2025-03-03@21:22:31 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1294

«Kwamishina»:

    Kungiyar Hamas ta bada sanarwan cewa gwamnatin HKI a yankin yamma da Kogin Jordan tana rusa gidajen Falasdinawa a sansanin yan gudun hijira na Nur- Ashamsh, a ranar farko ta watan Ramadan mai alfarma. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar Nihad Ashawish shugaban kwamitin mai kula da sansanin yan gudun hijirar...
    Gwamnatin kasar masar ta tabbatarwa gwamnatin Falasdinawa kan cewa tana goyon bayan falasdinawa a cikin dawo da hakkinsu, na kafa kasarsu mai cikekken yanci wacce take da gabacin birnin Qudus a matsayin babban birnin Kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Mostafa Madbouly ministan harkokin wajen kasar Masar yana fadar haka a...
    An kaddamar da taro na 10 na zaunannen kwamitin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin wato CPPCC karo na 14 a yau 1 ga watan Maris a nan birnin Beijing, inda memban hukumar siyasa na kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta Sin kuma shugaban majalisar CPPCC Wang Huning ya halarci taron....
    Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta gamu da cikas a kokarinta na darewa kan teburin gasar Laliga ta kasar Sifaniya, bayan rashin nasarar da ta yi a hannun Real Betis a filin wasa na Benito Villamarin da ke Seville. Tsohon dan wasan Real Madrid, Isco Alacon ne ya lashe kyautar gwarzon dan wasa a...
    Rundunar ’yan sandan Kano ta cafke wasu matasa biyu kan zargin satar wayoyin hannu a kasuwar waya ta Beirut da ke birnin na Dabo. Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ta ce an cafke ɗaya daga cikin ababen zargin ne yana yunƙurin satar waya a wani shago....
    Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Hansi Flick, ya bayyana cewa kungiyarsa za ta je har gidan Atletico Madrid ta doke ta a wasan kusa da na karshe na gasar cin kofin Coppa Del Rey, bayan da Barcelona da Atletico Madrid suka tashi 4-4 a wasan farko zagayen daf da karshe a Copa del Rey...
    Shugabar kasar Tanzaniya Samia Suluhu Hassan ta bayyana a jiya Juma’a cewa, tashar jirgin ruwa ta Tanga da kasar Sin ta inganta yanzu tana jigilar sama da tan miliyan 1.2 na kaya a duk shekara, adadin da ya karu daga jigilar tan 400,000 a kowace shekara. “Habaka tashar ta Tanga ya inganta ayyukanta.” a cewa...
    Salah ya kasance danwasa na farko a gasar Premier da ya ci ya kuma bayar aka ci a wasanni daban-daban har goma a kaka daya. Sannan shi ne danwasa na farko da ya yi haka a daya daga cikin manyan gasar Turai biyar tun bayan Lionel Messi da ya yi wannan bajinta a kakar 2014-15,...
    Shugaban Ƙasar Ukraine, Volodymyr Zelensky ya ce bai ga laifin da ya yi wa Shugaban Amurka Donald Trump, ballantana ya nemi afuwa. Zelensky ya bayyana haka ne bayan zazzafar cacar-baki da ya kaure a tsakaninsa da Trump a ofishin shugaban ƙasar Amurka. A cewarsa, “ina godiya ga Amurka da gudunmuwar da take ba mu,” in...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi watsi da shawarar da Isra’ila ta gabatar na tsawaita matakin farko na yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza, inda ta yi kira ga kasashen duniya da su matsa wa gwamnatin mamayar lamba don ci gaba da mataki na biyu na yarjejeniyar kamar yadda aka tsara tun farko. Yau...
    Shugaban kungiyar Ansarallah ta kasar Yemen Sayyed Abdul-Malik Al-Houthi, ya bayyana cewa Isra’ila na fakewa da goyan bayan Amurka tana keta yarjeejniyar tsagaita wuta a Gaza. Al-Houthi ya bayyana cewar: Kin janyewar makiya daga yankin Rafah, ya zamanto karara karya yarjejeniyar da aka kulla tsakanin Masar da makiya yahudawan sahyoniya. » Ya kara da cewa:...
    Shugabannin kasashen Afirka ta Kudu da Malaysia da Colombia sun jaddada aniyarsu ta hana jiragen ruwa da ke dauke da makamai zuwa Isra’ila amfani da tashar jiragen ruwansu, a daidai lokacin da gwamnatin kasar ke ci gaba da aiwatar da kisan kare dangi a zirin Gaza. “Za mu hana jiragen ruwa da ke dauke da...
    Allah Ya yi wa Sarkin Sasa, Alhaji Haruna Maiyasin rasuwa bayan shafe shekaru 125 a duniya. Fadar Sarkin Sasa da ke Ibadan, babban birnin Jihar Oyo, ce ta bayar da sanarwar rasuwar Sarkin wanda ke riƙe da muƙamin Sardaunan Yamma. HOTUNA: Gobara ta laƙume shaguna 100 a Kasuwar Sakkwato An raba wa ma’aikatan gona babura...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taba jaddada cewa, kasar Sin ta girmama ikon mallakar kasa da cikakken yanki na kasashen tsibirai na yankin tekun Pasifik, da girmama bukatunsu da al’adun kabilunsu da kuma hadin gwiwarsu wajen samun ci gaba da kansu. A kwanakin baya, yayin da firaministan kasar tsibiran Cook Mark Brown yake hira...
    Ana fargabar cewa wata gobara ta laƙume aƙalla shaguna 100 a Kasuwar Kara da ke Jihar Sakkwato. Gobarar wadda ta tashi tun da Asubahin wannan Asabar ɗin ta shafe sa’o’i 9 tana ta’adi. An raba wa ma’aikatan gona babura 200 a Yobe Yadda farashin kayan abinci ya sauka a kasuwannin Arewa Wani ɗan kasuwar da...
    Babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada kokarin sa kaimi ga ciyar da shirin kasar Sin mai kwanciyar zuwa matsayi mai girma. Xi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jagorantar taron nazari na ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS a jiya Juma’a. Inda ya yi kira da...
    Amma duk da haka, hatta wake-wake da raye-raye da kuma abinda ya shafi sinima, tsofaffin jarumai ne su ka kawo su a masana’antar Kannywood, saboda haka ya kasance wani lokaci mai ban sha’awa a tarihi lokacin da Hamisu Lamido Iyan-Tama ya hadu da Hindatu Bashir a kan dandamali don ba shi lambar yabo. Dukkanmu sai...
    Gwamnatin Yobe ta raba wa ma’aikatan gona babura guda 200 domin gudanar da ayyukan kula da harkokin noma a jihar. Kwamishinan ma’aikatar gona da albarkatun kasa, Ali Mustapha Goniri ne ya bayyana haka a lokacin da yake miƙa baburan ga waɗanda suka rabauta. Yadda farashin kayan abinci ya sauka a kasuwannin Arewa Yadda ake ‘Spring...
    Sunana Aisha T. Bello daga Jihar Kaduna: Rashi ramadan basket nasa a kore saurayi saboda ‘yan mata sun maida ramadan basket dole. Shawara ta ga al’ummar musulmi duniya shi ne; mu yi amfani da wannan dama gun rokon Allah, saboda in Allah ya nuna mana wanan mu gani ba lallai bane mu ga wani watan...
    Farashin kayayyakin abinci kamar masara da shinkafa da gero da dawa da wake da gari da waken soya da dai sauransu sun ragu, musamman a manyan jihohin da ake nomawa, kamar yadda wani bincike da Aminiya ta gudanar ya nuna. Wannan na faruwa ne gabanin watan Ramadan, wanda aka fara yau Asabar. Yadda ake ‘Spring...
    Mene ne ruwan kanwa? Ruwan kanwa wani ruwa ne da akeyiwa mai azumi yanada dadi sosai sannan idan mai azumi ya sha bayasa kasala yana warware cikin ko hanji cikin mutum zance, idan mai azumi yasaba da shan ruwan kanwa duk randa baisha ba bazai taba jin dadi ba.   Ya ake ruwan kanwa? Da...
    C- A nan ganyen zogalen da kika tafasa sai ki zuba a faranti ki yanka tumatir manya guda uku, ki yanka gurji (cocumber) babba guda daya, ki saka magi, gishiri kadan, mai kadan. Kar ki sa wulikuli. Zai yi miki maganin basir da cikowar gaba. Zai kara mi ki ni’ima da dandano sosai. 5) Ruwan...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno, ta sanar da ƙarin matakan tsaro yayin da al’ummar Musulmi suka shiga watan azumin Ramadan. Haka kuma, rundunar ta taya Musulmi murnar shigowar wannan wata mai alfarma. Gobara ta hallaka mutum 2 a sansanin ’yan gudun hijira a Borno Ramadan: Ga arahar kayan abinci ga rashin kuɗin saya Kakakin rundunar,...
    Dabi’un Da Suke Sa Malamin Makaranta Ya Ke Zama Nagartacce Ko dai su kasance suna koyar da manyan dalibai ne ko kuma lamarin ya zama suna koyar da kirga ce daga daya zuwa goma Azakakuran Malamai suna da wadansu dabi’u da suka yi kama da juna. Alal misali sanin kowa ne duk dai masu ilimi...
    A yau daya ga watan Maris ne dokar haramta amfani da tankunan dakon man fetur masu daukar lita 60,000 saboda yawan hatsarin da suke yi, wanda kuma yake lakume rayukan daruruwan mutane a ko wace shekara a duk fadin kasar. Jaridar Weeken Trust ya bayyana cewa hukumar ‘ The Nigerian Midstream and Downstream Petroleum Regulatory...
    Wata gobara da ta tashi cikin ta lalata wani ɓangare na Asibitin Ago da ke kan titin Ago Palace, Okota, a Jihar Legas. Gobarar ta fara ne da misalin ƙarfe 8:30 na daren ranar Juma’a, inda ta shafi wani sashe na ginin mai bene hawa ɗaya, inda asibitin yake. Gobara ta hallaka mutum 2 a...
    Tawagar yan wasan Damben Gargariya ta kasar Iran sun zama zakara a wasan damben da ya gudana a birnin Tirana babban birnin kasar Albaniya a makon da ya gabata, inda suka tashi da lambobin yabo 6 wadanda suka hada da zinari 4 azurfa da tagulla. Wannan nasara da ta maida kasar a matsayin zakara a...
    Kasashen Iran da Hadaddiyar Daular Larabawa sun gudanar da taron kwamitin Siyasa da al-adun na kasashen biyu a karon farko a birnin Abu Dhabi wanda ya kara tabbatar da irin ci gaban da suke samu a dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa kyautata dangantaka tsakanin...
    Shugaban kungiyar Ansarullah Sayyid Abdulmalik Badruddeen Huthi ya bayyana cewa kasar Yemen a shirye take ta sake shiga yaki idan yarjeniyar tsagaita wuta tsakanin bangarorin biyu ta wargaje. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Sayyid Huthi yana fadar haka a wani jawabin da ya gabatar ta hotunan bidiyo a jiya 28 ga...
    ‘Fake Inbestment Schemes’: Masu cuta na amfani da shafukan zuba jari na bogi domin damfarar mutane. Ransomware: Wasu barayin yanar gizo na saka kwayoyin cutar kwamfuta domin su hana mutum amfani da na’urarsa sai ya biya kudi. Hanyoyin Kare Kanka Yi amfani da kwayoyin kalmomin sirri masu karfi – A guji amfani da kalmomin sirri...
    Ya bayyana cewa rundunar ta damu matuka da faruwar lamarin, kuma ta himmatu wajen tabbatar da an yi adalci, yana mai cewa “Muna hada kai da hukumomin makarantar da sauran masu ruwa da tsaki domin zakulo wadanda ake zargin tare da kama su. Za a sanar da ci gaban lamarin a kan lokaci,” in ji...
    Janar Mai ritaya, tsohon Darakta Janar na NYSC, ya kuɓuta bayan kwana 22 a hannun ‘yan bindiga. Wata majiya ta tabbatar da cewa an sake shi a daren Juma’a, kuma yana karɓar kulawar likita a wani asibitin da ba a bayyana ba saboda dalilan tsaro. Tsiga ya faɗa hannun ‘yan bindiga ne a ranar 6...
    Tsohon Shugaban Hukumar Kula da Matasa Masu Yi Wa Ƙasa Hidima (NYSC), Manjo Janar Maharazu Tsiga (mai ritaya), ya kuɓuta bayan shafe kwana 22 a hannun ’yan bindiga. An sace shi ne a ranar 6 ga watan Fabrairu, 2025, a gidansa da ke garin Tsiga a Ƙaramar Hukumar Bakori a Jihar Katsina, yayin da wasu...
    Daga cikin Kasashen  da su ka fara azumi a yau Asabar, da akwai Saudiyya, Katar, Hadaddiyar Daular Larabawa, Omman, Bahrain da Kuwait. Saikuma Masar, Syria, Falasdinu, Yemen, Sudan,Somaliya, Libya, Tunisa da kuma Aljeriya. Kasar Moroko kuwa ta sanar da cewa, yau Asabar ne cikon watan Sha’aban, gobe Lahadi zai zama farkon Ramadan. A kasar Iraki,...
    Bayanai Hudu Da Ya Kamata A Sani Dangane Da Kiwon Kifi A Nijeriya: 1- Kimanin Kashi 40 Kacal Ake Iya Cimma Bukatar Samar Da Shi A Nijeriya: A cewar wata kididdiga ta Bankin Duniya, Nijeriya a 2018, ta samar da yawan Kifin da ya kai kimanin 1,169,478, wanda ya kai kimanin kashi 40 cikin 100,...
    Ofishin Jakadancin Saudiyya da ke Jihar Kano, ya bai wa jihar da wasu jihohin Arewa kyautar dabino katan 1,250, a matsayin wani ɓangare na shirin tallafin Ramadan na kowace shekara. Wannan shiri na cikin ayyukan jin-ƙai da Cibiyar Sarki Salman (KSrelief), ke gudanarwa don tallafa wa masu buƙata da kuma ƙarfafa dangantakar Saudiyya da Najeriya....
    Cecekucen dai a tsakanin Donald Trump da kuma Vladmir Zylinesky an yi shi ne saboda banbancin ra’ayin da bangarorin biyu suke da shi akan batun kawo karshen yakin Ukiraniya. Shugaban Amurka Donald Trump dai yana son ganon takwaransa na Ukiraniyan ya amince da kawo karshen yankin da kasarsa take yi da Rasha, yayin da Zylinesky...
    Ya yi nuni da cewa, wannan amincewa ta Shugaban Kwamitin; daidai take da irin manufar Shugaban Kasa Tinubu, ta son kara bunkasa kasar nan kafin zuwan zabukan 2027. Kwankwaso ya yaba wa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, kan irin hangen nesansa, musamman wajen mayar da hankali kan samar da wadataccen abinci da kuma kokarin sake...
    Azumin watan Ramadan na daga cikin shika-shikan Musulunci, kuma Allah ne Ya wajabta shi a kan bayinsa. Wannan wata yana da falala da lada mai yawa, domin Allah Ya keɓe shi da girma da ɗaukaka. Ga wasu daga cikin falalar azumin watan Ramadan: 1. Ana buɗe kofofin Aljanna, ana rufe ƙofofin wuta, kuma ana ɗaure...
    Azumin watan Ramadan na daga cikin shika-shikan Musulunci, kuma Allah ne Ya wajabta shi a kan bayinsa. Wannan wata yana da falala da lada mai yawa, domin Allah Ya keɓe shi da girma da ɗaukaka. Ga wasu daga cikin falalar azumin watan Ramadan: 1. Ana buɗe kofofin Aljanna, ana rufe ƙofofin wuta, kuma ana ɗaure...
    Hukumar abinci ta duniya ( FAO) ta sanar da cewa bisa la’akari da yadda adadin mutanen Afirka yake karuwa da kaso 2.3% a kowace shekara, hakan yana nufin cewa amfani da alkama zai karu. Bugu da kari hukumar abincin ta duniya ta ce da akwai wasu dalilan da za su sa Rashan ta kara yawan...
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce za ta duba yiwuwar inganta cibiyar lafiya tare da kafa makarantar sakandare a garin Samamiya da ke karamar hukumar Birnin Kudu. Gwamna Umar Namadi ya bayyana haka a lokacin kaddamar da sabon masallacin Juma’a da gidan marayu da makarantar islamiyya, wanda dan asalin yankin Alhaji Muhammad Abubakar Samamiya ya...
    Ita kuwa Kasar Algeria, ita ce ta uku; inda ta noma Dabino kimanin tan miliyan 1.25. Hadakar tsakanin Gwamnatin Jigawa da Saudiyya da kuma wani kamfanin aikin noma da ke kasar nan, wato ‘Netay Agro-Tech’, za ta kara taimakawa wajen sake habaka noman Dabinon a jihar. A duk shekara, Nijeriya na noma Dabino kimanin tan...
    Kazalika, wannan kimiyya abar maraba ce ga masu kiwon Shanu, musamman ga wadanda ke bukatar fadada samar da ingantacciya kuma wadatacciyar Madara a guraren kiwonsu. Kirkirar kimiyyar, ta zo kan gaba duba da kokarin niyyar da Ma’aikatar Bunkasa Kiwon Dabbobi ta sanya a gaba, ta zamanantar da kiwon dabbobi da kuma habaka samar da wadatacciyar...
    An shawarci gwamnatin tarayya da ta sanya ido sosai kan yadda za a biya ariyas na kudaden fansho da suka kai biliyan ₦758. Wani masani kan harkokin kudi, Farfesa Yushau Ibrahim Ango ne ya bayar da wannan shawarar a Kaduna yayin da yake mayar da martani kan rahotannin da ke cewa PENCOM ta yi alkawarin...
    Hukumar Karɓar Koke-Koke da Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Kano (PCACC), ta kama Shugaban Ƙaramar Hukumar Ƙiru, Abdullahi Mohammed, bisa zargin sayar da filin da aka tanada don gina Filin Wasa na Kafin Maiyaki. Ana zargin cewa Mohammed, ya sayar wa wani kamfani mai suna Mahasum filin. An ga watan Ramadan a Najeriya An...
    Hukumar bada lamuni ta Duniya IMF da kuma bankin duniya, manya-manyan cibiyoyin kudade a duniya sun ce ba zasu bada kudade don sake gina kasar Lebanon ba, sai sun cika wasu sharudda zuwa wani lokaci. Kuma sune samar da huldar jakadanci da HKI da kuma kwance damarar kungiyar Hizbullah. Jaridar Al-Akhbar ta kasar Lebanon ta...
    Kakakin Majalisar dinkin MDD Stephane Dujarric ya bada sanarwan cewa yana makaranta a Gaza fiye da 100,000 suka fara karatu a makarantu a yankin a ranar 23 ga watan Fabrayrun da muke ciki. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jami’in MDD yana fadar haka a jiya Alhamis kwanaki huda da fara karatu...
    Wata kungiyar kare hakkin bil’adama mai zaman kanta wacce take da cibiya a birnin Geneva na kasar Swizlanta ta bada sanarwan cewa ta sami cikekken shaidu wadanda suke tabbatar da cewa gwamnatin HKI tana azabtar da falasdinawa wadanda take tsare da su. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kungiyar tana bada wannan...