2025-04-12@20:52:40 GMT
إجمالي نتائج البحث: 838

«Yan uwa»:

    Lamarin ya faru ne a lokacin da matashin mawakin yake kan dandamali ya na rera daya daya daga cikin fitattun wakokinsa, har zuwa lokacin wannan rahoto, Bilal Billa bai fitar da wata sanarwa a kafafen sadarwar ba, amma kuma faruwar lamarin ya janyo cece kuce inda wasu a bangare guda ke ganin abin da aka...
    Daga karshe ta ce da farko ta samu turjiya daga wajen wasu mutane a kan kudurinta na fara harkar fim amma kuma ta yi biris dasu ta fara, amma kuma yanzu wadanda a baya ke hanata shiga fim su ne yanzu ke yi mata murnar samun nasara hakan ya matukar bata mamaki, duba da cewar...
    Ilimi Gishirin Rayuwa Babu shakka ba tun yanzu ba, dan’adam ya dade da fahimtar muhimmancin ilimi ga cigaban rayuwarsa. Walau ilimin addini ko na cigaban rayuwa. Addinin Musulunci ya koyar da mu muhimmancin bai wa ilimi fifiko, kamar yadda aka rawaito a cikin Hadisi. Ma’aikin Allah (SAWA) yana cewa ‘mu nemi ilimi ko da...
    Ga kuma yadda ake sarrafawa: Da farko, a zuba ruwa a tukunya a sa a wuta domin ya tafasa. A rage wuta kadan, sannan a zuba garin alabo a hankali cikin ruwan da ke tafasa, ana juyawa da muciya ko cokali ko leda mai kauri don kada ya yi kolalla. A ci gaba da juyawa...
    Tun da safiyar yau Asabar ne dai ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci ya isa birnin Mascut na kasar Oman da can ne za a yi tattaunawar da ba ta gaba da gaba ba a tsakanin jamhuriyar musulunci da Amurka. Jim kadan bayan isar tasa birnin Mascut ministan harkokin wajen na jamhuriyar musulunci ta Iran...
    Al’ummar garin Idi Araba da ke Ƙaramar Hukumar Munshin a Legas sun wayi gari da fashewar wani abu mai ƙarar gaske, wanda ya tayar da gobara a wani garejin ’yan gwangwan da ke unguwar. Lamarin da ya faru ranar Alhamis na makon jiya ya yi sanadiyar mutuwar wani da ke sana’ar gwangwan mai suna Najib...
    Hukumar da take kula da hakkin bil’adama ta MDD ta bayyana cewa; Mafi yawancin wadanda yaki ya rutsa da su a Gaza mata ne da kananan yara. Mai Magana da yawun hukumar ta kare hakkin bil’adama ta MDD Rafina Shamdsani ce ta bayyana hakan a wurin taron hukumar da aka yi a birnin Geneva tana...
    Sojojin kasar Yemen sun yi amfani da jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa kan cibiyoyin makamai na HKI wadanda suka Yaffa (tel aviv) saboda daukar fansa kan kashe-kashen da take yi a Gaza. Tashar talabijin Presstv a nan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labaran YAF na kasar Yemen yana fadar haka a jiya Jumma’a,...
    Ya zamto kowacce rana kina hada salad me yawa ki cinye shi, kar ki cika cin abin da zai birki ta miki ciki don kuwa shifa zai dinga rage miki ruwan jikinki ne, ki dage da cin kayan dadi sosai a wannan watannin. (2b) Abubuwa masu mahimmacin da ya kamata su zama abincinki: Tuffa, Baure,...
    Shugaban hukumar yan gudun hijira na MDD Filippo Grandi wanda ya ziyarce sansanonin yan gudun hijira na kasar Sudan a Chadi ya bayyana cewa akwai bukatar kasashen duniya su taimaka don kula da bukatun yan kasar sudan wadanda suke gudun hijira a kasar Chadi. Grandi ya kara da cewa akwai bukatar agaji da gaggawa zuwa...
    Ministan ya ce maganar da ya faɗa da farko wadda ba a ruwaito ta a daidai ba ita ce: “E, lallai an samu cigaba a harkar tsaro a sassa daban-daban na ƙasar nan, ko da yake ba a kawar da duk wani aikin tashin hankali gaba ɗaya ba. “Hukumomin tsaro suna aiki ba dare ba...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Masu shigar da kara sun bukaci kotun da ta hana wadannan jami’an gudanarwa gudanar da taro, ko kuma jagorantar babban taron jam’iyyar na kasa, bisa hujjar cewa an kore su daga jam’iyyar NNPP. Ko da yake, alkali mai shari’a Justice MA Hassan ya yanke hukuncin cewa kotun ba ta da hurumin sauraren karar, inda ya...
    ’Yan bindigan da suka sace Fasto Samson Ndah Ali na cocin ECWA da ke Mararaba Aboro a Ƙaramar Hukumar Sanga ta Jihar Kaduna, sun sake shi sannan sun tsare wanda ya kai kuɗin fansar, Yusuf Shehu Ambi, wanda shi ne sakataren cocin. Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Aminiya...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ba kamar kayayyakin manyan kamfanoni irin su Ajinomoto, Bedan wadanda aka zuba su a cikin kwali, ana sayar da su cikin lafiyayyen mazubi kuma NAFDAC ta amince da su ba, wadannan danyun kaya ne da ba su da wata alama. Babban abin ban tsoro shi ne ba za a iya gano masana’antunsu don bincikar sahihancinsu...
    ’Yan bindiga sun kai hari garin Mahuta da ke Ƙaramar Hukumar Kafur a Jihar Katsina, inda suka harbi wani alkali, Rabiu Mahuta, a hannu da kuma dansa. A lokacin harin na daren Talata, maharan sun raunata mutane uku tare da yin garkuwa da wasu mutane 13, ciki har da matar alƙalin da kuma biyar daga...
    Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana gamsuwarta da yadda ake ci gaba da gudanar da ayyukan gina tituna da gyare-gyare a fadin jihar.   Kwamishinan ayyuka da samar da ababen more rayuwa na jihar Alhaji Lawal Barau Bungudu ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Gusau babban birnin jihar.  ...
    Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara, ta ce an shirya shirye-shirye domin karfafa tsaro a jihar da kuma tabbatar da mazauna yankin suna rayuwa cikin yanayi na zaman lafiya da tsaro.   Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Adekimi Ojo ne ya bayyana haka da yake zantawa da manema labarai a hedikwatar ‘yan sanda da ke Ilorin.  ...
    Sama da gidaje dari biyu da arba’in ne aka lalata a daren Talatar da ta gabata, ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka shafe sa’o’i ana yi a unguwar Garin Kestu Atuwo dake karamar hukumar Shanga ta jihar Kebbi.   Da yake jajantawa wadanda abin ya shafa, Gwamna Nasir Idris ya shawarci gidajen da...
    Mataimakin shugaban kasar wanda ya samu wakilcin Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Na Musamman Kan Ayyuka Na Ofishin Mataimakin Shugaban Kasa, Aliyu Modibbo Umar ya ce, “Kalubalan Nijeriya ya ta’allaka a tsarin tarayyarmu,” in ji Shettima. “Ba batu ne na wai nawa ne kowace rukunin tarayya ke samu ba, magana ce ta yadda ake amfani...
    Rahotanni daga kasar Yemen sun ambaci cewa jiragen yakin Amurka sun kai jerin hare-hare a yankuna mabanbanta na kasar Yemen da su ka hada da birnin San’aa. Tashar talabijin din al-masirah ta ambaci cewa; jiragen yakin Amurka sun kai hare-haran ne har sau 7, biyu a cikin yankin Hamadan, da Banu Hashish sai kuma babban...
    Fira ministan HKI Benjamine Netanyahu ya yi suka cikin fushi saboda Fira ministan kasar Mark Carney  Canada ya bayyana cewa abinda yake faruwa a Falasdinu kisan kiyashi ne. Shi dai Fira ministan kasar Canada Mark Carney wanda ya halarci taron yankin neman zabe a garin Calgary, yayin da wani daga cikin mahalarta, ya daga murya...
    Sojojin HKI suna ci gaba da yin kiyashi a sassa mabanbata na Gaza, da a bayan nan su ka yi wa mutane 30 kisan kiyashi a unguwar Shuja’iyya dake birnin Gaza.  Majiyar asibitin Falasdinawa ta ambaci cewa; Harin da sojojin HKI su ka kai da manyan bindigogi sun yi sanadiyyar shahadar mutane 17 a unguwar...
    Ana fargabar matafiya da dama sun rasu bayan kifewar wani  kwalekwale ɗauke da ’yan kasuwa a yankin Kogin Neja. Hatsarin kwalekwalen ya auku ne ƙauyen Sokun da ke yankin Ƙaramar Hukumar Lapai, a sakamakon iska mai ƙarfi da ta haddasa juyawar igiyar ruwan. Shaidu sun ce hatsarin ya auku ne a yayin da kwalekwalen ke...
      Daga nan sai ya ce, kasar Sin na aiwatar da matakan ramuwar gayya na wajibi game da cin zalin Amurka, ba kawai don kare ikon mulkin kanta, da kare tsaro da muradun ci gabanta ba ne, har ma da tabbatar da gaskiya da adalci tsakanin sassan kasa da kasa, da wanzar da tsarin cinikayyar...
    Gwamnatin Yobe ta bayyana shirinta na mayar da tubabbun mayaƙan Boko Haram cikin al’ummarsu da aka yi wa shirin kawar da tsattsauran ra’ayi, gyara da sake haɗewa da iyalansu ƙarƙashin rundunar Operation Safe Corridor (OPSC). Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ne ya bayyana haka a ranar Alhamis a Damaturu lokacin da ya karɓi baƙuncin...
    Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bada sanarwan cewa yana kokarin cimma matsaya da kasar Chaina dangane da kamfanin sadarwa da kuma yanar gizo na TIK Tok. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto shugaban yana fadar haka a shafinsa na ‘Trump Social, Labarin ya kara da cewa shugaban yana fadar haka a...
    Sojojin HKI wadanda suka yi ritaya da kuma masu jiran aiki ko Reserv sun watsa wata bukata da suka rubuta ta kawo karshen yakin da Benyamin Natanyahu yake jagoranta a Gaza. Sojojin sun kara da cewa a halin yanzu yakin yana cimma manufar Natanyahu ne kawai, ba don manufar HKI ake yins a ba. Kamfanin...
    Wadannan ayyuka domin inganta harkar ilimi da kuma nuna gaskiya, sun sa Jigawa ta zama abin koyi ga sauran jihohi.   Tunda farko, Gwamna Malam Umar Namadi, a nasa jawabin, ya ce gwamnati ta dauki kwakkwaran matakai na magance matsalar rashin ilimi bayan wani bincike da wani masani mai zaman kansa ya fitar cewa, yawancin...
    Jigo a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya bayyana yadda Shugaba Bola Tinubu, ya taimaki ’yarsa ta samu aiki a Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Ƙasa (NUPRC). Galadima, ya bayyana haka ne yayin wani shiri a gidan talabijin na AIT. Matatar Ɗangote ta rage farashin fetur zuwa N865 Yadda masu safarar ɗan Adam ke...
    Jigo a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya bayyana yadda Shugaba Bola Tinubu, ya taimaki ’yarsa ta samu aiki a Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Ƙasa (NUPRC). Galadima, ya bayyana haka ne yayin wani shiri a gidan talabijin na AIT. Matatar Ɗangote ta rage farashin fetur zuwa N865 Yadda masu safarar ɗan Adam ke...
    Gwamnatin Najeriya ta nuna damuwarta kan yadda masu safarar mutane ke ƙara amfani da kafafen sadarwa na zamani wajen yaudarar mutane da kuma yi musu cin zarafi, inda ta bayyana hakan a matsayin barazana wadda ba ta da iyaka kuma mai saurin yaɗuwa wadda ke buƙatar ɗaukar mataki cikin gaggawa. Da yake jawabi a taron...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Irin alaƙar da ke tsakanin wasu abokai na da matuƙar kusanci da kyau, ta yadda a wasu lokutan ma ba a iya banbance dangantakar tsakaninsu ta ’yan uwan na jini ko kuma abota. Irin wannan dangantaka ya kamata ne a ce ana samun ta a tsakanin ’yan uwa...
    A ranar Talata ne mai martaba Sarkin Kano Malam Mohammad Sunusi II ya amince da nadin Alhaji Mannir Sunusi a matsayin sabon Galadiman Kano.   Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban ‘yan jarida da yada labarai na masarautar Kano, Saddam Nasir Na’ando ya fitar, kuma ya mika wa gidan rediyon Najeriya...
    Mazauna karamar hukumar Gezawa ta Kano sun shiga cikin tashin hankali da makoki sakamakon nutsewar wasu mata biyu a cikin wani tafki.   Rahotanni sun nuna cewa matan (an sakaya sunansu) sun gamu da ajalinsu ne a lokacin da suke wanka a kogi bayan sun dawo daga aiki a wata masana’antar sarrafa hibiscus.   A...
    Ya tabbatar da cewa majalisar za ta ci gaba da mara wa shirye-shiryen da za su bunƙasa ilimi da jin daɗin al’umma baya. Shugaban majalisar ya ƙara da cewa salon shugabancin gwamnan wanda ke ku8nshe da gaskiya da riƙon amana ya taimaka wajen amincewar jama’a ga gwamnati. Ya ce Gwamna Yusuf jagora ne mai sauraron...
    Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya nuna kaɗuwar sa bisa rashin da aka yi na ɗan Majalisar Dokokin jihar, Hon. Aminu Ibrahim Kasuwar Daji, ɗan Majalisa mai wakiltar mazaɓar Ƙauran Namoda ta Kudu. Iyalai sun bayyana cewa Hon. Aminu Kasuwar Daji ya rasu ne a cikin barcin sa da asubahin ranar Larabar nan a...
    “Ina rokon Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta masa, ya sa ya huta har abada.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) za ta hada gwiwa da kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ) a yaki da hako ma’adinai da kuma ayyukan ta’addanci a kasar nan.   Mukaddashin Daraktan shiyyar Kaduna mai kula da shiyyar Kaduna, Mista Bawa Usman Kaltungo ne ya bayyana hakan a lokacin da ya...
    “Ina rokon Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta masa, ya sa ya huta har abada.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Assalamu alaikum masu sauraro barakammu da war haka, sharhin bayan labarummu zai yi magana dangane da ‘Siyasar Amurka ta fara yakin kudaden fito tsakaninta da China da kasashen Turai da sauransu. Wanda ni tahir amin zan karanta. ///.. A ranar laraba 2 ga watan Afrilun da muke ciki ne shugaban kasar Amurka Donal Trump ya...
    Domin tabbatar da bin bin doka da oda a tsakanin al’umma, ma’aikatar muhalli da sauyin yanayi ta ce za ta fara wani gangamin wayar da kan jama’a na tsawon mako takwas.   A cewar kwamishinan, gangamin zai mayar da hankali ne wajen wayar da al’umma, masana’antu, da sauran masu ruwa da tsaki kan sabbin dokokin...
    Rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara ta tabbatar da wani mummunan hari da ‘yan bindiga suka kai a garin Banga, da ke cikin karamar hukumar Kauran Namoda, inda aka kashe mutane biyu tare da sace wasu da dama. Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda ta jihar, DSP Yazid Abubakar, ne ya bayyana hakan cikin...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa JMI ba zata taba jada baya a kan shirinta na makamashin Nukliya ba, kuma yayi allawadai da duka wani shiri na kaiwa cibiyoyin nukliyar kasar Hare-hare. Tashar talabijin ta Presstv ta nakalto shugaban yana fadar haka a taron raya ranar Nukliya ta karo karo na 19 a...
    Jiragen yakin HKI sun kashe akalla mutane 38 a wurare daban-daban a zirin Gaza, kuma mafi yawan wadanda ta kashen yara kanana ne. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar Falasdinawa a Gaza na cewa da sassafe jiragen yakin sun kaiwa wani gidan Bene a unguwar shujaiyya na wajen garin Gaza inda...
    A ran 7 ga watan nan da muke ciki bisa agogon gabashin kasar Amurka, kasar ta Amurka ta kara barazanar kakkaba wa Sin karin haraji na kashi 50%, kasar Sin a nata bangaren ta bayyana aniyarta ta daukar matakan da suka dace don kare muradunta.   Tattalin arzikin Sin na samun bunkasa yadda ya kamata...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira da a gina al’umma mai kyakkyawar makomar bai daya tare da kasashe makwabta, da kuma kokarin bude sabon babi na ayyukan da suka shafi kasashe makwabtan kasar Sin.   Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kwamitin kolin...
    An yi kira ga Gwamna Mohammed Umar Bago na jihar Neja da ya sanya baki kan rikicin fili mai fadin sama da hektar saba’in da biyar da ake zargin Hakimin Tegina da ke karamar hukumar Rafi ya kwace daga hannun mamallakinsa a Pangu Gari.   Babban Limamin Pangu Gari, Alhaji Umar Musa Danladi ne ya...