandan rundunar, AS Dandaura, ya tabbatar da kamen a Damaturu, Babban Birnin jihar, inda ya ce an gano wuraren ajiya uku da ake amfani da su don ɓoye...
Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana cewa ƙarin kuɗin makarantar Jami’ar Jihar Gombe (GSU) da kashi 120 cikin 100 ya zama dole domin tabbatar da ɗorewar ingancin ilimi a jami’ar. Gwamnan ya bayyana haka ne yayin rantsar da kwamitocin gudanarwa na manyan makarantu da hukumomin gwamnati, inda ya jaddada cewa kuɗaɗen makaranta na...
Ana matukar bukatar jami’an ilimi saboda kuwa sune suke da alhakin tabbatar dukkan tsare tsaren ilimi da manufofi ana amfani da su kamar yadda ya kamata.Suna aiki da Shugabannin makarantu da sauran masu ruwa da tsaki domin tabbatar da dalibai suna msaun nagartaccen ilimi. Hakanan ma jami’an ilimi ma na bukatar su rika gabatar da...
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, ta ca zata saki ‘yan Isra’ila shida yau Asabar a matakin karshe na yarjejeniyar tsagaita wuta ta farko da ta cimma da Isar’ila. An kuma tsara Isra’ila za ta saki fursunonin falasdinawa Falasdinawa 602 a wannan Asabar a musayar wacce ita ce ta bakwai tun cimma yarjejeniyar a ranar 19...
Iran ta jadadda anniyarta ta karfafa alaka da kasashen Afrika, kamar yadda ma’aikatar harkokin wajen kasar ta tabbatar. A cikin wani sako da ya aike ta shafin X a ranar Juma’a, kakakin ma’aikatar, Esmaeil Baghaei, ya yi tsokaci kan ganawar da aka yi a ranar Alhamis tsakanin mataimakin shugaban kasar na farko Mohammad Reza Aref...
Sanata Sunday Marshall Katung, mai wakiltar Kudancin Kaduna a Majalisar Dattawa, ya bayyana damuwarsa kan yadda wasu mazauna yankin ke taimaka wa miyagu wajen aiwatar da ayyukan ta’addanci. Da yake magana a taron manema labarai na Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Kudancin Kaduna (SKJF) a Zonkwa, hedikwatar Ƙaramar Hukumar Zangon Kataf, Sanata Katung, ya jaddada cewa...
Tawagogi na ci gaba da isa Beirut, domin halartar jana’izar tsohon sakataren kungiyar Hezbollah ta Lebanon mirigayi Sayyid Hassan Narsrallah. Iran, ma ta sanar da aikewa da wata babbar tawaga zuwa kasar ta Lebanon domin halartar jana’izar shahiddan Sayyid Hasan Nasrallah da Sayyed Hashem Safieddine. A gobe Lahadi ne za a gudanar da jana’izar wadannan...
Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, a karon farko ya yi Allah-wadai da kasar Rwanda kan goyon bayan da take bai wa mayakan kungiyar M23 a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango (DRC). Kwamitin ya kuma nemi ksar ta Rwanda da ta”gaggauta” janye sojojinta daga gabashin Jamhuriyar Demokuradiyyar Kwango. Kudurin na ranar Juma’a “ya kuma yi kakkausar...
Shugabannin kasashen Larabawa sun tattauna kan batun Gaza dama halin da ake ciki yankin. Bisa gayyatar Yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohammed bin Salman, an gudanar da taron ‘yan uwantaka na yau da kullun a birnin Riyadh a ranar Juma’a inji kamfanion dilancin labaren kasar na SPA. Taron ya samu halartar sarki Abdullah II...
Gwamnatin Jihar Yobe, ta rattaba hannu kan kwangilar gina gadar sama da titin ƙarƙashin ƙasa a tsakiyar garin Damaturu, Babban Birnin Jihar, kan kuɗi Naira biliyan 22.3. Wannan wani mataki ne na ci gaba a ƙoƙarin gwamnatin samar wa al’umma ababen more rayuwa. Sanata Katung ya damu kan yadda wasu ta’azzara ta’addanci a kudancin Kaduna...
Arangama Tsakanin NLC Da Gwamnatocin Soji Ga duk mutumin da yai duba na tsanaki ga hakikanin manufofin samar da wannan kungiya ta NLC, la-budda, wajibi ne a rika samun sa-toka-sa-katsi tsakaninta da gwamnatoci musamman irin na Soja. Ba kawai gwamnatocin soja ba, da tafiya ta kara nikatawa kamar yadda za a gabatar nan gaba cikin...
Sanata Sunday Marshall Katung, mai wakiltar Kudancin Kaduna a Majalisar Dattawa, ya bayyana damuwarsa kan yadda wasu mazauna yankin ke taimaka wa miyagu wajen aiwatar da ayyukan ta’addanci. Da yake magana a taron manema labarai na Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Kudancin Kaduna (SKJF) a Zonkwa, hedikwatar Ƙaramar Hukumar Zangon Kataf, Sanata Katung, ya jaddada cewa...
Karamar hukumar Birnin Kudu dake Jihar Jigawa ta ce za ta dauki nauyin dalibai ‘yan asalin yankin su 80 da ke kwalejin Ilmi ta tarayya ta Jama’are a Jihar Bauchi, da kwalejin fasaha ta Dutse da kuma kwalejin fasahar sadarwa ta Kazaure. Shugaban Karamar Hukumar, Dr. Muhammed Uba Builder ya bayyana haka ga manema labarai...

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Taimakawa Shirye-shiryen Zabe A Jamhuriyar Afrika Ta Tsakiya
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Taimakawa Shirye-shiryen Zabe A Jamhuriyar Afrika Ta Tsakiya
Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Ƙasa (TCN), ya bayyana cewa wasu yankunan Abuja za su fuskanci katsewar wuta a ƙarshen mako saboda aikin gyara da za a yi wa na’urorin lantarki. A wata sanarwa da kamfanin ya fitar a ranar Juma’a, ya ce ana yin wannan aikin ne na shekara-shekara, kuma za a gudanar da...
Ƙasurgumin fitaccen shugaban ‘yan Bindiga, Bello Turji, ya ƙaƙaba harajin Naira miliyan 22 a wasu ƙauyuka huɗu na jihar Sokoto, kan kashe ɗaya daga cikin mutanensa a wani samame da sojoji suka yi a yankin. Acewar mutanen yankin, wannan harajin, yana matsayin diyya ga makaman da suka bace yayin artabun da mutanensa suka yi da...
Bugu da kari, ministan ya ce bana lokaci ne na Afrika, duba da cewa za a gudanar da taron kolin G20 a nahiyar Afrika a karo na farko tun bayan da AU ta zama cikakkiyar mamba. Ya ce ya kamata a saurari kiraye-kirayen nahiyar, a kuma yi la’akari da damuwarta, kana a taimakawa ayyukanta da...
Daftarin Sin Ya Samar Wa Kamfanoni Masu Jarin Waje Damammaki Masu Kyau
Ma’aikatan Gidan Rediyon Tarayya (FRCN) da na Hukumar Gidan Talabijin ta Najeriya (NTA) da suka yi ritaya, sun bayyana jin dadinsu kan karin haske da Ministar Kudi ta yi game da wadanda za su ci gajiyar Naira Biliyan 758 da aka amince da su don biyansu kudaden fansho da suke bi. A tsokacin da suka...
Fitaccen dan jarida na Amurka wanda Patrick Heili ya yi hira da shi ta Podcast, ya bayyana cewa; Shugaban kasar Amurka Donald Trump yana son ya ci gaba da zama akan kujerar mulki har abada. Hirar da Thomas Friedman ta mayar da hankali ne akan salon mulkin Donald Trump da yadda yake son sauya yadda...