2025-03-19@02:45:05 GMT
إجمالي نتائج البحث: 6

«dokar ta ɓaci a»:

    Dalilin wannan doka shi ne rikice-rikicen addini tsakanin Musulmai da Kiristoci a watan Satumba 2001, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 2,000.   A Jihar Borno Ma An Taɓa Sanya Dokar, Amma Ba A Jihar Baki Ɗaya Ba   A shekarar 2011, Shugaba Goodluck Jonathan ya ayyana dokar ta-ɓaci a wasu ƙananan hukumomin jihohin Borno, Adamawa, da Yobe saboda yawaitar hare-haren Boko Haram.   A 2013, Jonathan ya faɗaɗa dokar ta-ɓacin zuwa ɗaukacin jihohin Borno, Yobe, da Adamawa sakamakon tsanantar matsalar tsaro.   Wannan mataki ya bai wa jami’an tsaro ƙarin iko domin dawo da zaman lafiya.   Sai Kuma Jihar Ribas a Yanzu   Shugaba Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a Jihar Ribas saboda rikicin shugabanci...
    Iyalan marigayi Janar Sani Abacha, sun gargaɗi Tsohon Shugaban Mulkin Soja, Janar Ibrahim Babangida, da ya daina faɗin maganganun da ka iya ɓata sunan mahaifinsu. A cikin wata sanarwa da Mohammed Abacha, ya fitar a madadin iyalan marigayin a ranar Lahadi, sun musanta iƙirarin da Babangida ya yi a cikin littafinsa mai suna ‘A Journey in Service’. Ramadan: Ali JC ya bai wa jama’a tallafin kayan abinci a Gombe An samu tsohon shugaban hukumar tsaron Faransa da zamba Ya ce Janar Abacha ne, ya ke da alhakin soke zaɓen shugaban ƙasa na ranar 12 ga wata Yunin 1993. “Duk wani yunƙuri na ɗora wa Janar Sani Abacha laifin soke zaɓen, wanda a lokacin ya kasance babban jami’in soja a mulkin...
    Ana fargabar cewa wata gobara ta laƙume aƙalla shaguna 100 a Kasuwar Kara da ke Jihar Sakkwato. Gobarar wadda ta tashi tun da Asubahin wannan Asabar ɗin ta shafe sa’o’i 9 tana ta’adi. An raba wa ma’aikatan gona babura 200 a Yobe Yadda farashin kayan abinci ya sauka a kasuwannin Arewa Wani ɗan kasuwar da ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce tun da misalin ƙarfe 6:30 amma sai wurin ƙarfe 3:30 na rana aka samu nasarar kashe ta. A cewarsa, gobarar ta yi ta’adi a ɓangaren shagunan masu sayar da abinci da suka haɗa da gero, dawa da masara da shinkafa. Haka kuma, majiyar ta ce wutar ta yi ɓarna a ɓangaren masu ƙyamare da layin maƙera da masu...
    Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano ya ba al’ummar yankin Sheka awa 24 su kawo wa rundunar sunayen manyan ’yan daban da ke addabar yankin. Rundunar ta ba da wannan wa’adin ne bayan matsalar ’yan daba ta ya ƙi ci ta ƙi cinyewa a yankin da ke Ƙaramar Hukumar Kumbotso. A yayin wani zama na musamman da kwamishinan rundunar ta yi da al’ummar yankin ne aka ba su wannan sanarwar. Kwamishinan ’yan sandan, wanda ya samu wakilci DPO na yankin Dakata, ACP Yusha’u Mus’ud, ya ce muddin al’umma ba su taimaka da bayanan jagororin ’yan daban ba, ta ɓata-garin an kama su ba, babu yadda za a yi ɓata-garin su daina addabar yankin. Ɗan fashi ya yi wa ɗaliban jami’a uku...
    Wasu da ake zargin ’yan fashi ne sun yi awon gaba da wani jirgin ruwa ɗauke da fasinjoji 20 a hanyar ruwan daga Bonny zuwa Okrika a Jihar Ribas. Sai dai jami’ai a ƙaramar hukumar Bonny ta ce ta kuɓutar da tara daga cikin fasinjojin yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike don ceto sauran. Jirgin Amurka ɗauke da mutum 10 ya ɓace Magungunan Jabu: ’Yan majalisa sun nemi yin hukuncin ɗaurin rai da rai Shugaban Ƙaramar hukumar Bonny, Hon Anengi Barasua Claude-Wilcox ya ce, an ceto mutanen tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro. Claude-Wilcox a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Boma Waribor ya fitar a ranar Juma’a, ya ce direban jirgin...
    Ma’aikata a Jihar Alaska da ke Amurka sun bazama neman wani ƙaramin jirgin sama na kasuwanci a ranar Juma’a da ya ɓace ɗauke da mutum 10. Kamar yadda hukumomin yankin suka ce, a wani sabon afkuwar da ya afku ta jirgin Amurka. Magungunan Jabu: ’Yan majalisa sun nemi yin hukuncin ɗaurin rai da rai Lakurawa sun kashe mutum 1 sun jikkata 6 a Kebbi Rundunar ’yan sandan Jihar Alaska ta sanar da cewa, jirgin samfurin Cessna Caraɓan mai fasinjoji tara da matuƙin jirgi ɗaya ne, an samu rahoton ne ranar Alhamis. Jirgin da ya tashi daga Unalakleet zuwa Nome da ƙarfe 4:00 na yamma agogon Alaska (0100 GMT) da ya ɓace. Biranen biyu suna da nisan mil 146 (kilomita 235)...
۱