2025-03-12@12:11:16 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1601
«Sabon Kwamishina»:
Rahotanni sun bayyana cewa Majalisar Dokokin Jihar Ribas ta hana Gwamna Similanayi Fubara shiga cikinta a safiyar wannan Larabar. Bayanai sun ce gwamnan ya ziyarci majalisar ne domin gabatar mata da Kasafin Kuɗin jihar na 2025. Sai dai bayan isowar gwamnan tare da tawagarsa, ya tarar da ƙofar shiga majalisar a garƙame da kwaɗo kuma...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi kakkausar suka ga matakin da gwamnatin Trump ya dauka kan Iran, yana mai bayyana cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba Ukraine ba ce, kuma ba za ta yi shawarwari da Amurka bisa barazana ko tilasci ba. “Dole ne mu kiyaye dangantaka da duniya. Ba ma son mu yi...
Jami’ar kula da manufofin ketare ta Tarayyar Turai, Kaya Kalas, ta tabbatar da cewa, EU za ta iya sake kakaba takunkumi kan kasar Syria, idan aka samu tabarbarewar lamurra, tana mai nuni da yadda ake cin zarafin fararen hula a gabar tekun Syria. Kaya Kalas ta shaidawa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya cewa, “Muna...
Rundunar sojan Uganda ta sanar da tura dakaru na musamman domin tabbatar da tsaro a babban birnin Sudan ta Kudu bisa bukatar Juba, a daidai lokacin da ake fargabar sake barkewar yakin basasa, musamman a halin da ake ciki tsakanin shugaban Sudan ta Kudu da mataimakinsa na farko. A wannan Talata rundunar sojin Uganda ta...
Majalisar Dokokin Jihar Jigawa ta jaddada kudurin ta na tabbatar da gaskiya da adalci a shirin ciyarwa na azumin watan Ramadan da ke gudana a fadin jihar. Shugaban kwamitin duba rabon abincin buda baki kuma wakilin mazabar Kiyawa, Alhaji Yahaya Muhammad Andaza, ya bada tabbacin haka lokacin da ya kai ziyarar bazata a wasu cibiyoyin...
Shugaban ofishin yada labarai a Gaza Salama Marouf, ya yi Allah wadai da ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi, saboda kin janyewa daga yankin Salahul Din a kudancin Gaza da kuma ci gaba da kutsawa da da kai hare-hare a cikin Rafah. Marouf ya yi gargadin...
Wasu ’yan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun kai hari garin Farin Duse da ke Ƙaramar Hukumar Nasarawa, inda suka kashe wata mata juna, Azumi Allah Gaba, tare da wasu mutum 10. Binciken Aminiya ya nuna cewa rikicin ya samo asali ne lokacin da wani makiyayi ke kiwon shanunsa, ya yanke wata bishiyar mangwaro...
Ya kuma yi kira a gare shi da ya fuskanci ƙalubalen tsaro da ke Kano tare da ɗaukar matakan da suka dace don daƙile matsalolin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin...
Kasar Yemen ta sanar da cewa za ta ci gaba da kai hare-haren soji kan jiragen ruwan Isra’ila a wasu muhimman yankunan teku da ke gabar tekun kasar bayan cikar wa’adin da ta gindaya wa Isra’ila na ta sake bude mashigar zirin Gaza tare da bayar da damar kai agaji cikin yankunan Falasdinawa da yaki...
Kasar Ukraine ta bayyana aniyarta ta amincewa da shawarar da Amurka ta gabatar, game da dakatar da bude wuta nan take tsakaninta da Rasha har tsawon kwanaki 30, biyowa bayan fara tattaunawa da tawagar Amurka a birnin Jeddah na kasar Saudiyya. Wata sanarwar hadin gwiwa tsakanin wakilan Ukraine da na Amurka da aka fitar a...
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta ce matakin da Isra’ila ta dauka na hana shigar da kayayyakin jin kai da bukatun yau da kullum a zirin Gaza da aka yi wa kawanya ya zama “laifi na yaki da kuma hukuncin gama-gari.” A cikin wata sanarwa da ta fitar, Hamas ta ce matakin rufewar ya saba...
Kungiyar tarayyar turai ta jaddada bukatar warware batun Iran ta hanyar diflomatsiyya. Da taek sanar da hakan babbar Jami’ar kula da harkokin ketare ta kungiyar ta ce babu wata hanyar da za’a bi wajen warware matsalar Iran in ba ta diflomasiyya ba. ‘’ta hanyar diflomatsiyya ne za’a warware takaddamar da ake game da batun yarjejeniyar...
Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da daruruwan fasinjoji a ranar Talata a wani yunkurin ci gaba da ta da hankali da wata kungiyar ’yan aware ke yi a Kudu maso yammacin Pakistan. ’Yan bindigar sun raunata direban jirgin kasan a kokarinsu na kwace iko da jirgin a yankin Balochistan mai duwatsu da ke iyaka...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Bayan ɗimbin falala da yawan samuwar ibadun da ke ƙara kusanta bayi ga Ubangijinsu, da azumin watan Ramadan ke zuwa da shi kamar yadda malamai suka saba faɗa, Hakazalika kuma a watan na zuwa da wata al’ada mai ɗimbin tarihi da ke ɗebe wa al’umma musamman na Arewacin...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Bayan ɗimbin falala da yawan samuwar ibadun da ke ƙara kusanta bayi ga Ubangijinsu, da azumin watan Ramadan ke zuwa da shi kamar yadda malamai suka saba faɗa, Hakazalika kuma a watan na zuwa da wata al’ada mai ɗimbin tarihi da ke ɗebe wa al’umma musamman na Arewacin...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Da wannan nasarar ne Barcelona ta samu nasarar zamowa kungiya ta farko da ta tsallaka zuwa matakin kwata fainal a sabon jadawalin gasar Zakarun Turai da aka fara amfani da shi bana. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku....
Assalamu alaikum masu sauraro sharhin bayan labarammu zai yi magana dangane da ‘Atisayen sojojin ruwa mai taken (“damarar tsaro na shekara ta 2025”) wandake ke gudana a nan Iran. Wanda ni tahir amin zan karanta. ////.. A ranar litinin da ta gabata ce sojojin ruwa na kasashen China, Rasha da kuma Iran suka fara atisayen...
Gamayyar ƙungiyoyin manyan makarantu na gwamnatin Jihar Adamawa sun tsunduma yajin aikin sai baba ta gani a yau Talata, 11 ga watan Maris. Ma’aikatan manyan makarantun da suka haɗa da masu karantarwa da waɗanda ba sa karantarwa sun shiga yajin aiki ne bayan wa’adin yajin aikin gargaɗi na kwanaki bakwai da ya ƙare a jiya...
Kasar Uganda ta sanar da aikewa da sojojinta zuwa birnin birnin kasar Sudan Ta Kudu, Juba saboda ba shi kariya. Sai dai har yanzu gwamnatin Sudan din ba ta tabbatar da hakan ba. Babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Uganda Janar Muhoozi Kainerugaba ya bayyana cewa; Rundunar musamman ta Ugandan ta shiga cikin birnin Juba, domin...
Ya kara da cewa an samu wasu kayayyaki a wurin, ciki har da babbar motar dakon kaya ɗauke da buhuna takwas na ‘Monazite’ da aka sarrafa, wanda nauyinsa ya kai kilogiram 1000, wanda darajar kowanne buhu ta kai naira miliyan hudu, da kuma wasu ma’adinai da ba a sarrafa ba da ake zargin an haƙo...
Tare da cewa Rasha ta sanar da kakkabo jiragen sama marasa matuki fiye da 60 da Ukiraniya ta harba, sai dai an sanar da mutuwar mutum daya a birnin Moscow. Kantoman yankin Moscow Andrey Vorobyov ne ya sanar da cewa mutum daya ya rasa ransa yayin da wasu 3 su ka jikkata, sanadiyyar hare-haren da...
Rahotannin da suke fitowa daga Syria sun ambaci cewa kungiyoyin ‘yan ta’adda da suke da alaka da shugaban gwamnatin Syria, Julani sun fara dauke gawawwakin mutanen da su ka yi wa kisan kiyashi zuwa wasu wurare da ba a san ko’ina ne ba. Saboda yadda fushin kasashen duniya yake karuwa akan kisan kiyashin da ‘yan...
Hukumar da take fada da yi wa tattalin arzikin kasar Najeriya ta’annatii ta kwato da kudaden da sun kusa dalar Amurka miliyan 500. Haka nan kuma hukumar ta kwato man fetur da sauran dangoginsa da sun kai ton 931,000, sai kuma gidajen da sun kai 975. A cikin rahoton da ta fitar a ranar litinin...
An gargaɗi mazauna da su kwana cikin shirin daƙile yaɗuwa cutar Sanƙarau a yayin da cututtuka masu alaƙa da ita suka soma bayyana a wasu ƙananan hukumomin Jihar Sakkwato. Kwamishinan Lafiya na jihar, Dakta Faruk Umar Wurno ne ya yi wannan gargaɗi haɗi da bayar da shawarar a wani jawabi da ya fitar a ranar...
Mayaƙan Lakurawa sun kashe mutum 13 a wani harin ramuwar gayya da suka kai yankin Birnin Debe da ke Ƙaramar Hukumar Arewa a Jihar Kebbi. Wani mazauni mai suna Musa Gado, ya ce maharan wanda suka kai harin a ranar Lahadi, sun kuma ƙone ƙauyuka takwas daga cikin tara da ke yankin. Tsohon shugaban Philippines...
Hukumar kula da yanayi ta Nijeriya NiMet ta yi gargaɗin cewa akwai yiwuwar a fuskanci tsananin zafin rana a wasu jihohin ƙasar na tsawon kwanaki huɗu. Wata sanarwa da Nimet ta fitar ranar Litinin a Abuja, ta ce mutane su guji fita cikin tsananin zafi musamman daga karfe 12 na rana zuwa karfe 3. Ainihin...
Shugaban Kwamitin Tallafa wa Marayu na Riyadissalihin Funtua, Alhaji Lawal Mekaji (Madugun Kasuwar Funtua), ya yi kira ga al’umma, musamman iyaye da masu hannu da shuni, da su bada gudunmawa wajen tallafa wa marayu da inganta rayuwarsu. Ya yi wannan kira ne yayin da yake raba kayan sutura da abinci ga marayu a Funtua a...
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya yi Allah-wadai da matakin da gwamnatin Amurka ta dauka na haramtawa al’ummar Iraki ‘yancinsu na samun wutar lantarki, da ma wasu ababen more rayuwa. “Muna tare da al’ummar Iraki, kuma mun tabbatar da alkawarinmu ga gwamnatin Iraki na ba da hadin kai wajen tinkarar matakan da Amurka ta...
Kimanin fararen hula 1,000 ne aka kashe tare da jikkata wasu daruruwa a hare-haren jiragen yaki marasa matuki a nahiyar Afirka, yayin da ake ci gaba da yin amfani da jirage marasa matuka a nahiyar. A cewar jaridar The Guardian, masu sharhi da nazari na cewa , daga shekara ta 2021 zuwa 2024, jami’an tsaro...
UNRWA ta yi kira ga Isra’ila da ta kawo karshen hana shigar da kayan agaji a zirin Gaza domin dakile bazuwar yunwa da wahala a yankin. “Mun riga mun ga alamun farko na karin farashi a kasuwa,” in ji Kwamishinan UNRWA Philippe Lazzarini yayin taron manema labarai a wannan Litinin, ya kara da cewa yayin...
Wani babban jami’in ‘yan sanda a jihar Uttar Pradesh ta Indiya ya bukaci musulmi da su yi sallar Juma’a a gida. A cewar radiyon gwamnatin Pakistan, Firimiyan Jihar Uttar Pradesh Yogi Adityanath ya kare kalaman jami’in ‘yan sandan game da musulmi, inda ya ce, “A yayin da ake gudanar da bukukuwan Holi sau daya a...
An kora Kungiyar Kwallon Kafa ta Manchester United gida a Gasar cin Kofin FA na bana, bayan Fulham ta doke ta da ci 2-1 har gida a filin wasanta na Old Trafford a makon da ya wuce. Manchester United ta yi bankwana da gasar ne alhali ita ce ke mai riƙe da Kofin FA da...
Kamfanin Man Fetur na Najeriya NNPC ya ce yarjejeniyar da ya ƙulla da Matatar Dangote domin sayar mata da ɗanyen man fetur a farashin naira za ta ƙare a wannan wata na Maris. Sai dai kamfanin ce yana tattaunawa da Matatar Dangote domin tsawaita yarjejeniyar sayar mata da ɗanyen mai a naira. An hana tashe...
Kamar yadda ta riƙa kasancewa a shekarun baya bayan nan, bana ma dai jami’an tsaro sun haramta al’adar nan ta tashe da aka saba gudanarwa daga zarar an kai azumi na goma a watan Ramadana. Auwalu Sani Nalako, Sarkin Gwagwaren Kano kuma jagoran dabbaka al’adar tashe ne ya tabbatar hakan yayin hirarsa da manema labarai...
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi imanin cewa barazanar da Isra’ila ke yi na sake dawo da yaki a zirin Gaza ba ta da amfani, tana mai cewa tattaunawar tsagaita bude wuta ce hanya daya tilo da Isra’ila za ta iya ceto rayukan ‘yan kasarta da take garkuwa ranar Litinin 10 ga watan Maris,...
Majalisar Dinkin Duniya, ta yi tir da matakin Isra’ila na kate wutar lantarki a Gaza, tana mai matukar gargadi game da ilan da hakan zai janyo wa Zirin. Matakin da Isra’ila ta dauka na katse wutar lantarki a zirin Gaza da aka yi wa kawanya zai hana yankin Falasdinawa samun “ruwa mai tsafta,” in ji...
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya soki matakin da sabuwar gwamnatin Amurka ta dauka na janye sassaucin da ta yi wa Iraki na shigo da wutar lantarki daga Iran. Araghchi ya bayyana matakin da gwamnatin Trump ta dauka a matsayin “abin takaici.” Ya kara da cewa gwamnatin Amurka ta na kokarin hana al’ummar iraki...
Shugaban kasar Ghana, John Darmani Mahama ya nemi kungiyar Ecowas da ta amince da kungiyar kawancen kasashen Sahel din nan guda uku da suka balle daga cikinta. Mista Mahama, ya bayyana hakan a kafofin sada zumunta a ranar Litini jim kadan gabanin ya ziyarci kasar Burkina faso, bayan ya kai irin wanan ziyara kasashen Mali...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Fagen siyasar Najeriya na ci gaba da ɗaukar salo iri-iri yayin da ’yan kasa da dama suka yi kasaƙe suna jiran girgiza ta gaba wadda wasu suke ganin tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai, ya ɗiga mata ɗanba. A baya-bayan nan dai an yi ta tsegunguma da...
Sakataren baitul malin Amurka Scott Bessent ya sha nanata cewa, tattalin arzikin kasar Sin ya dogara a kan kayayyakin da ake fitarwa zuwa kasashen ketare fiye da kima, kuma Amurka na neman yin ciniki bisa adalci da daidaito. Sai dai kuma, da yake mayar da martani a yau Litinin 10 ga watan Maris, yayin wani...
Mayar da hankali kan taruka biyu na kasar Sin, wato taron majalisar wakilan jama’ar kasar (NPC) da kuma taron majalisar bada shawarwari kan harkokin siyasar kasar (CPPCC), muhimmin abu ne ga manyan shugabannin kamfanonin kasashen waje dake kasar Sin. Zuwa karshen shekara ta 2024, adadin kamfanonin da baki ’yan kasashen waje suka zuba jari don...
Tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya kaddamar da tallafin kayan abinci ga magidanta dubu 30 a fadin jihar. A yayin da yake kaddamar da tallafin tare da bayar da jari ga masu kananan sana’oi a gidansa a ranar Litinin, ya bayyana cewar tallafin wani mataki ne na saukakawa mabukata halin kunci a...
’Yan bindiga sun kashe aƙalla manoma 14 yayin wani hari da suka kai yankuna huɗu a Ƙaramar Hukumar Akure ta Arewa da ke Jihar Ondo. Yankunan da abin ya shafa — Aba Alajido, Aba Sunday, Aba Pastor da Ademekun— galibi mazaunansu ƙananan manoma ne. Abba zai naɗa sabon Kwamishina a Kano Yadda za a samu...
Da yake jawabi a wurin taron, Maj.-Gen. Waidi Shuaibu, kwamandan OPHK, ya ce matakin na daga cikin kokarin da ake yi na tabbatar da zaman lafiya a yankin da kuma dawo da wadanda rikicin Boko Haram ya shafa. Shuaibu ya jaddada aniyar rundunar na dawo da zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabas ta...
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya miƙa wa majalisar dokokin jihar sunan Ibrahim Yakubu Adamu domin tantancewa da tabbatar da naɗinsa a matsayin sabon Kwamishina. Kakakin Majalisar, Alhaji Jibrin Falgore ne ya bayyana hakan yayin da yake karanta wasiƙar gwamnan a zaman majalisar da ya gudana a yau Litinin. Yadda za a samu rufin asiri...
Adelaja ya jaddada mahimmancin ƙarfafa musayar bayanan sirri da haɗin gwiwar hukumomi, duba da irin kaifin basira da masu fasa-kwari ke amfani da wasu a ‘yan kwanakin nan wurin cimma muradunsu. “Masu fasa kwauri na ci gaba da bunkasa a ayyukansu, kuma don tunkararsu yadda ya kamata, dole ne mu hada kai ta hanyar...
Ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi ya bayyana a wajen taron manema labaru na ministan harkokin waje da aka shirya a harabar manyan tarukan kasar Sin guda biyu, lokacin da yake magana kan batun Taiwan cewa: suna daya tilo na Taiwan a Majalisar Dinkin Duniya shi ne “Lardin Taiwan na kasar Sin”. Kuma wasu...
Wani matashi mai sana’ar ɗinki, Malam Muhammad Sani Tela ya bayyana cewar, ya shafe fiye da shekara 30 ya na ɗinki. Ya ce wannan sana’a ta zama tamkar jini da tsoka a gare shi sakamakon yadda ya riƙe ta da hannu bibbiyu. Ko dai Gwamna Fubara ya yi murabus ko a tsige shi — APC...
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta bayyana cewa tattaunawa tare da barazana ba tattaunawa ake kiransa ba, sai dai tursasawa. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmael Baghaie ya na fadar haka a yau litinin a jawabin mako-makon da ya saba gabatarwa a ko wace ranar...