2025-04-26@05:00:49 GMT
إجمالي نتائج البحث: 927

«Sansanin yan gudun hijira»:

    Kasashen Mali, Nijar da kuma Burkina faso dake hade a kawancen Sahel na AES, sun sanar da kiran jakadunsu a Aljeriya domin tuntuba. A wata sanarwa da aka karanta a gidan talabijin na kasar Mali a yammacin jiya Lahadi, kasashen uku sun sanar da kirawo jakadunsu domin tuntuba bayan da Aljeriya ta kakkabo wani jirgi...
    Iran ta bakin kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar, Esmail Baghai, ta ce nahiyar turai sun tafka kure na tarihi, ta hanyar goyon bayan Isra’ila ta hanyar yin watsi da sammacin kama Benjamin Netanyahu. Esmail Baghai ya bayyana haka ne a cikin wani sako a asusunsa na X, bayan ziyarar aiki da Netanyahu ya kai kasar...
    Ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza ya bayyana cewa adadin ma’aikatan yada labarai da aka kashe a hare-haren da Isra’ila ke kaiwa Zirin tun daga watan Oktoban 2023 ya kai 210 bayan kashe dan jarida Helmi al-Faqawi. Al-Faqawi na cikin akalla mutane biyu da suka mutu a lokacin da jiragen yakin Isra’ila suka kai hari...
    Zanga-zangar adawa da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta ɓarke a wasu manyan biranen Nijeriya da suka haɗa da Abuja da Legas da kuma Fatakwal. Zanga-zangar wadda wata ƙungiyar gwagwarmaya ta Take It Back ta shirya na gudana ne duk da gargaɗin da ’yan sanda suka yi. Mutanen da Sanƙarau ta kashe sun kai 151 —...
    Wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne sun kai hari kauyen Izge da ke Ƙaramar Hukumar Gwoza a Jihar Borno, inda suka kashe sojoji tare da rasa mayaƙansu da dama. Rahotanni na cewa harin ya auke ne da misalin karfe 1:00 na ranar Lahadi a lokacin da ’yan ta’addan suka mamaye sansanin sojin Nijeriya...
    Ƙungiyar Take It Back ta ce zanga-zangar da za gudanar a yau babu gudu babu ja da baya domin nuna adawa da dokar ta-baci da aka sanya a Jihar Ribas da kuma abin da ta kira cin zarafin bil’adama da kuma amfani da dokar ta’addancin yanar gizo ba bisa ka’ida ba. Wannan dai na zuwa...
    Rafael Grossi shugaban hukumar makamashin nukliya ta duniya (IAEA) ya bayyana cewa JMI bata da makamin Nukliya, sai dai tana dukkan kayan aikin da ake bukata,  da kuma fasahar kera makamin idan tana bukatar yin hakan.   Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Grossi yana fadar haka a wata hira da yayi...
    Ƙungiyar ƙwallon kafa ta Southampton ba za ta buga gasar Firimiya Lig na badi ba, bayan da su ka koma gasar yan dagaji ta kasar Ingila, Southampton ta yi rashin nasara a hannun Tottenham Hotspur wanda kuma shi ne ya yi sanadiyar da Southampton ta koma gasar Championship ta kasar Ingila. Hakan ya sa ta...
    Babban bankin kasar ya lura da cewa wannan raguwar ya samo asali ne sakamakon faduwar farashin danyen mai na Bonny Light na Nijeriya, wanda ya fadi zuwa dala 75.66 kan kowacce ganga daga dala 82.23 a zango na uku na shekarar 2024. Bugu da kari, karin fitar da danyen mai daga ganga 1.33 kowace rana...
    Jami’an tsaro sun jiran kayan ado na ’yan kunnayen zinare su wuce ta na’urar binciken fasinjan jirgin sama kafin a gano kayan da aka sace a hukumance. An kama wani mutum mai shekara 32, mai suna Jaythan Lawrence Glider bisa zargin satar ’yan kunne biyu na zinare na sama da Dala Amurka 769,000 kwatankwacin Naira...
    Hotunan faifan bidiyo da ke fallasa kisan da sojojin mamaya na Isra’ila suka yi wa likitoci 15 a Rafah, ya tilastawa “Isra’ila” ja da baya kan labarin da ta kirkiro, tana mai cewa karyar da ta yi “ba da gangan ba ce”. An kara da’awar kuma daga baya an karyata ta ta hanyar shaidun bidiyo,...
    Sakataren Harkokin Wajen Birtaniya, David Lammy, ya soki matakin Isra’ila na hana wasu ‘yan majalisar dokokin Birtaniya biyu shiga ƙasar, yana mai cewa matakin bai dace ba kuma abin damuwa ne. Tsarewa da hana ‘yan Majalisar Wakilan Birtaniya biyu da ke cikin tawagar ‘yan majalisa zuwa Isr’aila shiga cikin ƙasar, abin da ba za a...
    Tsohon Gwamna Jihar Oyo, Omololu Olunloyo ya riga mu gidan gaskiya. Wata sanarwa da iyalansa suka fitar ta ce ya rasu yayin da rage kwanaki tara kacal ya cika shekaru 90 a doron ƙasa. Finafinan Kannywood da suke tashe da kuma manyan marubutansu An yi wa wata mata ƙarin jini sau 36 Tsohon gwamnan wanda...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya soki abunda ya danganta da barazanar Amurka ga Teheran, yana mai cewa kasarsa a shirye take ta shiga tattaunawa ta hakika ba tare da barazana ba. “Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana neman tattaunawa ta gaskia, a yayin da suke barazana ga Iran a daya bangaren kuma suna neman yin...
    Sanannen abu ne cewa irin shagulgulan da ake gudanarwa a lokacin bukukuwan sallah a Kano na samar da nishaɗi da walwala ga mazauna jihar da ma baƙi da ke zuwa kallo daga sassa daban-daban na duniya. Haye-hayen Sallah da Sarkin Kano da hakimansa da sauran ’yar majalisarsa ke yi na daga cikin abubuwan mafi bankaye...
    Wakiliyar musamman ta MDD akan Falasdinu Francesca Albanze ta sanar da cewa; Bayanan da jaridar ” New York Times”  masu kunshe da hotuna na laifin kashe masu aikin ceto a Rafah, suna dakile riwayar Isra’ila.” Wakiliyar ta MDD ta fada wa tashar talabijin din Aljazeera cewa, abindaya faru kisan kiyashi ne’ sannan ta kara da...
    A wata sanarwa da kungiyar ta malaman addinin musulunci ta duniya ta ce wajibi ne akan kowane musulmi wanda yake da iko a fadin duniyar musulunci da ya taimakawa mutanen Gaza da makamai da kayan yaki domin dakile ta’addancin Isra’ila da yake cigaba. A jiya Juma’a ne kungiyar malaman addinin musuluncin ta duniya ta fitar...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Benuwe, ta ceto fasinjoji 14 da wasu ’yan bindiga suka sace yayin da suke tafiya a kan hanyar Makurdi zuwa Otukpo. Sai dai uku daga cikin fasinjojin sun rasu, ciki har da direban motar. Sabon harajin Trump zai jefa tattalin arziƙin duniya cikin matsala — WTO Ɗalibai za su koma makaranta...
    Shugaba Masoud Pezeshkian ya ce Iran ba ta neman yaki da kowace kasa, amma ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kare kanta saboda tana da kyakkyawan shiri a kan hakan. Da yake magana a wata tattaunawa ta wayar tarho da yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohammed bin Salman, Pezeshkian ya ce...
    Mai magana da yawun jam’iyyar APC a Jihar Ogun, Tunde Oladunjoye, ya rasu. Ya rasu ne a ranar Juma’a, 4 ga watan Afrilu, 2025, yayin da yake jinya a ƙasar waje kan wata rashin lafiya da ba a bayyana ba. An haramta wa Akpabio da Natasha tattaunawa da manema labarai Yadda aka yi jana’izar Dokta...
    Dubun-dubatar al’ummar kasar Aljeriya sun gudanar da wani gagarumin gangami da jerin a wannan Juma’a a birnin Algiers babban birnin kasar, domin yin Allawadai da laifukan yaki da Haramtacciyar Kasar Isra’ila take aikatawa a kan al’ummar yankin zirin Gaza. Kamar yadda kungiyar Movement of Society for Peace ta yi kira, dubban  ‘yan kasar Aljeriya ne...
    Cibiyar da ke sa ido kan tsattsauran ra’ayi da ke karkashin cibiyar ilimi ta Al-Azhar ta Masar, ta fitar da wata sanarwa da ta yi kira da a kame firaministan Haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu a matsayin mai laifin yaki. Shafin sawtbeirut.com ya bayar da rahoto kan sanarwar da ke cewa, cibiyar yaki da tsattsauran...
    A wani muhimmin mataki na karfafa zaman lafiya da sulhu, gwamnatin jihar Jigawa ta kaddamar da kwamitocin zaman lafiya da sulhu a kananan hukumomin Jahun da Miga. A lokacin bikin kaddamarwar, Sakataren Gwamnatin Jihar, Malam Bala Ibrahim, ya bayyana aikace-aikacen da aka dora wa kwamitocin. Ya jaddada bukatar kwamitocin su gano musabbabin rikice-rikicen da suka...
    Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja, a ranar Juma’a, ta haramta wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio tattaunawa da manema labarai yayin da ’yar majalisar ta shigar da ƙara a gaban kotu. Mai shari’a Binta Nyako ce ta yanke hukuncin a ranar Juma’a bayan ƙorafin da lauyan da ke...
    Wanda ya jagoranci sallar juma’a a nan birnin Tehran Hujjatul-Islami Wal Muslimin Muhammad Hassan Abu Turabi Fard; Duniyar musulmi tana fuskantar jarabawa mai girma da ita ce kare al’ummar Falasdinu, da takawa masu girman kai na duniya birki,haka nan ‘yan Sahayoniya ‘yan daba. Limamin na birnin Tehran ya jaddada muhimmacin fuskantar ‘yan sahayoniya ‘yan daba...
    Ta ce, “Abin da nake gani shi ne, INEC na taimaka wa masu shigar da kara kan yadda za su kammala ayyukansu na haram. “Wannan shi ne karon farko da aka gabatar da koken, ba su da adireshi, lambobin waya, duk da hana amma INEC ta shiryar da su yadda za su gabatar da bayanan...
    Adadin waɗanda suka mutu sakamakon hare-haren baya-bayan nan a ƙaramar hukumar Bokkos da ke Jihar Filato ya kai 52 kamar yadda hukumomin yankin suka bayyana. Hakan ya biyo bayan sake gano wasu gawarwaki 40 ne a ranar Laraba da Alhamis da daddare yayin da masu aikin ceto suka ci gaba da kutsawa cikin dazuka don...
    Da yake tofa albarkacin bakinsa kan sayar da danyen mai da naira, wani babban jami’in gwamnati wanda ke da masaniya sosai kan lamarin da ke aiki da kwamitin da aka kafa don shirin ya bayyana cewa gwamnati ba wai ta dakatar da tsarin bane gaba daya. “Shirin cinikayyar danyen mai a kan naira zai ci...
    Dubban mutane ne suka halarci jana’izar shahararren malamin addinin Musuluncin nan kuma Babban Limamin Masallacin Juma’a na Dutsen Tanshi da ke Bauchi, Sheikh Dokta Idris Abdulaziz. Malamin ya rasu ne a ranar Alhamis a gidansa da ke Bauchi bayan fama da doguwar rashin lafiya. Kotun ƙoli ta sauke Julius Abure daga shugabancin jam’iyyar LP Batun...
    Dubban mutane ne suka halarci jana’izar shahararren malamin addinin Musuluncin nan kuma Babban Limamin Masallacin Juma’a na Dutsen Tanshi da ke Bauchi, Sheikh Dokta Idris Abdulaziz. Malamin ya rasu ne a ranar Alhamis a gidansa da ke Bauchi bayan fama da doguwar rashin lafiya. Kotun ƙoli ta sauke Julius Abure daga shugabancin jam’iyyar LP Batun...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan a zantawarsa tan wayar tarho da yerima mai jiran gadon sarautar kasar Saudiya sannan Firai ministan kasar Muhammad bin Salman ya taya shi murnin salla karama ya kuma yiawa dukkan kasashen musulmi fatan alkhairi. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana cewa, JMI bata neman yaki...
    Jakadan kasar Iran a cibiyoyin MDD a kasashen Turai ko Geneva Ali Gahraini ya yi tir da amincewar da hukumar kare hakkin bil’adama ta MDD ta yi da zargin kasar ta take hakkin bil’adama a taronta na baya-bayan nan abirnin Geveva. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Baraini yana cewa, hukuncin da...
    Yayin gabatar da rahoton an raba lambar yabo ga Hakiman da aka fi samun gudunmawar Zakkar daga gundumominsu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe...
    Dokta Hakeem Baba-Ahmed, ya yi murabus daga matsayin mai bai wa Shugaba Bola Tinubu shawara kan harkokin siyasa. Majiyoyi daga fadar shugaban ƙasa sun tabbatar da cewa ya aike da takardar murabus ɗinsa kimanin makonni biyu da suka wuce, inda ya ce dalilansa na ƙashin kai ne. Batun na yanke jiki na faɗi ƙarya ce...
    Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya musanta jita-jitar da ake yaɗawa cewar ya yanke jiki ya faɗi har aka kai shi asibiti a ƙasar waje. Ya ce wannan ƙarya ce da maƙiyansa na siyasa suka ƙirƙira don kawar da hankalin mutane. NAJERIYA A YAU: Dalilan Kamuwa Da Cutar Hawan Jini Da Hanyoyin Magance Ta...
    Jiragen yakin Isra’ila sun kai karin hare-hare ta sama kan kasar Siriya, inda suka bijirewa gargadin Majalisar Dinkin Duniya game da hadassa asarar fararen hula yayin da suke ci gaba da kai wa kasar ta Larabawa hare-hare. Rahotanni sun ce a ranar alhamis, jiragen saman Isra’ila sun kai hare-hare a kalla sau biyu a kan...
    Kwamishinan kare hakkin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya ya gargadi Isra’ila game da harin da ya yi sanadin mutuwar ma’aikatan ceto a Gaza yana mai cewa hakan zai iya kasancewa ‘lafin yaki’. Ma’aikatan agaji 15 ne suka ras arayukan a wani kazamin hari da Isra’ila ta kai kan motocin daukar marasa lafiya a...
    Fitaccen malamin addinin Islama da ke Jihar Bauchi, Dokta Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ya riga mu gidan gaskiya. Almajiransa sun tabbatar wa Aminiya cewa ya rasu ne a gidansa da ke Bauchi inda za a yi jana’izarsa a safiyar wannan Juma’ar. Malamin ya yi fama da rashin lafiya inda gabanin watan Ramadana ya fita neman...
    Cibiyar yaƙi da ta’addanci ta ƙasa (NCTC) ta miƙa tsohon Darakta-Janar na masu yi wa ƙasa hidima (NYSC), Birgediya Janar Maharazu Tsiga (mai ritaya) ga mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Nuhu Ribadu. Tsiga, wanda aka kuɓutar bayan ya kwashe kwanaki 56 a tsare, a ranar Laraba an miƙa shi ne tare...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana yau Alhamis cewa, kasar Sin ta bukaci Amurka da ta gyara kuskuren da ta yi na kakaba “harajin ramuwar gayya,” kana ta magance sabanin dake tsakaninta da kasar Sin da sauran kasashen duniya dangane da tattalin arziki da cinikayya, ta hanyar yin shawarwari bisa daidaito,...
    Dakarun Yaman sun sanar da mayar da martani kan harin baya-bayan nan da Amurka ta kai kan kasarsu, wanda ya hada da hare-hare ta sama har sau 36 a yankuna da dama a cikin gundumomin Sanaa, Sa’ada, da wasu jahohin kasar, wanda ya yi sanadin mutuwa da jikkatar mutane da dama. Kakakin Rundunar sojin Yaman...
    Kungiyar malaman musulmi ta duniya ta fitar da wata sanarwa inda ta bayyana cewa laifuffukan gwamnatin sahyoniyawa a Gaza sun ketare dukkanin iyakokin kasa da kasa, tare da yin kira da a kawo karshen kashe-kashen mata da kananan yara da makamai masu guba, da yunwa, kishirwa, da cututtuka. A cewar jaridar Arabi 21, kungiyar malaman...
    Ya ce, “Akwai rahoton cewa Turji ya shirya zai ziyarci yankin Gabashin Gatawa domin gudanar da bukukuwan Sallah, amma matakin da jama’a suka dauka na sanar da jami’an tsaro ya dakatar da shi ga hakan.   “Wannan na iya zama dalilin da ya sa Bello Turji ya huce fushinsa a kan manoman da ba su...
    Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta bayyana cewa buƙatar da wasu suka shigar don yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Mazaɓar Kogi ta Tsakiya kiranye, bai cika sharuɗa ba. INEC ta ce yunƙurin bai cika sharuɗan Sashe na 69(a) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya tanadar ba. Bello Turji ya kashe manoma 11 a...
    Akalla mutane 2 ne suka rasa rayukansu a sabbin hare-haren da jiragen Amurka suka kai kan kasar Yemen a jiya Laraba da yamma, saboda hanata tallafin da take bawa falasdinawa a Gaza wadanda sojojin HKI sukewa kissan kare dangi a gaza. Tare da hana abinci shigowa yankin kimani watanni 2 da suka gabata. Tashar talabijin...
    Gwamnatin Afirka Ta Kudu ta sake jaddada azamarta ta bibiyar HKI a kotun duniya ta manyan laifuka akan laifukan kisan kiyashi da ta aikata a Gaza. Gwamnatin ta Afirka ta kudu, ta kuma yi watsi da duk wani matsin lamba da Amurka yake yi ma ta domin tilasta ma ta, ta ja da baya. Ministan...
    Asusun Bada Lamuni na Duniya (IMF), ya buƙaci Gwamnatin Najeriya da ta tabbatar da cewa manufofin tattalin arziƙin ƙasar sun kare muradun mutane masu rauni. Daraktar Hulɗa da Jama’a na IMF, Julie Kozack, ta bayyana hakan a yayin wata ganawa da manema labarai a birnin Washington, D.C. NAJERIYA A YAU: Ƙalubalen Da Iyaye Ke Fuskanta...
    Rahotanni daga kasar Lebanon sun ce jiragen yakin HKI sun kai hari a garin “Naqura” dake kudancin Lebanon da safiyar yau Alhamis. Jiragen yakin na ‘yan sahayoniya sun kai harin ne har sau uku ajere akan wata tsohuwar cibiyar kiwon lafiya dake cikin garin, haka nan kuma akan wasu gudajen mutane da suke a kusa....
    Da marecen jiya Laraba jiragen yakin HKI sun kai wasu jerin hare-hare akan biranen Damascus, Hums,  Dar’ada Humah. Tashar Talabijin din ‘almayadin’ wai watsa shirye-shiryenta daga kasar Lebanon ta bayyana cewa; An kai harin ne akan wata cibiyar bincike a yankin Barzah dake arewacin birnin Damascus. Wata majiyar asibiti ta shaida wa tashar talabijin din...
    Babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa Rafael Grossi ya sanar da shirin kai ziyara birnin Tehran nan da makwanni masu zuwa a yayin da ake ci gaba da tattaunawa don tsaida takamaimen lokacin. Ziyarar ta zo ne a wani bangare na ci gaba da huldar diflomasiyya tsakanin Iran da hukumar...