2025-03-01@17:21:59 GMT
إجمالي نتائج البحث: 356

«Sansanin yan gudun hijira»:

    Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya gargaɗi ƙasashe cewa Najeriya ba za ta yarda da rashin girmamawa daga kowace ƙasa ba. Ya bayyana hakan ne bayan da Ƙasar Kanada ta hana wasu jami’an sojin Najeriya takardae izinin shiga ƙasar, duk da cewa an gayyace su don halartar wasannin Invictus a Vancouver. ’Yan bindiga...
    ’Yan bindiga sun kashe wasu mazauna ƙauyen Gwargwada da ke Ƙaramar Hukumar Kuje a saboda jinkirin biya musu kuɗin fansa. Mutanen da aka kashe, sun haɗa da Mohammed Danladi da Nasiru Yusuf, wanɗanda aka sace su ne a ranar Laraba tare da wani makiyayi da wata mata a mahaɗar Gwombe, a kan hanyar Gwargwada zuwa...
    Dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran sun sanar da gano da kuma rusa wata kungugun masu yi wa Amurka da Isra’ila leken asiri a yankin Arewacin Iran. Kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci a yankin Mazandaran dake arewacin Iran ne ya sanar da bankado da kuma rusa gungun masu yi wa abokan...
    Ma’aikatar tsaron Rasha ta sanar da cewa, ta kakkabo jiragen saman marasa matuki 9 da kasar Ukiraniya ta harba mata. Sanawar ta ma’aikatar harkokin tsaron Rasha ta ci gaba da cewa; A daren jiya ne  aka kakkabo jiragen sama  marasa matuki 3 na kasar Ukiraniya da aka harba a kan yankin Biryansk, sai kuma wani...
    Sakataren harkokin waje na kasar Amurka Marco Rubio ya bayyana cewa kasashen Amurka da Rasha sun kuduri anniyar kawo karshen yakin Ukrai, banda haka zasu kara kyautata dankon zumunci da tattalin arziki a tsakaninsu. Shafin yanar gizo na labarai, Arabnews ta gwamnatin kasar Saudiya ya bayyana cewa, ya nakalto Rubio yana cewa kasashen biyu sun...
    Kakakin ma’aikatan shari’a a kasar Iran ya bayyana cewa jami’an tsaro na kasar Iran sun kama mutane biyu yan kasar Burtaniya tare da tuhumar aikin liken asiri a lardin Kerman na kasa. Kamfanin dillancin labaran (IP) na kasar Iran ya bayyana cewa mutanen biyu suna tafiye-tafiye zuwa lardunan kasar Iran suna tattara bayanai a cikin...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci A nan Iran Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya gana da shuwagabannin kungiyar Jihadul Islami na kasar Falasdinu da aka mamaye a jiya Talata. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ya bayyana cewa Ziyad Nakhalah shugaban kungiyar ne ya jagoranci tawagar kungiyar zuwa ganawa da jagoran. Labarin ya nakalto Jagoran...
    Burgediya Janar Amir Ali Hajizadeh babban kwamandan sojojin sararin samaniya ya bada labarin cewa sojojinsa, zasu kai farmakin ‘Wa’adusadik na 3 nan ba da dadewa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Janar Ali Hajizadeh yana fadar haka a jiya Talata, a hirar da ta hadashi da wata kafar yada labarai labaran kasar....
    Gwamnatin tarayya ta ce ta bai wa gwamnatin jihar Jigawa tallafin kayayyakin noma na sama da naira biliyan 5 domin bunkasa noman abinci a fadin jihar.     Ministan noma da samar da abinci Sanata Abubakar Kyari ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a garin Dabi da ke karamar hukumar Ringim a...
    Kasar Sin na maraba da duk kokarin da ake yi cikin lumana don warware rikicin kasar Ukraine, ciki har da tattaunawa tsakanin Amurka da Rasha, kuma Sin na fatan dukkan bangarori da masu ruwa da tsaki za su shiga cikin shawarwarin samar da zaman lafiya in lokaci yayi. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewa: Barazanar makiya a kan kasar Iran da al’ummarta ba ta yi nasara ba Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa: Gagarumar zanga-zamga da al’ummar Iran suka gudanar a ranar 22 ga watan Bahman ta tabbatar da cewa barazanar makiya a...
    Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa; Iran tana taka rawa ta musamman wajen wanzar da kwanciyar hankali da tsaron yankin Tekun Pasha Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta hanyar mallakar mafi yawan layukan kan iyaka da tekun Pasha da kuma iko da mashigar Hormuz, ta...
    Babban kwamandan sojojin kasar Iran ya bayyana cewa: Sun sabunta hanyoyin da sojojin Iran zasu mayar da martani kan duk wani harin wuce gona da iri kamar yadda Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bada umarni Babban kwamandan sojojin kasar Iran Manjo Janar Abdur-Rahim Mousawi ya bayyana cewa: Tun tsawon kwanaki da suka gabata jagoran...
    Jaridar Ma’ariv ta Isra’ila ta bayyana adadin wadanda suka jikkata a cikin sojojin mamayar Isra’ila da kuma miliyoyin yahudawan sahayoniyya da suka samu matsalar tabin hankali a lokacin yakin Gaza Jaridar “Ma’ariv” ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta bayyana a jiya litinin, adadin wadanda suka mutu a cikin jerin sojojin mamayar Isra’ila a yayin mummunan ayyukan...
    Jagoran al’umar yankin Neja Delta, Cif Edwin Clark ya rasu yana da shekaru 97 a duniya.
    Dakarun “Kassam” na kungiyar Hamas sun sanar da shahadar Muhammad Shahin wanda daya ne daga cikin kwamandojinta da ya yi shahada sanadiyyar harin da HKI ta kai masa a birnin Saida na kasar Lebanon. Sanarwar ta dakarun “Kassam” ta ce, Muhammad Ibrahim Shahin wanda ake yi wa lakabi da Abul-Bara’a ya yi shahada ne a...
    Nijar ta bayyan fatanta na ganin ta kulla yarjejeniya da kafofin yada labarai na Iran. Wannan bayanin na kunshe ne a bayyannin da jakadan Nijar a Tehran Malam Seydou Ali Zataou, ya yi a ganawarsa da shugaban hukumar gidan radiyo da talabijin sashen kasashen waje na Iran, Ahmad Norozi a wannan Litinin. Bangarorin sun bayyana...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa kokarin da makiya suke yi na haifar da sabani a tsakanin al’ummar kasar ta hanyar yi musu barazana ya ci tura. Babban tattakin da al’ummar kasar suka yi a ranar 10 ga watan Fabrairu ya nuna cewa barazanar makiya ba ta...
    Ministan tattalin arziki na kasar Iran Abdunnaser Himmati yana halatan taro dangane da matsaloli da kuma dammakin da kasashen masu tasowa suka fama da su a birnin Riyad na kasar Saudiya. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa Himmati yana halattan wannan taro na kwanaki biyu ne tare da gayyatar tokwaransa na...
    Gwamna Umar Namadi  ya kaddamar da aikin gina titin Kanya Babba (Kwanar Duzau) zuwa Kankare zuwa Ballada zuwa Duzau zuwa Danhill zuwa Kyambo zuwa Mundu zuwa Goron Maje. Aikin wanda aka bayar da shi kan kudi naira biliyan 6 da miliyan 300, wani muhimmin mataki ne a yunkurin gwamnatin jihar na inganta ababen more rayuwa...
    Wakiliyar babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin ta yi hira da shugaban Pakistan, Asif Ali Zardari, dake ziyarar aiki a kasar Sin, a baya bayan nan a birnin Beijing. Yayin hirar, Zardari ya bayyana cewa, ci gaban kasar Sin al’amari ne mai kyau, kuma Sin ba ta taba zama mai mamaya ba. Bisa...
     Rahotanni da suke fitowa daga Bukavu sun ambaci cewa ‘yan tawayen kungiyoyin M 23 da kuma AFC sun kwace iko da filin sauran jiragen sama na Kavumu wanda yake da tazarar kilo mita 45 daga birnin. mutanen sun kauracewa zirga-zirga akan titunan birninna  Bukavu saboda rashin tabbacin abinda zai biyo baya. Mafi yawancin ‘yan siyasa...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci ya yi kira ga kasasnen larabawa da na musulmi da su nuna cikakken goyon bayansu al’ummar Falasdinu domin dakile makircin hadin gwiwa a tsakanin Amurka da Isra’ila na korar Falasdinawa daga gidansu. Ministan harkokin wajen na Jamhuriyar musulunci ta Iran, Abbas Arakci ya bayyana hakan ne a lokacin da...
    Kiyaye taruwar maiƙo da kwayoyin cuta a fuska da kirji. Wannan kan dan yi wahala amma ta wadannan dabaru za a samu nasara: 1- Rage maiƙo a cikin abinci. Misali, idan aka soya wani abinci, yana da kyau a tsane mai da mayanin kicin wafif ko tawul ko tushu mai tsabta kafin a ci. Idan...
    Wasu fusatattun matasa sun banka wa ofishin ’yan sanda na yankin Ifon, da ke Ƙaramar Hukumar Ose wuta a Jihar Ondo. Lamarin ya faru ne bayan da ake zargi ’yan sanda da azabtar da wani matashi har ya mutu a hannunsu. An tsinci gawar ɗan sanda a Otal a Ogun NAFDAC ta gano wajen da...
    Wasu fusatattun matasa sun banka wa ofishin ’yan sanda na yankin Ifon, da ke Ƙaramar Hukumar Ose wuta a Jihar Ondo. Lamarin ya faru ne bayan da ake zargi ’yan sanda da azabtar da wani matashi har ya mutu a hannunsu. An tsinci gawar ɗan sanda a Otal a Ogun NAFDAC ta gano wajen da...
    Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa; Tsaron ruwa bai kamata ya zama kayan aikin matsin lamba kan kasashen waje ba Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Bai kamata tsaron teku ya zama wani makami na matsin lamba kan kasashen waje ba, sai dai ya zama sakamakon hadin gwiwa tsakanin kasashen yankin....
    Mataimakin ministan harkokin wajen Iran ya ce: Tuntubar juna tsakanin Iran da Iraki ya zama wajibi don inganta matakan tsaro tsakanin kasashen biyu Mataimakin ministan harkokin wajen Iran kan harkokin siyasa Majid Takht Rawanji ya jaddada da cewa: Ziyarar da ya kai zuwa Iraki ta zo ne bisa tsarin tuntubar juna ta fuskar siyasa da...
    Kungiyar Tarayyar Afirka ta yi Allah Wadai da duk wani Shirin tilastawa Falasdinawa gudun hijira daga muhallinsu Batun neman tilastawa Falasdinawa gudun hijira daga kasarsu ta gado yana ci gaba da fuskantar tofin Allah da Allah wadai a duk fadin duniya da kuma a taruka daban-daban, kuma batun Falasdinu shi ne kan gaba a ajandar...
    “Jami’anmu na kara zage damtse wajen ganowa tare da wargaza ma’ajiya da wuraren ajiya ba bisa ka’ida ba inda ‘yan fashin suka rika tara kayayyakin da aka sace. Dole ne FCT ta kubuta daga hannun wadannan miyagun abubuwa.” Aikin dai ya biyo bayan nasarar da aka samu a makon da ya gabata inda rundunar tare...
    Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ce, Amurka ta na son mallakar ma’adanan na kasar Ukiraniya, wadadensu ya  kudadensu ya kai dalar Amurka biliyan 500, a matsayin mayar da kwaryar taimakon Amurkan ta fuskar soja da makamai. A wata hira da tashar talabijin ta  “FOX NEWS” ta yi da shi, shugaban kasar ta Amurka Donald...
    Babban sakataren MDD Antonio Guterres  wanda ya halarci taron kungiyar tarayyar Afirka AU da aka bude a birnin Addis Ababa na kasar Habasha, ya kira yi kungiyoyin kasa da kasa da su kai daukin gaggawa ga kasar Sudan ta fuskar bada kayakin agaji. Guterres ya nanata muhimmancin kai kayakin abinci da sauran kayakin da ake...
    Nijeriya na shirin shiga cikin jerin ƙasashen da ke ƙera motoci masu amfani da lantarki. Hakan na zuwa ne a da kokarin tsohon babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Tukur Buratai, ya yi na buɗe cibiyar bincike ta Tukur Buratai gabarar yin bincike wajen samar da na’urorin da ba za su ringa amfanin da makamashi...
    Ya ce wajibi ne Sin da Amurka su kauracewa rikici, idan ba haka, duniya ce za ta wahala. Sannan ya yi kira da a karfafa tattaunawa da inganta fahimta da karfafa aminci. Ya ce kamata ya yi kasashen biyu su hada hannu wajen shawo kan kalubalen duniya, domin hakki ne da ya rataya a kan...
    Sai dai ya ce, dole ne a fayyace gaskiya don hana wannan yaudarar samun gindin zama. Ya ce: “Karo na farko da Mista Gambaryan da tawagar sa suka zo Nijeriya, sun zo ne karan kansu ba tare da wata gayyata daga gwamnati ba. Sai dai da aka sanar da gwamnati wani batu na neman cin...
    Wasu magidanta da suka mallaki wani zakara (Ricco) jinsin Bantam daga Bourgoin-Jallieu a sashen Isère na kasar Faransa, sun karɓi sammaci domin bayyana a gaban kotu sakamakon korafin da wani makwabcinsu ya yi game da carar zakaran. Korafin da suka yi ya hada da, rashin barci saboda karar zakaran yake yi a yayin carar, kamar...
    Ministan kudi da tattalin arziki na kasar Iran yana kan hanyarsa ta zuwa kasar Saudiya don halattar wani taro mai muhimmaci na tattalin arziki. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan tattalin yana fadar haka a shafinsa na X, ya kuma kara da cewa, yana zuwa wannan taron ne tare da gayyar...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baka’i ya yi tir da harin ta’addancin da aka kai a yankin na Baluchestan na kasar Pakistan wanda ya yi sanadiyyar mutuwa da kuma jikkatar mutane da dama. A jiya juma’a ne dai kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Iran ya fitar da sanarwar akan kisan da ‘yan ta’addar...
    Gwamna Dauda Lawal ya mika makaman da gwamnatinsa ta bayar ga rundunar soji domin kafa hedkwatar rundunar Operation Safe Corridor na jihohin Arewa maso Yamma, a karamar hukumar Tsafe domin kwance damarar makamai, da lalata su da kuma shigar da barayin da suka tuba su koma cikin al’umma.   Gwamnan a wajen bikin mika ragamar...
    Fim din da aka yi shi da kagaggun hotuna mai suna “Ne Zha 2” ya zama fim din kasar Sin na farko da ya samu zunzurutun kudi har yuan biliyan 10, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 1.39 bisa jimillar kudadensa da aka samu a duniya, ciki har da na ba da sautonsa, inda ya zarce misalin...
    Yau Jumma’a, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin, Guo Jiakun ya gudanar da taron manema labarai na yau da kullum. Yayin taron, ya ce, a ko da yaushe Sin tana kiyaye karfinta na nukiliya a matsayin mafi karancin mataki da ake bukata don tsaron kasa, kuma ba ta shiga gasar makamai da sauran kasashen duniya. Ya...
    Shugaban Kungiyar Yarbawa zalla ta Afenifere, Pa Ayodele Adebanjo ya rasu yana da shekara 96. Rahotanni sun ce dattijon ya rasu ne da safiyar Juma’a a gidansa da ke Lekki a Jihar Legas. An tabbatar da rasuwarsa a wata sanarwa da iyalansa suka fitar. Fursunoni 3 sun lashe Gasar Al-Ƙur’ani a Kano Ta kacame tsakanin...
    Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jaddada aniyar gwamnatinsa na ci gaba da bibiyar ’yan ta’adda har sai an fatattake su, an ruguza su tare da murƙushe su. Gwamnan ya miƙa kayan aikin da gwamnatin jihar Zamfara ta samar domin kafa hedikwatar tsaro ta dakarun sojin ‘Operation Safe Corridor’ na jihohin Arewa maso Yamma. A...
    Gwamnatin jihar Kwara ta ware naira biliyan 5 domin inganta cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko guda 70 a kananan hukumomin uku na jihar.   Babban Sakatariyar Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko ta Jihar Kwara (KWHCDA), Farfesa Nusirat Elelu ce ta bayyana haka a lokacin rattaba hannu kan kwangilolin da aka yi a...
    Kungiyoyin farar hula masu yaki da zazzabin cizon sauro, rigakafi da abinci mai gina jiki (ACOMIN), reshen jihar Taraba, ta koka kan matsalar karancin kayan gwajin cutar kanjamau a jihar.   Shugaban kungiyar na jiha, Alhaji Muhammad ​​Danburam ya bayyana haka a lokacin da ya kai ziyarar wayar da kan hukumar yaki da cutar kanjamau...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi gargadin cewa makiya kasarsa suna neman murkushe al’ummar kasar  ta hanyar takunkumi da barazana. Pezeshkian ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ta yi da masana da masu fada aji na lardin Bushehr da ke kudancin kasar a ranar Alhamis , inda ya ce “Makiya suna son...
    Amurka ta kakaba takunkumi kan babban mai shigar da kara na kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa dangane da binciken da kotun ta ICC ke yi kan yiwuwar aikata laifukan yakin Isra’ila a Gaza da sojojin Amurka. Ma’aikatar Baitulmalin Amurka ta sanar da kakabawa Karim Khan takunkumi a matsayin martani ga umarnin shugaba...
    Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), ta tabbatar da cewa an tanadar wa maniyyatan Najeriya 52,000 guraben aikin Hajjin na shekarar 2025. Wannan na cikin wata sanarwa da Mataimakiyar Daraktan Bayanai ta NAHCON, Fatima Sanda Usara, ta fitar. An kama likita kan laifin yi wa ’yan bindiga magani a Katsina Kwastam ta lalata magungunan biliyan N100...
    Ma’aikatar harkokin wajen Sin ta sanar a yau Alhamis cewa, firaministan kasar Li Qiang, zai halarci bikin rufe gasar wasannin lokacin hunturu ta kasashen Asiya karo na 9, wanda za a yi gobe Juma’a a Harbin, babban birnin lardin Heilongjiang na kasar Sin. Li Qiang zai kuma shirya liyafar maraba da shirye shiryen da suka...
    Jami’an tsaro sun kama wani ma’aikacin lafiya da ake zargi da yi wa wasu ’yan bindiga da suka raunata magani a Ƙaramar hukumar Safana ta Jihar Katsina. Daga cikin majinyatan nasa har da ƙasurmin da ake nema Usman Modi Modi, wanda aka sanar da bada ladar Naira miliyan 50 don nemo shi. Tirela ta murƙushe...