2025-03-31@02:30:42 GMT
إجمالي نتائج البحث: 14

«wanda yake yawan yin salati»:

    Imam sayyid Aliyul Khamina’ie Jagoran juyin juya halin musulunci na kasar Iran yayi kira ga mutanen kasar su fito kwansu da kwarkwatansu don halattar zanga-zangar ranar Kududs ta duniya a yau Jumma’a. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jagoran yana fadar haka a wani jawabin da ya gabatar a jiya Alhahamis da yamma. Ya kuma kara da cewa fitowar zanga-zangar ranar Kudus ta duniya alama ce ta hadin kan mutanen kasar Iran, sannan cika alkawali ne ga al-ummar kasar Falasdinu kan cewa mutanen kasar Iran ba zasu taba barinsu su, su kadai ba. Ranar Qudus ta duniya dai, rana ce wacce Imam Khomaini (q) wanda ya kafa JMI ya ware a ko wace ranar Jumma’a ta karshe...
    Kakakin ma’aikatar kasuwanci ta Sin He Yadong, ya bayyana a yau Alhamis cewa, kasar Sin za ta ci gaba da samar da kyakkyawan yanayin kasuwanci da ya dace da kasuwa, da doka da kuma mizanin kasa da kasa. He Yadong ya bayyana haka ne a gun taron manema labarai na yau da kullum, inda ya ce, a wannan lokaci da ake ciki, wasu manyan jami’an kamfanonin kasa da kasa na kawo ziyara kasar Sin. Kuma kamfanonin sun yi nuni da cewa, babbar kasuwa, da cikakken tsarin masana’antun samar da kayayyaki, da kuma karfin kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha na Sin, dukkansu babbar dama ce a gare su, kuma zuba jari a Sin yana nufin cin gajiyar wannan dama. Bugu da kari,...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan, a sakonsa na karshe ga Iraniyawa a shekara ta 1403 na kalandar Iraniyawa, ya bukaci mutanen kasar su hada kai don kaiwa ga manufofin kasar, wadanda suka hada da bunkasar tattalin arziki, da kauda tsadar rayuwa da kuma rashin bawa makiya damar cutar da kasar. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a jawabinda na ‘Nuruz’ ko sabon shekara ta 1404 wanda ya shigo yau. Pezeshkiyan ya bukaci All…ya yi rahama ga shuwagabannimmu da muka rasa a shekaran da ta kare, wadanda suka hada da Shahid Ibrahim Ra’isi da abokan tafiyar, da sharing maso gwagwarmaya a ciki da wajen kasar, wadanda suka hada da shahidan Lebanon Falasdin Siriya da...
    Rahotannin da suke fitowa daga yankin Gaza na kasar Falasdinu da aka mamaye sun nuna cewa, a cikin sa’o’ii 24 da suka gabata Falasdinawa 71 ne suka yi shahada a yayinda wasu da dama suka ji rauni. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa a wannan karon jiragen yakin HKI da jiragen ruwan yake daga tekun medeteranina sun cilla wuta kan garuruwan Beit –Lahia, Rafah da kuamKhan Yunus inda suka kashe da dama ko suka kaisu ga shahada. Labarin ya kara da cewa sojojin yahudawan sun sake mamayar yankin Netzarim wanda ya raba arewa da kudancin zirin gaza a yau Alhamis. Ya zuwa yanzu yawan falasdinawa da suka yi shahada ya kai 49,547 tun...
    Jaridar Financial Times ta Burtaniya ta bayyana cewa, masu zuba jari na kasashen waje suna kara “gano kasar Sin”, kuma sun yi imanin cewa, kasar Sin za ta iya samar da “kirkire-kirkire da damammaki” masu yawa a wasu fannoni. (Safiyah Ma) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan noma na kasar Gambiya Demba Sabally ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a kwanan baya cewa, goyon baya da taimakon fasaha na kasar Sin sun taka muhimmiyar rawa wajen samar da gagarumin ci gaba a fannin aikin gona na Gambiya a shekarun baya-bayan nan.  Ministan ya ce, yawan amfanin gona da kasar ta Gambiya ke samu na ci gaba da karuwa, inda yawan shinkafar da kasar ta samar ya haura tan 48,000 a shekarar 2024, wanda ya kafa tarihi. Sabally ya kuma bayyana cewa, kirkire-kirkire a fannin samar da ababen more rayuwa, da fasahohin aikin gona masu yawan gaske da tawagogin kasar Sin suka yi amfani da su, sun taka rawa wajen kai wa ga wannan matsayi. Halayen...
    Sun nuna wannan bukatar ce, biyo bayan hasashen raguwar bukatar Manfetur din da kuma dabarar fitar da shi, daga kasashen da ba sa cikin kungiyar ta OPEC+. Sai dai, a ranar Litinin da ta gabata kungiyar ta tsaya daram kan tsarinta na kara yawan Man da ake hakowa a watan Afirilu. Kazalika, binciken na kafar Reuters ya kuma gano yawan adadin karuwar Man na OPEC wanda ya kai Ganguna 80,000 da suke fitowa daga kasar Iran wanda ya kai Ganuna miliyan 3.30, wannan ya kai daidai na alkaluman watan Satumba, wanda ya haura tun a 2018. Bugu da kari, binciken ya sanar da cewa, fitar da danyan mai daga Iran ya farfado lokacin gwamnatin tsohon shugaban Amurka, Joe Biden duk...
    Rundunar ’yan sandan Kano ta kama wasu mutum huɗu da take zargi ’yan bindiga ne da tarin makamai da kuɗaɗe a hannunsu. Da yake yi wa manema labarai jawabi, mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce an cafke ababen zargin ne a ranar 6 ga wannan wata na Maris. NMDPRA ta ba da lasisin gina sabbin matatun mai 3 a Nijeriya Dalilin da muka dakatar da Sanata Natasha — Majalisar Dattawa SP Kiyawa ya ce an kama ababen zargin ne da kimanin naira 1,028,800 a gidan mai na Chula da ke unguwar Hotoro suna ƙoƙarin sayen bindigar AK-47. Sanarwar ta ce an samu mutanen huɗu waɗanda dukkansu matasa ne da wasu ƙananan bindigogi ƙirar gida, da...
    Yayin da aka fara tsinkar tumatari dan rani a Kano da sauran jihohin da ke samar da tumatar a fadin Nijeriya, rahotanni sun bayyana cewa, farashinsa ya fadi sosai fiye da yadda aka yi zato, lamarin da ya jefa manoman cikin damuwa. Binciken da Jaridar Aminiya ta gudanar ya nuna cewa, a halin yanzu, ana sayar da kwando daya na tumatir a kan Naira 3,500, yayin da ake sayar da babban kwando a kan Naira 10,000. 40% na matan Kano sun fuskaci cin zarafi a gida —Shugaban Majalisa Dan kwallon Najeriya ya mutu bayan fadowa daga bene a Uganda Wani manomin tumatir, Isah Bello Abba ya bayyana cewa, wannan yanayi ya sa manoma cikin fargaba saboda sun kashe kudade masu...
    Yau Alhamis, ma’aikatar kula da kasuwanci ta Sin ta sanar cewa, tun bayan kaddamar da bikin sayen kayayyakin daddadun kantuna na shekarar 2025, manyan ayyukan da suka shafi bikin sun sa yawan kudin da aka kashe ta intanet da kuma a zahiri ya zarce yuan biliyan 1.6. An ba da rahoton cewa, bikin sayen kayayyakin daddadun kantuna na shekarar 2025, wanda ma’aikatar kula da kasuwanci, da babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG, da kuma gwamnatin birnin Beijing suka shirya tare, tun daga ranar 7 ga watan Janairu, ya sa kananan hukumomi daban daban da kuma dandamalin kasuwanci ta intanet sun mayar da hankali kan lokacin bikin bazara, kuma sun kaddamar da ayyuka fiye da 100 don...
    An bayyana cewa  Iran ce kasar ta 10 a duniya wajen samar da wutar lantarki, da yawan megawati dubu 94 da 846. Manajan da yake kula da tsara manyan ayyuka a ma’aikatar makamashi ta Iran, Behruz Muradi ya bayyana cewa, shekru 46 da su ka gabata, wato a lokacin juyin juya halin musulunci, yawan megawatin da Iran take samarwa ya yi kasa da wanda ake da shi a yanzu har sau hudu. Manajan ya kuma kara da cewa wutar lantarki da ake da ita a Iran da karfin tsarin da take da shi, tana taka rawa mai muhimmanci wajen gina tattalin arzikin kasar. Haka nan kuma ya ce, da akwai kyakkyawan tsarin da ake da shi ya samar da cigaba...
    Darakta-Janar na Hukumar yi wa kasa hidima ta kasa NYSC, Birgediya Janar Yushau Ahmed, ya tabbatar wa masu yi wa kasa hidima a fadin kasar nan cewa ba za a tura su yankunan da ke da kalubalen tsaro ba. Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga matasa masu yi wa kasa hidima da ke samun horo a sansaninsu da ke Gusau, babban birnin jihar Zamfara. Darakta Janar na NYSC wanda ke rangadi a sansanin masu yi wa kasa hidimar a jihar Zamfara, ya bayyana jin dadinsa kan yadda ak tsaurara matakan tsaro a sansanin. Ya jaddada cewa, tsaro da jin dadin matasan na da matukar muhimmanci ga hukumar. Birgediya Janar Ahmad ya jaddada bukatar...
    Hukumar kwastam ta kasar Sin ta ce an samu ci gaba sosai a yawan kayayyakin da Sin ta fitar zuwa kasashe da yankuna 160 na duniya a shekarar 2024. Alkaluman da hukumar ta fitar sun nuna cewa, yawan kayayyakin da kasar ta fitar ya karu da kaso 7.1 a shekarar, wanda ya kai yuan triliyan 25.45, kimanin dala triliyan 3.55, shekaru 8 a jere ke nan ana samun wannan ci gaba. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
    Wani jami’in gwamnati a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo ya sanar da cewa yanzu haka sojojin ƙasar ne ke iko da mafi yawan unguwannin birnin Goma, da ke gabashin ƙasar. Muhingo Nzangi, wanda shi ne ɗan majalisa mai wakiltar yankin ya shaida wa ƴan jarida cewa sojojin sun yi maganin ƴan tawayen M23 waɗanda MDD ta ce na samun goyon bayan Rwanda. Sai dai har yanzu ƴan tawayen na iƙirarin cewa suna iko da birnin. Wakiliyar BBC ta ce M23 na ikirarin cewa tana kokarin kare tsirarun ƴan ƙabilar Hutu ne waɗanda ake ci wa zarafi, kuma wannan lamari ne da Rwanda take goyon baya, sai dai ta ce ba ta tsoma hannu kai-tsaye cikin rikicin ba duk kuwa da cewa Majalisar...
۱