2025-03-28@23:41:01 GMT
إجمالي نتائج البحث: 542
«Kungiyar Agaji»:
Ƙungiyar Jama’atul Nasrul Islam (JNI) , ta raba kayayyaki da sauran kyatuttukan Sallah ga marayu 50 gabanin bikin Sallah ƙarama a garin Maiduguri, babban birnin Jihar Borno. An gudanar da bikin ba da tallafin ne a harabar makarantar sakandare ta Bulabulin da ke birnin na Maiduguri. Yadda kisan ’yan Arewa 16 a Edo ya tayar...
Manyan Matakai Biyar Da Manoma Da Masu Zuba Hannun Jari A Fannin Aikin Noma Ya Kamata Su Yi La’akari Da Su Kamar Yadda kwararrun Suka Bayar Da Shawara: 1- Irin Kwakwar Manja Na Malesiya Bukatar da ake da ita ta Irin Kwakwar Manjan Nijeriya a duk shekara, ya kai na tan miliyan 3, inda kuma...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmaeil Baghaei ya ce hare-haren da sojojin Amurka ke kaiwa kasar Yemen da keta hurumin yankunanta barazana ce karara ga zaman lafiya da tsaron kasa da kasa. A cikin wata sanarwa da ya fitar yau Juma’a, Baghaei ya yi tir da hare-haren da Amurka ke kai wa Yemen ba bisa...
A cewar shugabannin Ƙwadago, dole ne a sauya irin wadannan lamari don kare mutuncin tsarin dimokuradiyya a Nijeriya. Sun jaddada wahalar da dokar ta-ɓaci ta haifar wa ma’aikatan kananan hukumomi, da yawa daga cikinsu har yanzu ba su karɓi albashinsu ba. Sanarwar ta lura cewa hana albashin ma’aikata ya jefa su cikin matsin tattalin arziki,...
A ranar Juma’a kasuwar ta rufe a cikin makon makon inda masu zuba hannun jarin, suka yi asarar Naira biliyan 166.43. Duk a cikin makon, saye da sayawar da aka yi ta shiyar ta kai ta jimlar Naira biliyan 3.281 da kuma wata shiyar ta Naira biliyan 63.517, duk a cikin hada-hada guda 60,782 da...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno, ta kama wasu matasa uku da ake zargi da satar kekunan ɗinki guda 19 a cibiyar koyon sana’a ta Dala Lawanti da ke Maiduguri. A cewar ’yan sanda, wani mai gadi a cibiyar, Kaka Modu Mustapha, mai shekaru 34, ya haɗa baki da wasu matasa biyu – Bukar Mustapha mai...
Ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS), ta kammala gyara wata cibiya don kula da masu fama da shan miyagun ƙwayoyi a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano (AKTH) da ke Kano, tare da miƙa ta ga asibitin domin amfanin jama’a. Jami’in ECOWAS mai kula da shirin hana yawaitar shan miyagun ƙwayoyi, Dokta Daniel...
kungiyar ta koka kan cewa bai dace a yi amfani da EFCC wajen kamun Jami’an gwamnatin jihar Bauchi da nufin nuna yatsa wa Gwamna Bala Muhammad wanda ya kasance mai fitowa da hakikanin gaskiyar halin da talakawa ke ciki da nema musu hakkinsu daga wajen shugaban kasa. kungiyar ta lura da cewa in ana amfani...
Sojojin Iran sun fitar da bayani a daidai lokacin da ake shirin raya ranar Kudus ta duniya, suna masu bayyana cewa; Hanyar da za ta warware matsalar Falasdinu ita ce yin gwgawarmaya da kuma samun goyon baya daga al’ummun duniya. Bayanin ya kuma kara da cewa; A daidai lokacin da al’ummar Falasdinu suke fuskantar zalunci,ta’addanci,...
Bayanai daga falasdinu na cewa an kashe Hamas Abdul-Latif al-Qanou wani kakakin kungiyar Hamas a wani harin da Isra’ila ta kai a arewacin Gaza. Kamfanin dillancin labaran Quds na Falasdinu ya bayar da rahoton cewa, jami’in ya yi shahada ne a wani harin da Isra’ila ta kai ta sama a kan tantinsa a garin Jabalia...
Gwamnatin jihar Kano ta bayyana kudirinta na tallafawa shirin inganta ilimi na bunkasa Afirka (BEAR) III, wani shiri na hadin gwiwa da hukumar kula da ilimi da kimiya da al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya (UNESCO) da Jamhuriyar Koriya suka yi. A wata sanarwa mai dauke da sa hannun daraktan wayar da kan jama’a ma’aikatar...
Kamfanin Hisense South Africa, da kamfanin CNBM, sun sanya hannu kan wata yarjejeniyar hadin gwiwa bisa matsayin koli, ta gudanar da aikin samar da hidimomin kyautata amfani da makamashi mai tsafta a Afirka ta kudu. Kamfanonin biyu sun rattaba hannu kan yarjejeniyar ne a jiya Talata, a birnin Johannesburg, yayin bikin baje hajojin da suka...

Gwamnatin Tarayya ta ayyana Litinin da Talata a matsayin hutun sallaGwamnati Ta Ayyana 31 Ga Maris Da 1 Ga Afrilu A Matsayin Ranakun Hutu Don Bukin Eid-el-Fitr Gwamnatin Tarayya ta ayyana Litinin, 31 ga Maris, da Talata, 1 ga Afrilu, a matsayin ranakun hu
Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Litinin, 31 ga watan Maris, da Talata, 1 ga watan Afrilu, a matsayin ranakun hutun ƙaramar salla. Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da sakataren ma’aikatar, Magdalene Ajani, ya fitar a ranar Laraba. Ahmad Lawan ya raba tallafin N27m da buhun shinkafa 300...
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na Duniyarmu a yau shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhummanci a makon da ya gabata, dangane da siyasa tattalin arziki zamantake tsaro da sauran, sannan mu yi masu karin bayani daga karshe mu ji ra’ayin masana dangane da su....
Gidauniyar Daily Trust (DTF) tare da haɗin gwiwar ƙungiyar WRAPA, Hamu Legal, da Bahama Chambers, sun biya tarar fursunoni 21 domin su samu damar fita daga gidajen gyaran hali a Jihohin Kaduna da Katsina. A Kaduna, an ’yanta mutum 17 bayan da DTF da abokan aikinta suka biya tarar su har Naira miliyan biyu da...
Ministan Tsaro, Mohammed Abubakar Badaru, ya ziyarci Cibiyar Horar da Sojoji da ke Zariya, inda ya yi alƙawarin samar da ƙarin kayan aiki da ci gaba da inganta horon kuratan sojoji domin su dace da buƙatun zamani. A lokacin ziyarar, Ministan ya bayyana gamsuwarsa da horon da kurata na kashi 88 ke samu, inda ya...
Dakarun (RSF) sun sanya sabbin takunkumai kan isar da kayan agaji a yankunan da ke karkashin ikonsu, lamarin da ya kara ta’azzara matsalar ayyukan jin kai, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito. Matsalolin dai na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar RSF ke kokarin kafa gwamnatin daga bangarenta a yammacin kasar...
Wani rahoto da aka fitar yau Talata, yayin zaman taron shekara-shekara na shekarar 2025, na dandalin tattaunawa na Asiya na Boao, ya nuna yadda kasar Sin ke ci gaba da kasancewa cibiyar rarraba hajojin da masana’antu ke sarrafawa. Rahoton mai taken “Nazarin tattalin arzikin Asiya, da hadadden rahoton ci gaba na shekarar”, ya nuna yadda...
Tsohon Shugaban Nijeriya, Cif Olusegun Obasanjo ya ce mulkin dimokuraɗiyya ya gaza wajen kawo ci gaba a nahiyar Afirka. Ya ce tsarin ya gaza ne saboda abin da ya ƙunsa bai zo daidai da al’adu, da yadda ake tafiyar da rayuwa a nahiyar ba, da abubuwan da mutanen nahiyar suka yi amanna da su ba....
Ba wannan tarihi na kanfar iko da ayarin farko na “yan majalisun wannan kasa ke da shi ne abin kallo ko la’akari ba, cikakkiyar dama da suke da ita a yau, tare da turbude hancin bukatun masu zabe, shi ne babban abin nadama da kaico!!!. Idan a wancan lokaci za a ce Turawa sun rike...
A ƙoƙarinta na tallafa wa marayu da mabuƙata, gidauniyar Zakkah da Wakafi a Gombe ta raba wa yara marayu da mabuƙata 100 kayan Sallah. Da yake jawabi a lokacin rabon tufafin, Shugaban gidauniyar, Amir Abdullahi Abubakar Lamido, ya ce al’adar gidauniyar ce ta riƙa zaƙulo mabuƙata tare da tallafa musu musamman a lokutan bukukuwan Sallah....

Shugaban Majalisar Dokokin Kasar Lebanon Ya Ce Basa Da Wani Shiri Na Samar Da Haldar Jakadanci Da HKI
Shugaban majalisar dokokin kasar Lebanon Nabih Berry ya bayyana cewa HKI tanason jawosu cikin tattaunawar diblomasiyya wanda zai kai kasar ga samar da huldar jakadanci da ita, amma mu bama tare da wannan ra’ayin. Nabih Berry ya bayyana haka ne a lokacinda yake zantawa da jaridar ‘Sharqul Awsad’ ya kuma kara da cewa a halin...
Wannan ya taimaka wajen kawo ƙarshen yaƙin basasa a Laberiya da Saliyo. Duk da haka, ƙungiyar ta fuskanci ƙalubale, musamman bayan juyin mulki a ƙasashen Mali, Burkina Faso, da Nijar a cikin shekarun baya-bayan nan. Shin ECOWAS na iya ci gaba da aiwatar da ayyukanta kamar da? Sai dai har yanzu wasu na yi wa...
Kungiyar gwagwarmayar falasdinawa ta Hamas, ta bayyana cewa Isra’ila ta yi amfani da sulhun da aka cimma wajen tattara bayanai kan shugabannin kungiyar ta bi tana kashe su. Saidai mai magana da yawun kungiyar ya ce kungiyar tana da tushe sosai a Falasdinu wanda kisan gillar da Isra’ila ke yi wa shugabanninta ba, bai zai...
Kungiyar ‘Yan Jaridu ta Najeriya (NUJ) reshen Jihar Kebbi ta raba kayan abinci da kudi ga iyalan mambobinta da suka rasu a lokacin da suke kan aikin jarida, a matsayin kyautar azumin Ramadan. Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban Kungiyar na Jiha, Kwamared Bello Sarki Abubakar, ya ce suna gudanar da wannan shiri a...
Samira Sani ‘yar asalin garin Kano ne da ta shigo Masana’anrtar Kannywood a 2022. A tattaunarta da Aminiya, ta ba da tarihinta da kuma yadda ta daɗe tana mu’amala da ‘yan Kannywood kafin ta fara fitowa a fim: Za mu so ki gabatar da kanki? Suna na Samira Sani, jaruma a Masanartar Fim ta Kannywood....
Rahotanni daga Falasdinu na cewa akalla Falasdinawa 61 ne sukayi shahada a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, in ji ma’aikatar lafiya ta Gaza. A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, ma’aikatar ta ce an gano gawarwaki hudu a karkashin baraguzan gini, sannan an kwantar da mutane 134 da suka jikkata a asibiti...
A yau Litinin ne kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Guo Jiakun, ya jagoranci taron manema labarai na yau da kullum, inda wani dan jarida ya yi tambaya game da ko Sin za ta shiga tattaunawa da Amurka, game da hakan Guo Jiakun ya ce, a ko da yaushe kasar Sin na da imanin cewa, kiyaye...
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Juventus ta raba gari da mai horas da ’yan wasanta, Thiago Motta, yayin da ko kaka ɗaya bai cika ba a kwantaragin da ya ƙulla da ƙungiyar ta Italiya. A cewar Jaridar wasanni ta La Gazzetta dello da Gidan Talabijin na Sky Sport, Juventus ta maye gurbin Thiago Motta da tsohon...
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Juventus na shirin raba gari da mai horas da ’yan wasanta, Thiago Motta, yayin da ko kaka ɗaya bai cika ba a kwantaragin da ya ƙulla da ƙungiyar ta Italiya. A cewar Jaridar wasanni ta La Gazzetta dello da Gidan Talabijin na Sky Sport, Juventus na shirin maye gurbin Thiago Motta...
Aƙalla fursunoni 12 ne suka tsere baya sun fasa wani gidan yari da ke garin Kotonkarfe a Jihar Kogi. Kwamishinan watsa labarai na jihar, Kingsley Fanwo ya tabbatar da aukuwar lamarin. Za mu farfaɗo da Madatsar Ruwa ta Biu — Zulum Wasu manyan ’yan Nijeriya sun yi wa Gwamna Radda ta’aziyya a Saudiyya Mista Fanwo...
Iran ta yi gargadin cewa zaluncin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi wa kasar Labanon na da matukar hadari kuma barazana ga zaman lafiya da tsaron kasa da kasa, inda ta bukaci kasashen duniya da su dauki matakin da ya dace. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmaeil Baghaei ya yi kakkausar suka kan hare-haren...
Ƴansandan sun gayyaci Sanata Sunday Karimi domin bayani kan zarginsa na cewa ƙungiyar leƙen asirin ƙasar Rasha ta KGB ta samu shiga cikin Majalisar Dokoki, wanda ke barazana ga tsarin dimokuraɗiyya a Nijeriya. Zargin ya samo asali ne daga rahoton da Sanata Karimi ya raba akan ƙungiyar ta WhatsApp a Majalisar Dattijai a ranar 23...
Kungiyar gwagwarmayar Falastinawa ta Hamas ta fitar da wata sanarwa dangane da shahadar Salah al-Bardawil, mamba a ofishin siyasa na kungiyar kuma wakilin majalisar dokokin Falasdinu. A rahoton tashar Al-Alam, bayanin Hamas yana cewa: Dr. Salah Al-Bardawil, wanda ya yi fice a fagen siyasa, kafofin watsa labarai, da fagage na kasa da kasa, kuma ake...
Kungiyar da ke sa ido da kare hakkin dan adam ta Syria (SOHR) ta fitar da fayafan bidiyo guda hudu da ke dauke da hotunan azabtarwa da kisa da jami’an tsaron sabuwar gwamnatin kasar karkashin kungiyar Tahrir Sham suke aiwatarwa a kan fararen hula tsiraru marasa rinjaye a kasar. Kungiyar da ke sa ido kan...
A yau Lahadi, kwararren masanin tattalin arziki dan kasar Amurka Jeffrey Sachs ya bayyana cewa, matakan kariyar cinikayya da Amurka ke aiwatarwa babban kuskure ne. Jeffrey wanda ya halarci dandalin bunkasa kasa na Sin na shekarar nan ta 2025 a birnin Beijing, ya kara da cewa Amurka na kara karkata ga salon kariyar cinikayya karkakin...
Shugqbqn kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen sayyed Abdulmalik Badaruddin Huthi ya bayyana cewa tura wani kataparen jirgin ruwan yaki zuwa gabas ta tsakiya wanda shugaban kasar Amurka yayi wata gazawace. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalti Alhuthi yana fadar haka yau Lahadi a wani jawabin da ya gabatar ,inda yake bayyana irin...
Gwamnonin Arewa sun aike wa Gwamna Dikko Umar Radda na Jihar Katsina, saƙon ta’aziyya game da rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Safara’u Umaru Baribari, wadda ta rasu tana da shekaru 93. Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa (NSGF) kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana Hajiya Safara’u a matsayin uwa mai tausayi da riƙon gaskiya, wadda...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi, ta kama wasu matasa huɗu da ake zargi da yin garkuwa da kuma kashe wani yaro ɗan shekara shida, Shuaibu Safiyanu, a ƙauyen Sade da ke Ƙaramar Hukumar Darazo. Aminiya ta ruwaito cewar mahaifin yaron, Safiyanu Abdullahi ne, ya sanar da Sarkin garinsu, Musa Isah, cewa a ranar 20 ga...
Kasar Rasha ta bayyana cewa dole Moscow da Beijing su shiga shawarwarin tattaunawar nukiliya da Iran. Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha Maria Zakharova ta bayyana cewa, Moscow a shirye take ta samar da ingantacciyar hadin gwiwa da dukkan bangarorin kan batun yarjejeniyar nukiliyar Iran. “ Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar...
Ana sa ran, za a yi jana’izarta yau Lahadi 23 ga watan Maris, 2025 kamar yadda addinin Musulunci ya tanada da misalin 4 na yamma (4pm) a garin Radda, ƙaramar hukumar Charanchi da ke jihar Katsina. Hajiya Radda, jigo ce da za a rika tunawa da ita bisa hikima da juriya wanda hakan ya...
Allah Ya yi wa mahaifiyar Gwamnan Katsina, Dikko Umar Radda rasuwa. Wakilinmu ya ruwaito cewa, mahaifiyar Gwamnan, Hajia Safara’u Umar Radda, ta rasu ne a wani asibiti da ke birnin Katsina. Cikin wani saƙo da tsohon mai magana da yawun gwamnan, Isah Miqdad ya wallafa a shafinsa na X, ya ce Hajiya Safara’u ta riga...
Gwaje-gwajen da aka yi a ranar 17 ga Maris sun nuna cewa dan wasan tawagar farko Marc Casadó yana da rauni a gefen damansa, za a kara yin gwajin dan wasan don sanin girman raunin da kuma kwanakin da zai shafe ta na jinya, hakazalika Gwaje-gwaje a wannan rana kuma sun tabbatar da cewa dan...
Ministan harkokin wajen kasar Iran, Abbas Araghchi, ya yi kakkausar suka kan zaluncin da gwamnatin Isra’ila ke yi kan al’ummar Falasdinu da ba su da kariya a yankin Zirin Gaza, yana mai jaddada bukatar hadin kai da daukar matakin gaggawa na kasashen musulmi domin dakile wadannan laifuka. Babban jami’in diflomasiyyar ya bayyana hakan ne a...
Kungiyar Taliban ta ce Amurka ta cire tallafin dala miliyan 10 ga duk wanda ya bayar da bayanai kan Sirajuddin Haqqani, mataimakin shugaban kungiyar kuma ministan harkokin cikin gida. A cewar Abdul Mateen Qani, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin cikin gidan Taliban, an janye tukuicin da aka bayar a baya a karkashin shirin bayar...

Kao Kim Hourn: Ba Ta Hanyar ‘Siddabaru’ Kasar Sin Ta Cimma Nasarori A Fannin Ci Gaba Ba Sai Dai Ta Hanyar Aiki Tukuru Kuma Mai Dorewa
A kwanan nan ne sakatare janar na kungiyar ASEAN Kao Kim Hourn ya bayyana a wata hirar da ya yi da wakilin babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG cewa, nasarorin da Sin ta samu ta fuskar ci gaba ba sakamakon ‘siddabaru’ ba ne, illa sakamakon aiki tukuru kuma mai dorewa. Kao...
Kyari ya ci gaba da cewa, wannan bangare na noma don samun riba; shi ma zai amfana da Naira biliyan 500, wanda ya kai kimanin dala biliyan 300, wanda su ma wadannan kudaden za a bai wa Bankin Aikin na Noma. Kazalika, Kyari ya yi kira ga Bankin EBRD, da ya zuba hannun jari a...
Kamfanin dillancin labarun “Anatoli” na Turkiya ya ambato cewa; Ministan harkokin cikin gida na Jamhuriyar Nijar Mohamed Toumba ne ya bayar da labarin cewa, mutane da dama sun kwanta dama sanadiyyar harin da su ka kai wa masu masu salla a garin Fonbita dake gundumar Kokorou. Rahotannin sun tabbatar da cewa adadin masu sallar da...
Gwamnatin Jihar Borno, ta ɗauki matakin hukunta wasu ma’aurata, Mamman Sheriff da matarsa, da aka kama suna cin zarafin wata yarinya a unguwar Pompomari Bypass da ke Maiduguri. Bayan bayyanar faifan bidiyon da ya nuna ma’auratan suna dukan yarinyar, mutane da dama sun yi tir da abin a shafukan sada zumunta. Majalisar Wakilai ta musanta...
Wata kungiya mai suna Grassroots Mobilizers for Better Nigeria Initiative (GMBNI), ta yi Allah wadai da kisan gilla da aka yi wa wani Almajiri a ƙaramar hukumar Gwaram, Jihar Jigawa. Ƙungiyar ta bayyana matuƙar bakin ciki da ɓacin rai game da wannan cin zarafin da aka yi wa yaron, wanda ya kai ga mutuwarsa cikin...