2025-03-26@05:56:51 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1251

«Gwamnatin Nijeriya»:

    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya sanar da cewa har yanzu Iran ba ta mayar da martani kan wasikar da shugaban Amurka Donald Trump ya aike kan shirin nukiliyar Iran ba. Sai dai ya ce ana shirin mayar da amsa kuma za a mika ta hanyoyin da suka dace nan ba da jimawa ba....
    Amurka ta shigo da sama da ganga miliyan biyu na man jiragen sama daga matatar Dangote a watan Maris. Matatar ta tabbatar da hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata, inda ta ce hakan ya tabbatar da “nagartar da ba ta misaltuwa” na kayayyakin matatar da kuma aminci da kasashen...
    Wani rahoto da aka fitar yau Talata, yayin zaman taron shekara-shekara na shekarar 2025, na dandalin tattaunawa na Asiya na Boao, ya nuna yadda kasar Sin ke ci gaba da kasancewa cibiyar rarraba hajojin da masana’antu ke sarrafawa. Rahoton mai taken “Nazarin tattalin arzikin Asiya, da hadadden rahoton ci gaba na shekarar”, ya nuna yadda...
    A yanzu nan ne Aminiya take samun labarin rasuwar fitaccen jarumin Kannywood, Malam Abdullahi Shu’aibu wanda aka fi sani da Baba Ƙarƙuzu ko Ƙarƙuzu na Bodara. Hakan dai na kunshe ne cikin wani sako da jarumi a masana’antar Kannywood kuma Shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Kano, Abba El-Mustapha, ya wallafa a shafinsa na Instagram. SShi...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Tawagar Super Eagles ta Nijeriya ta gamu da cikas a ƙoƙarinta na neman yankar tikitin shiga Gasar  Kofin Duniya ta baɗi, bayan da ta tashi canjaras 1-1 da Zimbabwe. Victor Osimhen ne ya fara ci wa Nijeriya kwallo a minti na 74 a filin wasa na Godswill Akpabio da ke Uyo, babban birnin Jihar Akwa...
    Amurka ta shigo da sama da ganga miliyan biyu na man jiragen sama daga matatar Dangote a watan Maris. Matatar ta tabbatar da hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata, inda ta ce hakan ya tabbatar da “nagartar da ba ta misaltuwa” na kayayyakin matatar da kuma aminci da kasashen...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Guo Jiakun ya ce a jiya Litinin, ma’aikatar harkokin wajen Sin ta gudanar da taron karawa juna sani na kasa da kasa, mai taken “Karfafa rawar da MDD ke takawa, tare da habaka ra’ayin cudanyar bangarori daban daban” a nan birnin Beijing. Guo ya bayyana hakan ne yayin taron manema...
    A cewarsa ya zaɓe shi ne bisa la’akari da kwarjininsa da kuma gwanintarsa. Farfesa Worika yana da digiri na uku a fannin Dokar Muhalli ta Ƙasa da Ƙasa da Man Fetur daga Jami’ar Dundee da ke Birtaniya. Ya yi aiki a fannoni daban-daban da suka haɗa da harkokin ilimi da kuma ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa....
    Sai dai, tabbas za a karya tsarin, ganin yadda ba a samun adalci a ciki. Mun san kasar Sin daya ce daga cikin kasashen da suka warware dabaibayin hana ci gaba da kasashen yamma suka daura musu, inda ta raya tattalin arzikinta, tare da taka muhimmiyar rawa a cikin tsarin duniya ta fuskar samar da...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya musanta zargin kasar Amurka na cewa wasu jiragen ruwan JMI suna amfani da tudan kasar Iraqi sun kai kawo a ruwayen yankin. Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta fadawa Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran, kan cewa Aragchi yana fadar haka ne a jiya litinin, a...
    Gwamnatin tarayyar Najeriya ta kafa runduna ta musamman a kasar don magance matsalolin tsaro daban-daban wadanda kasar take fama das u. Jaridar Premium times ta Najeriya ta nakalto ministan tsaron kasar Muhammad Badaru yana fadar haka a lokacinda yake kaddar da wani bangaren na rundunar a barikin Kabala da ke barikin Jaje a kusa da...
    A ranakun 11, 19, da 25 ga Fabrairu, an dawo da mutum 484. A ranakun 4 da 18 ga Maris, an dawo da mutum 320. Hon. Dabiri-Erewa ta ƙara da kira ga ‘yan Nijeriya da su guji tafiya ƙetare ta ɓarauniyar hanya, musamman ta Libya, wacce ke fama da matsaloli da rikici. Ta kuma jaddada...
    Shugaban riƙo na Jihar Ribas, Ibok-Ete Ibas (mai ritaya), ya sanar da naɗin Farfesa Ibibia Lucky Worika a matsayin sabon Sakataren Gwamnatin Jihar Ribas. Wata sanarwa da ta fito daga Fadar Gwamnatin da ke birnin Fatakwal a wannan Talatar, ta ce naɗin ya biyo bayan nazari kan ƙwarewar Farfesan da gogewarsa a fannoni daban-daban. Za...
    Wannan ya taimaka wajen kawo ƙarshen yaƙin basasa a Laberiya da Saliyo. Duk da haka, ƙungiyar ta fuskanci ƙalubale, musamman bayan juyin mulki a ƙasashen Mali, Burkina Faso, da Nijar a cikin shekarun baya-bayan nan. Shin ECOWAS na iya ci gaba da aiwatar da ayyukanta kamar da? Sai dai har yanzu wasu na yi wa...
    Wasu lauyoyi 77 a Jamus sun bukaci gwamnatin kasar da ta mutunta sammacin kotun hukunta manya laifuka ta duniya ICC, na cafke firaministan Isra’ila Banjamin Netanyahu.  A cikin wata sanarwar hadin gwiwa da da suka fitar, fitattun lauyoyin 77 sun kuma bayyana yiwuwar kasancewar Netanyahu a Jamus a matsayin take doka da kuma hakkin kasar....
    Za a ɗauko hayar ƙwararrun sojoji daga ƙetare domin horar da sojin ƙasar aikin ƙundumbala wajen tunkarar ’yan ta’adda da kuma ƙwato mutanen da aka yi garkuwa da su a Nijeriya. Ministan Tsaron Nijeriya, Badaru Abubakar ya sanar da haka lokacin ƙaddamar da aikin horar da sojojin 800 a Jaji da ke Jihar Kaduna. Gaskiyar...
    A yankunan kamar Birnin Gwari a Kaduna, ana samun ci gaba bayan ƙarin matakan tsaro da aka ɗauka. Gwamnati na fatan wannan horo zai taimaka wajen rage hare-haren ‘yan bindiga, ceto mutanen da ake garkuwa da su, da kuma kawo ƙarshen rashin tsaro a yankunan da ke fama da matsalar. Ana sa ran wannan shiri...
    A yankunan kamar Birnin Gwari a Kaduna, ana samun ci gaba bayan ƙarin matakan tsaro da aka ɗauka. Gwamnati na fatan wannan horo zai taimaka wajen rage hare-haren ‘yan bindiga, ceto mutanen da ake garkuwa da su, da kuma kawo ƙarshen rashin tsaro a yankunan da ke fama da matsalar. Ana sa ran wannan shiri...
    Sai dai duk da yaba wa Amurka bisa irin taimakon da ta bayar a baya, Byanyima ta nuna damuwa kan yadda aka dakatar da tallafin kwatsam ba tare da shiri ba. Wannan na iya haddasa koma baya a ƙoƙarin da aka shafe shekaru ana yi na rage yawan masu kamuwa da cutar, musamman a yankunan...
    Kungiyar ‘Yan Jaridu ta Najeriya (NUJ) reshen Jihar Kebbi ta raba kayan abinci da kudi ga iyalan mambobinta da suka rasu a lokacin da suke kan aikin jarida, a matsayin kyautar azumin Ramadan. Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban Kungiyar na Jiha, Kwamared Bello Sarki Abubakar, ya ce suna gudanar da wannan shiri a...
    “SDP jam’iyya ce mai zaman kanta, kuma za mu ci gaba da bin tsarukanmu da dokokinmu wajen zaɓen ‘yan takara,” in ji shi. “Za Mu Fi Mayar da Hankali Kan Ci Gaban Jama’a” Shugaban jam’iyyar ya bayyana damuwa kan halin da ‘yan Nijeriya ke ciki, musamman matsalar tsadar rayuwa da rashin tsaro. Ya ce SDP...
    Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa za a samu mutum 2,000 sabbin kamuwa da cutar SIDA duk rana a faɗin duniya. MDD ta ce tana wannan gargaɗi ne sakamakon matakin Amurka na katse taimakon agajin ƙasashen duniya ƙarƙashin Hukumar ta USAID. Matasa sun daka wawa kan kayan abincin da Seyi Tinubu zai raba a...
    Misalan Wannan Hassada: 1. Hassadar Fir’auna a Kan Annabi Musa (AS): Fir’auna ba ya son aiken da Allah Ya yi wa Annabi Musa (AS) ba, domin yana tsoron cewa mulkinsa zai ƙare. Ya so cewa wannan matsayi na shugabanci da iko ya kasance a gare shi kawai. Allah Ta’ala Ya ce:” Fir’auna kuma ya ce:...
    A yau Litinin ne kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Guo Jiakun, ya jagoranci taron manema labarai na yau da kullum, inda wani dan jarida ya yi tambaya game da ko Sin za ta shiga tattaunawa da Amurka, game da hakan Guo Jiakun ya ce, a ko da yaushe kasar Sin na da imanin cewa, kiyaye...
    A kwanakin nan, birnin Beijing na Sin ya karbi tarin ‘yan siyasa da ‘yan kasuwar kasar Sin dake kawo ziyara kasar, sai dai kuma idan an yi la’akari da yanayin yakin cinikayya tsakanin sassan kasa da kasa dake wakana yanzu haka, a iya cewa ziyarce-ziyarcen sun zo da mamaki. Yayin da gwamnatin Amurka ke matsa...
    Rundunar ‘yan sandan Birnin Tarayya ta ce ta kama damin alburusai 488 da aka ɓoye a jarkar manja a tashar mota. Mataimakin kwamishinan ‘yan sandan da ke kula da sintiri na musamman a Abuja, DCP Ishaku Sharu, ne ya bayyana hakan lokacin da yake holen wanda ake zargin a ofishin rundunar a ranar Litinin. Matasa...
    Mataimakin firaministan kasar Sin He Lifeng ya bayyana a jiya Lahadi cewa, kasar Sin za ta ci gaba da bude kofa ga kasashen waje, kuma tana maraba da kamfanonin kasashen duniya da su fadada zuba jari a kasar Sin, domin zurfafa samun moriyar juna da samun nasara tare. He ya bayyana hakan ne a wata...
    Al’ummar duniya mai kyakkyawar makomar bai daya na nufin makomar kowace al’umma da kowace kasa tana da nasaba da juna. Hakan na nufin ya kamata mu yi rayuwa tare duk rintsi duk wuya, muna more daukaka da wahala tare da kuma kokarin mayar da duniyarmu al’umma guda mai jituwa, inda za mu mai da burin...
    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Juventus na shirin raba gari da mai horas da ’yan wasanta, Thiago Motta, yayin da ko kaka ɗaya bai cika ba a kwantaragin da ya ƙulla da ƙungiyar ta Italiya. A cewar Jaridar wasanni ta La Gazzetta dello da Gidan Talabijin na Sky Sport, Juventus na shirin maye gurbin Thiago Motta...
    Iran ta yi gargadin cewa zaluncin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi wa kasar Labanon na da matukar hadari kuma barazana ga zaman lafiya da tsaron kasa da kasa, inda ta bukaci kasashen duniya da su dauki matakin da ya dace. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmaeil Baghaei ya yi kakkausar suka kan hare-haren...
    Ebrahim Rasool, jakadan Afirka ta Kudu da gwamnatin Trump ta kora, ya samu tarba a wannan Lahadin daga daruruwan magoya bayansa da suke rera wakoki  domin karrama shi a filin jirgin sama na Cape Town. Jama’a sun kewaye Rasool da matarsa ​​Rosieda bayan isowarsu, yayin da ‘yan sanda suka yi musu rakiya har zuwa tashar...
    Dubban mutane ne a birnin Amman babban birnin kasar Jordan suka gudanar da zanga-zanga bayan sallar Juma’a domin yin Allah wadai da sake dawo da laifukan da Isra’ila ke aikatawa a Gaza. A rahoton factjo, dubban mutane sun bayyana goyon bayansu ga al’ummar Gaza a wani gagarumin maci na wannan Juma’a. Mahalarta tattakin sun yi...
    Wasu manyan ’yan Nijeriya da suka tafi Umarah sun yi wa Gwamnan Katsina Dikko Umar Radda ta’aziyya a Saudiyya. A safiyar Lahadi ce dai Allah Ya karɓi rayuwar mahaifiyar Gwamnan, Hajiya Safara’u Umaru Baribari bayan shafe tsawon lokaci tana jinya a Jihar Katsina. Wata mata ta haifi jaririn da ba nata ba NAJERIYA A YAU:...
    Wata mata mai suna Krystena Murray ’yar Amurka, wadda ta ɗauki ciki tare da haife jariri namiji ba tare da sanin cewa ba ɗanta ba ne, ta fara ɗaukar matakin shari’a a kan wani asibitin da ke taimaka wa mata samun ciki ta hanyar dashen ɗantayi (IBF). Matar tana zargin asibitin da yi mata dashen...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Hausawa sun yi gaskiya da suka ce ‘yawan mutane su be kasuwa’. Yawan hada hadar da ake yi tsakanin ‘yan kasuwa da abokan cinikinsu na ɗaya daga cikin abun da zai tabbatar maka kasuwanci na gudana kamar yadda ake so. Sai dai da zarar an ce watan Ramadana...
    Mataki na uku shi ne mutum ya so samun irin wannan ni’ima kamar yadda wani yake da ita, ba tare da yana so ta gushe daga hannun wanda yake da ita ba. Wannan kuwa ba hassada ba ce, sai dai ana kiranta da fatan alheri ga kai.” Duba Kitãbu at-Tashīlu Li’ulūmi at-Tanzil [4/226] Fashin Baƙi:...
    A yau Lahadi, kwararren masanin tattalin arziki dan kasar Amurka Jeffrey Sachs ya bayyana cewa, matakan kariyar cinikayya da Amurka ke aiwatarwa babban kuskure ne. Jeffrey wanda ya halarci dandalin bunkasa kasa na Sin na shekarar nan ta 2025 a birnin Beijing, ya kara da cewa Amurka na kara karkata ga salon kariyar cinikayya karkakin...
    Shugqbqn kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen sayyed Abdulmalik Badaruddin Huthi ya bayyana cewa tura wani kataparen jirgin ruwan yaki zuwa gabas ta tsakiya wanda shugaban kasar Amurka yayi wata gazawace. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalti Alhuthi yana fadar haka yau Lahadi a wani jawabin da ya gabatar ,inda yake bayyana irin...
    Shugaba hukumar makashin Nukliya na kasar Iran Mohammad Islami ya bada sanarwan cewa a ranar 8 ga watan Afrilu mai zuwa. Yace hukumarsa za ta kaddamar da sabbin magunguna da ta samar tare da amfani da makamashin Nukliya, a dai dai na ranar makamashin Nukliya ta kasar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ta...
    A gobe Litinin 24 ga watan Maris ne tawagogin masu tattaunawa na kasashen Amurka da Rasha zasu hadu a birnin Rayida na kasar Saudiya don ci gaba da tattaunawan da suka fara a yan makonnin da suka gabata dangane da yakin da ke faruwa a Ukraine, shekaru fiye da 3 da suka gabata, da kuma...
    A jiya Asabar 22 ga watan nan, jakadan kasar Sin a Amurka Xie Feng, ya amsa gayyatar halartar taro na 2 na tattaunawar sassan Sin da na Amurka game da batun tattalin arziki karkashin cibiyar Jimmy Carter, inda ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo.  A cikin jawabinsa, jakada Xie Feng ya ce ko kadan,...
    Gwamnonin Arewa sun aike wa Gwamna Dikko Umar Radda na Jihar Katsina, saƙon ta’aziyya game da rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Safara’u Umaru Baribari, wadda ta rasu tana da shekaru 93. Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa (NSGF) kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana Hajiya Safara’u a matsayin uwa mai tausayi da riƙon gaskiya, wadda...
    Aƙalla jami’an rundunar tsaron al’umma ta Zamfara (CPG) 10 ne, suka rasu, yayin da wasu 14 suka jikkata a wani hari da ’yan bindiga suka kai musu a yankin Anka da ke Jihar Zamfara. Sun kai harin ne a ranar Asabar bayan da jami’an tsaro suka kai farmaki wani sansanin ’yan bindiga da ke dajin...
    Kungiyar ta ce a maimakon neman cin mutuncin Uguamaye kamata ya yi gwamnatin tarayya ta dukufa neman kawo sauyin da zai rage wa jama’a wahalhalun da suke fuskanta da magance matsalolin tattalin arziki da kasar ke ciki. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi, ta kama wasu matasa huɗu da ake zargi da yin garkuwa da kuma kashe wani yaro ɗan shekara shida, Shuaibu Safiyanu, a ƙauyen Sade da ke Ƙaramar Hukumar Darazo. Aminiya ta ruwaito cewar mahaifin yaron, Safiyanu Abdullahi ne, ya sanar da Sarkin garinsu, Musa Isah, cewa a ranar 20 ga...
    Ya kara bayanin cewa an dauki matakin ne inda har abin ya shafi daliban da suke mazabun majalisar Dattawa biyu na Jihar Osun. Ya nuna jin dadinsa inda ya furta ce wa“Wani abin farinciki ne gare ni dana samu yawan daliban da suka samu damar yin rajista daga mazaba ta da kuma saiuran mazabun na...
    Wani abin al’ajabi da ban tsoro ya auku inda rana tsaka garin Zip da ke Jihar Taraba ya nutse baki dayansa a cikin Kogin Biniwai. Wakilin Aminiya ya ziyarci garin domin gani da ido, inda ya ruwaito cewa a halin yanzu babu sauran wani gini ko bishiya da ake gani a garin, duk kogin ya...
    Kasar Rasha ta bayyana cewa dole Moscow da Beijing su shiga shawarwarin tattaunawar nukiliya da Iran. Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha Maria Zakharova ta bayyana cewa, Moscow a shirye take ta samar da ingantacciyar hadin gwiwa da dukkan bangarorin kan batun yarjejeniyar nukiliyar Iran. “ Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar...
    An kama wani jami’in rundunar sa-kai ta JTF, Modu Mallam Gana mai shekaru 27 a garin Monguno, bisa zarginsa da harbin wasu gungun matasa wanda ya yi sanadin mutuwar mutane biyu tare da raunata daya. Wata majiyar leƙen asiri ta shaida wa Zagazola Makama cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 6:15 na safiyar...