2025-04-13@08:59:06 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1923

«Janar Tsiya»:

      Amfanuwa Da Mamakon Arziki Da A Ka Yi Mana Baiwarsu Babu shakka, mutuwar zuciya ce ta mai da jama’ar wannan Kasa tamu ta Nijeriya dogara kacokan da sabgar man fetur, a matsayin wata hanya daya tilo da za ta rika samar mana da sama da kashi tamanin ga tattalin arzikinmu na Kasa!. Hakika akwai...
    An gurfanar da wani mutum a gaban Kotun Majistare ta 17 a Kano bisa zargin shi da karɓar kuɗi a hannun wasu fursunoni da alƙawarin cewa zai fitar da su daga gidan yari. Ana zargin wanda ake tuhumar, Kabiru Ahmed, da karɓar jimillar kuɗi naira dubu dari shida da goma daga Abdul Mukhtar, Bilkisu Shehu...
    Fira ministan HKI Benjamine Netanyahu ya yi suka cikin fushi saboda Fira ministan kasar Mark Carney  Canada ya bayyana cewa abinda yake faruwa a Falasdinu kisan kiyashi ne. Shi dai Fira ministan kasar Canada Mark Carney wanda ya halarci taron yankin neman zabe a garin Calgary, yayin da wani daga cikin mahalarta, ya daga murya...
    Mahukunta a kasar Syria sun kafa dokar hana zirga-zirga a yankin Dar’a dake kudancin kasar Syria. Tashar talabijin din ‘almayadin’ ta ambato cewa; jami’an tsaron kasar ta Syria sun kafa dokar ta baci a yankin “Basra-sham’ dake yankin Dar’a. Sai dai har yanzu babu wani cikakken bayani akan dalilin da ya sa aka kafa wannan...
    Kazalika, a wani binciken kwanan baya na gama gari kan yawan alummar kasar, ya gano cewa, kaso 53 na wasu matasan kasar, a kullum suna rungumar wannan dabi’ar. Sai dai, muna sane da cewa, wasu ‘yan Nijeriya, na kallon yin cacar tamkar wata aba ce, ta nishadi kawai, amma wasu bincike sun bayyana cewa, wani...
    Ana fargabar matafiya da dama sun rasu bayan kifewar wani  kwalekwale ɗauke da ’yan kasuwa a yankin Kogin Neja. Hatsarin kwalekwalen ya auku ne ƙauyen Sokun da ke yankin Ƙaramar Hukumar Lapai, a sakamakon iska mai ƙarfi da ta haddasa juyawar igiyar ruwan. Shaidu sun ce hatsarin ya auku ne a yayin da kwalekwalen ke...
    Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta yi hasashen za a yi ruwan sama mai ƙarfi da ambaliya a jihohi 30 da kuma babban birnin tarayya Abuja. Jihohin da ake fargabar fama da ambaliyar ruwan sun haɗa da: Abia, Adamawa, Akwa Ibom, Anambra, Bauchi, Bayelsa, Benue, Borno, Cross-Riɓer, Delta, Ebonyi, Edo, Gombe, Imo, Jigawa, Kebbi, Kogi, Kwara, Lagos,...
      Daga nan sai ya ce, kasar Sin na aiwatar da matakan ramuwar gayya na wajibi game da cin zalin Amurka, ba kawai don kare ikon mulkin kanta, da kare tsaro da muradun ci gabanta ba ne, har ma da tabbatar da gaskiya da adalci tsakanin sassan kasa da kasa, da wanzar da tsarin cinikayyar...
    Gwamnatin Yobe ta bayyana shirinta na mayar da tubabbun mayaƙan Boko Haram cikin al’ummarsu da aka yi wa shirin kawar da tsattsauran ra’ayi, gyara da sake haɗewa da iyalansu ƙarƙashin rundunar Operation Safe Corridor (OPSC). Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ne ya bayyana haka a ranar Alhamis a Damaturu lokacin da ya karɓi baƙuncin...
    Wani muhimmin abun lura ma shi ne ita kanta Amurka ba za ta tsira daga mummunan tasirin wannan yaki na cinikayya da take rura wutarsa ba. Ko shakka babu matakin zai haifarwa Amurka matukar koma bayan tattalin arziki, da hauhawar farashi a cikin gida, da dakile guraben ayyukan yi da sauransu. Tuni ma kasuwannin Amurkan...
    Yau Alhamis ranar 10 ga wata, an fara “Ranar Sinanci ta MDD” ta shekarar 2025, wato bikin nuna fina-finan Sinanci na babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin na CMG karo na 5 a hukumance.   An kaddamar da bikin bisa hadin gwiwar CMG da kungiyar wakilan kasar Sin na MDD dake...
    Ƙungiyar Ƙwadago a Jihar Sakkwato (NLC), ta musanta iƙirarin da shugaban ƙungiyar ma’aikatan ƙananan hukumomi ta ƙasa (NULGE), Ali Kankara, ya yi cewa gwamnatin jihar ba ta fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi na Naira 70,000 ba. Shugaban NLC na jihar, Kwamared Aliyu Abdullahi, ya bayyana wa manema labarai a ranar Laraba cewa Gwamnatin Sakkwato...
    Sojojin kasa na kasashen Iran ta Armenia sun fara atisayen soje na hadin guiwa a tsakaninsu, don kyautata tsaro na kan iyakar kasashen biyu na kuma tsawon kwanaki biyu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa dakarun kare juyin juya halin musulunci na kasar Iran ne suke jagorantar wannan atisayen. Da nufin...
    Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bada sanarwan cewa yana kokarin cimma matsaya da kasar Chaina dangane da kamfanin sadarwa da kuma yanar gizo na TIK Tok. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto shugaban yana fadar haka a shafinsa na ‘Trump Social, Labarin ya kara da cewa shugaban yana fadar haka a...
    Sojojin HKI wadanda suka yi ritaya da kuma masu jiran aiki ko Reserv sun watsa wata bukata da suka rubuta ta kawo karshen yakin da Benyamin Natanyahu yake jagoranta a Gaza. Sojojin sun kara da cewa a halin yanzu yakin yana cimma manufar Natanyahu ne kawai, ba don manufar HKI ake yins a ba. Kamfanin...
    Kamfanin Media Trust Limited na farin cikin sanar da al’umma cewa daga ranar Juma’a 11 ga watan Afrilun 2025, Rediyonta na Tusts Radio zai fara shirye-shiryen gwaji. Tashar za ta fara yaɗa shirye-shiryenta a kan mita 92.7 a zangon FM a birnin tarayya Abuja da kewaye, kuma wannan na daga cikin tsare-tsaren da kamfanin ke...
    Wadannan ayyuka domin inganta harkar ilimi da kuma nuna gaskiya, sun sa Jigawa ta zama abin koyi ga sauran jihohi.   Tunda farko, Gwamna Malam Umar Namadi, a nasa jawabin, ya ce gwamnati ta dauki kwakkwaran matakai na magance matsalar rashin ilimi bayan wani bincike da wani masani mai zaman kansa ya fitar cewa, yawancin...
    Ta kara da cewa, “Ta hanyar hada tsarin horaswa na ayyukan masana’antu a cikin tsarinmu na TVET, muna rage gibin rashin kwarewar da bude kofa ga sana’o’i masu kyau a fannin fasahar sadarwa na zamani na Kenya,” (Mai fassara: Mohammed Yahaya) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Yobe ta samu gagarumar nasara a ƙoƙarinta na yaƙi da miyagun laifuka, inda ta cafke wasu fitattun mutane biyu da ake zargi da garkuwa da mutane. Waɗanda aka kama sun haɗa da: Babaro Baushe mai kimanin shekara 40 da Umaru Dau’a, mai kimanin shekara 25 da suka fito daga ƙauyen Askuwari...
    Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya jagoranci wata tawaga zuwa Jihar Edo domin binciko gaskiyar abin da ya faru game da kisan mafarauta ’yan asalin jihar a ƙauyen Uromi. Gwamna Abba Kabir Yusuf ne, ya umarci a kafa wannan tawaga, wacce ta ƙunshi manyan shugabanni irin su Sarkin Rano, Kwamishinonin ma’aikatu da...
      Shugaban na kasar Sin ya kuma yi fatan alheri ga kasashe da jama’ar yankin na Latin Amurka da Caribbean wajen samun manyan nasarori a fannin ci gaba, da farfado da tattalin arziki, ta yadda za su ba da gagarumar gudummawa ga hadin kai da kuma hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa a duniya....
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka Tommy Bruce a cikin wata sanarwa da ya fitar ya bayyana cewa: Ministocin harkokin wajen Amurka da na Saudiyya sun tattauna kan yunkurin diflomasiyya a Gaza na sakin mutanen da aka yi garkuwa da su da kuma samar da tsagaita bude wuta mai dorewa a Gaza inda Hamas ta samu...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakchi ya tattauna ta wayar tarho da takwaransa na Masar Badr Abdelatty, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi yankin. Manyan jami’an diflomasiyyar Iran da Masar sun yi magana ta wayar tarho da yammacin ranar Laraba, a cewar shafin Telegram na kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran. Araqchi ya jaddada muhimmancin...
    Guguwar ruwan sama ya lalata gidaje da dama a ƙaramar hukumar Shanga ta Jihar Kebbi. Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris ya jajanta wa al’ummar Garin Kestu da ke unguwar Atuwo a Ƙaramar hukumar Shanga, ya kuma buƙaci iyalan waɗanda abin ya shafa da su ɗauki lamarin a matsayin wata ƙaddara. Yadda Tinubu ya taimaka wa...
    Jigo a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya bayyana yadda Shugaba Bola Tinubu, ya taimaki ’yarsa ta samu aiki a Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Ƙasa (NUPRC). Galadima, ya bayyana haka ne yayin wani shiri a gidan talabijin na AIT. Matatar Ɗangote ta rage farashin fetur zuwa N865 Yadda masu safarar ɗan Adam ke...
    Jigo a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya bayyana yadda Shugaba Bola Tinubu, ya taimaki ’yarsa ta samu aiki a Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Ƙasa (NUPRC). Galadima, ya bayyana haka ne yayin wani shiri a gidan talabijin na AIT. Matatar Ɗangote ta rage farashin fetur zuwa N865 Yadda masu safarar ɗan Adam ke...
    Al’ummomin Jihar Kastina sun shiga sabon tashin hankali bayan da ’yan bindiga suka kai wasu munanan hare-hare a wasu yankuna biyu a Jihar Katsina a ƙarshen makon jiya, inda suka kashe mutane shida tare da yin garkuwa da wasu 59. A daren Lahadi, kusan ƙarfe 10:30, ’yan bindiga ɗauke da makamai suka kai farmaki ƙauyen...
    Gwamnatin Najeriya ta nuna damuwarta kan yadda masu safarar mutane ke ƙara amfani da kafafen sadarwa na zamani wajen yaudarar mutane da kuma yi musu cin zarafi, inda ta bayyana hakan a matsayin barazana wadda ba ta da iyaka kuma mai saurin yaɗuwa wadda ke buƙatar ɗaukar mataki cikin gaggawa. Da yake jawabi a taron...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa Jagoran juyin juya halin Musulunci na kasar Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ba shi da wata adawa da Amurkawa masu zuba jari a kasar. “Muna maraba da masu zuba jari.” amma ba tare da tauye mutunci ko tsaron kasa ba. Har ila yau kalaman nasa sun sake tabbatar...
    Gwamnatin Washington ta sanar da kakabawa Iran sabbin takunkumai kan shirinta na nukiliya an zaman lafiya, a matakin da Amurka ke ganin shi ne kawai hanyar matsin lamba kan Iran domin ta mika wuya game da shirint ana nukiliya. Takunkumin, wanda ma’aikatar baitul malin Amurka ta sanar a jiya Laraba, ya shafi hukumomi biyar da...
    Kungiyar ci gaban kasashen yammacin Afirka, ECOWAS ta nuna damuwa kan takun-tsakar da ya kunno kai tsakanin kasar Mali da makwafciyarta Aljeriya, lamarin da ya kai ga kasashen biyu janye jakadu a tsakaninsu. A cikin wata sanarwa da ta fitar, Ecowas ta ce “Tana bibiyar abin da ke faruwa wanda ya shafi dangantakar da ke...
    Wannan rikicin haraji ya faro ne tun shekarar 2018, lokacin da Trump ya fara ƙaƙaaba wa China da wasu ƙasashe haraji mai tsanani kan kayayyakin da ake shiga da su Amurka, a wani yunƙuri na kare masana’antu da ayyukan yi a cikin gida. Sai dai masana tattalin arziƙi sun ce wannan mataki zai iya kawo...
    Buhari ya gode wa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu bisa gyaran da aka yi masa a gidansa na Kaduna. Ya gode wa gwamnonin APC da suka kai masa ziyara domin taya shi murnar Sallah, inda ya ce wasu daga cikinsu ya yi aiki tare da su, yayin da wasu kuwa sabbi ne. Shugaban gwamnonin kuma Gwamnan...
    Runduna ta 8 ta sojojin Najeriya ta fara gasar wasanni ta kasa da ake gudanarwa duk shekara a jihar Sokoto da nufin karfafa sojojin Najeriya don shiryawa tsaron kasa.   Babban Jami’in Kwamandan runduna ta takwas Manjo Janar Ibikunle Ajose ya ce gasar tana nuni ne kai tsaye ga hafsan hafsoshin sojin kasar na ganin...
    Lauyan kare hakkin bil’adama Femi Falana SAN ya yabawa jihar Kano bisa yadda take tafiyar da harkokin shari’a.   Falana ya bayyana hakan ne a yayin wani taron karawa juna sani ga masu gabatar da kara kan ingancin gudanar da shari’ar laifuka da Kurawa Hussein And Associates tare da hadin giwar Ma’aikatar Shari’a ta Kano...
    Rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi, ta tabbatar da sace wani dalibi dan aji 4 na Jami’ar Tarayya ta Birnin Kebbi, mai suna Augustine Madubiya, mai shekaru 23 da haihuwa, wanda ke Sashen Tattalin Arziki zuwa inda ba a san inda aka nufa ba.   Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Nafiu Abubakar, ya shaida wa...
    Buhari ya gode wa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu bisa gyaran da aka yi masa a gidansa na Kaduna. Ya gode wa gwamnonin APC da suka kai masa ziyara domin taya shi murnar Sallah, inda ya ce wasu daga cikinsu ya yi aiki tare da su, yayin da wasu kuwa sabbi ne. Shugaban gwamnonin kuma Gwamnan...
    Ya jinjina wa haɗin kai tsakanin jami’an tsaro da al’umma, yana mai cewa hakan ya taka muhimmiyar rawa wajen nasarar aikin. Gwamnati ta yaba da ƙwazon jami’an da suka halarci aikin kuma ta sha alwashin ci gaba da yaƙi da ‘yan ta’adda a faɗin jihar. “Za mu ci gaba da fatattakar waɗanda ke barazana ga...
    Bisa umarnin haramcin, za a dakatar da duk wasu huldodin fitar da hajoji daga kasar Sin zuwa wadannan kamfanoni nan take. Kazalika, a cewar ma’aikatar cinikayyar ta Sin, idan akwai wata bukata ta wajibi, dole ne sassan da za su gudanar da wata hulda mai alaka da hakan su tabbatar sun nemi izni.   Ban...
    Al’ummar Karamar Hukumar Maigatari sun yi kira ga gwamnatin jihar Jigawa da ta taimaka wajen gina hanyoyin da za su hada garuruwansu. Wani mazaunin yankin, Malam Ali A. Bulama Turbus, wanda ya wakilci al’ummomin yayin da yake magana da Rediyon Najeriya a Maigatari, ya jaddada muhimmancin aikin gina hanyar. Ya bayyana cewa samar da hanya...
    Dokar bunkasa ci gaban Afirka da samar da dama ga yankin (AGOA), wacce ta bai wa kasashen yankin damar fitar da kayayyaki zuwa Amurka ba tare da haraji ba, ta shiga gararamba bisa yadda karin harajin zai kassara masana’antu kamar su masaku, da na karafa, da kuma noma.   Nijeriya da Afirka ta Kudu da...
    Assalamu alaikum masu sauraro barakammu da war haka, sharhin bayan labarummu zai yi magana dangane da ‘Siyasar Amurka ta fara yakin kudaden fito tsakaninta da China da kasashen Turai da sauransu. Wanda ni tahir amin zan karanta. ///.. A ranar laraba 2 ga watan Afrilun da muke ciki ne shugaban kasar Amurka Donal Trump ya...
    Rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara ta tabbatar da wani mummunan hari da ‘yan bindiga suka kai a garin Banga, da ke cikin karamar hukumar Kauran Namoda, inda aka kashe mutane biyu tare da sace wasu da dama. Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda ta jihar, DSP Yazid Abubakar, ne ya bayyana hakan cikin...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa JMI ba zata taba jada baya a kan shirinta na makamashin Nukliya ba, kuma yayi allawadai da duka wani shiri na kaiwa cibiyoyin nukliyar kasar Hare-hare. Tashar talabijin ta Presstv ta nakalto shugaban yana fadar haka a taron raya ranar Nukliya ta karo karo na 19 a...
    Kungiyar tarayyar Turai ta yi maraba da tattaunawa tsakanin Amurka da JMI dangane da shirinta na makamashin Nukliya, tare da kara jaddada cewa hanyar diblomasiyya kadai ta rage don warware wannan matsalar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa a halin yanzu dai kungiyar tarayyar ta Turai ta na ci gaba da...
    Sojojin kasar Yamen sun bada sanarwan maida martani ga hare-haren jiragen yakin kasar Amurka a kan kasar na baya-bayan nan, kuma zasu ci gaba da kai hare-haren kan wadannan wurare har zuwa lokacinda za’a kawo karshen yaki a Gaza. Tashar talabijin ta presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin sojojin kasar Yemen Burgediya Janar Yahyah...
    Gwamnatin kasar China ta bada sanarwan kara kodaden fito kan kayakin Amurka wadanda suke shigowa kasa har na kasha 80% sannan a shirye take ta ci gaba da yakin kasuwanci da gwamnatin shugaba Trump har zuwa karshe. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jami’an gwamnatin kasar China na fadar haka a yau...
    Manajan daraktan cibiyar CGIAR Ismahane Elouafi, ta jaddada cewa idan ana son rage tsadar shigar da abinci nahiyar, wanda a yanzu ya kai kimanin dala biliyan 100 a kowacce shekara, zuba jari wajen inganta kyawun kasa da samar da ruwa da rainon ingantattun irrai masu samar da kyakkyawar yabanya, na da matukar amfani.   Ta...
    Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Sha’anin Tsaro, Nuhu Ribadu, ya roƙi ’yan Najeriya da su daina biyan ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane kuɗin fansa. Ribadu, ya ce biyan kuɗin fansa ba ya sa ana sakin waɗanda aka sace, kuma hakan na ƙara dagula al’amuran tsaro. Harajin China da Amurka: Mece ce...
    A ran 7 ga watan nan da muke ciki bisa agogon gabashin kasar Amurka, kasar ta Amurka ta kara barazanar kakkaba wa Sin karin haraji na kashi 50%, kasar Sin a nata bangaren ta bayyana aniyarta ta daukar matakan da suka dace don kare muradunta.   Tattalin arzikin Sin na samun bunkasa yadda ya kamata...