2025-03-10@16:44:57 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1856
«Jihar Kogi»:
Gwamnatin jihar Kebbi, ta kaddamar da rabon kayayyakin noman rani da kayan abinci na watan Ramadan ga manoma da al’ummar jihar, inda ta umurci jami’an tsaro da su kama duk wanda aka samu yana sayar da kayan abinci da na aikin noma. A jawabinsa yayin kaddamar da rabon, gwamnan jihar, Kwamared Nasir Idris ya bayyana...

Nijeriya Za Ta Fara Aiwatar Da Yarjejeniyoyin Haɗin Gwiwa Da Kafofin Watsa Labarai Na Sin – Ministan Yaɗa Labarai
Ya ce: “Nijeriya da Chana sun kai matakin haɗin gwiwa mafi girma a tarihin dangantakar su. Wannan ne ya sa aka rattaba hannu kan yarjejeniyoyi guda goma a taron FOCAC, kuma guda biyu daga cikin su suna da alaƙa da ma’aikatar nan. “NTA ita ce babbar tashar talbijin a Afrika baki ɗaya, tana da...
“Ina son in nuna jin daɗina ga Babban Hafsan Sojin Sama, wanda kafin ziyarar tasa a yau, ya aiko da wata tawaga mai ƙarfi ƙarƙashin jagorancin ɗaya daga cikin manyan hafsoshi daga hedikwatar domin jajanta mana da al’ummar Zamfara. Ya aika da tawaga zuwa Zamfara a lokuta biyu daban-daban. “Ina son nanata cewa a...
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta yabawa gwamnatin jihar Jigawa bisa yadda ta nuna damuwarta kan harkokin tsaro a jihar. Mataimakin Sufeta na ‘yan sanda mai kula da shiyya ta daya, AIG Ahmed Ammani, ya bayyana haka a lokacin da ya kai wa Gwamna Umar Namadi ziyarar ban girma a gidan gwamnati dake Dutse babban...

Nazarin CGTN: Manufar Sanya Muradun Amurka Gaba Da Komai Na Lalata Dangantakar Dake Tsakaninta Da Turai
Wani nazari da kafar yada labarai ta CGTN ta gudanar, wanda mutane 15,257 daga fadin kasashe 38 suka bayar da amsa, ya bayyana cewa manufar sanya muradun Amurka gaba da komai tana da mummunan tasiri kan dangantakar Amurkar da Turai, yayin da adadin wadanda suka aminta da Amurka daga kasashe kawayenta daga cikin masu bayar...
Kwanaki 29 ke nan da wasu ‘yan bindiga suka mamaye garin Tsiga da ke ƙaramar hukumar Bakori a Jihar Katsina, inda suka yi awon gaba da Birgediya Janar Maharazu Tsiga mai ritaya da wasu mutane. An yi garkuwa da Tsiga, wanda tsohon Darakta-Janar na Hukumar Yi Wa ƙasa hidima (NYSC) ne tare da wasu mazauna...
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ce matsayarsa na ƙin amincewa a yi sulhu da ’yan bindiga na taimakawa wajen dawo da zaman lafiya a jihar. Ya bayyana haka ne a ranar Alhamis yayin da yake karɓi baƙuncin Hafsan Sojin Sama, Air Marshal Hassan Bala Abubakar. An kama ’yan Pakistan biyu da laifin yin garkuwa...
Maj.-Gen. Kangye ya kara da cewa dakarun da ke yaki da satar mai sun kwato lita 452,396 na danyen mai da aka sata, lita 224,175 na Man gas da aka tace ba bisa ka’ida ba, da kuma lita 1,920 na man fetur. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da...
Gwamnan babban bankin kasar Sin Pan Gongsheng, ya ce Sin na maraba da masu zuba jari na sassan kasa da kasa, da su shigar da jarinsu cikin kamfanonin fasaha na Sin. Pan Gongsheng, ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da manema labarai a Alhamis din nan, a gefen zaman majalissar wakilan jama’ar kasar Sin na...
Sanarwar ta ƙara da cewa, ziyarar wani bangare ne na tsarin Gwamna Dauda Lawal na tabbatar da ingantattun ayyuka a faɗin jihar da kuma tabbatar da kammala ayyukan a kan lokaci. “A ranar Talata ne Gwamna Dauda Lawal ya fara ziyarar aiki domin duba ɗimbin ayyukan da gwamnatinsa ta fara aiwatarwa. “An fara...
Shugaban kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN Ali Muhammad Ali ya ce manyan taruka biyu na kasar Sin wato taron NPC da CPPCC sun zama muhimmiyar hanya ta fahimtar manufofin da gwamnatin Sin ke dauka da yadda take daidaita harkokinta da basirarta na zamanantar da al’ummar Sinawa. Ali Muhammad ya bayyana haka ne yayin hirar da ya...
Yayin da tattalin arzikin kasar Sin ke kara samun tagomashi, masana daga sassa daban daban, na ganin hakan dama ce ta ci gaban duniya baki daya. Kamar dai yadda sakamakon wani bincike, na asusun ba da lamuni na duniya IMF ya nuna yadda bunkasar tattalin arzikin kasar Sin ke shafar ci gaban tattalin arzikin duniya...
Jami’an hukumar ’yan sandan Jihar Legas sun kama wasu ’yan ƙasar Pakistan guda biyu, Roman Gull mai shekara 19 da kuma Aftab Ahmad mai shekara 28 bisa zargin jagorantar wata ƙungiyar masu garkuwa da mutane a jihar. Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa waɗanda ake zargin tare da wasu mutum biyar ne, sun kama wani ɗan...
Don haka, Majalisar Dattawa ta dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan na tsawon watanni shida saboda saba ka’idojinta na majalisar dattawa. Bugu da kari, majalisar ta bukaci Natasha da ta maido da duk wani abu mallakin majalisar ga mai kula da Majalisar har sai lokacin dakatarwar ya cika. Sanata Imasuen ya bayyana cewa, “A...
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Jihar Neja ta sanya ranar 1 ga watan Nuwamba, 2025 domin gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi. Shugaban Hukumar Zaɓen, Mohammed Jibrin Iman ne ya bayyana haka a lokacin da yake ƙaddamar da jadawalin ayyukan gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi na shekarar 2025 a hedikwatar hukumar da ke Minna, babban...
Da yammacin yau Alhamis ne babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban kasar, kana shugaban kwamitin kolin soja Xi Jinping, ya ziyarci mambobin taro na uku na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa wato CPPCC karo na 14 ta kasar Sin, wadanda suka zo daga kungiyar dimokuradiyya ta kasar Sin,...
Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya jaddada kudurin Najeriya na aiwatar da cikakken yarjejeniyar biyu da aka kulla tsakanin China Media Group da manyan gidajen watsa labarai na gwamnati a Najeriya – Hukumar Talabijin ta Najeriya (NTA) da Hukumar Rediyon Tarayyar Najeriya (FRCN) a taron hadin gwiwa tsakanin Sin...
Majalisar Dokokin ECOWAS, ta kafa wani kwamiti na musamman domin tattaunawa da shugabannin kasashen Burkina Faso, Mali, da Nijar da suka fice daga kungiyar, tare da kokarin magance matsalolin siyasa a yankin Yammacin Afirka. Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Sanata Barau Jibrin, wanda mamba ne a Majalisar ECOWAS, ya tabbatar da haka a wata tattaunawa...
Shugaban Amurka Donald Trump ya shaidawa kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ta Hamas cewa zai ba da izinin sake kai sabbin hare-hare a zirin Gaza muddin kungiyar bat a saki sauran Isra’ilawan da ta yi garkuwa da sub a. Barazanar ta Trump ta zo ne a wata tattaunawa kai tsaye a Doha tsakanin wakilinsa kan al’amuran da...
Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya dage dakatarwar da aka yi wa mai bashi shawara na musamman kan harkokin albashi da fansho, Bashir Ado Kazaure da aka mishi a baya ba tare da bata lokaci ba. Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Jigawa Malam Bala Ibrahim ya sanyawa...
Dubban al’ummar Musulmi ne suka halarci jana’izar Mataimakin Shugaban Ƙungiyar Izala na Ƙasa, Sheikh Hassan Jingir, a garin Jos. An gudanar da sallar jana’izar ne a ranar Alhamis a unguwar Anguwan Rimi da ke Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato. Majalisar Dattawa ta dakatar da Sanata Natasha na watanni 6 An sako ɗaliban...
Har ila yau, jim kadan bayan ficewar Zelenskyy daga Washington, shugabannin kasashen Turai da suka hada da na Jamus da Faransa da Italiya da kuma Birtaniya suka yi gaggawar mara masa baya, yayin da wasu ‘yan majalisar dokokin Amurka suka yi kakkausar suka ga Ukraine wanda a cewar Sanata Lindsey Graham na jam’iyyar Republican ta...
Majalisar Dattawa ta dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, na tsawon watanni shida. Wannan hukunci ya biyo bayan amincewa da rahoton Kwamitin Ladabtarwa da Ɗa’a na Majalisar, wanda ya bincike ta kan zargin karya dokokin majalisar. Tsarin Sufuri: Gwamnatin Kano da kamfanin Stata sun ƙulla yarjejeniya Majalisar Dattawa na shirin dakatar...
Gwamnatin Jihar Kano, ta ƙulla yarjejeniya da kamfanin Stata Logistics Limited domin kafa sabon tsarin sufuri na zamani da za a dogara da amfani da CNG (Compressed Natural Gas) a jihar. A taron da aka gudanar a Ma’aikatar Sufuri ta Kano, Daraktan Kamfanin Stata Logistics, Chuks Nwani, ya bayyana cewa shirin zai rage cunkoson ababen...
Gwamnatin Jihar Ogun ta rufe masana’antu guda biyu, na Quantum Steel Industry da ke Ogijo, a Ƙaramar Hukumar Sagamu da kuma kamfanin Xinfeng Plastics Limited da ke kan hanyar Legas zuwa Ibadan. An rufe kamfanonin sakamakon haɗurran da ake samu a masana’antun da suka yi sanadin asarar rayuka. An sako ɗaliban jami’ar da aka yi...
Jami’an hukumar yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi ta NDLEA a Kano sun shiga hannu bayan sun harbe wata budurwa mai shekaru 19, Patience Samuel, a unguwar Jaba. Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:55 na dare a ranar Laraba, inda rahotanni suka nuna cewa jami’an ‘yansanda sun kai ɗauki, suka kwashe ta zuwa Asibitin...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kwamitin Majalisar Dattawa ya bayar da shawarar a dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, na tsawon watanni shida. Kwamitin ladabtarwa da ɗa’a ne, ya bayar da shawarar biyo bayan zargin da ta yi wa Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio, kan cin zarafinta. Sheikh Sa’idu Hassan Jingir ya rasu A yi adalci a...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya NUJ, FRCN Kaduna Chapel, ta jaddada kudirinta na inganta jin dadin mambobinta ta hanyar bullo da sabbin tsare-tsare da shirye-shiryen tallafi. Shugaban kungiyar, Kwamared Umar Adamu Sarikin Fada ne ya bayyana haka a lokacin rabon kayan abinci na Ramadan ga ‘yan kungiyar a Kaduna. Umar Adamu Sarikin Fada ya bayyana...
Daliban da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a Jami’ar Tarayya ta Joseph Sarwuan Tarka da ke Jihar Binuwai sun kubuta. Daliban sun lubauta ne bayan shafe kwanaki takwas a hannun ’yan ta’addan.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’ila Bakai, ya ce, Iran tana kokarin ganin cewa an gudanar da taron kungiyar kasashen musulmi domin tattauna batun barazanar tilasta mutanen Gaza yin hijira. Haka nan kuma ya ce, wannan tunanin na korar falasdinawa daga Gaza, ba wani abu ba ne sai cigaba da kisan kiyashi, ta hanyar amfani...
Kasar Tunisiya ta shiga cikin sabuwar dambaruwar siyasa saboda yadda ake yi wa wasu fitattun ‘yan siyasa, lauyoyi da kuma ‘yan jarida 40 shari’a, bisa zargin cewa suna yi wa kasa makarkashiya. An jibge jami’an tsaro masu yawan gaske a bakin kotun, yayin da a wajenta kuma masu fafutuka suke bayar da taken nuna kin...
Kamfanin dillancin Labarun “Resuters” ya nakalto cewa jami’an tsaro sun killace gidan mataimakin shugaban kasa da wasu manyan jami’an soja da fararen hula. Baya ga mataimakin shugaban kasa Riek Machar da sojoji su ka yi wa daurin talala a cikin gidansa, an kuma kama mataimakin hafsan hafsoshin sojan kasar Jamar Gabriel Doup Lam, sai kuma...
Jaridar Telegraph da ake bugawa a Birtaniya ta buga wata kasida da a ciki ta bayyana zancen aikewa da sojojin kasar zuwa Ukiraniya a matsayin abin dariya wanda yake son komawa da gaske bayan da ya kasance abin dariya. Marubuciyar wannan kasida Allison Pearson ta ce ba a taba yin wani lokaci da fira ministan...
Wakilin ɗan wasan, Jorge Mendes, ne ya tabbatar da batun sabon kwantiragin, yana mai cewa, duba da yadda Yamal ke taka leda a halin yanzu, yana da muhimmanci ya ci gaba da kasancewa tare da Barcelona. Ƙungiyoyi da dama sun nuna sha’awar ɗaukar Yamal, amma Barcelona ta dage cewa ba za ta bari ya bar...
Liverpool na farautar ɗan wasan Bournemouth mai shekara 21 daga Hungary Milos Kerkez kan fam miliyan 40. (Telegraph – subscription required) West Ham na kokarin ganin ta saye ɗan wasan tsakiya a Ingila, Angel Gomes mai shekara 24 daga Lille a sabuwar kaka. (Guardian) Manchester United na tunanin ɗauko mai tsaron raga a...
Jami’ai a Ukraine sun ce mutane huɗu sun mutu, 29 da suka jikkata, a wani harin makami mai Linzami da Rasha ta kai kan wani Otel a birnin Kryvyi Rih – Mahaifar shugaba Zelensky. Masu aikin ceto na ƙoƙarin zaƙulo masu sauran numfashi a ɓaraguzan gine-gine. Wannan hari na zuwa ne sa’o’i bayan...
Shugaban kungiyar marubuta wasanni ta kasa SWAN, Kwamared Isaiah Benjamin, ya bukaci sabon kwamitin hadin gwiwar SWAN da aka kaddamar da su farfado da kungiyar ta hanyar jawo masu zuba jari don tallafa wa marubutan wasanni a fadin kasar nan. Da yake jawabi yayin kaddamar da aikin kwamred Isaiah Benjamin ya jaddada mahimmancin karfafa...
Shugaban hukuma mai lura da hada hadar samar da kudade ta kasar Sin Li Yunze, ya ce kasar za ta kara azamar samar da kudaden gudanar da kamfanoni masu zaman kan su, da kanana da mafiya kankantar sana’o’i. Li, wanda ya yi tsokacin a Larabar nan, a gefen taron majalisar wakilan jama’ar kasar Sin dake...
A wani yunkuri na bunkasa sana’o’in hannu da kuma karfafa wa masu bukata ta musamman, wata kungiya mai zaman kanta mai suna Women Farmers Advancement Network (WOFAN) ta kaddamar da wata cibiyar kasuwanci ta mata masu sarrafa kayayyaki tare da baiwa masu bukatar su 450 a yankin Karfi. Wannan yunƙurin na da nufin ƙarfafa su...
Kwamandan runduna ta 6 ta sojan Nijeriya a jihar Taraba, Birgediya Janar Kingsley Chidiebere Uwa, ya karbi bakuncin mahalarta kwas din Cibiyar Bayar da Agaji ta Sojojin Najeriya (NARC) karo na 7/2025 a wani rangadin karatu a jihar Taraba a hedkwatar rundunar dake Jalingo. A yayin ziyarar, Janar Uwa ya yi wa mahalarta taron...
Gwamnatin Sakkwato ta buƙaci a yi adalci a binciken da ake yi kan silar rasuwar ɗan ƙwallon ƙafan nan ɗan asalin jihar, Abubakar Lawal, wanda ya rasu a satin da ya gabata kasar Uganda inda yake taka leda. Kwamishinan Matasa da Wasanni na jihar, Injiniya Almustafa Muhammad Kofar Marke ne ya sanar da hakan a...
Yayin da watan Ramadan ya shiga kwana na 6, masu lura da al’amura da dama na kokawa kan tsadar kayan marmari a Kano, wanda suke ganin wani muhimmin bangare ne na karin kumallo da ake yi a sahur da kuma lokacin buda baki. Malam Bello Ibrahim da Abdulmajeed Baba, masu amfani da ’ya’yan itatuwa...
An yi kira ga al’ummar musulmi da su kara yawan ruwa da ‘ya’yan itatuwa a lokacin azumin watan Ramadan domin inganta sinadaran jiki. Wani kwararre a fannin lafiya a Jami’ar Ilorin, Farfesa AbdulRahman Afolabi ne ya yi wannan kiran a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Ilorin, jihar Kwara. Ya ce...
A ranar 29 ga watan Janairu, 2025, ƙasashen Burkina Faso, Mali, da Nijar – waɗanda suka haɗe a ƙarƙashin Ƙawancen Ƙasashen Sahel (AES) – sun sanar da ficewarsu daga ECOWAS. Duk da hakan, ECOWAS ta tabbatar da cewa babu wata matsala a ɓangaren sufuri da kasuwanci tsakanin ƙungiyar da ƙasashen AES, domin har yanzu ana...
Jam’iyyar PDP a jihar Gombe ta bayyana rashin jin dadin ta ga gwamna Inuwa Yahaya kan rabon kayan abinci da gwamnatin tarayya ta baiwa jihar a matsayin tallafin azumin watan Ramadan. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na jam’iyyar Abdulkadir Ahmad ya fitar a Gombe. Jam’iyyar ta...
Gwamna Dauda Lawal ya amince da nadin Yakubu Sani Haidar a matsayin babban shugaban ma’aikatan jihar Zamfara. Nadin wanda ke fara aiki nan take, ya fito ne a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar (SSG), Malam Abubakar Mohammad Nakwada, ta bakin babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Sulaiman...
Hukumar Tsaro ta Sibil Difens (NSCDC) ta samu sahalewar Shugaban Ƙasa na ƙara daukar sabbin ma’aikata. Babban Kwamandan Hukumar, Ahmed Aifi, na ya sanar da haka, a yayin ƙaddamar da Baban Ofishin Yanki na Hukumar a Ƙaramar Hukumar Bwari da ke yankin Babban Birnin Tarayya a ranar Laraba. “Nan gaba kaɗan za mu ɗauki ’yan...
Hukumar Tsaro ta Sibil Difens (NSCDC) ta samu sahalewar Shugaban Ƙasa na ƙara daukar sabbin ma’aikata. Babban Kwamandan Hukumar, Ahmed Aifi, na ya sanar da haka, a yayin ƙaddamar da Baban Ofishin Yanki na Hukumar a Ƙaramar Hukumar Bwari da ke yankin Babban Birnin Tarayya a ranar Laraba. “Nan gaba kaɗan za mu ɗauki ’yan...