2025-03-12@16:18:47 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1608

«Sabon Kwamishina»:

    ’Yan bindiga sun kashe aƙalla manoma 14 yayin wani hari da suka kai yankuna huɗu a Ƙaramar Hukumar Akure ta Arewa da ke Jihar Ondo. Yankunan da abin ya shafa — Aba Alajido, Aba Sunday, Aba Pastor da Ademekun— galibi mazaunansu ƙananan manoma ne. Abba zai naɗa sabon Kwamishina a Kano Yadda za a samu...
    Da yake jawabi a wurin taron, Maj.-Gen. Waidi Shuaibu, kwamandan OPHK, ya ce matakin na daga cikin kokarin da ake yi na tabbatar da zaman lafiya a yankin da kuma dawo da wadanda rikicin Boko Haram ya shafa.   Shuaibu ya jaddada aniyar rundunar na dawo da zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabas ta...
    Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya miƙa wa majalisar dokokin jihar sunan Ibrahim Yakubu Adamu domin tantancewa da tabbatar da naɗinsa a matsayin sabon Kwamishina. Kakakin Majalisar, Alhaji Jibrin Falgore ne ya bayyana hakan yayin da yake karanta wasiƙar gwamnan a zaman majalisar da ya gudana a yau Litinin. Yadda za a samu rufin asiri...
    Adelaja ya jaddada mahimmancin ƙarfafa musayar bayanan sirri da haɗin gwiwar hukumomi, duba da irin kaifin basira da masu fasa-kwari ke amfani da wasu a ‘yan kwanakin nan wurin cimma muradunsu.   “Masu fasa kwauri na ci gaba da bunkasa a ayyukansu, kuma don tunkararsu yadda ya kamata, dole ne mu hada kai ta hanyar...
    Ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi ya bayyana a wajen taron manema labaru na ministan harkokin waje da aka shirya a harabar manyan tarukan kasar Sin guda biyu, lokacin da yake magana kan batun Taiwan cewa: suna daya tilo na Taiwan a Majalisar Dinkin Duniya shi ne “Lardin Taiwan na kasar Sin”. Kuma wasu...
    Wani matashi mai sana’ar ɗinki, Malam Muhammad Sani Tela ya bayyana cewar, ya shafe fiye da shekara 30 ya na ɗinki. Ya ce wannan sana’a ta zama tamkar jini da tsoka a gare shi sakamakon yadda ya riƙe ta da hannu bibbiyu. Ko dai Gwamna Fubara ya yi murabus ko a tsige shi — APC...
    Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta bayyana cewa tattaunawa tare da barazana ba tattaunawa ake kiransa ba, sai dai tursasawa. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmael Baghaie  ya na fadar haka a yau litinin a jawabin mako-makon da ya saba gabatarwa a ko wace ranar...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya ce shirin makamashin Nukliyar kasar Iran, na zaman lafiya ne, kuma babu wani shiri na samar da makaman Nukliya a cikinsa, sannan ya kara da cewa Iran ba za ta taba shiga tattaunawa da kasar Amurka mai cin zalin wasu kasashe ba. Kamfanin dillancin labaran IP na...
    Manya-manyan Jiragen ruwan yaki na kasashen Rasha da China sun isa tashar Jeragen ruwa ta Chabahar dake kudu maso gabacin kasar Iran a bakin tekun india don fara atisayen soje a tsakanin kasashen uku, wanda aka sanyawa suna ‘damarar tsaro na shekara ta 2025. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa wannan...
    Yau Litinin, aka rufe taro na 3 na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin wato CPPCC karo na 14 a nan birnin Beijing. Shugaban kasar Sin Xi Jinping da sauran manyan jami’an gwamnati da jami’yyar kwaminis ta kasar Sin wato JKS, sun halarci taron. A gun bikin rufe taron, an zartas...
    Jakadan kasar Rasha na din din din a cibiyoyin MDD da suke Vienna, ya bayyana cewa dakatar da aiwatar da yarjeniyar shirin Nukliya na kasar Iran wanda ake kira JCPOA, wacce kuma aka samar da shi a shekara ta 2015, da kasashen yamma suka yi, shi ne ya haddasa dukkan matsalolin da suka biyo baya....
    Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya ce gwamnatinsa ta dauki wani muhimmin mataki na tabbatar da tsaron makarantunta, inda za a hada hannu da masu ruwa da tsaki  don kara karfafa tsaro a yankunan da makarantu suke. Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan ne a yayin bikin bude taron masu ruwa da...
    Jam’iyyar APC ta yi kira ga Gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara da ya sauka daga mulki ko kuma a tsige shi. Shugaban APC na Jihar Ribas, Tony Okocha ne ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai yau Litinin a birnin Fatakwal. An cafke mutum uku kan satar wayoyin lantarki a Adamawa Abin da ya sa...
    ’Yan sanda sun cafke wasu mutum uku bisa zargin lalatawa da kuma satar wayoyin lantarki a ƙauyen Bororo da ke Ƙaramar Hukumar Michika ta Jihar Adamawa. An cafke ababen zargin ne da wayoyin lantarkin yayin wani sintiri da jami’an ’yan sanda suka gudanar a ranar 9 ga wannan wata na Maris. Abin da ya sa...
    Tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya tabbatar da sauya sheƙa daga jam’iyyar APC mai mulkin ƙasar zuwa jam’iyyar SDP. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da ya wallafa ranar Litinin ne a shafukansa na sada zumunta. ’Yan bindiga sun yi garkuwa da matashi a Kano Tsohon Mataimakin Gwamnan Kogi Patrick Adaba ya rasu El-Rufai ya...
    Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) tare da hadin gwiwar gwamnatin jihar Jigawa, sun fara horas da mata 600 kan inganta muhalli ta hanyar bola jari. Shugaban Hukumar Kare Muhalli ta Jihar Jigawa JISEPA, Alhaji Adamu Sabo ya bayyana haka a wajen taron tunawa da ranar mata ta duniya da kuma...
    Tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya tabbatar da sauya sheƙa daga jam’iyyar APC mai mulkin ƙasar zuwa jam’iyyar SDP. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da ya wallafa ranar Litinin ne a shafukansa na sada zumunta. ’Yan bindiga sun yi garkuwa da matashi a Kano Tsohon Mataimakin Gwamnan Kogi Patrick Adaba ya rasu El-Rufai ya...
    Tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya tabbatar da sauya sheƙa daga jam’iyyar APC mai mulkin ƙasar zuwa jam’iyyar SDP. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da a wallafa ranar Litinin ne a shafukansa na sada zumunta. El-Rufai ya ce, “yanzu na yanke shawarar komawa jam’iyyar Social Democratic Party, kuma zan kasance a cikin ta wajen...
    Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya fice daga jam’iyyar APC tare da komawa SDP. Majiyoyi sun ce ficewarsa ta biyo bayan rashin gamsuwa da tafiyar jam’iyyar. A cewar El-Rufai, APC ta kauce daga ainihin manufofinta, don haka ba zai ci gaba da kasancewa a cikinta ba. Ban Bar PDP Ba, Ina Gangamin Hadin Gwiwa...
    ’Yan bindiga sun yi garkuwa da wani matashi mai shekaru 20, Muhammed Bello a ƙauyen Zakirai da ke Ƙaramar Hukumar Gabasawa ta Jihar Kano. Aminiya ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne yayin da ’yan bindigar suka kai hari a gidan wani mai suna Alhaji Yusha’u Ma’aruf, wanda yake da wani asibiti mai zaman kansa...
    Wasu ‘yan bindiga sun farmaki gidan Alhaji Yusha’u Ma’aruf, mamallakin wani asibiti mai zaman kansa, a garin Zakirai da ke ƙaramar hukumar Gabasawa a jihar Kano, inda suka sace wani matashi mai shekaru 20 tare da jikkata ɗan uwansa. Rahotanni sun bayyana cewa maharan uku ɗauke da bindigogi da adduna sun afka wa gidan da...
    Ƙungiyar SERAP, mai fafutukar haƙƙin ɗan Adam da yaƙi da cin hanci da rashawa a Nijeriya, ta buƙaci Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio da ya gaggauta janye dakatarwar da majalisar ta yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan. SERAP ta ce dakatarwar da aka yi wa Sanata Natasha ba komai ba ne illa tauye mata ’yancinta...
    Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Da fatan Allah Ya amfanar damu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban bayani kan alherai goma ga ma’aurata cikin Ramadan. 4. Salon buɗa baki Ma’aurata za su yi amfani da lokacin buɗa baki don ƙara kusanci, farfaɗo da shau’uka cikin zuciya...
    Gwamnatin Isra’ila ta tura wa tawaga zuwa kasar Qatar a daidai lokacin da ake takun saka tsakanin Isra’ilar da masu shiga tsakani ciki har da Amurka. Wannan ya biyo bayan tattaunawar kai tsaye da ba a taba yin irinta ba tsakanin Hamas da wakilin Amurka Adam Boehler dake kula da mutanen da akayi garkuwa da...
    Shugabana kasar Ghana John Dramani Mahama, ya ziyarci kasashen Mali da Nijar a wani bangare na ran gadin diflomatsiyya da ya fara a kasashen sahel din nan uku da suka balle daga kungiyar Ecowas. Bayan birnin Bamako a ranar Asabar, shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama ya je birnin Yamai a ranar Lahadi, inda wasu...
    Tsohon Mataimakin Gwamnan Kogi, Cif Patrick Adaba ya riga mu gidan gaskiya. An ruwaito cewa Cif Adaba wanda ya shafe shekaru 78 a doron ƙasa ya rasu ne bayan ya yi fama da jinya a Abuja. Abba ya ƙaddamar da bincike kan zaftare albashin ma’aikatan Kano Blatter da Platini sun sake gurfana a kotu kan...
    Kasar Qatar ta bukaci hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa da ta sanya ido kan cibiyoyin nukiliyar Isra’ila. A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Qatar ta fitar ta bayyana cewa, Doha ta bukaci hukumar ta (IAEA) da ta sanya damar gudanar da bincike da ka’ida daga hukumar ta MDD, kan...
    Gwamnatin Isra’ila ta sanar da katse wutar lantarki a Zirin Gaza. Ministan Makamashi na Isra’ila Eli Cohen ne ya sanar da matakin da gwamnatin kasar ta dauka na katse wutar lantarki a zirin, a yayin da wasu rahotanni ke cewa mataki na gaba bayan katsewar wutar lantarkin, shi ne yanke ruwa a arewacin zirin Gaza....
    Tawagar matasan yan wasan ƙwallon ƙafa ta Nijeriya ta mata (Flamingos) ta yi nasarar doke mai masaukin baƙi Bantwana ta Afrika ta Kudu da ci 3-1 a wasan farko na gasar cin kofin duniya na mata ‘yan kasa da shekaru 17 na shekarar 2025 a filin wasa na Lucas Moripe, Pretoria a ranar Asabar, in...
    Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yi tsattsauran gargaɗi dangane da rahotannin da ke yawo kan cirar kuɗi daga albashin ma’aikatan gwamnati ko kuma ƙin biyan su gaba ɗaya. Ya bayyana hakan a matsayin cin zarafin ma’aikata da cin amanar jama’a, yana mai jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci hakan ba. Blatter da...
    Tsohon Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA) Sepp Blatter, da tsohon Shugaban Hukumar Kwallon Kafar Turai (UEFA) Michel Platini, sun sake gurfana a gaban wata kotu a kasar Switzerland, domin sake duba tuhume-tuhumen da ake musu na cin hanci da rashawa. Wata kotun daukaka kara ta musamman da ke zama a Muttenz ce ta...
    Shugaba Masoud Pezeshkian ya ce manufar Iran ta ginu ne kan  samar da hadin kai a yammacin Asiya, kamar yadda kuma ta yi imanin cewa duk wani rikici da tashin hankali a yankin to zai illata kowa. Pezeshkian ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da Firaministan Norway Jonas Gahr Støre a...
    Babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Naim Qassem ya bayyana cewa, gwagwarmayar al’ummar kasar Lebanon na nan da karfinta, duk da asarorin da ta yi da kuma sadaukarwa. A wata hira da yayi da tashar talabijin ta Al Manar, Sheikh Qassem ya bayyana cewa, ‘yan gwagwarmaya a kasar Lebanon sun yi nasarar cimma yarjejeniyar tsagaita bude...
    Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da tashin hankalin da ya farke a gabar tekun Syria a ranar Lahadin da ta gabata, a daidai lokacin da rahotanni ke nuna cewa an kashe wasu iyalai baki daya a wannan tashin hankali, abin da Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana a matsayin “mai matukar tayar da hankali”....
    Fiye da fursunoni 40 na Isra’ila da ke hannun kungiyoyin gwagwarmayar Falastinawa ne suka mutu a hare-haren da sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila suka yi ta kaddamarwa kan al’ummar yankin tun  daga ranar 7 ga Oktoba, 2023, kamar yadda wani rahoton baya-bayan nan na jaridar New York Times ya bayyana. Binciken, wanda jaridar ta New York...
    Rahotanni daga kasar Syria na cewa wata tawagar Majalisar Dinkin Duniya ta shiga birnin Jableh da ke yankin Latakia na kasar Siriya a karon farko a daren jiya Lahadi, kamar yadda wata majiya ta kasar ta shaida wa Al Mayadeen. Tawagar ta Majalisar Dinkin Duniya sun  zagaya a unguwannin Jableh, inda suka duba shaguna da...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Watan azumi lokaci ne da akan samu wasu ma’aikatu sun sassauta wa ma’aikata ta hanyar yi musu rangwame kamar rage musu yawan sa’o’in aiki. Sai dai a lokacin da waɗannan mutane suke samun rangwame, akwai waɗanda suke ayyuka ko sana’o’in da suka dogara da su ciyar da iyalansu....
    Shehun malami al-Imam Ibnu Juzai Allah Ya yi masa rahama, ya bayyana cewa babban dalilin da ya sa Alƙur’ani ya sauka shi ne kira ga bautar Allah da shiga cikin addininsa. Wannan magana tana da tushen ilimi mai zurfi wanda ke da nasaba da tauhidi da shari’a, da hikimar shiriya. 1. Tauhidi a Matsayin Asalin...
    A yayin bikin Ranar Mata ta Duniya, Hajiya Sa’adatu Ali Isa JC, matar Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Balanga da Billiri, ta tallafa wa mata 150 da injinan markaɗe domin su samu hanyar dogaro da kai. Da ta ke jawabi yayin rabon kayan, Hajiya Sa’adatu ta ce manufar wannan tallafi ita ce taimaka wa mata...
    Ministar kula da ma’aikata da al’umma ta kasar Sin Wang Xiaoping, ta ce kasar za ta kara albarkatu da kudi domin tallafawa samar da ayyukan yi a bana, a wani yunkuri na gina wani tsarin raya kasa mai samar da ayyukan yi. Wang Xiaoping ta bayyana haka ne a yau Lahadi, yayin wani taron manema...
    Assalamu alaikum masu sauraro sharhin bayan labarammu zai yi magana dangane da ‘Korar sojoijin Faransa daga kasa ta 7 a yammacin Afirka tare bukatar’ macron ya nemi uzurin kasashen’ wanda ni tahir amin zamn karanta. ///…Madalla, Bayan da kasashen Mali da Burkina faso, da Nigerda Ivory Coast suke kori sojojin Faransa daga kasashensu, a yanzun...
    Babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta sake ɗage babban taronta na ƙasa (NEC), zuwa ranar 15 ga watan Mayu, 2025. A wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar, wanda babban sakatarenta, Sunday Ude-Okoye, ya bayyana hakan. Iyalan Abacha sun gargaɗi Babangida kan ɓata sunan mahaifinsu An samu tsohon shugaban hukumar tsaron Faransa da zamba Tun asali,...
    Shugaban Majalisar shawarar musulunci ta Iran Muhammad Bakir Kalibaf, ya bayyana cewa; Babu yadda za a yi Iran ta zauna teburin tattaunawa da gwamnatin Amurka alhali tana yi ma ta barazana. Har ila yau ya ce zancen bayan nan na shugaban kasar Amurkan akan tattaunawa manufarsa ita ce yaudara da kuma kokarin raba Iran da...
    Kamfanin dillancin labarun “ Irna” ya nakalto cewa; Jiragen ruwa na soja da kuma dakarun kare juyin musuluni na Iran za su shiga cikin atisayen na hadin gwiwa da kasashen Rasha da kuma China. Bugu da kari da akwai wasu kasashen da za su turo sojojin masu sa ido, da su ne; jamhuriyar Azerbaijan, Afirka...
    Tashar talbijin din ‘almayadin’ mai watsa shirye-shirye daga Lebanon ta ambaci cewa; Wasu kauyuka na mabiya mazhabar Alawiyya dake Tartus, da kuma Lazikiyya, sun fuskanci hare-hare daga masu dauke da makamai. A yau Lahadi, masu dauke da makaman sun kutsa cikin wasu kauyukan Ramilah, Naq’a dake kusa da Jabalah. Daga jiya zuwa yau masu dauke...
    Masana a jami’ar Tehran sun samar da wani sabon salo na magance matsalar rashin haihuwa da wasu maza suke fama da shi. Ta hanyar aikin hadin gwiwa tsakanin injiniya a fagen kere-kere dake jami’ar Tehran Muhammad Mahdi Takiyyah, da kuma Mahdi Zand, da Mansurah muwahhidin daga jami’ar Tarbiyat-Mudarrris, an samar da hanyar magance rashin haihuwar...
    A bara, alkaluman tattalin arziki na GDP na kasar Sin sun kai yuan triliyan 134.9, inda aka samu karuwar kaso 5 cikin dari, lamarin da ya sa shi kasancewa tattalin arziki mafi saurin ci gaba cikin kasashen duniya masu karfin tattalin arziki. Ci gaban da ake samu na ingantuwar tattalin arzikin kasar ya haifar da...
    Iyalan marigayi Janar Sani Abacha, sun gargaɗi Tsohon Shugaban Mulkin Soja, Janar Ibrahim Babangida, da ya daina faɗin maganganun da ka iya ɓata sunan mahaifinsu. A cikin wata sanarwa da Mohammed Abacha, ya fitar a madadin iyalan marigayin a ranar Lahadi, sun musanta iƙirarin da Babangida ya yi a cikin littafinsa mai suna ‘A Journey...
    Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Balanga/Billiri a Jihar Gombe, Ali Isa JC, ya raba wa Musulmai da Kiristoci 2,000 kayan abinci don rage wahalar Azumin watan Ramadan da na Kiristoci. Ali JC ya bayyana cewa wannan tallafi yana da muhimmanci don sauƙaƙa wa jama’a gudanar da ibadarsu cikin sauƙi. An samu tsohon shugaban hukumar tsaron...
    Abin haka yake, akwai kasashe sama da 190 a duniyarmu, idan kowace kasa na bin manufar ba kanta fifiko, to nuna fin karfi zai zama a ko ina a duniyarmu, kuma kasashe masu karamin karfi su ne za su fi fuskantar matsalar. Amma abin farin ciki shi ne, har yanzu akasarin kasashen duniyarmu na rungumar...