2025-04-04@03:51:04 GMT
إجمالي نتائج البحث: 317

«makarantun firamare»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    A dai-dai lokacinda jijiyoyin wuya suke kara tashi tsakanin JMI ta kuma HKI, jami’an tsaron HKI sun kama daya daga cikin yan rahotomta sun tsare. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban hukumar gidajen radiyo da Talabijin ta kasar (IRIB), Peyman Jebelli yana fadar haka ya kuma  kara da cewa dan rahoton hukumar baya Gaza, yana cikin kasashen Falasdinu da aka mamaye ne. Sannan hukumar ta fara kokarin ganin an sake shi. Labarin ya kara da cewa tun ranar da aka fara yakin tufanul Aksa a ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023 jami’an tsaron HKI sun kashe yan jaridu 205, sannan ta kama wasu 75, sannan har yanzun wasu 42 kuma tana tsare da su....
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa duk wani hari kan daya daga cikin cibiyoyin Nukliyar kasar Iran daga HKI ko Amerika, wannan wata musiba ce da yankin, kuma wadanda suka kai harin zasu gamu da maida martani ba tare da jinkiri ba. Tashar talabijin ta Presstva nan Tehran ta nakalto Abbas Aragchi yana fadar haka a wata hirar da ta hada shi da tashar talabijin ta Sky News a nan Tehran. Ya kuma kara da cewa, ban tsamman zasu yi haka ba. Amma idan sun, to kuwa ba zasu ji ta da dadi ba. Yace: JMI ta rattaba hannu a kan yarjeniyar Nukliya da manya-manyan kasashe 6 a duniya kan shirin ta na makacin Nukliya wanda...
    Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar III ya buƙaci al’ummar Musulmi da su fara duba sabon watan Sha’aban na kalandar musulunci daga daren Laraba. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Wazirin Sakkwato kuma shugaban kwamitin bayar da shawara kan harkokin addini a fadar, Farfesa Sambo Wali Junaidu, ya raba wa manema labarai a ranar Litinin. Gaskiyar batun kama Bello Turji —Sojoji Kotu ta hana ’yan sanda sake taɓa Muhuyi Rimingado  Kwamitin ganin wata na Nijeriya a Fadar Sarkin Musulmi ya ce ranar Laraba ce za ta zama 29 ga watan Rajab, 1446, daidai da 29 ga watan Janairun 2025. Sanarwa da Fadar Sarkin Musulmin ta fitar, ta ce idan aka ga watan a kai rahoto zuwa ga hakimi ko kuma...
    Kalaman shugaban Amurka na cewa zai tsarkake Zirin Gaza na Falasdinu ta ruda kawayen kasarsa na Larabawa tare da hargitsa su Wani mai sharhi na jaridar Washington Post David Ignatius ya ce kalaman shugaban Amurka Donald Trump na tsarkake Gaza da mika Falasdinawa zuwa Masar da Jordan ya sanya kasashen Larabawa da suke kawancen da Amurka cikin halin fargaba da dardar. Shafin watsa labaran Al-Quds Al-Arabi, ta yi nuni da cewa Trump ya gabatar da tunaninsa domin hanyar gabatar da shawarwari da tunani tana da dama tare da sabani da siyasa a aikace. Ta ce Trump na fuskantar daukan matakin yin kasadar da zai lalata kyawawan ra’ayinsa da bayyana munanan tunaninsa. Jaridar ta kara da cewa: shugaban na Amurka zai...
    Hamas ta bayyana komawar Falasɗinawa a matsayin nasara, tana mai cewa hakan ya karya yunƙurin da aka yi na tilasta wa mutanen barin gidajensu.
    Abinda Ya Faru A Lebanon Nasara Ce Akan Isra’ila Babban magatakardar kungiyar Hizbullah  Sheikh Na’im Kassim ya gabatar da jawabi na farko bayan cikar kwanaki 60 daga tsagaita wutar yaki da HKI. A jawabin nasa sheikh Na’im Kassim ya bayyana cewa a lokuta da dama sun yi tunanin mayar da martani akan keta tsagaita wutar yaki, sai dai an bukace su da su dakata, domin bayar damar a dauki wasu matakai na daban. Sheikh Na’im Kassim ya zargi Amurka da rashin daukar mataki akan HKI ta dakatar da keta yarjejeniyar da take yi, duk da cewa tana cikin masu sa ido akan tsagaita wutar. Haka nan kuma ya yi ishara da komawar mutanen kudancin Lebanon zuwa garuruwa da gidajenu duk...
    Dubban daruruwan Falasdinawa da suka rasa matsugunansu sun fara komawa yankin arewacin zirin Gaza da yaki ya daidaita bayan da aka cimma matsaya tsakanin Hamas da Isra’ila. Tuni kungiyar Hamas ta yaba da komawar Falasdinawan zuwa arewacin Gaza wanda ta danganta a abun tarihi. An cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas bayan shafe watanni 15 ana gwabza kazamin yaki a Gaza. An fara aiwatar da kashin farko na yarjejeniyar a ranar 19 ga watan Janairu, kuma ana sa ran za’a saki Falasdinawa sama da 1,890 da ‘yan Isra’ila 33, wadanda ke cikin 240 da kungiyoyin Hamas ta yi garkuwa dasu a harin ranar 7 ga watan Oktoban shekarar 2023. Tun lokacin yakin ya lakume rayukan Falasdinawa akalla 47,306,...
    Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun kera wani jirgi maras matuki ciki mafi girman da suka Sanya masa suna “Gaza” A jiya Lahadi, a gefen atisayen soji mai taken “Manzon Allah Mai Girma na 19” da aka gudanar da gwajin makamansu, sun samu nasarar gwajin sabon jirgin sama maras matuki ciki mai suna “Gaza” wanda ake daukansa a matsayi mafi girman jirgin saman maras matuki ciki da zai iya yin luguden wuta mafi girma da tsanani, jirgin yana cin dogon zango kuma shi ne mafi girma da Iran ta kera wajen kai farmakin da zai jefa bama-bamai 8 akan wurare 8 a kasa. Jirgin Gaza maras matuki (wanda ake kira Shahed 149) shi ne jirgi mara matuki...
    Kwamandan runduna ta 1 ta sojojin Najeriya Gusau, Birgediya Janar Opurum Timothy, ya baiwa al’ummar jihar Zamfara aniyar rundunar sojojin Najeriya wajen ci gaba da aiki tukuru domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.   Ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a karshen taron rundunar sojojin Najeriya ta yammacin Afirka WASA 2024 da aka gudanar a Gusau.   Kungiyar WASA wani taron ne na shekara-shekara da rundunar sojojin Najeriya ke shiryawa domin murnar dimbin al’adun gargajiya na wannan kasa mai girma.   Taron na shekara-shekara yana tattaro Jami’ai, Sojoji, da iyalansu a cikin annashuwa don bikin da kuma nuna ƙarshen ayyukan shekara.   Janar Opurum wanda ya jaddada kudirin rundunar na kawar da...
    Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam da Gaskiya a Harkokin Jama’a (SERAP), ta maka Shugaba Bola Tinubu da Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC), a kotu kan karan kudin kiran waya da data zuwa kashi 50. NCC ta amince da karin, wanda ya sa kudin kiran waya ya tashi daga Naira takwas zuwa 16.5 a minti daya, yayin da kudin sayen data 1G ya tashi daga Naira 287.8 zuwa Naira 431.25. Shin wannan ce kaka mafi muni ga Man-United a Gasar Firimiya? Ƙungiyoyin da za su fafata da juna a Copa del Rey  Shi kuwa kudin aika sakon kar ta kwana ya tashi zuwa Naira shida daga na hudu da ake biya a baya. SERAP, ta ce wannan karin an yi sa...
    Bugu da kari, a ran 25 ga watan kuma, CMG ya gabatar da wannan bidiyo a kasar Jamus, inda gidajen sinima na manyan biranen kasar ciki har da Berlin da Frankfurt, da Dresden da kuma Dortmund da sauransu, suka watsa wannan bidiyo. Kazalika, a ran 24 ga watan, a birnin Asuncion, hedkwatar kasar Paraguay, an fara watsa wannan bidiyo a manyan allunan dake titunansa har tsawon kwanaki 7 masu zuwa a jere. Wannan shi ne karon farko da aka watsa irin wannan bidiyo a wannan kasa dake kudancin nahiyar Amurka. An ba da labari cewa, UNESCO ta shigo da bikin bazara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, wato Bikin Bazara cikin jeren sunayen dake wakiltar kayayyakin al’adun gargajiya na tarihi...
    Wakilin babban rukunin gidajen rediyo da talibijin na kasar Sin (CMG) kwanan nan ya tattauna tare da shugaban kasar Sri Lanka Anura Kumara Dissanayake, wanda ya kawo ziyara kasar Sin a karon farko tun bayan hawansa mulki. Da yake magana game da nasarar da kasar Sin ta samu na zamanantar da kanta, Dissanayake ya bayyana cewa, yawan al’ummar kasar Sin ya kai kusan kashi daya bisa biyar na al’ummar duniya, amma kasar Sin ba ta da kashi daya bisa biyar na albarkatun duniya. Ya ce Kasar Sin ta dage kan bin hanyar ci gaba da ta dace da ita, kuma kasar ta samu ci gaba, jama’arta kuma suna rayuwa da aiki cikin kwanciyar hankali. Ya ce, ina ganin yin nazari...
    Gwamnatin Jihar Jigawa ta yaba da shirin tallafawa al’umma da Shugaban karamar hukumar Sule Tankarkar ya bullo da shi a yankin. Gwamnan Jihar, Mallam Umar Namadi ya bayyana haka a lokacin da ya halarci taron kaddamar da rabon tallafin da aka gudanar a karamar hukumar. Malam Umar Namadi, ya bayyana matukar jin dadinsa bisa wannan gagarumin tallafi, da ya haɗa da bayar da kayayyaki da jari ga rukunin al’umma daban-daban. Yana mai nuni da cewar, wannan mashahurin shiri ya nuna kyakkyawan hangen nesa na Shugaban karamar hukumar, Alhaji Tasi’u Adamu, wajen tallafa wa mutanen karkara da ke fama da kalubale daban daban. Namadi, ya kaddamar da rabon tallafi ga mutane fiye da 350 a karamar hukumar Sule Tankarkar....
    Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya bukaci masu tsara manufofi a fannin ilimi a Najeriya da su dauki kwararan matakai don magance gibin da ke tattare da zamantakewa da al’adu da ababen more rayuwa da manufofin da ke haifar da yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a kasar. Shugabar ofishin UNICEF na Kano, Rahama Rihood Farah, ne ya yi wannan kiran a wani taron manema labarai na bikin ranar ilimi ta duniya ta shekarar 2025. Ya yi nuni da cewa, Jihohin Kano, da Jigawa da Katsina suna da adadin yara miliyandaya da dubu dari takwas da sittin da uku, da dari biyu da bakwai (1,863,207) da ba sa zuwa makaranta a matakin firamare,  da...
    Dan takarar zaben maye gurbin Dan Majalisar Tarayya da ke wakiltar Mazabar Chikum da Kajuru a jam’iyar APC Arc Sani A Abbas Sardaunan Chikum ya nada kwamitin mutane 7 domin raba tallafin karatu ga daliban yankin sa su 100 da suke karatun kimiyya da fasaha a manyan marantun Gwamnati. Wannan wata manuniya ce game da kudurin Arc Sani Abbas na karfafa matasa ta bangaren ilimin don gobe su tayi kyau. Babban aikin wannan kwamitin shi ne tantance daliban da suka cancanci amfana da wannan tallafin musamman wadanda babu ke barazanar hana su karatu. Wanda yin haka zai taimaka wajen tallafa musu su nemi ilimi don cike gibin da ake samu ta wannan bangaren. Wannan tallafin kadan ne daga cikin irin...
    Babban kwamandan sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Atisayen soji na “Manzon Allah Mai Girma na 19” ya cimma gagarumar nasara Babban kwamandan sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Admiral Ali Reza Tangsiri ya sanar da cewa: Atisayen soji mai take “Manzon Allah Mai Girma na 19” ya cimma gagarumar nasara da burin da ake son kai wa bayan samun nasarar gwada sabbin na’urori da gudanar da ayyuka daban-daban, tare da samun nasarar gwajin kai hari kan wuraren abokan gaba. A wata hira da ya yi da manema labarai a yau Lahadi, Admiral Tangsiri ya bayyana cewa: A rana ta biyu ta atisayen “Manzon Allah Mai Girma na 19”...
    Bayan tsawon shekaru 40 a tsare, shugaban fursunonin Falasdinawa, Mohammed Al-Tous, ya samu ‘yancinsa Kungiyar kula fursunonin Falasdinawa da suke tsare a gidan yarin haramtacciyar kasar Isra’ila ta bayyana cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila ta saki Muhammad al-Tous, wanda shi ne fursuna mafi tsufa a hannunta, tare da tasa keyar shi tare da wasu fursunoni 69 zuwa kasar Masar, a wani bangare na yarjejeniyar musayar fursunoni tsakaninta da kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas. A ranar Asabar din da ta gabata ne gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta saki fursunonin Falasdinawa 200 a madadin wasu mata sojoji hudu da kungiyar Hamas ke tsare da su a Zirin Gaza. Al-Tous (mai shekaru 69) yana tsare tun 1985 kuma yana cikin kungiyar Fatah an yanke...