2025-02-21@14:26:01 GMT
إجمالي نتائج البحث: 142

«yarjejeniya»:

    Jami’an diblomasiyya da dama daga kasashen kungiyar G20 ne suka isa birnin Johannesburg na kasar Afirka ta kudu, don halattar taro na kwanaki biyu. Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov ya isa birnin Johannesburg a jiya Alhamis kwanaki biyu kacal da ya gana da tokwaransa na kasar Amurka a birnin Riyad na kasar Saudiya....
    Jimi’in ofishin siyasa na kungiyar jihadul-Islami ya bayyana cewa: Marigayi Sayyid Hasan Nasrallah ya baiwa Falastinu da gwagwarmaya abin da harshe ba zai iya siffanta shi ba Mamba a ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmaya ta Jihadul-Islami ta Falasdinu Ihsan Ataya ya yaba da irin tsayin dakan da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi a...
    Motocin bas-bas guda uku sun tarwatse a birnin Tel Aviv, lamarin da ya haifar da rudani a tsakanin yahudawan sahayoniyya Motocin bas-bas guda uku sun fashe da yammacin jiya Alhamis a wurare daban-daban a yankin Bat Yam da ke kudancin birnin Tel Aviv a tsakiyar haramtacciyar kasar Isra’ila. Kafofin watsa labaran haramtacciyar kasar Isra’ila sun...
    Gwamnatin jihar Jigawa ta yi alkawarin ci gaba da gudanar da ayyukan kiwon lafiya da aka gudanar karkashin hadin gwiwarta da Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF), da shirin samar da rigakafin cututtuka a kasashe masu tasowa(GAVI) a cikin shekaru uku da suka gabata. Haɗin gwiwar wanda aka fara shi da...
    Kamfanin mai na kasar Sin (CNPC) ya sanar a yau Alhamis cewa, ya kammala aikin hakar rijiyar man fetur mafi zurfi a yankin Asiya, yayin da rijiyar ta kai zurfin mita 10,910 a hamadar arewa maso yammacin kasar Sin. Rijiyar wacce aka fi sani da “Shenditake 1” da ke tsakiyar hamadar Taklimakan a cikin kwarin...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta mika gawawwakin mutum hudu ‘yan Isra’ila ga kungiyar agaji ta Red Cross. Mutanen dai Isra’ila ta kasha su a cikin wadanda Hamas ta yi garkuwa da su lokacin kai hare-hare a Gaza. Kungiyar agaji ta Red Cross ta nufi wani wuri a Gaza domin karbar gawawwakin ‘yan Isra’ilan hudu...
    Gidauniyar Tunawa Da Sir Ahmadu Bello Za Ta Gudanar Da Taronta Karo Na 11 A Bauchi.Gidauniyar Tunawa da Sir Ahmadu Bello ta sanar da cewa za ta gudanar da bikin tunawa da Sir Ahmadu Bello na shekara karo na 11 a ranar Litinin, 24 ga Fabrairu, 2025, a Bauchi, Jihar Bauchi. Taron, wanda aka shirya...
    Jarin da kasar Sin ke zubawa wajen inganta lafiyar muhalli mai dorewa a duniya ya nuna muhimmiyar rawar da take takawa ta wannan fuskar. A shekarar 2024, kasar ta jagoranci duniya wajen zuba jarin sauya makamashi, inda ta zuba dalar Amurka biliyan 818 a wannan bangare. Wannan jarin ya sanya kasar Sin ta zama cibiyar...
    Kungiyar manyan sakatarorin ma’aikatun jihar Zamfara(ZASPEF) ta sha alwashin ci gaba da bayar da shawarwari don inganta iyyuka da sha’anin mulki. Zababben shugaba Malam Yakubu Sani Haidara ne ya bayyana hakan a lokacin kaddamar da su a matsayin sabbin shugabannin kungiyar a Gusau. Yakubu Sani Haidara ya bayyana cewa, yayin da ma’aikatan gwamnati ke...
    Shugaban kungiyar Hamas Khalilul-Hayyah, ya fadi cewa; A ranakun Alhamis da Asabar masu zuwa ne za a mikawa ‘yan mamaya fursunoni rayayyu da kuma wasu gawawwaki a cikin bude wani shafin na musaya.  A jiya Talata ne dai Khalilul-Hayyah ya sanar da cewa, a bisa yadda aka cimma matsaya a musayar farko da aka yi,...
    Dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran sun sanar da gano da kuma rusa wata kungugun masu yi wa Amurka da Isra’ila leken asiri a yankin Arewacin Iran. Kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci a yankin Mazandaran dake arewacin Iran ne ya sanar da bankado da kuma rusa gungun masu yi wa abokan...
    Sakataren harkokin waje na kasar Amurka Marco Rubio ya bayyana cewa kasashen Amurka da Rasha sun kuduri anniyar kawo karshen yakin Ukrai, banda haka zasu kara kyautata dankon zumunci da tattalin arziki a tsakaninsu. Shafin yanar gizo na labarai, Arabnews ta gwamnatin kasar Saudiya ya bayyana cewa, ya nakalto Rubio yana cewa kasashen biyu sun...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci A nan Iran Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya gana da shuwagabannin kungiyar Jihadul Islami na kasar Falasdinu da aka mamaye a jiya Talata. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ya bayyana cewa Ziyad Nakhalah shugaban kungiyar ne ya jagoranci tawagar kungiyar zuwa ganawa da jagoran. Labarin ya nakalto Jagoran...
    Gwamnatin Jumhuriyar Nijer daga jiya Talata ta fara aikin hana yan Najeriya dauke da Passport na kungiyar ECOWAS shiga kasar. Kafin haka dai mutane daga kasashen ECOWAS suna shiga kasashen kungiyar ba tare da bukatar visar shiga ko wace kasa daga cikin kasashe kungiyar ba. Amma bayan da kasashe 3 Nijer, Burkina Faso da kuma...
    Tara Daga N100,000 Kan Amfani Da Mitar Wutar Lantarki Ta Ɓarauniyar Hanya – NERC
    Jaridar Ma’ariv ta Isra’ila ta bayyana adadin wadanda suka jikkata a cikin sojojin mamayar Isra’ila da kuma miliyoyin yahudawan sahayoniyya da suka samu matsalar tabin hankali a lokacin yakin Gaza Jaridar “Ma’ariv” ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta bayyana a jiya litinin, adadin wadanda suka mutu a cikin jerin sojojin mamayar Isra’ila a yayin mummunan ayyukan...
    Kula da walwalar maniyyatan Najeriya ya shiga tangal-tangal bayan wani kamfanin kula da alhazai na kasar Saudiyya ya yi barazanar maka Najeriya a Kotun Hukunta Manyan Laifuka na Duniya (ICC), kan saba yarjejeniyar kwangilar aikin Hajji. Kamfanin Mashariq Al Dhahabiah Al Mutawazi na kasar Saudiyya, wanda Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) da Hukumomin Jin...
    ’Yan sanda sun yi nasarar kama wasu mutane biyu da ake zargi da laifin yi wa wata yarinya ‘yar shekara 12 fyaɗe a kauyen Jalingo da ke Ƙaramar Hukumar Tarmuwa a Jihar Yobe. Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Dungus Abdulkarim, ya fitar a Damaturu ranar Litinin....
    Kungiyoyin Hamas, Jihad Isalami da kuma sauransu a kasar Falasdinu da aka mamaye sun bayyana yi allawadi da HKI saboda yadda suke zazabtar da fursinonin Falasdinawa a gidan yarin Ofer, kamar yadda labari ya ke isa daga ca. Tashar talabijin ta Presstv  na takalto cewa gidan yarin ofer ya na yammacin birnin Ramallah, a...
    Najeriya ta nuna adawa da wani yunkuri na sake fasalin Sashen Harkokin Siyasa, Zaman Lafiya da Tsaro na Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) (PAPS), saboda damuwa game sanadin da ka iya tabarbarewar hanyoyin zaman lafiya da siyasa na kungiyar. Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Ambasada Yusuf Tuggar ne ya sanar da wannan matsayi a madadin Shugaba Bola...
    Kungiyar Tarayyar Afirka ta yi Allah Wadai da duk wani Shirin tilastawa Falasdinawa gudun hijira daga muhallinsu Batun neman tilastawa Falasdinawa gudun hijira daga kasarsu ta gado yana ci gaba da fuskantar tofin Allah da Allah wadai a duk fadin duniya da kuma a taruka daban-daban, kuma batun Falasdinu shi ne kan gaba a ajandar...
    Ƙasashen da suke da saukin cin hanci a duniya Mafi yawan kasashen da rahoton ya nuna cewa babu yawaitar matsalar cin hanci da rashawa suna a nahiyar Turai ne. Bakwai daga cikin kasashen 10 na farko, wadanda ba su da matsalar Rasha duk a yankin Tarayyar ta Turai suke. Qasar da ta fi kowace a...
    Ya ce wajibi ne Sin da Amurka su kauracewa rikici, idan ba haka, duniya ce za ta wahala. Sannan ya yi kira da a karfafa tattaunawa da inganta fahimta da karfafa aminci. Ya ce kamata ya yi kasashen biyu su hada hannu wajen shawo kan kalubalen duniya, domin hakki ne da ya rataya a kan...
    Ministan kudi da tattalin arziki na kasar Iran yana kan hanyarsa ta zuwa kasar Saudiya don halattar wani taro mai muhimmaci na tattalin arziki. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan tattalin yana fadar haka a shafinsa na X, ya kuma kara da cewa, yana zuwa wannan taron ne tare da gayyar...
    Sojojin HKI sun kaseh Falasdinawa 4 a yankin yamma da kogin Jordan a lokacinda suke fadada hare-haren da suke kaiwa kan falasdinawa wanda kuma yake daukar rayukar Falasdinawa a yankin. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jaridar WAFA ta falasdinwa wacce ta nakalti majiyar ma’aikatar kiwon lafiya a yankin tana cewa sojojin...
    Duk da kasancewar Malam Murtala Abubakar nakasasshe mara kafafu, amma bai lamunci yin bara ba. Hasali ma, ya rabu da matarsa ta fari saboda dabi’arta ta yin bara. Shekaru 50 da suka wuce Malam Muratala ya rasa kafafunsa, tun yana dan shekara bakwai a duniya. A haka ya ci gaba da rayuwarsa, inda a halin...
    Shugaban Kungiyar Yarbawa zalla ta Afenifere, Pa Ayodele Adebanjo ya rasu yana da shekara 96. Rahotanni sun ce dattijon ya rasu ne da safiyar Juma’a a gidansa da ke Lekki a Jihar Legas. An tabbatar da rasuwarsa a wata sanarwa da iyalansa suka fitar. Fursunoni 3 sun lashe Gasar Al-Ƙur’ani a Kano Ta kacame tsakanin...
    Wasu fursunoni uku da ke tsare a gidajen yari daban-daban sun lashe Gasar Musabakar Al-Kur’ani da aka gudanar a Jihar Kano. Fursunoni sun lashe gasar da Hukumar Kula da Gidajen Yari ta Jihar Kano ta shinrya a matsayin wani bangare na tsarin ilimin fursunoni. An shirya musabakar ce da nufin sauya tunanin fursunoni domin su...
    Kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ) karkashin jagorancin shugaban kasa Alhassan Yahaya, ta jaddada aniyar ta na inganta aikin jarida da kuma jin dadin ‘yan jarida a fadin Najeriya.   Kungiyar tana aiki tukuru don ganin an zartar da kudurin dokar inganta kafafen yada labarai a majalisar dokokin kasar don karfafa masana’antar.   A cikin...
    Gwamnatin jihar Kwara ta ware naira biliyan 5 domin inganta cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko guda 70 a kananan hukumomin uku na jihar.   Babban Sakatariyar Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko ta Jihar Kwara (KWHCDA), Farfesa Nusirat Elelu ce ta bayyana haka a lokacin rattaba hannu kan kwangilolin da aka yi a...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi gargadin cewa makiya kasarsa suna neman murkushe al’ummar kasar  ta hanyar takunkumi da barazana. Pezeshkian ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ta yi da masana da masu fada aji na lardin Bushehr da ke kudancin kasar a ranar Alhamis , inda ya ce “Makiya suna son...
    Tawagar ta tattaro hukumomi da suka hada da hukumar kula da yanayi (NiMET), hukumar kula da ayyukan ruwa, da hukumar bada agajin gaggawa ta kasa karkashin kulawar ofishin mataimakin shugaban kasa. Wannan yana tare da hadin gwiwar ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai kula da ayyukan jin kai (OCHA).   A duk duniya, OCHA, wacce ke...
    Ƙungiyar Malaman Makarantu ta Ƙasa (NUT) da Ƙungiyar Ma’aikatan Ƙananan Hukumomi ta Ƙasa (NULGE), sun umarci malaman makarantun firamare da ke ƙarƙashin Sashen Ilimin Ƙananan Hukumomi (LEA) da su sake tsunduma yajin aiki. Haka kuma an umarci ma’aikatan ƙananan hukumomi shida na Babban Birnin Tarayya, da su dakatar da aiki daga ranar Alhamis, 13 ga...
    Babbar Kotun Jiha ta 5 a Gombe, ƙarƙashin Jagorancin Mai Shari’a A.M. Haruna, ta yanke wa wani matashi mai suna Abdullahi Suleiman hukuncin sare masa hannu, bisa samunsa da laifin sare hannun wani yaro mai suna Khalifa Abubakar, ɗan shekara 14 da adda. Lamarin ya faru ne a ranar 12 ga watan Fabrairu, shekarar 2022,...
    Kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hamas ta sanar da cewa, za a ci gaba da musayar fursunoni kamar yadda aka tsara a karkashin yarjejeniyar da aka cimmawa. A yau Alhamis ne dai kungiyar ta Hamas ta sanar da  cewa za ta saki fursunoni kamar yadda yake a jadawalin da aka tsara. Tashar talabijin din Aljazira ta...
     Mutanen Najeriya suna  bayyana fushinsu akan kara kudaden sayen cajin shiga kafar sadarwa na Internet –Data- da manyan kamfanoni irin su MTN da Airtel su ka yi, saboda yadda ake fama da matsalar rayuwa. Kamfanin MTN shi ne mafi girma a tsakanin kamfanonin samar da hidimomi na hanyar sadarwa, inda a yanzu ake sayar da...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewa: Karfin kariyar Iran abin alfahari ne ga kawayenta yayin da makiyanta suke kara tsoro Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya dauki wannan batu na kare al’umma da tsaron kasar a matsayin muhimmin abu, ya kuma ce: Karfin tsaron da Iran take...
    Kungiyar Hamas ta yi kira ga ƙungiyoyin duniya da su fitar da matsayinsu a ranakun Juma’a da Asabar da kuma Lahadi don yin watsi da batun neman tilastawa Falasdinawa yin hijira daga Zirin Gaza Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta yi kira ga al’ummar Falastinu, al’ummar Larabawa da al’ummar musulmi da dukkan ‘yantattun kasashe a...
    An bude babban taron majalisar gudanarwar kungiyar tarayyar Afirka, watau AU karo na 46, a hedkwatar kungiyar da ke Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, inda taron ya jaddada bukatar gaggauta karfafa kokarin da ake yi na bunkasa ci gaban nahiyar, da kwanciyar hankali. Taron na kwanaki biyu, wanda ya kunshi ministocin harkokin waje na mambobin kungiyar ta AU,...
    A yau Laraba, kafar yada labarai ta CGTN ta hada gwiwa da tashar watsa labarai ta lardin Heilongjiang na kasar Sin ta kamfanin CMG, wajen shirya wani bikin musayar al’adu na kasa da kasa, wanda ya shafi gasar wasannin kankara ta nahiyar Asiya dake gudana a Harbin, gami da bikin fitilu na gargajiyar kasar Sin....
    Taro kan fasahar kirkirarriyar basira ta AI da ya gudana a Paris na Faransa, ya ja hankalin duniya. Masu rattaba hannu 61 ciki har da Faransa da Sin da India, sun fitar da wata sanarwa cewa za su nace wajen raya wannan fasaha bisa ka’ida ba tare da rufa rufa ba, kuma ta kowane bangare....
    Hukumar kula da ‘yan sama jannati na kasar Sin (CMSA), a yau Laraba, ta bayyana sunayen tufafin ‘yan sama jannati da motar zirga-zirga a duniyar wata na aikin binciken wata na kasar. CMSA ta ce, an sa ma tufafin na ‘yan sama jannati suna Wangyu, wanda ke nufin kallon duniyar sama, kuma ya yi daidai...
    Kungiyar Hamas a Gaza ta godewa kasashen duniya musamman kasashen Jordan da Masar dangane da kin amincewarsu da korar Falasdinawa a Gaza. Kafin haka dai shugaban kasar Amurka Donal Trump ya ce zai kwace zirin Gaza daga hannun Falasdinawa, sannan zai tsugunar da su a kasashen Masar da kuma Jordan, suna so ko basa so....
    Iran ta yi kakkausar suka kan barazanar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi na yin amfani da karfi a kan kasar, inda ta bayyana hakan a matsayin barazana da rashin da’a. A cikin wata wasika da ya aike a wannan Talata zuwa ga shugaban Majalisar Dinkin Duniya da shugaban kwamitin sulhu na dindindin jakadan...
    Kungiyar Tarayyar Afirka ta bayyana cewa: Sudan ce kasar da aka fi fama da matsalar jin kai a duniya A zaman tattaunawa da Kungiyar Tarayyar Afirka ta gudanar ta bayyana yakin basasar Sudan a matsayin “mafi girman matsalar jin kai a duniya,” inda ta yi gargadin irin mummunar illar da yake yi kan fararen hula,...
    Masu fafutikar kare haƙƙin bil Adama da ƙwararru a fannin kiwon lafiya haɗi da fasihai a ɓangaren shari’a sun buƙaci a tsananta hukunci kan masu yi wa mata kaciya a Nijeriya. Masu ruwa da tsakin sun yi kira da a ƙara wayar da kan al’umma domin ganin an daƙile kaciyar mata gaba ɗaya a ƙasar...
    Shugaban Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya gargaɗi Hamas da ta yi gaggawar sakin Isra’ilawan da take tsare da su a hannunta. Netanyahu ya ce ya bai wa ƙungiyar wa’adin zuwa ranar Asabar da ta saki Isra’ilawan da take garkuwa da su kamar yadda aka amince a yarjejeniyar tsagaita wuta da ke tsakaninsu ta tanada. Gwamnatin Kano...
    Har kullum, na kan ce, ci gaban kasar Sin wata dama ce ba kalubale ba. A matsayin ’yar Afrika, ci gaban kasar Sin daidai yake da ci gaban nahiyar Afrika domin duk wata nasara da ta samu, ba ta kyashin kai wa Afrika, kuma burinta shi ne ta ga nahiyar ta amfana, ta samu ci...
    Kungiyoyin da suke dauke da makamai sun kashe fararen hular da ba su gaza 55 ba a wani hari da su ka kai wa wasu kauyuka da sansanin ‘yan hijira a Arewacin DRC. Mahukunta a yankin na Arewacin DRC sun ambaci cewa wasu masu dauke da makamai na kungiyar CODECO sun kai wa wasu kauyuka...
    Abin Kunya Ne Nijeriya Har Yanzu Ba Ta Iya Ciyar Da Kanta – Gwamna Bala