2025-02-20@08:54:00 GMT
إجمالي نتائج البحث: 8
«kwayoyin cuta»:
Kiyaye taruwar maiƙo da kwayoyin cuta a fuska da kirji. Wannan kan dan yi wahala amma ta wadannan dabaru za a samu nasara: 1- Rage maiƙo a cikin abinci. Misali, idan aka soya wani abinci, yana da kyau a tsane mai da mayanin kicin wafif ko tawul ko tushu mai tsabta kafin a ci. Idan an yi haka an rage man kusan da kashi hamsin cikin dari ko ma fiye. 2- Yin amfani da sabulu mai kashe kwayoyin cuta wajen wanke fuskar safe da yamma. 3- Shan kayan itatuwa da cin ganyayyaki a kai –a-kai ya kan tsane maikon cikin jini ya kara karfin garkuwar jiki wajen yakar kwayoyin cuta. 4- Ga wanda wadannan Dabaru ba su yi musu aiki...
In an taba rarrauna a gabanka, kana da ikon kare masa, to ka kare masa, kin kare masa sakaci ne ba hakuri ba ne. An ruwaito cewa, Annabi (SAW) bai taba dukan wata daga cikin Matansa ba ko kuma cikin masu masa hidima a gida ko a waje. An kama wani Mutum da yake shirin kashe Annabi (SAW), aka gurfanar da shi gaban Annabi (SAW), sai jikinsa ya fara makyerkyata, Annabi (SAW) ya ce masa, kar ka firgita, ko da ka yi niyyar kashe ni, Allah ba zai dora ka a kaina ba. Zaidu dan Sa’anatal Yahudi ya zo wurin Annabi (SAW) kafin ya Musulunta yana neman Annabi (SAW) ya biya shi bashin da ya karba a wurinshi. Sai ya...
Hukumar yaƙi a sha da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA) reshen Jihar Kano ta kama wani tsoho mai shekaru 75, Nuhu Baba, bisa zargin sayar da miyagun ƙwayoyi ga matasa. Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Sadiq Muhammad-Maigatari, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata a Kano, inda ya ce wanda ake zargi ya amsa laifinsa, yana mai cewa ya rungumi sana’ar ne domin rayuwa a unguwarsu da ke ƙaramar hukumar Gezawa. NDLEA Ta Cafke Masu Ta’ammali Da Ƙwayoyi 18,500 A 1 – Marwa NDLEA Ta Gargadi Iyaye Kan Bayyanar Alawar Ƙwaya A Kano Hukumar ta kwato nau’ikan kwayoyi daban-daban, ciki har da Tramadol, wiwi, Diazepam, Exol-5 da man shafawa mai sa maye. Kakakin hukumar...
Sin: Kasar Amurka Ce Ta Haifar Da Matsalar Miyagun Kwayoyi A Cikin Gidanta
“Sauran abubuwan baje kolin da aka kwato daga hannun mutanen biyu sun hada da: bindigogi guda uku da aka kera a cikin gida; bindiga guda da aka yi a gida guda biyu; bindigar zamani guda daya; bindigar gida guda daya; cartridges guda uku da 9mm mara komai da gatari mai kan karfe. “Wani farmakin da aka kai Legas, ya kai ga kama skunk mai nauyin kilogiram 47, wani nau’in tabar wiwi, da kuma Nitrous Odide mai nauyin kilogiram 25.46 da aka fi sani da dariya a unguwar Akala da ke Mushin,” Babafemi ya kara da cewa. A Jihar Ekiti, Babafemi ya ce jami’an NDLEA sun kama wani matashi dan shekara 26 mai suna Adepoju Taiwo, dauke da kilo 1.950 na...
Hukumar yaƙi da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi (NDLEA) reshen Jihar Yobe ta ce ta kama wasu haramtattun ƙwayoyi da nauyinsu ya kai kilo 537 tare da kama wasu mutum 46 da ake zargi da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi a shekarar 2024. Kwamandan hukumar ta NDLEA a Jihar Yobe, Mista Abdulazeez Ogungboye ne ya bayyana hakan a Damaturu yayin da yake bitar ayyukan hukumar na shekara guda da ta gabata. Kiristoci sun yi addu’ar ɗorewar zaman lafiya a Kudancin Kaduna DAGA LARABA: Dalilan Da Mutane Suke Son Haihuwar Maza Fiye Da Mata Ya ce magungunan da aka kama sun haɗa da kilo 396.526 na tabar wiwi da kilo 141.2 na sauran kayayyakin maye. Ogunboye ya ce hukumar ta miƙa mutane 21...

An Kammala Gwaje-Gwajen Wasan Kwaikwayo Na Shirye-Shiryen Bikin Sabuwar Shekarar Sinawa Na CMG Na 2025
An gudanar da gwajin wasan kwaikwayo karo na biyar na shirye-shiryen bikin sabuwar shekarar Sinawa na CMG na 2025 jiya Lahadi. Ya zuwa yanzu, an kammala dukkanin ayyukan share fagen shirye-shiryen bikin sabuwar shekarar Sinawa na CMG na 2025. (Safiyah Ma)
Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke Fagge ’Yan Alluna a Jihar Kano, ta yanke wa wani matashi hukuncin ɗaurin shekara biyu, a gidan yari bayan samun sa da laifin satar wayoyin salula. An gurfanar da Aliyu Rabi’u Rijiyar Lemo a gaban kotun, bayan kama shi a kan titin Ibrahim Taiwo tare da wasu biyu, inda suke amfani da Adaidaita Sahu wajen satar wayoyin hannun fasinjoji. ’Yan bindiga sun sace matashiya bayan karɓar kuɗin fansa a Kano ’Yan bindiga sun sace mutum 22 a ƙauyukan Kaduna A wajen da aka kama shi, wasu fusatattun mtsne sun ƙone Adaidata Sahun da suke amfani da shi wajen aikata laifin. An tuhume shi da haɗa baki don aikata laifi, sata, da tayar da hankalin...