2025-04-03@09:44:21 GMT
إجمالي نتائج البحث: 315

«makarantun firamare»:

    Babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa Rafael Grossi ya sanar da shirin kai ziyara birnin Tehran nan da makwanni masu zuwa a yayin da ake ci gaba da tattaunawa don tsaida takamaimen lokacin. Ziyarar ta zo ne a wani bangare na ci gaba da huldar diflomasiyya tsakanin Iran da hukumar IAEA, da nufin tinkarar batutuwan da suka shafi Nukiliya, da samar da hadin gwiwar fasaha cikin tsarin alkawurran da Iran ta dauka a karkashin yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya (NPT). Ziyarar ta kuma jaddada irin hadin gwiwar da Tehran ke ci gaba da yi da hukumar ta IAEA, duk da matsin lamba daga waje da kuma zargin siyasa daga kasashen yammacin Turai. Da yake amsa...
    Ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi ya nanata shirin Tehran na shiga tattaunawar da Amurka kan shirinta na nukiliya na zaman lafiya, yana mai gargadin cewa barazanar soji daga Amurka na dagula halin da ake ciki a yanzu. “Jamhuriyar Musulunci, kamar yadda ta kasance a baya, a shirye take don yin shawarwari na hakika,” in ji Araghchi a wata wayar tarho da takwaransa na Holland, Caspar Veldkamp, yau Laraba. Ya jaddada cewa wannan “yana bukatar yanayi mai kyau da kuma nisantar hanyoyin da suka shafi barazana.” Ministan ya yi Allah wadai da barazanar da jami’an Amurka suka yi wa Iran da cewa “ba za a amince da su ba”, ya kara da cewa sun saba wa kundin tsarin mulkin MDD...
    Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau I. Jibrin, ya ziyarci iyalan mafarauta 16 da aka kashe a yankin Uromi da ke Jihar Edo, tare da ba su tallafin Naira miliyan 16. Matan matatan sun fito ne daga ƙananan hukumomin Bunkure, Kibiya, Rano, da Garko a Jihar Kano. Mutum 2 sun rasu, 13 sun ɓace a hatsarin jirgin ruwa a Bayelsa HOTUNA: Yadda aka yi jana’izar Galadiman Kano Barau ya gana da iyalan mamatan a Masallacin At-Taqwa da ke Bunkure a ranar Laraba tare da Ministan Harkokin Gidaje, Yusuf Abdullahi Ata da sauran manyan jami’ai. Barau, ya yi ta’aziyya da kuma tabbatar da cewa waɗanda suka aikata laifin za su fuskanci hukunci. “Na zo nan ne domin na taya ku jaje kan...
    Ƙungiyar matasan Arewa ta yi Allah-wadai da jita-jitar da ake yaɗawa cewa an kashe wani ɗan ƙabilar Ibo a Jihar Kano saboda kisan wasu Hausawa mafarauta da ɓatagari suka yi kwanan a Jihar Edo. A wani taron manema labarai da gamayyar ƙungiyoyin matasa na ƙabilu daban-daban, ta ce abin takaici ne kisan da aka yi wa Hausawa kuma tana miƙa ta’aziyya ga iyalan waɗanda lamarin ya rutsa da su. Isra’ila ta kashe yara 322 cikin kwanaki 10 a Gaza — UNICEF Babu dokar da na karya saboda yin taro a mazaɓata — Natasha Kazalika, ƙungiyoyin sun yaba wa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, bisa koƙarinsa na tabbatar da zaman lafiya ya ci gaba da ɗorewa a jihar ta hanyar ɗaukar...
    Babban mai bawa jagoran juyin juya halin musulunci Dr Ali Larijani, ya ce duk tare da cewa jagoran juyi juya halin musulunci ya bada fatawar hana kera makaman nukliya, amma idan an kaiwa kasar Iran hari kan shirinta na makamashin nukliya, wannan yana iya tunzura kasar ta kai ga mallakar makaman Nukliya. Jaridar Tehran time ta nakalto Dr Larijani ya kara da cewa idan Amurka ko HKI ko duka biyu suka kaiwa cibiyoyin nukliyar kasar, to kuwa zata kera makaman nukliya. A ranar Lahadin da ta gabata ce, Dr Larijani ya bayyana haka. Sai dai a daren Litinin ne Dr Larijani ta kara jaddada wannan matakin. Sai dai kafin haka shugaban ma’aikatar leken asiri na Amurka ta tabbatarwa tashar talabijin...
    Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara kuma Sanata mai wakiltar mazabar Zamfara ta Yamma, Dakta Abdul’aziz Yari, ya yi kira ga ‘yan siyasa da masu hannu da shuni da su kara kaimi wajen gudanar da ayyukansu na alheri fiye da watan Ramadan.   Da yake zantawa da manema labarai a mahaifarsa Talatan Mafara, a wani bangare na sakonsa na Sallah, Yari ya jaddada muhimmancin ci gaba da al’adun bayar da Zakka, Sadaka, da sauran nau’o’in tallafi ga marasa galihu a duk shekara.   Ya yabawa gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa bullo da shirye-shiryen jin dadin jama’a da nufin inganta rayuwar ‘yan Najeriya.   Dokta Yari ya yi kira ga ‘yan kasar da su ba da cikakken goyon baya ga kokarin shugaban...
    Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Arakci ya bayyana cewa, duk wata barazana da za a yi wa Iran za ta sa makiya su yi babbar nadama. A wata hira a tashar talabijin din almasirah ta kasar Yemen ta yi da shi, ministan harkokin wajen na Iran  ya ce, farfagandar da ake yi ta cewa, kai wa kasar Yemen hari  share fage ne na yaki da Iran ba sabon abu ba ne, an sha yin irin wannan barazanar a baya. Abbas Arakci ya kara da cewa; Iran ba za ta taba kyale duk wani mahaluki da zai rika yin Magana da ita da harshe na barazana ba, sannan ya kara da cewa makiya za su yi nadamar wannan barazanar. Da yake...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya yi kakkausan gargaɗi kan barazanar Amurka da ƙawayenta na kai wa ƙasarsa hari. Khamenei ya sha alwashin maida mummunar martani idan har Amurka da ƙaddamar da hare-hare a ƙasar ta Iran. Gargaɗin nasa martani ne kan barazanar da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi wa ƙasar cewa za su kai mata hari. Muna jiran ganin hukuncin da za a ɗauka kan kashe ’yan Arewa a Edo — Sarkin Musulmi Kisan Mafarauta: Matakan da gwamnatin Edo da ta Kano suke ɗauka “Suna yi min barazana, kuma idan suka sake suka kawo min hari tabbas zan rama,” in ji shi. Yayin wata tattaunawa a ranar Asabar ne Trump ya yi alƙawarin kai wa Iran...
    Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta gayyaci mai kula da harkokin kasar Switzerland da ke Tehran domin nuna fishi kan irin munanan ayyukan Isra’ila a yankin da kuma barazanar da shugaban Amurka Donald Trump ke yi kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Babban daraktan ma’aikatar harkokin wajen Iran Issa Kameli ne ya gayyaci jami’in diflomasiyyar na Switzerland, wanda kasarsa ke wakiltar muradun Washington a Tehran, yau Litinin. Kameli ya mika gargadin na Iran a hukumance ga wakilin kasar Switzerland dangane da duk wani aiki na barna tare da bayyana aniyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran na mayar da kakkausan martani cikin tsauri kan duk wata barazana. Jami’in diflomasiyyar na Iran yayi tir da kalaman tunzura tashe-tashen hankula wandanda kuma suka sabawa dokokin...
    Yan wasan kwallon kafa na kasar Iran sun zama zakara karo na 4 a kwallon kafa na yashin bakin teku a karo na 4 a cikin kasashen Asiya. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ba bayyana a gasa ta karshe wanda kungiyar kwallon kafa ta yashin bakin take wanda aka gudanar tsakanin JMI da kuma Omman an tashi da ci 8-1. Wannan nasarar dai ta tabbatar wa kasar Iran fifiko a wannan wasar har saw hudu a jere. Kuma ba’a taba samun nasara a kan ta gaba daya a dukkan wasannin da ta yi a duk tsawon gasar ba. Mai horar da yan wasan Iran a wannan gasar Ali Nadiri ya bayyanawa IP kan cewa nasarar da JMI ta...
    Sabon tsarin sayar da man fetur a Najeriya ya haifar da ƙarin farashi, inda ake sayar da kowace lita a kan Naira 930 a Legas da kuma Naira 960 a Arewa. A ranar 28 ga watan Maris, 2025, sabon tsarin ya fara aiki bayan da aka dakatar da sayar wa matatar Dangote mai a farashin Naira. Gwarzon gasar Alƙur’ani ya kuɓuta daga hannun ’yan bindiga a Katsina Talakawa su girmama shugabanni yayin bayyana matsalolinsu — Sarkin Musulmi Wannan ya sa gidajen mai suka ƙara farashi daga Naira 860 zuwa Naira 930 a Legas, da Naira 940 a yankin Kudu maso Yamma da Kwara, sannan Naira 960 a jihohin Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas. Rahotanni sun nuna cewa farashin...
    Sheikh Na’im Qasim babban sakatarin kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ya bayyana cewa JMI ce ginshikin goyon bayan al-ummar Falasdinu, kuma itace gaba-gaban a duk wani yunkuri na yentar da falasdinawa da Falasdinu daga hannun HKI da masu goya mata baya. A wani jawabin da ya gabatar a jiya Asabar, shugaban kungiyar ta Hizbullah, ya bayyana cewa ware ranar jumma’a ta karshe na watan Ramadan wata hikima ce ta jagoran juyin juya halin musulunci Imam Ruhullah Alkhomaini(q) wanda ya dace da hakan kan musulmi a kan wannan al-amari. Kuma tare da yardarm All…ana ci gaba da samun nasara a kan wannan manufar. Sheikh Kasim ya kara da cewa duk tare da gagarumin taimakon da HKI take samu daga kasashen yamma...
    An fara wallafawa ranar 13 ga Mayu, 2022 A halin yanzu al’ummar Musulmi sun yi haramar fara shagulgulan Karamar Sallar bana bayan kammala Azumin Ramadan. A kan haka ne muka rairayo muku abubuwan da malamai suka kwadaitar da Musulmai su yi a irin wannan rana ta farin ciki da godiya ga Allah bisa ni’imominsa da kammala azumin Ramadan: Kabbarori: Daga lokacin da aka ga jinjirin watan Shawwal (Karamar Sallah) ana so mutum ya rika yin kabbarori a bayyane har zuwa lokacin da za a tayar da Sallar Idi. Daya daga cikin siffoffin yadda ake kabbarorin shi ne: Allahu Akbar Allahu Akbar Allahu Akbar la ilaha illal Lah, Allahu Akbar Allahu Akbar walil Lahil hamd. Zakkar Kono: Wajibi ne ga duk wanda...
    Majalisar Karamar Hukumar Jahun dake Jihar Jigawa ta kaddamar da rabon tallafin kayan noman rani ga manoma 300.   A jawabinsa wajen bikin da aka gudanar a Garin Darai, shugaban Karamar Hukumar, Alhaji Jamilu Muhammad Danmalam yace hakan na daga cikin manufofin Gwamna Umar Namadi na bunkasa noman rani da na damina domin kawar da yunwa da kuma samar da abinci ga al’umma. A cewar sa, karamar Hukumar ta ware wasu yankunan Sahara domin fara noman rani a karo na farko dan fadada harkar noma a kan Tudu.   Alhaji Jamilu Danmalam yace an zabi kauyen Tunubu dake mazabar Kanwa domin fara noman Rani. Ya kara da cewar, wadanda suka anfana da tallafin za su ci moriyar kaso...
    Wani babban mai bawa jagoran juyin juya halin musulunci Imam Ayatullahi Sayyid Aliyul Khaminae shawara kan harkokin tsaro ya bayyana cewa hare-haren ‘WaaduSsadik na III’ don maida martani kan HKI saboda hare-haren da ta kaiwa Iran a shekarar da ta gabata suna kan hanya. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Manjo Janar Yahya Rahim Safavi yana fadar haka a jiya Jumma’a ya kuma kara da cewa, Tehran tana kan bakanta na maida martani kan HKI saboda hare-haren da ta kai kan wasu wurare a nan Iran daga cikin har da wani barikin sojoji a nan birnin Tehran a shekarar da ta gabata. Safari ya kara da cewa, jinkirin da aka samu na maida-martani yana da hikima a...
    Wanda ya jagoranci sallar juma’a a nan Tehran a jiya Juma’a ya bayyana cewa; Jerin gwanon ranar Kudus tana da matukar muhimmanci a addinin musulunci, yana mai kara da cewa: Muna godewa Allah madaukakin sarki cewa, ranar kudus ta wannan shekarar ta bunkasa fiye da shekarun baya.” Haka nan kuma ya kara da cewa; Imam Khumaini ( r.a) da ya ayyana ranar Kudus a duniya a 1979, wacce ita ce juma’ar karshe ta watan Ramadan, a wancan lokacin manyan kasashen duniya masu takama da karfi suna kokarin ganin an mance da batun Falasdinu da kuma kasakantar da shi da cewa batu ne na Larabawa kadai. Limamin na Tehran ya kuma kara da cewa, abinda Imam Khumain ( r.a) ya yi...
    Manyan Matakai Biyar Da Manoma Da Masu Zuba Hannun Jari A Fannin Aikin Noma Ya Kamata Su Yi La’akari Da Su Kamar Yadda kwararrun Suka Bayar Da Shawara: 1- Irin Kwakwar Manja Na Malesiya Bukatar da ake da ita ta Irin Kwakwar Manjan Nijeriya a duk shekara, ya kai na tan miliyan 3, inda kuma wanda ake samarwa a cikin kasar, ya ragu da tan miliyan 1.4. Kazalika, a gonar da ake noman Kwakwar Manja, za a iya samar da tan 12.5 a kowace hekta daya a duk shekara. Misali, a 2023 a heckta 20 a cikin shekara daya, an girbe Kwakwar da ta kai kimanin tan 250, inda akalla aka samu ribar kimanin Naira 150,000 na kowanne tan daya,...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmaeil Baghaei ya ce hare-haren da sojojin Amurka ke kaiwa kasar Yemen da keta hurumin yankunanta barazana ce karara ga zaman lafiya da tsaron kasa da kasa. A cikin wata sanarwa da ya fitar yau Juma’a, Baghaei ya yi tir da hare-haren da Amurka ke kai wa Yemen ba bisa ka’ida ba, wanda ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula da raunata jama’ar kasar tare da lalata kayayyakin more rayuwa na kasar. Ya ce ya kamata kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya kawo karshen rashin daukar mataki da kuma yin shiru dangane da farmakin da sojojin Amurka ke kaiwa Yemen. Ya ce Amurka na ci gaba da kai hare-haren soji kan kasar Yemen tare da...
    A cewar shugabannin Ƙwadago, dole ne a sauya irin wadannan lamari don kare mutuncin tsarin dimokuradiyya a Nijeriya. Sun jaddada wahalar da dokar ta-ɓaci ta haifar wa ma’aikatan kananan hukumomi, da yawa daga cikinsu har yanzu ba su karɓi albashinsu ba. Sanarwar ta lura cewa hana albashin ma’aikata ya jefa su cikin matsin tattalin arziki, musamman ma a irin wannan lokaci da ake samun tsadar rayuwa a cikin kasar nan. Ƙungiyar Ƙwadago ta yi gargadin cewa dokar ta-vaci na iya haifar da mummunan sakamako na tattalin arziki, tana mai jaddada muhimmancin da Jihar Ribas ke da ita ga tattalin arzikin Nijeriya da yankin Neja Delta gaba daya. Ta ce da ma can kasar nan ta riga ta fuskanci hauhawar farashi,...
    A safiyar yau ne aka fara gudanar da jerin gwano na ranar Qudus ta duniya a duk fadin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, inda aka samu halartar jama’a da dama karkashin taken “Muna ci gaba da cika alkawarin da muka dauka.” Mahalarta taron za su yi tattaki ne daga masallatai da manyan filaye a birane da kauyukan kasar zuwa wuraren da ake gudanar da Sallar Juma’a. A birnin Mashhad da ke gabashin Iran, tun da sanyin safiya ne aka fara gudanar da jerin gwano a wani bangare na bikin na shekara-shekara. A halin da ake ciki dai jama’a a birnin Tehran sun fara taruwa daga wurare daban-daban a kan titin juyin juya hali domin tunawa da wannan rana. A cewar wakilin...
    Sarkin Musulmi, Mai Alfarma Muhammad Sa’ad Abubakar, ya umarci al’umma da su fara duban watan Shawwal daga gobe Asabar, 29 ga watan Ramadan 1446, wanda ya yi daidai da 29 ga watan Maris, 2025. Shugaban kwamitin harkokin addini na masarautar Sakkwato, Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaidu, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar. ’Yan sanda sun ƙwato wa mutumin da aka sace kuɗin fansarsa a Kano NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Ya Kamata Musulmi Su Yi Kafin Da Kuma Ranar Sallah Ya ce duk wanda ya ga jinjirin watan Shawwal ya sanar da Hakimi ko Uban Ƙasa mafi kusa da shi, domin a kai rahoto ga Sarkin Musulmi. Wazirin Sakkwato, ya yi addu’a Allah Ya taimaka...
    Majalisar Dattawa, ta buƙaci Ma’aikatar Sadarwa da ta yi aiki tare da kamfanonin sadarwa domin rage kuɗin data, ta yadda kowa zai iya samun Intanet mai sauƙi a Najeriya. A zaman majalisar na ranar Laraba, Sanata Asuquo Ekpenyong (APC – Kuros Riba), ya nuna damuwa kan yadda farashin data ya ƙaru da kusan kashi 200. Ribas: Za mu ɗauki matakan da za su shafi tattalin arzikin Nijeriya — ’Yan ƙwadago Kakakin ’yan sandan Taraba, Abdullahi Usman, ya rasu Ya ce ƙarin yana hana mutane da dama musamman matasa, samun damar amfani da Intanet. “Ƙarin farashin data ba wai kawai yana hana mutane shiga Intanet ba ne, har ma yana wahalar da matasa ’yan kasuwa da masu aiki daga gida,” in...
    Kasashen Iran, Lebanon, Iraki, da kuma Yemen sun kaddamar da wani atisayen hadin gwiwa na sojojin ruwa domin nuna goyan baya ga  Falasdinawa a zirin Gaza, wadanda ke ci gaba da fuskantar zalinci  na gwamnatin Isra’ila. An fara faretin hadin gwiwa a tekun Fasha, da yankin gabar tekun Makran, da kuma tekun Caspian da ke arewaci da kuma kudancin yankin ruwan Iran yau Alhamis gabanin ranar Qudus ta duniya. Kwamandan rundunar sojojin ruwa na IRGC Rear Admiral Alireza Tangsiri ya ce jiragen ruwa masu nauyi da marasa nauyi 3,000 ne ke halartar faretin. Ya kara da cewa, faretin na da nufin nuna karfin ruwa na bangaren ‘yan gwagwarmaya da kuma isar da sako ga miyagu da azzalumar gwamnatin Isra’ila. A...
    Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun Litinin 31 ga watan Maris da Talata 1 ga watan Afrilu a matsayin ranakun hutun karamar Sallah. Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin cikin gida wadda babbar sakatariyar ma’aikatar Magdalene Ajani ta sanya wa hannu. A cikin sanarwar, ministan harkokin cikin gida na Najeriya Olubunmi Tunji-Ojo ya buƙaci dukkanin Musulmai su rungumi tausayawa da karamci da zaman lafiya, inda ya jaddada muhimmancin nuna soyayya da yafiya da haɗin kai domin gina alumma mai cike da zaman lafiya. Ya kuma buƙaci alummar Musulmi su yi wa Najeriya addu’ar ɗorewar zaman lafiya da samun ci gaba, kuma ya yi kiran gudanar da bukukuwan sallah lafiya.
    Kantoman Jihar Ribas, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya), ya dakatar da dukkanin masu riƙe da muƙaman siyasa da jami’an gwamnatin jihar nan take. A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, Ibas, ya bayyana cewa ya ɗauki matakin ne bisa izinin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba shi. Gwamnatin Tarayya ta ayyana Litinin da Talata ranakun hutun sallah Ministan tsaro ya yi alƙawarin kawo sauyi a cibiyar horar da sojoji Waɗanda abin ya shafa sun haɗa da Sakatare na Gwamnatin jihar, Shugaban Ma’aikata, Kwamishinoni, shugabannin hukumomi, da masu ba da shawara na musamman. Ya umarci duk waɗanda abin ya shafa da su miƙa ragamar ayyukansu ga sakatarorin ma’aikatunsu. Ya ce hukumomin da babu sakatare, sai a...
    Babban Mataimaki na Musamman kan Harkokin Rediyo ga Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Tanka Galadanci, ya rasu. Ya rasu ne a ranar Laraba 26 ga watan Maris, 2025, bayan gajeriyar rashin lafiya a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano. Majalisa ta amince da karatu na biyu kan ƙirƙirar sabbin Jihohi 4 Ministan tsaro ya yi alƙawarin kawo sauyi a cibiyar horar da sojoji Kakakin Gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa ne ya tabbatar da rasuwar cikin wata sanarwa da ya fitar. Sanarwar ta bayyana marigayin a matsayin ƙwararren ɗan jarida da ya taka rawar gani wajen inganta harkokin sadarwa a jihar. Za a yi jana’izarsa da misalin ƙarfe 5:30 na yammacin yau Laraba a Filin Masallacin Galadanchi da ke kusa da...
    Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Litinin, 31 ga watan Maris, da Talata, 1 ga watan Afrilu, a matsayin ranakun hutun ƙaramar salla. Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da sakataren ma’aikatar, Magdalene Ajani, ya fitar a ranar Laraba. Ahmad Lawan ya raba tallafin N27m da buhun shinkafa 300 a Yobe Tsohon hadimin gwamnan Kano, Abdullahi Tanka Galadanci, ya rasu Ya taya al’ummar Musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan cikin nasara, tare da yin kira a gare su da su ci gaba da halaye nagari da suka koya a watan. Haka kuma ya jaddada muhimmancin soyayya, yafiya, da haɗin kai wajen gina al’umma. Tunji-Ojo, ya buƙaci ’yan Najeriya da su yi amfani da wannan...
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na Duniyarmu a yau shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhummanci a makon da ya gabata, dangane da siyasa tattalin arziki zamantake tsaro da sauran, sannan mu yi masu karin bayani daga karshe mu ji ra’ayin masana dangane da su. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu. ////.. Madallah, masu sauraro shirinmu na yau zai yi dubi dangane da “ranar Qudus ta Duniya’ wacce aka rayata a jiya Jumma’a ce 27 ga watan Ramdan shekara ta 1446 wanda yayi dai-dai da 28 ga watan Maris shekara ta 2025 miladiyya ne aka gudanra da ranar Qudus ta duniya, a nan kasar Iran da kuma...
    Tsohon Mataimaki na Musamman kan Harkokin Rediyo ga Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Tanka Galadanci, ya rasu. Ya rasu ne a ranar Laraba 26 ga watan Maris, 2025, bayan gajeriyar rashin lafiya a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano. Majalisa ta amince da karatu na biyu kan ƙirƙirar sabbin Jihohi 4 Ministan tsaro ya yi alƙawarin kawo sauyi a cibiyar horar da sojoji Kakakin Gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa ne ya tabbatar da rasuwar cikin wata sanarwa da ya fitar. Sanarwar ta bayyana marigayin a matsayin ƙwararren ɗan jarida da ya taka rawar gani wajen inganta harkokin sadarwa a jihar. Za a yi jana’izarsa da misalin ƙarfe 5:30 na yammacin yau Laraba a Filin Masallacin Galadanchi da ke kusa da...
    Kwamitin tallafawa marayu da masu karamin karfi na kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah wa Ikamatis Sunnah dake karamar hukumar Babura ta jihar Jigawa ya tallafawa gidajen marayu da masu karamin karfi da kayan abinci na kusan naira miliyan 9. Shugaban kungiyar Sheikh Hassan Sabo Musa ya bayyana hakan yayin rabon kayan da aka gudanar a karamar hukumar Babura.   Yace, an sami gudunmawar  kudade da kayan abinci daga al’umma da kungiyoyi. Sheihk Hassan Musa ya kara jadadda bukatar cewar, ya zama wajibi a rika jibintar al’amuran marayu domin samun falala daga Allah.   A jawabinsa, shugaban kwamitin tallafawa marayu,  Malam Nura Sale ya ce wannan shine karo na goma Sha biyu na shirin. Ya godewa wadanda suka bayar...
    Ko da yake an samu rage yawan hare-haren Boko Haram a baya-bayan nan, rahotanni na nuna cewa suna ƙara kai hare-hare kwanan nan. Tun daga shekarar 2009, rikicin Boko Haram ya yi sanadiyyar mutuwar fiye da mutane 200,000 tare da tilasta wa miliyoyin mutane tserewa daga gidajensu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Taraba, SP Abdulahi Usman, ya rasu bayan fama da doguwar jinya. Kakakin rundunar ’yan sandan Najeriya, Olumuyiwa Adejobi ne, ya tabbatar da rasuwarsa cikin wata sanarwa a ranar Laraba. ’Yan fashi 4 sun mutu yayin tsere wa ’yan sanda a Nasarawa Ribas: Za mu ɗauki matakan da za su shafi tattalin arzikin Nijeriya — ’Yan ƙwadago Ya bayyana Usman a matsayin jajirtaccen ɗan sanda kuma gada tsakanin jami’an tsaro da al’umma. “SP Usman ya shafe shekaru uku yana ƙarfafa hulɗa tsakanin ’yan sanda da jama’ar Taraba. “Ƙwarewarsa, mutuntaka da jajircewarsa wajen neman adalci sun an samu tasiri,” in ji Adejobi. Ya ƙara da cewa rasuwar Usman babban rashi ne ga rundunar ’yan sanda, abokan aikinsa...
    Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Taraba, SP Abdulahi Usman, ya rasu bayan fama da doguwar jinya. Kakakin rundunar ’yan sandan Najeriya, Olumuyiwa Adejobi ne, ya tabbatar da rasuwarsa cikin wata sanarwa a ranar Laraba. ’Yan fashi 4 sun mutu yayin tsere wa ’yan sanda a Nasarawa Ribas: Za mu ɗauki matakan da za su shafi tattalin arzikin Nijeriya — ’Yan ƙwadago Ya bayyana Usman a matsayin jajirtaccen ɗan sanda kuma gada tsakanin jami’an tsaro da al’umma. “SP Usman ya shafe shekaru uku yana ƙarfafa hulɗa tsakanin ’yan sanda da jama’ar Taraba. “Ƙwarewarsa, mutuntaka da jajircewarsa wajen neman adalci sun an samu tasiri,” in ji Adejobi. Ya ƙara da cewa rasuwar Usman babban rashi ne ga rundunar ’yan sanda, abokan aikinsa...
    Bayan gazawar tattaunawar da hukumar ta IAEA ta yi da Tehran, babban daraktan hukumar Rafael Grossi ya jaddada muhimmancin komawa kan teburin shawarwari nan gaba don tabbatar da cewa Iran ba ta mallaki makamin nukiliya ba. Hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa ta ce tattaunawar da ta yi da wani babban jami’in kasar Iran a baya-bayan nan, ba a samu wani ci gaba kadan ba a cikin binciken nukiliyar da aka shafe shekaru ana yi kan kasar Iran, yana mai jaddada bukatar gaggauta warware takaddamar diflomasiyya da ke tsakanin Tehran da Washington. A wata hira da Bloomberg babban darektan hukumar Rafael Grossi ya tabbatar da cewa nan ba da jimawa ba zai koma Tehran domin ci gaba...
    Dakarun sojin Yaman sun ce sun kara kai hare-hare na nuna kyama ga Isra’ila da Amurka a matsayin nuna goyan baya a kan zirin Gaza. Kakakin rundunar Yahya Saree ya ce a daren jiya litinin sojojin na Yaman sun kai hari filin tashi da saukar jiragen sama na Ben Gurion na Isra’ila da makami mai linzami guda biyu da suka hada da Zulfiqar mai gudun tsiya. Ya kara da cewa hare-haren na goyon bayan Falasdinawa ne a Gaza. Saree ya yi nuni da cewa, dakarun kasar Yemen sun kuma kai hari kan jirgin yakin Amurka Harry S. Saree ya ce harin da aka kai kan jiragen ruwan yakin Amurka shi ne irinsa na biyu cikin sa’o’i 24 da suka gabata....
    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Juventus ta raba gari da mai horas da ’yan wasanta, Thiago Motta, yayin da ko kaka ɗaya bai cika ba a kwantaragin da ya ƙulla da ƙungiyar ta Italiya. A cewar Jaridar wasanni ta La Gazzetta dello da Gidan Talabijin na Sky Sport, Juventus ta maye gurbin Thiago Motta da tsohon ɗan wasan ƙungiyar, Igor Tudor. Fursunoni 12 sun tsere bayan fasa gidan yari a Kogi Za mu farfaɗo da Madatsar Ruwa ta Biu — Zulum Juventus dai za ta ɗora wa sabon kocin nauyin jajircewa wajen ganin ƙungiyar ta ƙare a cikin sahun huɗun farko na teburin Gasar Serie A ta bana, domin samun damar buga Gasar Zakarun Turai a kaka mai zuwa. A halin...
    Iran ta yi gargadin cewa zaluncin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi wa kasar Labanon na da matukar hadari kuma barazana ga zaman lafiya da tsaron kasa da kasa, inda ta bukaci kasashen duniya da su dauki matakin da ya dace. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmaeil Baghaei ya yi kakkausar suka kan hare-haren da Isra’ila ke kai wa a sassa daban-daban na kasar Lebanon, wanda ya yi sanadin mutuwar fararen hula da dama a kasar a baya-bayan nan. Baghaei ya alakanta hare-haren da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke kai wa kan kasashen Labanon da Siriya da yunkurin kisan kiyashi da Tel-Aviv ta yi a baya-bayan nan a Gaza da kuma gabar yammacin gabar kogin Jordan da ta mamaye,...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya yi kira ga kasashen duniya da su kawo karshen rikicin da Isra’ila ke ci gaba da haifarwa a yankin gabas ta tsakiya. A wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Masar Badr Abdelatty, Araghchi ya yi Allah wadai da sabbin hare-haren da Isra’ila ke kai wa zirin Gaza tare da hana kai agajin jin kai a yankin  a matsayin keta haddin yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta watan Janairu. Ya kuma yi kira da a dauki matakin gaggawa a duniya kan yadda Isra’ila ke ci gaba da ruruta wutar rikici a yankin baki daya. Isra’ila ta kaddamar da yakin kisan kare dangi a Gaza a ranar 7 ga Oktoba, 2023, amma ta...
    Shugaba hukumar makashin Nukliya na kasar Iran Mohammad Islami ya bada sanarwan cewa a ranar 8 ga watan Afrilu mai zuwa. Yace hukumarsa za ta kaddamar da sabbin magunguna da ta samar tare da amfani da makamashin Nukliya, a dai dai na ranar makamashin Nukliya ta kasar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ta nakalto Islami yana fadar haka a yau Lahadi, ya kuma kara da cewa wannan ci gaban kari ne, kan ci gaban da kasar ta samu a wannan fannin, wanda kuma zai kara kyautata bangaren lafiya na kasar sannan ya zama hanyar samar da kudade ga kasar. Shugaba hukumar makamashin nukliya ta Iran ya kara da cewa a cikin shekarar Iraniyawa wanda ya kara kadai kasar...
    Allah Ya yi wa mahaifiyar Gwamnan Katsina, Dikko Umar Radda rasuwa. Wakilinmu ya ruwaito cewa, mahaifiyar Gwamnan, Hajia Safara’u Umar Radda, ta rasu ne a wani asibiti da ke birnin Katsina. Cikin wani saƙo da tsohon mai magana da yawun gwamnan, Isah Miqdad ya wallafa a shafinsa na X, ya ce Hajiya Safara’u ta riga mu gidan gaskiya bayan ta yi fama da doguwar jinya. Mabiya dandalan sada zumunta na ci gaba da bayyana alhini dangane da rasuwar Hajiya Safara’u.
    Wani ɗan ƙasar Turkiyya da ya rasa gidansa sakamakon wata gagarumar girgizar ƙasa a shekarar 2023, ya shafe shekara biyu yana zaune shi kadai a cikin wani ƙaramin kogo saboda yana ganin ya fi kowane gini da mutum zai yi karko.  A watan Fabrairun 2023, Kudancin Turkiyya ya fuskanci ibtila’in girgizar kasa mai karfin 7.8 da ta yi sanadiyyar mutuwar dubun-dubatar mutane tare da mayar da daukacin unguwanni tamkar kufai. An yi wa wata karya tiyatar ceton rai Dakatar da Gwamnan Ribas zubar da ƙimar Nijeriya ne a idon duniya — Jonathan Ali Bozoğlan, mahaifin ‘ya’ya uku daga lardin Hatay da ke kudancin kasar, ya rasa gidansa sakamakon girgizar kasar da aka yi a ranar 6 ga watan Fabrairu 2023....
    An ruwaito cewa, shirin aikin noman ranin da aka kaddamar a yankin na Lallashi, zai karade hekta 10, wanda kuma sama da kananan manoma 80, za su amfana da shirin kai tsaye. Bugu da kari, shirin zai taimaka wajen kara samar da girbin amfanin gona mai yawan gaske tare kuma da kara bunkasa tattalin arzikin jihar baki-daya. Malam Aliyu Musa, da yake yin jawabi a madadin sauran manoman da ke yankin ya bayyana cewa, samar da shirin a yankin da gwamnatin jihar ta yi, tamkar zuba hannun jari ne. A cewarsa, al’ummar yankin za su ci gaba da yin addu’a, domin shirin ya dore tare kuma da ganin an kara fadada shi, don su ma sauran yankunan jihar su amfana....
    Wata gobara da ta tashi a sansanin ’yan gudun hijira na Munna Albadawi da ke ƙaramar hukumar Jere a Jihar Borno, ta lalata wasu gidaje 10 tare da salwantar da rayuwar yaro mai shekara 7 mai suna Abubakar Gargar. A cewar shugaban sansanin, Babangida Mahmud gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe 3:00 asubahin safiyar ranar 20 ga watan Maris, 2025, inda gobarar ta laƙume kayayyakin abinci da tufafi da dai sauran kayayyaki. Taƙaddama: An kama wanda ya daɓa wa matarsa ​​wuƙa ta mutu ’Yan bindiga sun yi garkuwa da jami’in FRSC a Benuwe Wanda kawo yanzu ba a tantance adadin asarar da ta haifar ba baya ga salwantar rai guda. Hukumar kashe gobara ta Jihar Borno tare da haɗin...
    A halin yanzu, Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Borno (SEMA) da Hukumar Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) tare da wasu ƙungiyoyin jin-ƙai sun tura wakilansu don duba girman ɓarnar da gobarar ta haifar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan, a sakonsa na karshe ga Iraniyawa a shekara ta 1403 na kalandar Iraniyawa, ya bukaci mutanen kasar su hada kai don kaiwa ga manufofin kasar, wadanda suka hada da bunkasar tattalin arziki, da kauda tsadar rayuwa da kuma rashin bawa makiya damar cutar da kasar. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a jawabinda na ‘Nuruz’ ko sabon shekara ta 1404 wanda ya shigo yau. Pezeshkiyan ya bukaci All…ya yi rahama ga shuwagabannimmu da muka rasa a shekaran da ta kare, wadanda suka hada da Shahid Ibrahim Ra’isi da abokan tafiyar, da sharing maso gwagwarmaya a ciki da wajen kasar, wadanda suka hada da shahidan Lebanon Falasdin Siriya da...
    Gwamnatin Jihar Yobe ta kafa cibiyoyin bayar da abinci 85 domin samar wa almajirai abinci a dukkanin Ƙananan Hukumomin 17 na jihar, a lokacin azumin Ramadan. Sakataren zartarwa na Hukumar Ilimin Larabci da Addinin Musulunci ta Jihar Yobe, Malam Umar Abubakar ne, ya bayyana hakan a wata hira da Daily Trust a ranar Alhamis. Sanƙarau ta kashe mutum 55 saboda rashin tsafta a Kebbi Dabarun Rabauta Da Kwanaki 10 Na Ƙarshen Ramadan “Muna bai wa makarantun Tsangaya 85 kayan abinci 85, biyar a kowace Ƙaramar Hukuma, inda muke ciyar da almajirai tsakanin 300 zuwa 400 a kowace makaranta,” in ji shi. Ya ƙara da cewa Gwamna Mai Mala Buni ne, ya amince da wannan shiri domin tallafa wa yara marasa...
    (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Masu yi wa ƙasa hidima (NYSC), za su fara jin daɗin sabon alawus ɗin gwamnatin tarayya na N77,000.00 wanda aka sake duba shi da za a fara biya daga watan Maris, 2025. Babban Darakta Janar (DG) na NYSC, Birgediya Janar Olakunle Oluseye Nafiu ne ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga masu yi wa ƙasa hidima a babban birnin tarayya, a ofishin NYSC na shiyya ta 3 da ke Wuse Zone 3 Old Parade Ground a yankin Garki a ranar Alhamis. Gwamnan riƙon ƙwarya na Jihar Ribas ya isa gidan gwamnati ’Yan Boko Haram 7 sun miƙa wuya ga sojojin MNJTF a Borno Ya sanar da masu yi wa  ƙasar hidima cewa ma’aikatar kuɗi ta sanar da...
    ’Yan Najeriya na iya fuskantar karin farashin man fetur bayan da Matatar Man Dangote ta bayyana cewa ta daina sayar wa ’yan kasuwa man fetur a kudin Naira. Matatar, wacce ke siyan danyen mai da Naira bisa yarjejeniyar gwamnati, yanzu ta koma sayan danyen mai da dalar Amurka. An kirkiro yarjejeniyar siyan danyen mai da Naira ne domin rage tsadar mai. Bisa ga wannan yarjejeniya, Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPCL), yana da alhakin samar wa Matatar Dangote gangar danyen mai a kowace rana 385,000, domin ta tace ta kuma sayar da shi a farashin Naira. Sai dai rashin cika alkawari daga NNPCL ya sa yarjejeniyar ta gaza dorewa. Wata majiya ta bayyana cewa, “NNPCL bai cika alkawarin da ya...
    Aƙalla mutum 55 ne suka rasu sakamakon ɓarkewar cutar sanƙarau a ƙananan hukumomin Jega, Gwandu, Aliero, Bunza, da Birnin Kebbi da ke Jihar Kebbi. Hukumar Lafiya ta Jihar ta tabbatar da ɓullar cutar bayan gwaje-gwajen da aka yi a Abuja. Ƙungiyoyin ƙwadago sun buƙaci Tinubu ya mayar da Fubara kan kujerarsa Shugaban Dattawan Arewa ya ajiye sarautar Magajin Rafin Zazzau Sakataren Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kebbi, Dokta Nuhu Koko, ya bayyana cewa a Gwandu ne aka fi samun waɗana suka rasu, inda mutum 25 suka rasu, sai Jega da ke 16, sannan Aliero ke da mutum 14 da suka mutu. Yawancin waɗanda suka rasu sun ɗauka cewa zazzaɓin cizon sauro ne ke damunsu, wanda hakan ya sa ba su garzaya...
    A ranar 19 ga watan Maris na ko wace shekara ne mutanen Iran suke gudanar da bukukuwan tunawa da ranar da mutanen kasar tare da taimakon gwamnatin lokacin suka sami nasarar kwace kamfanin haka da sarrafa man fetur na kasar, daga hannun wani kamfanin mai na kasar Burtaniya suka maida shin a kasa. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya ce , wannan rana abin alfakhari ne ga mutanen kasar, don bayan haka ne kasar ta sami ikon kawo ci gaban tattalin arzikin kasar da kuma shimfida harsashen samun yencin kasar daga hannun kasashen yamma wadanda suka mamaye bangarori da dama a cikin al-amuran kasar. A ranar 19 ga watan Maris na shekara ta 1951 ne, wato shekaru 78...
    Matatar man Dangote ta sanar da dakatar da sayar da man fetur a naira. Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da matatar ta aika wa abokan huldarta a yammacin ranar Laraba. ‘Yan Bindiga Sun Sace Mutum 7 A Jihar Neja El-Rufai Ya Shiga Tsilla-tsilla Bayan Rasa Kujerar Minista – APC A cikin sanarwar, Matatar ta ce, wannan matakin na wucin gadi ne, inda ta bayyana dalilin da ya sa aka dauki matakin domin samar da daidaito tsakanin farashin danyen mai da aka siyo da Dala da kuma na Naira. “Muna so mu sanar da ku cewa, matatar man Dangote ta dakatar da sayar da man fetur a Naira na wani dan lokaci domin kauce wa rashin daidaito tsakanin danyen...
    Ma’aikatar tsaron kasar Rasha ta sanar da kakkabo jiragen sama marasa matuki 57 da kasar Ukiraniya ta harba zuwa yankuna mabanbanta na kasar. A yau Laraba ne ma’aikatar tsaron kasar ta Rasha ta sanar da cewa; An harbo jiragen marasa matuki 35 da aka harba wa yankin Kursk dake yammacin Syria a jiya da dare. Sai kuma wasu jiragen 13 da aka harba a yankin Oryol da kuma wasu 7 a samaniyar tekun Azorf. Sauran yankunan da sojojin Ukuraniya su ka harba wa makamai masu linzamin sun hada  Tola, da Biryansk. Kwanaki biyu da su ka gabaa ma dai sojojin na Rasha sun sanar da kakkabo wasu jirage marasa matuki na Kasar Ukiraniya 31 da aka harba a yankuna mabanbanta na...
    Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana a yayin da take mayar da martani ga tambayar da wani dan jarida ya yi mata a taron manema labaru na yau 18 ga wata cewa, kasar Sin ta damu matuka kan halin da ake ciki a tsakanin Falasdinu da Isra’ila,kuma tana fatan dukkan bangarorin za su sa kaimi ga ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta yadda ya kamata, da kaucewa daukar duk wani mataki da zai ta’azzara lamarin, da hana afkuwar bala’in jin kai a mataki mai girma. Hukumomin lafiya da ke Gaza sun ce adadin mutanen da suka mutu a hare-haren da Isra’ila ta kai a wurare daban-daban a zirin Gaza da...
    A yunkurin da gwamnatin jihar Jigawa ke yi na sauya fasalin harkar noma, majalisar zartaswa ta jihar ta amince da ware sama da naira biliyan daya da miliyan dari biyar domin fara aiki da sabon Kamfanin injinan noma na jihar. Kwamishinan Yada Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ne ya bayyana hakan ga manema labarai, jim kadan bayan kammala taron majalisar zartaswa da aka gudanar a fadar gwamnatin jihar da ke Dutse, babban birnin jihar. A cewarsa, an kafa kamfanin ne domin rage tsadar sarrafa kayayyakin amfanin gona a fadin jihar. Ya kara da cewa, majalisar ta kuma amince da fitar da sama da naira miliyan dari tara da sittin da tara domin ci gaba...
    Shugaban kungiyar Ansarullah na kasar Yemen Sayyid Abdulmalik Husi ya bayyana cewa; Matukar Amurka ta ci gaba da kai wa Yemen hare-hare, to suna da hanyoyi da za su iya gasa mata aya a hannu masu yawa. Sayyid Abdulmalik al-Husi ya yi ishara da yadda dubun dubatar mutanen Yemen su ka fito a cikin birnin San’aa da kuma sauran biranen kasar domin raya da tunawa da rana da aka yi yakin Badar, yana mai cea; hakan yana a matsayin wani sako ne zuwa Amurka da Isra’ila, kuma tabbas idan su ka ci gaba da kai wa Yemen hari, to muna da zabi na  hanyoyin da za mu yi amfani da su domin dandana musu kudarsu.  Sayyid Husi wanda ya gabatar...
    Yau Litinin da safe, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwa ta Sin ya kira wani taron manema labarai, inda kakakin hukumar kididdiga ta Sin, Fu Linghui ya yi bayani kan yadda tattalin arzikin kasar ke gudana a cikin farkon watanni biyu na bana da suka gabata. Kididdiga na nuna cewa, daga watan Janairu zuwa Fabrairu na bana, masana’antar samar da kayayyaki na samun saurin bunkasa, inda ribar da kamfanoni da masana’antu da ke iya samun ribar da ta zarce dala miliyan 2.7 a duk shekara, ta karu da kashi 5.9% bisa na makamancin lokacin bara. Daga cikinsu, masana’antar ba da hidima ta fi samun bunkasuwa, inda alkaluman ci gabanta suka karu da kashi 5.6% bisa na makamancin lokacin bara, kuma...
    Al’ummar kasar Yemen sun gudanar da wani gagarumin ganganmi a fadin kasar, inda suka lashi takobin tinkarar ta’addancin Amurka ta hanyar kara karfin soji, da hada karfi da karfe, da kuma abokan gaba shakat. Gangamin ya zo ne bayan da jagoran gwagwarmayar kungiyar Ansarullah Abdul Malik al-Houthi ya bayyana cewa kasar a shirye ta ke duk wata barazanar Amurka.  “Ba mu tsoron kowa, kuma ba mu rusuna wa kowa sai Allah. Za mu fuskanci duk wani tashin hankali. ” inji shi “A shirye muke mu tunkari dukkan azzaluman duniya ba tare da wata fargaba ko tsoro ba. Abdul Malik al-Houthi ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya yi a ranar Lahadi, kwana guda bayan da Amurka ta kai...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeskiyan ya ba da sanya hannu a kan takardun yarjeniyar samar da zaman lafiya wanda kasashen Armenia da Azerbaijan suka yi. Ya kuma taya mutanen kasashen murmurnar wannan nasara. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto shugaban yana taya kasashen biyu murna a jiya lahadi, ya kuma kara da cewa, Iran a ko yauce tana fatan zaman lafiya a kasashe makobata da kasar sabuda dalilai da dama daga ciki Iran tana amfani da kasashe makobta don kyautata yanayin tattalin arziki a tsakanin kasashen biyu. Firai ministan kasar Armenia Nikol Pashjinyan a zantawarsa ta wayar tarko da shugaban kasar Iran ya ce: Gwamnatinsa zata yi kokarin ganin an aiwatar da yarjeniyar daki daki kamar yadda...
    Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran ya yi gargadin cewa, Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta taba neman wata kasa da yaki ba, amma kuma  a lokaci guda ta shirya tsaf domin mayar da mummunan martani ga duk wata barazana ko shishigi daga makiya. Janar Hossein Salami ya bayyana hakan ne a wannan Lahadi, bayan da Washington ta zargi Tehran da taimakawa sojojin Yaman a hare-haren da suka rika kaiwa haramtacciyar kasar Isra’ila a baya-bayan nan tare da yin kira da ta daina yin wanann zargi maras tushe balantana makama. Salami ya ce, “Iran ba za ta taba zama mai fara yaki ba, amma idan aka fuskanci barazana, za ta mayar da martani mai tsanani.”...
    Hajiya Asta Shehu Timta, mahaifiyar mai martaba Sarkin Gwoza, Alhaji Muhammadu Shehu Idrisa Timta ta riga mu gidan gaskiya. Wata sanarwa da Masarautar Gwoza da ke Jihar Borno ta fitar ta ce Hajiya Asta ta rasu ne yammacin jiya Asabar bayan shafe shekaru 80 a duniya. Yadda za a girka ‘Kamoniya’ An kama malama tana lalata da ɗalibinta Haka kuma, Hajiya Asta ita ce mahaifiyar Shugaban Ƙaramar Hukumar Gwoza, Yarima Abba Kawu Shehu Timta. Masarautar ta ce za a yi jana’izar marigayiya Hajiya Asta Shehu Timta a yau da Lahadi bayan sallar azahur a Fadar Sarkin Gwoza. A lokacin rayuwarta, Hajiya Asta Shehu Timta ta kasance tsohuwar malamar makaranta kuma har zuwa rasuwarta tana taimakawa wajen ci gaban ilimi a...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran y ace gwamnatin kasar Amurka bata da hakkin tsarawa kasar Iran yadda zata gudanar da manufofinta harkokin waje, wannan ya wuce tun bayana nasarar juyin juya hali musulunci a kasar a shekara ta 1979. Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a shafinsa na X. Aragchi yana maida martani ne ga shugaban kasar Amurka Donal Trump wanda ya tuta sojojinsa suka kai hare-hare kan kasar Yemen a jiya Asabar, don kada su hana jiragen ruwan HKI wucewa daga tekun Red Sea. Kuma ya ce: Ya gargadi Iran ta dakatar da tallafin da take bawa kungiyar Ansarullah. Don itace da alhakin duk abinda kungiyar take yi. Ministan ya kara da...
    Kwamandan dakarun kare juyin musulunci na Iran manjo  janar Salami wanda ya gabatar da jawabi a wurin tunawa da shahid Mahadi Bakiri a garin Tabriz ya bayyana cewa;; Babu yadda za ayi jamhuriyar musulunci ta Iran ta bude tattaunawa da Amurka a karkashin barazana, yana mai kara da cewa; yin gwawarmaya da jajurcewa a gaban masu girman kai da daga hanci, yana daga cikin muhimman koyarwar alkur’ani mai girma da kuma tsarin musulunci. Manjo janar Salami ya kara da cewa; ta hanyar tsayin daka da dunkulewar al’umma wuri daya, za a kai ga samun nasara. Haka nan ya kara da cewa; A tsawon shekaru 46 da su ka gabata, al’ummar Iran ta kasance a cikin fadaka wajen fuskantar duk wata...
    Kamitin Zakka na Masarautar Hadejia ya raba zakkar kayayyakin amfanin gona da na kudi kimanin naira miliyan 63 a gundumar Birniwa dake Jihar Jigawa. Sakataren kwamitin zakka na masarautar Hadejia, Injiniya Isma’ila Barde, ya bayyana hakan yayin kaddamar da rabon zakka ga mabukata a gundumar Birniwa. Injiniya Isma’ila Barde ya lissafa abubuwan da aka bayar a matsayin zakka, da suka hada da buhunan Gero 668, da Bahunan Dawa 152 da bahunan shinkafa 8 da rabi da Kuɗi kimanin naira miliyan 17 da dubu ɗari tara da goma sha shida. A nasa jawabin, Shugaban kwamitin zakka na masarautar Hadejia, Barrista Abdulfatah Abdulwahab wanda babban limamin masarautar Hadejia Ustaz Malam Yusuf Abdurrahman ya wakilta, ya yaba wa al’ummar Birniwa bisa bayar da...
    Daga ranar 2 zuwa 4 ga watan Disamban shekarar 2024, an gudanar da taron kasa da kasa na “Fahimtar kasar Sin” a birnin Guangzhou. A yayin taron, fiye da baki 600 na kasar Sin da kasashen waje, ciki har da tsohon firaministan kasar Lebanon Hassan Diab, sun hallara don tattaunawa da yin musayar ra’ayi kan taken “Yin gyare-gyare-zamanintarwa irin ta kasar Sin da sabbin damammakin ci gaban duniya”, inda suka samu ra’ayin bai daya na gudanar da hadin gwiwa. A tattaunawar da ya yi da wakiliyar babban rukunin gidajen rediyo da talibijin na kasar Sin, wato CMG a takaice, Hassan Diab ya bayyana cewa, fahimtar kasar Sin yana da matukar muhimmanci, domin kasar na bude kofarta ga duniya. A cikin...
    Mai bai wa shugaban Daular Hadaddiyar Daular Larabawa da ya kawo ziyara Iran ya bayyana cewam ganawarsa da ministan harkokin wajen Iran ya yi kyau. Mai bai wa shugaban daular ta Hadaddiyar Daular Larabawa shawara, Muhammad Anwar Karkush ya wallafa a shafinsa na sada zumunta cewa:  Muna kimanta ttataunawa mai amfani da kuma  aiki tare.” Baya ga batutuwan da su ka shafi alaka a tsakanin kasashen biyu,  da kuma abubuwan da suke faruwa a cikin wannan yankin, Anwar Karkash ya zo da wasiki daga shugaban kasar Amurka Donald Trump.
    Shi ma, Manajan Darakta na CDI, Roland Oroh, ya goyi bayan wannan ra’ayi na Dakta Anyebe Idoga, inda ya sanar da cewa; wannan aiki, zai kara karfafa karfin Nijeriya wajen fitar da kaya zuwa ketare. “Mun ji dadi kan fara wannan yarjejeniya da mu, domin wannan zuba hannun jari, zai taimaka wa Nijeriya wajen kara habaka fitar da ingantaccen nama zuwa ketare”, in ji Oroh. Kazalika, an bijiro da wannan hadaka ce, sakamakon yadda Saudiyya ta nuna sha’awarta, na son shigar da nama zuwa kasarta daga Nijeriya, wanda ya kai tan 176,000 a duk shekara, tare da kuma ciyawar dabbobi ta alfalfa hay da abincin dabbobi da ake sarrafawa da kuma Waken Soya. A yanzu haka, CDI na ci gaba...
    “ Zuba hannun jari a bangaren da ake sauke kaya a Tashohin Jiragen Ruwa da kara fadada hanyoyin layin Jiragen kasa, za su iya taimakawa wajen bunkasa aiki da kuma kara sanya gasa a ayyukan tafiyar da Tashoshin Jiragen Ruwa. A cewar Dantsoho Ya sanar da cewa, samar da kyakaywan yanayin kasuwanci a kasar nan na da alaka da kokari da kuma yanayin gasar da aka samar na kasa a Tashishin Jiragen Ruwan, inda ya yi nuni da cewa, wadannan abubuwan sun taimaka wajen samun musayar kudade, daidaita tattalin ardikin kasar, kara habaka kauswanci da kuma samun masu zuwa zuba hannun jari. Dantsoho ya godewa Ministan Bunkasa Tattalin Arziki na Ruwa Adegboyega Oyetola, bisa goyon bayan ada yake ci gaba...
    Ya kara da cewa bisa sashin 10.7 da aka sake nazarinsa a 2019, ya rage cajin daga N65 zuwa N35 kan kowace hada-hada. Sai dai ya bayyana cewa za a biya Naira 100 ga duk wanda aka cire na Naira 20,000 ga kwastomomi daga wasu bankunan da ke yin mu’amala da ATM a harabar bankin. Onobun ya jaddada cewa abokan hulda daga sauran bankunan da ke yin mu’amala da ATMs a wajen harabar bankin, manyan kantuna, kasuwanni, da sauran wuraren taruwar jama’a, za a rika biyan su Naira 100 da karin N500. Majalisar a cikin kudurorin ta ta bukaci CBN da ya gaggauta dakatar da aiwatar da wannan manufa, har sai an yi huldar da ta dace da kwamitocin da...
    Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi da tsohon Kwamishinan sa ido da tantance ayyuka Muhammad Diggol sun gana da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Barau I. Jibrin a Abuja.  Taron ganawar wanda ya haɗa sauran masu ruwa da tsaki, ya mayar da hankali ne kan samar da ci gaba a Jihar Kano da kuma ciyar da ƙasa gaba. MC Tagwaye ya fice daga APC zuwa SDP Wata mata ta faɗa ruwa ta mutu a Legas A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Barau ya wallafa hotunan ganawar da aka yi tare da bayyana muhimmancin haɗin gwiwa wajen samun ci gaba mai ɗorewa. “Ci gaban jiharmu da ƙasa a kodayaushe yana kan gaba a ajandarmu, za...
    Dubun dubatar musulmi masu ibada ne suka gudanar da sallar Juma’a ta biyu na watan Ramadan a harabar masallacin Al-Aqsa, duk da tsauraran matakan da Isra’ila ta dauka na hana Falasdinawa shiga wurin mai tsarki. Sashen kula da masallacin da ke birnin al-Quds ya ce kimanin masu ibada 80,000 ne suka taru A daidai lokacin da ake fargabar ci gaba da tashin hankalin da gwamnatin Isra’ila ke yi ga mazauna yankin. Duk da wannan takunkumin, masu ibada sun yi ta tururuwa daga yankuna daban-daban na Yammacin Kogin Jordan don shiga wurin mai tsarki. Sojojin Isra’ila sun hana matasan Falasdinawa shiga daga Jenin da Tulkarm. Hamas ta yi Allah wadai da takunkumin Isra’ila a Masallacin Al-Aqsa
    “Muna kokarin kawar da bangaren dala. Abin da muke so mu yi shi ne mu biya a cikin kudin gida na duk kamfanonin jiragen sama. Kuma za a biya kudin ne daidai da farashin dala a halin yanzu a lokacin da ake biya. “Kason da ya dace ya ba ku damar gudanar da ayyukanku dukkan ne za a biya ku, bayan kammala aikin za a karasa biyanku sauran,” ya shaida. Tun da farko, shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Usman Saleh, ya ce, ayyukan jirage na sufuri na daga cikin muhimman ayyukan da ke gabansu wajen sauke nauyin aikin hajji. “Lamarin na bukatar kwarewa matuka gaya da kuma himma da azama. Wannan lamarin ba kawai ga batun sufuri ba ne, ya shafi...
    Hukumar EFCC ta kama wata mata da mijinta bisa zargin yin sojan gona da sunan mai ɗakin Gwamnan Jihar Katsina, Hajiya Fatima Dikko Radda, wajen damfarar kuɗi Naira miliyan 197.75. An gurfanar da su a gaban babbar kotun Jihar Kaduna, tare da wasu mutum biyu da ake zargi suna taimaka musu wajen aikata laifin. ’Yan bindiga sun kai hari ƙauyukan Kaduna, sun sace matasa 3 NAJERIYA A YAU: Rashin Aikin Yi Da Hanyoyin Magance Ta A Najeriya EFCC ta ce mutanen huɗu sun haɗa kai wajen amfani da sunan Hajiya Fatima Dikko Radda don samun canjin dala daga wani mai sana’ar canji. Matar ta gabatar da kanta a matsayin Fatima Dikko Radda, tana buƙatar a yi mata canjin dala. Mijinta...
    Ministan kasa a ma’aitar tsaro, Mohammed Bello Matawalle, ya ba magoya bayan jam’iyyar (APC) a jihar Zamfara gudumuwar kudi naira miliyan 500 domin a taimaka musu wajen gudanar da azumin watan Ramadan cikin sauki.   Mai ba da shawara na musamman kan harkokin siyasa Mattawalle, Alhaji Ibrahim Danmalikin Gidan Goga ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Gusau.   A cewar Gidan-Goga, Ministan ya zabi bayar da kudi ne maimakon kayan abinci, saboda tuni wasu ‘yan siyasa a jihar suka raba wa magoya bayansu hatsi.   Ya kuma jaddada cewa tallafin kudi zai baiwa magoya bayan jam’iyyar APC damar siyan wasu muhimman abubuwan da ake bukata a cikin watan Ramadan.   “A wannan karon,...
    Kwamandan sojojin kasa na JMI Laftanar-Janar Kiyomars Haydari ya bada sanarwan cewa; A bisa umranin jagoran juyin musulunci Imam Sayyid Ali Khamnei , sojojin kasa na JMI suna cikin shirin ko ta kwana domin mayar da martani akan kowace irin barazana ga tsaron kasar. Laftanar janar Haidari ya kuma ce: A halin yanzu da akwai rundunoni 11 da su ke cikin shiri a kan iyakoki kasar domin sanya idanu da tattara bayanai saboda tabbatar da tsaron kasar. Kwamandan sojan kasa na Iran ya kuma ce; Saboda sojojin suna cikin shirin ko-ta-kwana ne, barazanar da ake fuskanta ta zagwanye, da hakan ya ke a matsayin kandagarko. Har’ila yau Laftanar janar Haidari ya yi ishara da rawar dajin da sojojin kasa su...
    Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bada sanarwan amincewa da tsagaita budewa juna wuta tsakanin Rasha da Ukraine na tsawon kwanaki 30, wanda shugaban kasar Amurka Donal Trump ya gabatar, sai dai akwai bukatar karin bayani filla-filla kan yadda hakan zai kasance. Sannan yana fadar wannan zai kai ga tsagaita budewa juna wata na din din din. Shafin yanar Gizo na labarai Africa News ya nakalto shugaban yana fadar haka a yau Alhamis. Ya kuma kara da cewa akwai bukatar a kara tattaunawa da abokammu na kasar Amurka don kara fayyace yadda tsagaita wutan zai kasance. Daga cikin abubuwan da za’a tattauna akwai yiyuwar sabawa yarjeniyar da kuma matakan da za’a dauka don hana hakan faruwa ko kuma idan ya...
    Aƙalla mutum bakwai ne suka rasa rayukansu yayin da kadarori na sama da Naira miliyan 50 suka salwanta sanadiyyar gobarar a cikin watan Fabrairun 2025 a Jihar Kano. Kakakin hukumar kashe gobara, Saminu Yusif Abdullahi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a jihar. Galibin ’yan Najeriya na neman muƙaman gwamnati don arzuta kansu — Obasanjo Za a mayar da waɗanda Lakurawa suka raba da garuruwansu – Gwamnan Kebbi Ya ce, a cikin watan Fabrairu, 2025, hukumar kashe gobara ta jihar ta samu jimillar kiraye-kirayen lambar wayar kashe gobara 77, da lambar kiran neman ceto 11 da kuma ƙararrakin gobara na ƙarya uku. “Kimanin kadarori da gobara ta lalata a cikin watan Fabrairu sun kai darajar kuɗi N50,318,000 yayin da...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi maraba da matakin da kasar Yemen ta dauka na haramtawa jiragen ruwan Isra’ila shiga tekun Bahar Maliya Bayan sanarwar da kungiyar Ansarallah ta kasar Yemen ta fitar na cewa za ta dawo da haramcin da ta yi wa jiragen ruwan Isra’ila na tsallakawa tekun Bahar Rum, Hamas ta fitar da sanarwa inda ta yi maraba da matakin. ta bayyana wannan mataki a matsayin wanda ke nuna hakikanin matsayin al’ummar Yemen da gwamnatin kasar na goyon bayan gwagwarmayar al’ummar Falastinu. Har ila yau kungiyar ta yi kira ga dukkanin kasashen Larabawa da na Musulunci da kuma ‘yantatun kasashe a duniya da su kara zage damtse wajen matsin lamba ga ‘yan mamaya da magoya bayansu...
    Idan ka dauki bangaren tsofaffi da kananan yara, za ka iya cewa su ne mafi rauni a cikin al’umma. Tsofaffi sun gajiya don haka suna bukatar taimako, yara kanana kuma ba su kawo karfi ba, bisa haka dole suna bukatar madafa. A nan, sai mu ce gwamnatin Sin ta yi tunani mai kyau. Kundin rahoton ya kuma bayyana cewa, a shekarar 2025 gwamnatin kasar za ta kara zage damtse wajen raya kauyukan dake rabe da birane da gyara gine-ginen da suka tsufa. Ga duk wanda yake shiga yankunan kauyuka da ke cikin birane (kamar unguwannin masu karamin karfi) ko wadanda suke rabe da su zai ga ba su da kyawun gani, domin kayayyakin alatu da kayatattun gine-gine da ababen more...
    Majalisar Wakilai ta umarci Babban Bankin Najeriya (CBN), da ya dakatar da sabon tsarin ƙarin caji kan cire kuɗi ta na’urorin ATM. Wannan umarni ya biyo bayan wata sanarwa da CBN ya fitar, inda ya ƙuduri aniyar fara cajin Naira 100 kan duk cire Naira 20,000 daga ATM a banki, daga ranar 1 ga watan Maris, 2025. Hanyoyi 6 da mutum zai kare kansa daga tsananin zafi Zulum ya bai wa ƙananan ’yan kasuwa tallafin 1bn a Borno Ɗan majalisa Marcus Onobun (PDP, Edo) ne, ya jagoranci ƙudirin da ya buƙaci a dakatar da wannan tsari, inda ya bayyana cewa tsarin zai ƙara jefa ’yan Najeriya cikin wahala. Ya bayyana cewa, a shekarar 2019, an rage cajin cire kuɗi ta...
    Wata kungiyar kare hakkin bil’adama a kasar Bahrain ta bayyana cewa, gwamnatin kasar ta kara yawan kama mutane yan adawa daga ciki har da yara kanana saboda shiga cikin zanga-zanga, ko kuma bayyana ra’ayinsu na siyasa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kungiyar kare hakkin bil’adama ta ” The Americans for Democracy & Human Rights in Bahrain (ADHRB), ta kuma kara da cewa, bayan afwar da gwamnatin Bahrain ta yi wa yan adawar kasar kimani 1,584 a cikin watan Afrilun shekara ta 2024 da ya gabata, daga ciki har da yara 40, amma daga baya ta fara kama yan adawan tana  tsaresu. Suna kama dukan wanda ya nuna  kiyyarsa, ko ya bayyana ra’ayinsa na siyasa, ko kuma...
    Shugaban kwamatin duba rabon abincin azumi na majalisar dokokin jihar Jigawa a shiyyar Dutse kuma mataimakin Shugaban Majalisar, Alhaji Sani Isiyaku Abubakar ya bukaci masu aikin dafa abincin a karamar hukumar Gwaram da su dauki wannan aiki a matsayin turbar samun lada daga Allah Madaukakin Sarki ba wai hanyar neman riba kadai ba. Alhaji Sani Isayku Abubakar ya yi wannan kiran ne lokacin da ya jagoranci Yan kwamatin domin duba aikin dafawa da kuma rabon abincin azumi a unguwar Sabon Layi da ke karamar hukumar Gwaram. Ya ce rangadin duba rabon abincin azumi na daga aikin majalisa na duba ayyuka da shirye-shiryen gwamnati domin tabbatar da inganci da kuma shugabanci nagari. Alhaji Sani Isayku Abubakar tare da Yan kwamatin sun...
    Jami’ar kula da manufofin ketare ta Tarayyar Turai, Kaya Kalas, ta tabbatar da cewa, EU za ta iya sake kakaba takunkumi kan kasar Syria, idan aka samu tabarbarewar lamurra, tana mai nuni da yadda ake cin zarafin fararen hula a gabar tekun Syria. Kaya Kalas ta shaidawa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya cewa, “Muna shirye-shiryen mayar da takunkumi kan Syria, idan muka ga tabarbarewar lamurra na ci gaba, inda ta jaddada cewa, dole ne mika mulki ya kasance cikin lumana da kuma hadin kai, kuma dole ne a kare fararen hula a kowane hali.” Ta bukaci dukkan masu ruwa da tsaki na waje da su mutunta hadin kan Syria, da kuma iko da iyakokinta.”
    Alamomin cutar sun haɗa da ciwon kai mai tsanani, ciwon wuya, tari, da amai. Yaɗuwar cutar a Kebbi na iya shafar sauran jihohin da ke maƙwabtaka da ita, musamman Zamfara, Sakkwato, da Neja, inda ake yawan tafiye-tafiye tsakanin jihohin. Hakan na nuni da buƙatar gaggauta ɗaukar matakan kariya don hana cutar yaɗuwa zuwa sauran yankuna. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Tare da cewa Rasha ta sanar da kakkabo jiragen sama marasa matuki fiye da 60 da Ukiraniya ta harba, sai dai an sanar da mutuwar mutum daya a birnin Moscow. Kantoman yankin Moscow  Andrey Vorobyov ne ya sanar da cewa mutum daya ya rasa ransa yayin da wasu 3 su ka jikkata, sanadiyyar hare-haren da Ukiraniya ta kai wa birnin da makamai masu linzami masu yawa da safiyar yau Talata. Kantoman Mascow ya rubuta a shafinsa na “Telegram’ cewa; “ ya zuwa yanzu an sami labarin mutuwar mutum guda da kuma jikkata wasu 3 a garin Fidnoveh a kudancin Moscow.” Sai dai daga baya wasu kafafen watsa labarun Rasha sun ambaci cewa adadin wadanda su ka jikkata din ya karu...
    Hukumar da take fada da yi wa tattalin arzikin kasar Najeriya ta’annatii ta kwato da kudaden da sun kusa dalar Amurka miliyan 500. Haka nan kuma hukumar ta kwato man fetur da  sauran dangoginsa da sun kai  ton 931,000, sai kuma gidajen da sun kai 975. A cikin rahoton da ta fitar a ranar litinin hukumar ta  EFCC ta bayyana cewa,  ta sa an hukunta masu laifi har su 4,000 wanda shi ne adadi mafi girma tun kafa ta. Tuni an zuba wasu kudaden da aka kwato a cikin ayyukan gwamnati. A karshen rahoton hukumar  “Transparency International” ta bayyana Najeriya a matsayin kasa ta 140, a jerin masu fama da cin hanci da rashawa, bayan da a baya ta kasance...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya yi Allah-wadai da matakin da gwamnatin Amurka ta dauka na haramtawa  al’ummar Iraki ‘yancinsu na samun wutar lantarki, da ma wasu ababen more rayuwa. “Muna tare da al’ummar Iraki, kuma mun tabbatar da alkawarinmu ga gwamnatin Iraki na ba da hadin kai wajen tinkarar matakan da Amurka ta dauka ba bisa ka’ida ba,” in ji Araghchi a wani sakon da ya wallafa a shafin X. Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto wani babban jami’an makamashi  a kasar Iraki yana cewa, a halin yanzu Iraki ba ta da wasu hanyoyin da za su maye gurbin makamashin da ake shigowa dashi  daga kasar Iran, lamarin da zai haifar da babban kalubale wajen biyan bukatar wutar...
    Kimanin fararen hula 1,000 ne aka kashe tare da jikkata wasu daruruwa a hare-haren jiragen yaki marasa matuki a nahiyar Afirka, yayin da ake ci gaba da yin amfani da jirage marasa matuka a nahiyar. A cewar jaridar The Guardian, masu sharhi da nazari na cewa , daga shekara ta 2021 zuwa 2024, jami’an tsaro a kasashe daban-daban na nahiyar Afirka sun yi amfani da jiragen yaki marasa matuka wajen kai hare-hare, wanda kuma sau tari ana kashe fararen hula ne, maimakon masu aikata laifuka. Dole ne wannan ya kawo karshe, kuma dole ne kasashen duniya su dauki matakai da suka dace waje saka kaidoji kan amfani da jiragen yaki marasa matuka, domin rashin yin hakan zai ci gaba da...
    UNRWA ta yi kira ga Isra’ila da ta kawo karshen hana shigar da kayan agaji a zirin Gaza domin dakile bazuwar yunwa da wahala a yankin. “Mun riga mun ga alamun farko na karin farashi a kasuwa,” in ji Kwamishinan UNRWA Philippe Lazzarini yayin taron manema labarai a wannan Litinin, ya kara da cewa yayin da lokaci yake kara kurewa, tasirin haramcin yana karuwa a Gaza. Lazzarini ya kara da cewa “akwai hadarin komawa ga yanayin da muka fuskanta watannin da suka gabata, game da kara yaduwar yunwa a tsakanin mutanen  zirin Gaza sakamakon matakan da Isra’ila take dauka. “Isra’ila” ta sanar da dakatar da isar da kayayyakin jin kai zuwa Gaza a ranar 2 ga Maris, tare da yin...
    Kamfanin Man Fetur na Najeriya NNPC ya ce yarjejeniyar da ya ƙulla da Matatar Dangote domin sayar mata da ɗanyen man fetur a farashin naira za ta ƙare a wannan wata na Maris. Sai dai kamfanin ce yana tattaunawa da Matatar Dangote domin tsawaita yarjejeniyar sayar mata da ɗanyen mai a naira. An hana tashe bana a Kano — Nalako NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da ke Shirin Faruwa A Fagen Siyasar Najeriya Sanarwar ta NNPC na zuwa ne bayan wasu rahotonni sun ce kamfanin ya dakatar da sayar wa matatar mai a farashin naira, kamar yadda suka ƙulla yarjejeniya tun da farko. Wata sanarwa da mai magana da yawun kamfanin Olufemi Soneye ya fitar a ranar Litinin ta ce ba...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya soki matakin da sabuwar gwamnatin Amurka ta dauka na janye sassaucin da ta yi wa Iraki na shigo da wutar lantarki daga Iran. Araghchi ya bayyana matakin da gwamnatin Trump ta dauka a matsayin “abin takaici.” Ya kara da cewa gwamnatin Amurka ta na kokarin hana al’ummar iraki samun ababen more rayuwa kamar wutar lantarki, musamman gabanin watanni masu zafi na wannan shekara.” Babban jami’in diflomasiyyar Iran ya sake jaddada goyon bayan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ga al’ummar Iraki. Ya kara da cewa Iran ta tsaya tsayin daka kan kudurin ta ga gwamnatin Iraki na dakile ayyukan Amurka da suka sabawa doka. Kalaman Araghchi sun zo ne bayan da Amurka ta sanar da...
    Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta bayyana cewa tattaunawa tare da barazana ba tattaunawa ake kiransa ba, sai dai tursasawa. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmael Baghaie  ya na fadar haka a yau litinin a jawabin mako-makon da ya saba gabatarwa a ko wace ranar litinin. Baghaei ya kara da cewa JMI ba zata taba tattaunawa da Amurka tare da barazana da kuma takurawa kasar da takunkuman tattalin arziki ba.  Zabin tattaunawa ko kuma yaki, ba  tattaunawa sai dai tursasawa. Kafin haka dai shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana cewa JMI ba ta da zabi, ko ta shiga tattaunawa da Ita Amurka ko kuma ta shiyawa yaki. Kakakin ma’aikatar...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya ce shirin makamashin Nukliyar kasar Iran, na zaman lafiya ne, kuma babu wani shiri na samar da makaman Nukliya a cikinsa, sannan ya kara da cewa Iran ba za ta taba shiga tattaunawa da kasar Amurka mai cin zalin wasu kasashe ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Aragchi ya na fadar haka a shafinsa na X a yau Litinin, ya kuma ce wannan ita ce martanin Iran a kan sakon da Amurka ta ce aikawa jami’an gwamnatin kasar Iran, na cewa su zabi tattaunawa ko yaki. Kafin haka Jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya bayyana hakan, ya kuma kara da cewa, kasashen yamma musamman...
    Manya-manyan Jiragen ruwan yaki na kasashen Rasha da China sun isa tashar Jeragen ruwa ta Chabahar dake kudu maso gabacin kasar Iran a bakin tekun india don fara atisayen soje a tsakanin kasashen uku, wanda aka sanyawa suna ‘damarar tsaro na shekara ta 2025. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa wannan gagarumin atisayen sojojin ruwa tsakanin manya-manyan kasashen guda uku zai sami halattan wasu kasashe da dama a matsayin masu kallo. Labarin ya kara da cewa manya-manyan jami’an sojojin ruwa na sojojin Iran da kuma na dakarun IRGC ne suka tarbi jiragen ruwan yaki na wadannan kasashe. Sannan ana saran wakilai daga kasashen Azerbaijan, Iraki, Kazakhstan, Oman, Pakistan, Qatar, Afirka ta Kudu, Sri Lanka da Haddiyar...
    Jakadan kasar Rasha na din din din a cibiyoyin MDD da suke Vienna, ya bayyana cewa dakatar da aiwatar da yarjeniyar shirin Nukliya na kasar Iran wanda ake kira JCPOA, wacce kuma aka samar da shi a shekara ta 2015, da kasashen yamma suka yi, shi ne ya haddasa dukkan matsalolin da suka biyo baya. Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto, Mikhail Awliyonov yana fadar haka a hirar da ta hada shi da jaridar Ezustiyo na kasar Rasha. Jakadan ya kara da cewa a tsakanin shekara ta 2021 da kuma 2022 an tattauna da kasashen yamma kan yadda za’a aiwatar da yarjeniyar JCPOA da kasashen bayan da kasar Amurka ta fice daga yarjeniyar a shekara ta 2018,...
    Jam’iyyar APC ta yi kira ga Gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara da ya sauka daga mulki ko kuma a tsige shi. Shugaban APC na Jihar Ribas, Tony Okocha ne ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai yau Litinin a birnin Fatakwal. An cafke mutum uku kan satar wayoyin lantarki a Adamawa Abin da ya sa na sauya sheƙa daga APC zuwa SDP — El-Rufai Okocha ya ce gayyatar da Fubara ya aika wa ’yan majalisar dokokin jihar domin ya gana da su akwai lauje cikin naɗi. “Hukuncin Kotun Ƙoli ne ƙarshe babu wani abu da wani zai iya yi. Abun da ya rage wa gwamnan shi ne ko dai ya sauka, ko kuma a tsige shi,” in ji Okocha. Tun...
    An haife shi a ranar 21 ga Fabrairu, 1949, kuma ya yi karatu a Jami’ar Ohio da ke Athens a Amurka, a 1981, da Jami’ar Leicester ta ƙasar Birtaniya a 1987.   Ya yi aiki a kamfanin jaridun New Nigerian, da hukumar talbijin ta NTA, da Ofishin Yaɗa Labarai na Amurka (USIS). Haka kuma ya yi koyarwa a Kaduna Polytechnic, ya yi aiki a Bankin Arewa da kuma Bankin Union inda a nan ya yi ritaya a ranar 26 ga Yuni, 2005.   A cikin saƙon ta’aziyyar sa a ranar Asabar, Minista Idris ya bayyana rasuwar Malam Kabir Ɗangogo a matsayin babban rashi ga Nijeriya da fannin sadarwa a nahiyar Afirka.   Ya ce: “Mutuwa ta ƙwace mana ƙwararren ma’aikaci...
    Shugaba Masoud Pezeshkian ya ce manufar Iran ta ginu ne kan  samar da hadin kai a yammacin Asiya, kamar yadda kuma ta yi imanin cewa duk wani rikici da tashin hankali a yankin to zai illata kowa. Pezeshkian ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da Firaministan Norway Jonas Gahr Støre a yammacin waannan Lahadi, inda suka tattauna kan muhimman batutuwa ad suka shafi alaka tsakanin kasashen biyu, da kuma sauran batutuwa na yankin da kuma na kasa da kasa. Shugaban na Iran ya kara da cewa, Haramtacciyar Kasar Isra’ila na neman yada karya dangane da batun ayyukan nukiliyar Iran  a matsayin tushen rashin tsaro a yankin. Har ila yau ya jaddada cewa Iran ba ta taba...
    Assalamu alaikum masu sauraro sharhin bayan labarammu zai yi magana dangane da ‘Korar sojoijin Faransa daga kasa ta 7 a yammacin Afirka tare bukatar’ macron ya nemi uzurin kasashen’ wanda ni tahir amin zamn karanta. ///…Madalla, Bayan da kasashen Mali da Burkina faso, da Nigerda Ivory Coast suke kori sojojin Faransa daga kasashensu, a yanzun kuma kasar Senegal ta bada sanarwan korar sojojin kasar Faransa daga kasar. Tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar Mali da kuma korar sojojin kasashen waje, daga cikin har da sojojin kasar Faransa da kuma na Majalisar dinkin duniya daga kasar, daya bayan daya kasashen yankin yammacin Afirka kuma tsoffin kasashen da Faransa tayiwa mulkin mallaka suka suka fara korar sojojin faransa...