2025-03-28@16:36:46 GMT
إجمالي نتائج البحث: 535

«kanawa»:

    Har ila yau, Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya aike wa hukumomin tsaro wasiƙa yana sanar da shirinsa na gudanar da bikin. Gwamnatin jihar da masarautar Kano har yanzu ba su ce komai ba kan wannan haramci ba. Wannan mataki na zuwa ne bayan da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya sanar da...
    Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta haramta gudanar da bukukuwan hawan sallah da aka saba yi na al’ada a faɗin Jihar Kano. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori ya fitar a wani taron manema labarai da ya gudana a hedikwatar rundunar da ke Bompai a wannan Juma’ar....
    Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai samu nasarar lashe zaɓe don yin wa’adi na biyu a 2027, duk da ƙoƙarin ’yan adawa na ƙalubalantarsa. Yayin da yake jawabi a wajen liyafar buɗa-baki da ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar APC (PGF) ta shirya a Abuja, Akpabio ya nuna ƙwarin gwiwa cewa...
    “Jami’an ‘yansanda da ke ofishin ‘yansanda, Mayo Belwa, sun isa wurin, inda nan take suka garzaya da wanda abin ya shafa zuwa asibitin Cottage, Mayo-Belwa, domin  kokarin ceton ransa, amma abin takaici, an tabbatar da mutuwarsa a lokacin da ya ke karvar magani.” Kakakin rundunar ‘yansandan ya ce, ya yi saurin shiga tsakanin wanda ake...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa gwamnatin kasar ta Mayarwa Shugaban kasar Amurka Donal Trump amsar wasikarsa ga kasar danagne da shirinta na makashain Nulkiya ta hanyar kasar Omman. Aragchi ya bayyana haka a jiya Alhamis a lokacinda yake hira da kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran. Ya kuma kara...
    Mai magana da yawun ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin ya bayyana cewa, kasar tana matukar adawa da yunkurin Amurka na kara yawan dozin-dozin na kamfanoninta a cikin jerin kamfanonin da aka takaita fitar da kayayyakinsu zuwa kasashen waje. Jami’in, wanda ya bayyana haka a ranar Larabar nan, ya ce, matakin na Amurka ba komai ba...
    Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya sanar da soke bukukuwan Sallah na bana, saboda bukatar tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar. A wata sanarwa da aka fitar, Sarkin ya bayyana takaicinsa kan matakin amma ya jaddada cewa, tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi shi ne babban abin da ya sa a...
    A yau Alhamis sojojin na kasar Sudan sun sanar da abinda su ka kira; Yin shara a cikin birnin Khartum, domin gano inda gyauron mayakan dakarun rundunar sa-kai suka buya. Haka nan kuma sojojin na Sudan sun sanar da sakin farsunoni masu yawa da rundunar kai daukin gaggawa din suka tsare su, a lokacin da...
     Jiniyar gargadi ta kada a cikin sassa masu yawa na Falasdinu dake karkashin mamaya  bayan harbo makami mai linzami da mutanen Yemen su ka yi. Kafafen watsa labarun HKI sun ce, jiniyar gargadin ta kada a cikin garuruwa 255 a HKI daga cikin har da birnin Kudus. Jaridar “Yediot Ahronot” ta buga labarin dake cewa,...
    Wakilin dindindin na kasar Sin a ofishin MDD dake Geneva da sauran kungiyoyin kasa da kasa dake Switzerland Chen Xu, ya gabatar da jawabi a jiya Laraba, yayin taro na 58 na kwamiti mai kula da harkokin kare hakkin bil Adama na MDD, don bayyana ra’ayin kasar Sin kan halin da Palasdinu da Isra’ila ke...
    A Isra’ila dubban masu zanga-zanga ne suka taru a Tel Aviv domin nuna adawa da mulkin firaministan kasar Benjamin Netanyahu. Masu zanga zangar sun kuma bukaci a tsagaita bude wuta da kuma sako fursunonin da ake tsare da su a Gaza. Sun rike alluna masu dauke da hotunan wadanda  ake tsare da su a Gaza...
    Mai martaba Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya sanar da soke bikin Sallar Eid-el-Fitr Durbar, saboda matsalar tsaro da ya sa aka dakatar da shirye-shiryen.   Sarkin ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a fadarsa ta karamar hukumar Nasarawa da ke Kano.   Ya kuma jaddada...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi kira hadin kan kasashen duniya domin nuna goyon baya ga Falasdinu gabanin ranar Kudus ta Duniya. Kungiyar ta yi kira da a samar da hadin kai a kasashen duniya a ranar Juma’a da Asabar da Lahadi masu zuwa domin nuna goyon baya ga Gaza da Kudus, yayin da...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Sarkin Kano 15, Aminu Ado Bayero, ya soke shirinsa na gudanar da bikin hawan salla bayan shawarwari da dattawa da malaman addini suka ba shi. Ya bayyana cewa matakin ya biyo bayan buƙatar tabbatar da zaman lafiya a jihar, biyo bayan shiga ruɗani da jama’a suka yi. Hadimin Gwamnan Kano Tanka Galadanci ya rasu Majalisa...
    Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Litinin, 31 ga watan Maris, da Talata, 1 ga watan Afrilu, a matsayin ranakun hutun ƙaramar salla. Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da sakataren ma’aikatar, Magdalene Ajani, ya fitar a ranar Laraba. Ahmad Lawan ya raba tallafin N27m da buhun shinkafa 300...
    Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya bayar da gudummawar Naira miliyan 27 da buhunan shinkafa 300 ga mutanen da gobara ta shafa a ƙananan hukumomi uku da ke mazaɓarsa a Jihar Yobe. Ƙananan hukumomin da abin ya shafa sun haɗa da Machina, Nguru, da Yusufari. An kama mutum 3 kan zargin sata da...
    Rundunar sojan Sudan ta sanar da shimfida ikonta akan filin saukar jiragen sama na Khartum wanda shi ne tunga ta karshe da ta saura a hannun rundunar kai daukin gaggawa. Kwamandan rundunar sojan Sudan da take fada a birnin na Khartum Lafatnar kasar Abdurrahman al-Bilawi ne ya sanar da cewa, an  shimfida iko a  cikn...
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na Duniyarmu a yau shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhummanci a makon da ya gabata, dangane da siyasa tattalin arziki zamantake tsaro da sauran, sannan mu yi masu karin bayani daga karshe mu ji ra’ayin masana dangane da su....
    Kwamitin tallafawa marayu da masu karamin karfi na kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah wa Ikamatis Sunnah dake karamar hukumar Babura ta jihar Jigawa ya tallafawa gidajen marayu da masu karamin karfi da kayan abinci na kusan naira miliyan 9. Shugaban kungiyar Sheikh Hassan Sabo Musa ya bayyana hakan yayin rabon kayan da aka gudanar a...
    Ya ce, “Da misalin karfe 7:28 na safe ne wasu da ke sharar masallacin suka ga mutumin a kwance a cikin masallacin, sai suka yi kokarin tayar da shi domin su yi shara amma shiru.   Nan da nan, sai mutanen suka sanar da Musulman yankin lamarin, inda suka garzaya da shi zuwa asibiti, likitan...
    Bayan gazawar tattaunawar da hukumar ta IAEA ta yi da Tehran, babban daraktan hukumar Rafael Grossi ya jaddada muhimmancin komawa kan teburin shawarwari nan gaba don tabbatar da cewa Iran ba ta mallaki makamin nukiliya ba. Hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa ta ce tattaunawar da ta yi da wani babban jami’in...
    Wani rahoto da aka fitar yau Talata, yayin zaman taron shekara-shekara na shekarar 2025, na dandalin tattaunawa na Asiya na Boao, ya nuna yadda kasar Sin ke ci gaba da kasancewa cibiyar rarraba hajojin da masana’antu ke sarrafawa. Rahoton mai taken “Nazarin tattalin arzikin Asiya, da hadadden rahoton ci gaba na shekarar”, ya nuna yadda...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Guo Jiakun ya ce a jiya Litinin, ma’aikatar harkokin wajen Sin ta gudanar da taron karawa juna sani na kasa da kasa, mai taken “Karfafa rawar da MDD ke takawa, tare da habaka ra’ayin cudanyar bangarori daban daban” a nan birnin Beijing. Guo ya bayyana hakan ne yayin taron manema...
    Yansanda a kasar Turkiyya suna ci gaba da fafatawa day an adawa masu goyon bayan magajin garin birnin Istambul Ekram Imam oglu. Tashar talabijin ta Al-mayadeen ta kasar Lebanon ta bayyana cewa magajin garin na birnin Istambul yana daga cikin fitattun masu adawa da gwamnatin Urdugan, sannan a halin yanzu jami’an sharia a kasar sun...
    Gwamnatin tarayyar Najeriya ta kafa runduna ta musamman a kasar don magance matsalolin tsaro daban-daban wadanda kasar take fama das u. Jaridar Premium times ta Najeriya ta nakalto ministan tsaron kasar Muhammad Badaru yana fadar haka a lokacinda yake kaddar da wani bangaren na rundunar a barikin Kabala da ke barikin Jaje a kusa da...
    Bayan shafe sa’o’i 12 na tattaunawar sirri da aka yi a Saudiyya, jami’an Amurka da na Rasha sun kammala tattaunawa kan rikicin Ukraine a ranar Litinin. Hukumomin Rasha sun ruwaito cewa fadar White House da Kremlin za su fitar da sanarwar hadin gwiwa yau Talata kan tattaunawar da suka yi, wanda Moscow ta bayyana tun...
    Rahotanni daga Falasdinu na cewa akalla Falasdinawa 61 ne sukayi shahada a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, in ji ma’aikatar lafiya ta Gaza. A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, ma’aikatar ta ce an gano gawarwaki hudu a karkashin baraguzan gini, sannan an kwantar da mutane 134 da suka jikkata a asibiti...
    Cristiano Ronaldo ya zura ƙwallo a wasan da Portugal ta doke abokiyar karawarta ƙasar Denmark a daren ranar Lahadi, ƙwallon ita ce ta 929 da tsohon ɗan wasan na Manchester United ya jefa a tarihinsa na ƙwallon ƙafa, duk da cewar ya ɓarar da bugun daga kai sai mai tsaron gida a wasan da Portugal...
    Dubban mutane ne a birnin Amman babban birnin kasar Jordan suka gudanar da zanga-zanga bayan sallar Juma’a domin yin Allah wadai da sake dawo da laifukan da Isra’ila ke aikatawa a Gaza. A rahoton factjo, dubban mutane sun bayyana goyon bayansu ga al’ummar Gaza a wani gagarumin maci na wannan Juma’a. Mahalarta tattakin sun yi...
    Shugqbqn kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen sayyed Abdulmalik Badaruddin Huthi ya bayyana cewa tura wani kataparen jirgin ruwan yaki zuwa gabas ta tsakiya wanda shugaban kasar Amurka yayi wata gazawace. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalti Alhuthi yana fadar haka yau Lahadi a wani jawabin da ya gabatar ,inda yake bayyana irin...
    A gobe Litinin 24 ga watan Maris ne tawagogin masu tattaunawa na kasashen Amurka da Rasha zasu hadu a birnin Rayida na kasar Saudiya don ci gaba da tattaunawan da suka fara a yan makonnin da suka gabata dangane da yakin da ke faruwa a Ukraine, shekaru fiye da 3 da suka gabata, da kuma...
    Al’ummar Jihar Kano, sun shiga shida ruɗani yayin da rikicin Masarautar jihar, ya ɗauki wani sabon salo game da shirin gudanar da bikin hawan salla. Tsagin sarakunan jihar na 15 da na 16, wato Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero, sun shirya gudanar da hawan salla duk da shari’ar da ke gudana kan rikicin...
    Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Ilorin, karkashin jagorancin Mai shari’a Abimbola Awogboro ta yanke wa Musa Buba hukuncin daurin sa’o’i 300 da hidimar al’umma, bisa samunsa da laifin gudanar da harkokin kasuwanci na canji ba tare da wani cikakken lasisi ba. Hakazalika, alkalin ya kuma yanke hukuncin daure wani Akinwale Olamilekan daga...
    Jagoran ‘yan adawar Isra’ila Yair Lapid ya yi kira da a gudanar da zanga-zangar gama-gari idan Firaministan kasar Benjamin Netanyahu ya ki bin hukuncin da kotun kolin kasar ta yanke na dakatar da matakin da gwamnatinsa  na korar shugaban hukumar tsaron cikin gida ta Shin Bet.  Yair Lapid ya shaidawa dubban masu zanga-zanga a Tel...
    Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada bukatar bin dokar da ta hana kiwon dare da makiyaya ke yi a fadin jihar domin rage hadurra a tituna, wanda ke haddasa asarar rai ko shiga mawuyacin hali a sanadiyar raƙuman da ke bi ta manyan tituna. Gwamna Umar Namadi ya bayyana hakan yayin da ya karbi...
    A kwanakin baya, bankin Deutsche, banki mafi girma na kasar Jamus ya yi bayani game da yanayin kashe kudi ta kasar Sin cewa, karin Sinawa suna kara son kashe kudi. Bisa sabon rahoton da bankin ya gabatar, an ce, idan aka kwatanta da na shekarar bara, yawan masu kashe kudi na kasar Sin yana karuwa,...
    An ruwaito cewa, shirin aikin noman ranin da aka kaddamar a yankin na Lallashi, zai karade hekta 10, wanda kuma sama da kananan manoma 80, za su amfana da shirin kai tsaye. Bugu da kari, shirin zai taimaka wajen kara samar da girbin amfanin gona mai yawan gaske tare kuma da kara bunkasa tattalin arzikin...
    A kokarin Gwamnatin Jihar Jigawa na karfafa ayyukan noman rani tare da samar da wadataccen abinci da inganta rayuwa, ta kaddamar da shirin noman rani na Lallashi da ake amfani da rijiyoyin burtsatse a Karamar Hukumar Maigatari ta jihar. Rahoton na nuna cewa, an yi aikin ne domin canza salon noman rani da sauran ayyukan...
    KAmfanin dillancin labarun “al-Somariyya Newas” ya ambato jagoran ‘yan hamayyar siyasa na kasar Turkiya Uzgor Auzal yana fadin cewa: A daren jiya juma’a adadin wadanda su ka fito Zanga-zangar nuna kin jinin shugaba Rajab Tayyib Urdugan sakamakon sauke da kama ‘yan hamayyar siyasa da ya yi kaga kan mukamansu da su ka hada da magajin...
    “Bayan nazari da tattaunawa da gwamnati, Gwamna Bala Abdulkadir Muhammad ya amince da gudanar da wannan gagarumin biki,” in ji shi. Sanarwar ta ƙara da cewa za a fitar da cikakken jadawalin shirye-shiryen hawan nan gaba kaɗan, tare da fatan Allah Ya sanya ayi bikin lafiya. A tarihi, Hawan Daushe yana da muhimmanci sosai a...
    Sabon Kocin tawagar Super Eagles ta Nijeriya Eric Chelle, ya fara jagorantar tawagar da ƙafar dama, bayan samun nasara a wasan farko da ya jagorance ta. Chelle wanda ya zo Super Eagles watanni biyu da su ka gabata, ya jagoranci Super Eagles a wasan da su ka doke ƙasar Rwanda da ci biyu da nema...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wata kungiya mai suna Grassroots Mobilizers for Better Nigeria Initiative (GMBNI), ta yi Allah wadai da kisan gilla da aka yi wa wani  Almajiri a ƙaramar hukumar Gwaram, Jihar Jigawa. Ƙungiyar ta bayyana matuƙar bakin ciki da ɓacin rai game da wannan cin zarafin da aka yi wa yaron, wanda ya kai ga mutuwarsa cikin...
    Shugaban kasar Rasha Vladmir Putin ya mika sakon gaisuwar idin Nowruz na sabuwar shekarar hijira Shamsiyya ga jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan Nowruz, na  shigowar bazara da kuma sabuwar shekara ta Farisa. Putin ya kuma aike da sakon fatan alheri ga shugaban kasar...
    Dubban mutane ne a birnin Amman babban birnin kasar Jordan suka gudanar da zanga-zanga bayan sallar Juma’a domin yin Allah wadai da sake dawo da laifukan da Isra’ila ke aikatawa a Gaza. A rahoton factjo, dubban mutane sun bayyana goyon bayansu ga al’ummar Gaza a wani gagarumin maci na wannan Juma’a. Mahalarta tattakin sun yi...
    An gudanar da Sallar Juma’a a mako na uku na watan Ramadan a Masallacin Al-Aqsa, duk kuwa da tsauraran takunkumin da gwamnatin yahudawan sahyoniya ta dauka, tare da halartar Palasdinawa 80,000. Kamfanin dillancin labaran Al-Naba y bayar da rahoton  cewa, dubun dubatar Falasdinawa ne suka gudanar da sallar Juma’a ta uku na watan Ramadan a...
    Jakadan dindindin na kasar Sin dake ofishin MDD a birnin Geneva da sauran hukumomin kasa da kasa a kasar Switzerland, Chen Xu, ya gabatar da jawabi a madadin kungiyar abokantaka ta inganta hakkin bil’adama, da tattaunawa da hadin gwiwa da sauransu, yayin taron MDD karo na 58 da ya gudana a jiya Alhamis.  A cikin...
    Ƙungiyar Dattawan Arewa (NEF), ta buƙaci Shugaba Bola Tinubu da gaggauta janye dakatarwar da ya yi wa Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, Mataimakiyarsa, da ’Yan Majalisar Dokokin jihar. Da yake magana a madadin ƙungiyar, Farfesa Abubakar Jika Jiddere, ya ce babu wani dalili da ya dace da zai sa shugaban ƙasa ya ayyana dokar ta-ɓaci...
    Daruruwan Falastinawa fararen hula ne suka yi shahada tun bayan da Isra’ila ta dawo da hare-haren kisan kare dangi a kan al’ummar yankin zirin gaza, matakin day a yi hannun riga baki daya da yarejejeniyar dakatar da bude wuta da aka rattaba hannu a kanta karkashin jagorancin Amurka, Masar da kuma Qatar. Dakarun mamaya na...