2025-03-23@08:10:15 GMT
إجمالي نتائج البحث: 872
«Zakara»:
Wani ɗan ƙasar Turkiyya da ya rasa gidansa sakamakon wata gagarumar girgizar ƙasa a shekarar 2023, ya shafe shekara biyu yana zaune shi kadai a cikin wani ƙaramin kogo saboda yana ganin ya fi kowane gini da mutum zai yi karko. A watan Fabrairun 2023, Kudancin Turkiyya ya fuskanci ibtila’in girgizar kasa mai karfin 7.8...
Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada bukatar bin dokar da ta hana kiwon dare da makiyaya ke yi a fadin jihar domin rage hadurra a tituna, wanda ke haddasa asarar rai ko shiga mawuyacin hali a sanadiyar raƙuman da ke bi ta manyan tituna. Gwamna Umar Namadi ya bayyana hakan yayin da ya karbi...
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya bayyana a jiya cewa, kasar Sin na dora muhimmanci sosai kan hadin gwiwar dake tsakanin kasarsa da kasashen Japan da Koriya ta Kudu, kuma tana da kwarin gwiwa kan hakan. Wang ya bayyana hakan ne a lokacin da yake halartar taron firaministan kasar Japan Shigeru Ishiba a...
An ruwaito cewa, shirin aikin noman ranin da aka kaddamar a yankin na Lallashi, zai karade hekta 10, wanda kuma sama da kananan manoma 80, za su amfana da shirin kai tsaye. Bugu da kari, shirin zai taimaka wajen kara samar da girbin amfanin gona mai yawan gaske tare kuma da kara bunkasa tattalin arzikin...
Likitoci sun tabbatar da mutuwarsa, daga nan aka bai wa iyalansa gawarsa domin yin jana’iza. Kakakin ‘yansandan Bauchi, CSP Ahmed Mohammed Wakil, ya ce suna samun labarin lamarin, jami’ansu suka fara bincike, musamman a wajen POS da ke kusa da inda aka nemi a biya kuɗin fansar. A yayin binciken, sun kama wani matashi mai...
A wata hira da tashar talabijin din, manzon musamman na Amurka a yankin gabas ta tsakiya Steve Witkoff ya rubuta a shafinsa na; X cewa; Sakon da Trump ya aike wa Tehran ba ta nufin yin barazana. Manzon na Amurka ya riya cewa;wasikar ta kunshi cewa; Ni shugaban kasa ne mai son zaman lafiya ,...
“Bayan nazari da tattaunawa da gwamnati, Gwamna Bala Abdulkadir Muhammad ya amince da gudanar da wannan gagarumin biki,” in ji shi. Sanarwar ta ƙara da cewa za a fitar da cikakken jadawalin shirye-shiryen hawan nan gaba kaɗan, tare da fatan Allah Ya sanya ayi bikin lafiya. A tarihi, Hawan Daushe yana da muhimmanci sosai a...
Sabon Kocin tawagar Super Eagles ta Nijeriya Eric Chelle, ya fara jagorantar tawagar da ƙafar dama, bayan samun nasara a wasan farko da ya jagorance ta. Chelle wanda ya zo Super Eagles watanni biyu da su ka gabata, ya jagoranci Super Eagles a wasan da su ka doke ƙasar Rwanda da ci biyu da nema...
Gwamnatin Jihar Borno, ta ɗauki matakin hukunta wasu ma’aurata, Mamman Sheriff da matarsa, da aka kama suna cin zarafin wata yarinya a unguwar Pompomari Bypass da ke Maiduguri. Bayan bayyanar faifan bidiyon da ya nuna ma’auratan suna dukan yarinyar, mutane da dama sun yi tir da abin a shafukan sada zumunta. Majalisar Wakilai ta musanta...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
“Saboda haka, za a soke sunayen kadarorin da suka shafe sama da shekara goma ba a biya musu haraji ba nan take, Bugu da kari kuma, ana bayar da wa’adin kwanaki 21 ga masu rike da gidajen da ake rike da bashin kudin haraji na tsawon shekara daya zuwa goma, sannan kuma za a soke...
Gwamnatin Tarayya ta kama mutum 347 da ake zargi da haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba a sassa daban-daban na Najeriya, inda aka gurfanar 143 a kotu. Kama mutanen ya biyo bayan kafa wata runduna a shekarar 2024 don daƙile ayyukan haƙar ma’adanai ba ƙa’ida ba. Kotun ƙoli ta tabbatar da Anyanwu a matsayin sakataren...
Mai magana da yawun ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin He Yongqian, ta ce kasar za ta aiwatar da matakai na kara daidaita manufar jawo jarin waje a shekarar nan ta 2025, da aiwatar da matakan bude kofa a karin sassa, da kyautata yanayin kasuwanci a fannin. He Yongqian, wadda ta bayyana hakan yayin wani taron...
Kasar Sin ta mika rijiyoyin burtsatsai 66 ga wasu yankunan lardin Mashonaland na gabashin Zimbabwe, wadanda za su samar da ruwa mai tsafta ga mutane kimanin 16,500. Rijiyoyin wadanda kamfanin gine-gine na Geo-Engineering na kasar Sin ya gina, wani bangare ne na aikin hakar rijiyoyin burtsatsai 300 ga larduna 4 na kasar Zimbabwe. Kasar Sin...
A cewarsa, tun da farko mun kau da kai ga barin sanya hannun jari a shiyyar kasuwanci ta Olokola (OKFTZ), amma saboda manufofinku da kuma yanayin da masu zuba jari ke da shi, ina so in ce mun dawo kuma za mu yi aiki tare da gwamnatin jihar don komawa Olokola, kuma ana shirin gina...
Ƙungiyar Dattawan Arewa (NEF), ta buƙaci Shugaba Bola Tinubu da gaggauta janye dakatarwar da ya yi wa Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, Mataimakiyarsa, da ’Yan Majalisar Dokokin jihar. Da yake magana a madadin ƙungiyar, Farfesa Abubakar Jika Jiddere, ya ce babu wani dalili da ya dace da zai sa shugaban ƙasa ya ayyana dokar ta-ɓaci...
A ranar Juma’a aka rantsar da sabuwar shugabar ƙasar Namibia, Netumbo Nandi-Ndaitwah domin jagorantar ƙasar wadda aka ruwaito na fuskantar ƙalubale na rashin aikin yi da talauci. Kasancewar Netumbo Nandi-Ndaitwah mace ta biyu da aka taɓa zaɓa a matsayin shugabar ƙasa a nahiyar Afirka, kuma ta farko a Namibia na iya fuskantar ƙalubale. Bam ya...

Cibiya Mai Fafutukar Kare Hakkokin Falasdinawa “Global 195” Ta Shelanta Farautar Sojojin HKI Da Su KaTafka Laifukan Yaki
Cibiyar ta “ Global 196” ta bakin babban shugabanta ta sanar da cewa a cikin watanni 18 da su ka gabata, ta tattara bayanai akan laifukan yakin da Isra’ila ta tafka a Gaza.” Haka nan kuma cibiyar mai matsuguni a Birtaniya ta ce, ya zuwa yanzu ta tattara da dalilai da su ka dace da...
Jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya bayyana cewa; Amurkawa su kwana da sanin cewa, babu wani abu da za su samu, ta hanyar yi wa Iran barazana, kuma waninsu ma ya sani cewa, idan har su ka aikata wani abu maras kyau akan Iran, to za su fuskanci mayar...
Wata gobara da ta tashi a sansanin ’yan gudun hijira na Munna Albadawi da ke ƙaramar hukumar Jere a Jihar Borno, ta lalata wasu gidaje 10 tare da salwantar da rayuwar yaro mai shekara 7 mai suna Abubakar Gargar. A cewar shugaban sansanin, Babangida Mahmud gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe 3:00 asubahin safiyar...
Ya kuma buƙaci mambobin jam’iyyar da su ci gaba da haƙuri da fahimtar juna domin haɗa kai tare da tabbatar da goyon baya ga jam’iyyar. A nasa ɓangaren, Sakataren APC na Zamfara, Hon. Ibrahim Umar Dangaladima, ya gode wa Shugaban Ƙasa Tinubu da Minista Matawalle bisa wannan tallafi. Ya ce shinkafar ta zo a daidai...
A halin yanzu, Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Borno (SEMA) da Hukumar Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) tare da wasu ƙungiyoyin jin-ƙai sun tura wakilansu don duba girman ɓarnar da gobarar ta haifar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura...
Kazalika, a wata-wata, hauhawar farashin abinci a watan Fabrairun 2025 ya tsaya da kashi 1.67 cikin dari, idan aka kwatanta da watan Janairun 2025, an samu raguwar matsakaicin farashin kayan abinci kamar su dawa, dankali, wake, masara da garin masara da rogo. Hauhawar farashin kayayyakin masarufi a Nijeriya dai ya yi tashin gwauron zabi ne...

Shugaba Bola Ahmed Tinubu A Tarayyar Najeriya Ya Bada Umurnin A Gudanar Da Bincike Kan hatsarin Daren Laraban da Ta Gabata A Abuja
Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bada umurnin a gudanar da bincike don gano abinda ya hadda hatsarin day a faru a kan gadar Karuk an titin Abuja Keffi a daren Labaran da ta gabata, wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane da kuma jikatan wasu. Jaridar Premium Times ta nakalto shugaban kasar yana fadar haka...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan, a sakonsa na karshe ga Iraniyawa a shekara ta 1403 na kalandar Iraniyawa, ya bukaci mutanen kasar su hada kai don kaiwa ga manufofin kasar, wadanda suka hada da bunkasar tattalin arziki, da kauda tsadar rayuwa da kuma rashin bawa makiya damar cutar da kasar. Tashar talabijan ta Presstv a...
Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano ta ce ta samu nasarar kammala rijistar maniyyata aikin hajjin bana 3,155. Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Lamin Danbappa, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a Kano a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar gudanarwar Hukumar Shige da Fice a...
Gwamnatin Jihar Yobe ta kafa cibiyoyin bayar da abinci 85 domin samar wa almajirai abinci a dukkanin Ƙananan Hukumomin 17 na jihar, a lokacin azumin Ramadan. Sakataren zartarwa na Hukumar Ilimin Larabci da Addinin Musulunci ta Jihar Yobe, Malam Umar Abubakar ne, ya bayyana hakan a wata hira da Daily Trust a ranar Alhamis. Sanƙarau...
A wani gagarumin yunkuri na karfafa harkokin mulki da inganta ayyukan yi, gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da nada wasu mukamai da karin girma. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar. Sabbin canje-canje da suka samo asali...
Shi wannan azumi, na wani lokaci ya fi na wani lokaci kamar an so a dinga yin azumi sau Uku a cikin kowanne wata, lokacin kwanan wata yana 13 da 14 da 15, wannan kwanaki hasken wata ya fi haske a cikinsu, to kamar yadda suke haske haka zuciyarka za ta kara haske sabida saduwa...

Hukumar Alhazai Ta Jihar Kaduna Ta Bukaci Taimakon NAMA Don Gudanar Da Aikin Hajjin Bana Cikin Nasara
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna ta roƙi Hukumar Kula da Sararin Samaniyar Najeriya (NAMA) ta ci gaba da ba da goyon baya domin tabbatar da nasarar gudanar da aikin Hajjin bana. A ziyarar ayarin hukumar ƙarƙashin jagorancin Sakataren Gudanarwa, Malam Baba Mohammed Rufa’i, wanda ya wakilci Shugaban Hukumar, Malam Salihu...
(Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Tsohon mataimakin shugaban Nijeriya, Atiku Abubakar ya bayyana cewa yanzu haka ’yan adawar siyasa a ƙasar nan a shirye suke su ƙalubalanci shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027. Tun bayan da ya sha kaye a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, Atiku ya riƙa yin taro da ’yan adawa don neman karɓe...
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Mao Ning ta bayyana cewa, kakaba haraji da sauran shingayen kasuwanci ba za su amfani kowa ba, kuma suna matukar haifar da illa ga samar da wadatar tattalin arzikin duniya, da tafiyar da shi cikin kwanciyar hankali. Jami’ar wacce ta bayyana haka a yau Alhamis yayin...
Wata gobara mai muni ta laƙume gidaje uku a unguwar New GRA, a birinn jihar Gombe, a ranar Laraba inda ta bar iyalai cikin rashin matsuguni tare da asarar dukiya ta miliyoyin Naira. Waɗanda abin ya shafa sun koka kan rashin damar ceto komai daga kayan su, kuma yanzu haka suna neman tallafin gaggawa domin...
Masu yi wa ƙasa hidima (NYSC), za su fara jin daɗin sabon alawus ɗin gwamnatin tarayya na N77,000.00 wanda aka sake duba shi da za a fara biya daga watan Maris, 2025. Babban Darakta Janar (DG) na NYSC, Birgediya Janar Olakunle Oluseye Nafiu ne ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga masu...
Tun lokacin da Donald Trump ya hau mukaminsa na shugaban kasar Amurka a watan Janairu na bana, sau da dama gwamnatinsa ta dauki matakan kakaba harajin kwastan kan abokan cinikinta. A ganinsa, matakan za su tilasta kamfanoni da su maido da tsarin samar da kayayyaki zuwa Amurka, matakin da zai gaggauta bunkasuwar masana’antun kasar. Ko...
A shekarar 2004, lokacin da Olusegun Obasanjo ya ayyana dokar ta-ɓaci a Filato, matakin ya fuskanci suka daga jama’a da ɓangaren shari’a. Masana doka da ‘yan siyasa sun yi Allah-wadai da matakin da Tinubu ya ɗauka, inda Dokta Reuben Abati ya bayyana shi a matsayin “laifi da za a iya tuhumar Tinubu a kai”. Ya...
Dokta Saleh ya yaba wa Gwamna Abdullahi Sule bisa jajircewarsa wajen bunƙasa fannin kiwon lafiya a jihar, yana mai cewa gwamnan na ƙoƙarin tabbatar da cewa kowa yana samun ingantaccen kulawar lafiya. Har ila yau, a buƙaci a samu haɗin gwiwa da manema labarai da sauran masu ruwa da tsaki domin wayar da kan jama’a...
’Yan Najeriya na iya fuskantar karin farashin man fetur bayan da Matatar Man Dangote ta bayyana cewa ta daina sayar wa ’yan kasuwa man fetur a kudin Naira. Matatar, wacce ke siyan danyen mai da Naira bisa yarjejeniyar gwamnati, yanzu ta koma sayan danyen mai da dalar Amurka. An kirkiro yarjejeniyar siyan danyen mai da...
Wasu ‘yan tada ƙayar baya bakwai da ake zargin ’yan Boko Haram ne sun miƙa wuya ga rundunar haɗin gwiwa ta ƙasa da ƙasa (MNJTF) a Damasak da ke Jihar Borno tare da miƘa tarin makamai da kayan aiki. Kamar yadda Zagàzola Makama ya ambata wannan miƙa wuyan da waɗannan maharan suka yi ga sojojin...
Majalisar Wakilai ta amince da ayyana dokar ta-ɓaci da Shugaba Bola Tinubu ya yi a Jihar Ribas. Majalisar ta yanke wannan shawara ne a ranar Alhamis, ta hanyar kaɗa ƙuri’a da baki, inda ’yan majalisa 243 suka halarta. Muhimman ayyuka 8 a goman ƙarshe na Ramadan Fashewar Tanka: Asibitoci sun cika da mutane a Abuja...
Yan tawayen M-23 na kasar Kongo wadanda suke samun goyon bayan gwamnatin kasar Ruwanda sun kara nosawa zuwa gaba a mamayar da sukewa gabancin kasar ta Kongo. Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa yan tawayen sun kama garin Walikale a jiya Laraba kuma a halin yanzun sun kokarin zuwa sauran garuruwa a yankin. Labarin...
Rahotannin da suke fitowa daga yankin Gaza na kasar Falasdinu da aka mamaye sun nuna cewa, a cikin sa’o’ii 24 da suka gabata Falasdinawa 71 ne suka yi shahada a yayinda wasu da dama suka ji rauni. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa a wannan karon jiragen yakin HKI da...

Mutane Fiye Da 30 Ne Suka Rasa Rayukansu A Lokacinda Motar Dawkar Gas Ta Yi Bindiga A Abuja Na Tarayyar Najeriya
Mutane fiye da 30 ne aka tabbatar damutuwarsu a jiya Laraba a Abubja babban birnin tarayyar Najeriya sanadiyyar bindigan da wata motar daukar iskar gas ta yi a kan gadar Karo da misalign karfe 7:15 a jiya Laraba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa hatsarin na jiya ya aukune a dai...
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya umarci daukacin masarautun Jihar hudu da su fara shirye-shiryen Bikin Sallah Daba domin ganin jama’a da maziyarta sun ji dadin bukukuwan Sallah. Wannan umarni na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, bayan wani taron...
Aƙalla mutum 55 ne suka rasu sakamakon ɓarkewar cutar sanƙarau a ƙananan hukumomin Jega, Gwandu, Aliero, Bunza, da Birnin Kebbi da ke Jihar Kebbi. Hukumar Lafiya ta Jihar ta tabbatar da ɓullar cutar bayan gwaje-gwajen da aka yi a Abuja. Ƙungiyoyin ƙwadago sun buƙaci Tinubu ya mayar da Fubara kan kujerarsa Shugaban Dattawan Arewa ya...
Dakarun Sashe na 2 tare da hadin gwiwar sojojin sama na rundunar hadin gwiwa ta Operation Fansan Yamma sun ceto mutane 101 da aka yi garkuwa da su a fadin Kankara a jihar Katsina da Shinkafi a jihar Zamfara a ranakun 17 da 18 ga watan Maris 2025. A cewar sanarwar mai Magana da...
Wata gobara da ta tashi da sanyin safiya ta kone wani shago a wani gini mai daki 13 da ke rukunin gidajen Ile-Lodo a cikin garin Etan a karamar hukumar Ekiti a jihar Kwara. A cikin wata sanarwa da kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, Hassan Adekunle ya fitar, ya ce bayan an...
Gwamnatin jihar Kebbi, ta tabbatar da mutuwar mutane 56 a sakamakon barkewar cutar sankarau a jihar inda 25 a Gwandu, 16 a Jega, 14 kuma suka mutu a kananan hukumomin Aliero na jihar. Da yake zantawa da manema labarai, babban sakatare a ma’aikatar lafiya ta jihar, Dakta Nuhu Koko, ya ce an samu jimillar...