2025-04-27@22:34:18 GMT
إجمالي نتائج البحث: 181

«Gammayar Ƙungiyoyi»:

    Sanarwar ta kuma zayyana matakan fadada adadin shaguna masu iya mayar da kudin haraji domin bunkasa samar da kayayyaki da hidimomi masu ruwa da tsaki.   Haka kuma, za a kara kafa kantunan sayar da kayayyaki masu mayar da kudin haraji ga baki a manyan wuraren sayayya da gefen tituna da wuraren bude ido da...
    Haka zalika, mazauna jihohin da abin ya shafa, sun koka kan wasu abubuwan more rayuwa, kamar ruwan sha da sauran makamantansu. Masu Sayar Da Ruwa Sun Kara Farashi A Kano A Jihar Kano, wani mazaunin unguwar Hotoro ta Arewa, a Karamar Hukumar Nassarawa, Malam Gambo Muhammad, ya ce; ana sayar da kowacce jarka daya kan...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Imo ta kama wasu mata biyu a lokacin da suke yunƙurin sayar da wani yaro ɗan shekara huɗu da aka yi garkuwa da shi a Owerri kan kuɗi Naira miliyan 2.7. An yi garkuwa da yaron ne a Abuja a lokacin da yake tallan kayan miya, sannan aka kawo shi Owerri...
    Muƙaddashin Shugaban Jam’iyyar PDP na Ƙasa, Ambasada Umar Damagum, ya umarci jami’an jam’iyyar da su yi karɓi Arch. Setonji Koshoedo a matsayin mukaddashin sakataren jam’iyya na ƙasa. Gwamnonin PDP, a taron da suka yi a Ibadan, Jihar Oyo, sun amince da Koshoedo a matsayin mukaddashin sakatare har sai lokacin da shugabannin shiyyar Kudu maso Gabas...
    Da yake jawabi a fadar Mai Tangele (Sarkin Billiri), Danladi Sanusi Maiyamba, ya bayyana lamarin da matukar bakin ciki tare da fatan samun makoma mai kyau ga wadanda suka rasu, ya kuma warkar da wadanda suka samu raunuka da gaggawa.   Daga nan sai Gwamna Inuwa ya sanar da bayar da gudummawar Naira miliyan 2...
    Asusun bayar da lamuni na duniya ( IMF) ya yi gargadin cewa rashin tabbataci da Karin kudin harajin Amurka ya haddasa zai iya kawo tsaiko a cikin harkokin cinikiyya ta duniya. Sanarwar wacce babban jami’in ttatalin arziki na Asusun bayar da lamunin na duniya Pierre -Oliver-Gourinchas, ya bayyana ta kara da cewa; Za a iya...
    Al’ummar Gaza sun bukaci kasashen duniya da su tilasta daukan matakin shigar da kayan agaji cikinsu Al’ummar Falasdinawa a Zirin Gaza sun yi kira ga hukumomin kasa da kasa da na Larabawa da su tilasta shigar da kayan agaji cikin yankin, duba da munanan bala’in jin kai da al’ummar yankin ke fuskanta. A cikin wata...
    Wannan amincewar da kammala aikin ginin cibiyar, babban nasara ce wajen inganta harkokin kiwon lafiya, da inganta bayar da kulawa ga lafiyar al’ummar jihar Yobe.   A cikin wannan ziyarar, Gwamna Buni ya sami rakiyar Sanata Musa Mustapha, mai wakiltar Gabashin jihar Yobe, Mai Baiwa Gwamnan shawara kan Ayyuka na Musamman, Hon. Kachallah Mai Hassan,...
    Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam ta Amnesty International ta bayyana cewa: Gwamnatin Mamayar Isra’ila ta tabbatar da cewa ba za a amince da ita ba a duk wani bincike laifukan sojojinta Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta tabbatar da cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila ta sake tabbatar da rashin sahihancinta wajen binciken laifukan...
    Wasu Falasdinawa sun yi shahada a cikan kwana na 35 a sabon yakin da yahudawan sahayoniyya suka sake daurawa kan Zirin Gaza Sojojin gwamatin mamayar Isra’ila suna ci gaba da yakin kisan kiyashi a Zirin Gaza tun bayan sake ci gaba da yau tsawon kwanaki 35 da suka gabata, bayan da Fira minista Benjamin Netanyahu...
    Shugaban NDLEA, Brig.-Gen. Mohamed Buba Marwa, ya yaba wa jami’an hukumar bisa ƙoƙarinsu wajen yaki da magungunan da kwayoyi na haram, yana mai kira ga al’umma da su ci gaba da bayar da rahoton duk wani abu da ke shafar safarar magunguna. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da...
    Kungiyar Hamas ta yi watsi da kudirin baya bayan nan na Isra’ila na kwance damarar kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa domin tsagaita bude wuta a Gaza, tana mai kiran hakan a matsayin wani yunkuri na gurgunta ‘yancin Falasdinu. Tattaunawar da ake ci gaba da yi tsakanin Isra’ila da Hamas ta tsaya cik, inda Isra’ila ta matsa kaimi...
    Dakarun gwagwarmayar Yemen sun kaddamar da hare-haren daukan fansa kan yankin Jaffa da ke kusa da birnin Tel Aviv na Isra’ila Dakarun gwagwarmayar Yemen sun sanar da aiwatar da wasu matakan soji masu inganci kan yankin Jaffa da aka mamaye, da kuma kan jiragen ruwan Amurka masu dauke da jiragen saman yaki na Truman da...
    Gao ya kara da cewa, Sin da kasashen Afirka sun zamo misali na bunkasa hadin gwiwar kasashe masu tasowa, suna kuma gina al’umma mai makomar bai daya ga daukacin bil’adama, kana sun nunawa duniya cewa kasashe masu tasowa na da ikon samar da sabon salon wayewar kan bil’adama na kashin kan su, kuma za su...
    Sojojin mamayar Isra’ila sun sake aiwatar da wani sabon kisan kiyashi kan Falasdinawa 5 a sansanin Jabaliya da ke arewacin Gaza Fararen hula 5 da suka hada da yara biyu da mace daya ne suka yi shahada, wasu kuma suka bace sakamakon harin da rundunar sojin mamayar Isra’ila suka kai kan wani gida a sansanin...
    Akwai kuma Sanata Adeniyi Adegbonire dan jam’iyyar APC daga mazabar Ondo ta tsakiya, Sanata Seriake Dickson dan jami’yyar PDP, daga mazabar Bayelsa ta Gabas, Sanata Shehu Lawan Kaka, dan jam’iyyar APC, daga mazabar Borno ta tsakiya. Sauran sun hada da; Sanata Banigo Ipaligo dan jam’iyyar PDP, daga mazabar Ribas ta Yamma, Sanata Jarigbe Jarigbe dan...
    Shugaban ofishin siyasa na Hamas Khalil al-Hayya ya sanar da cewa, kungiyar a shirye take ta shiga cikin tattaunawa don tabbatar da cimma cikakkiyar yarjejeniyar musayar fursunoni, da tsagaita bude wuta a Gaza, da janyewar Isra’ila daga yankin, da kuma kaddamar da yunkurin sake gina yankin. A cikin wani jawabi da kungiyar ta fitar, al-Hayya...
    Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar da wani babban kwamiti kan kidayar jama’a da gidaje mai zuwa, inda ya umurci mambobin su gabatar da rahoton farko cikin makonni uku. Shugaban wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatan fadar sa, Femi Gbajabiamila, a wajen taron da aka gudanar a fadar gwamnati da ke Abuja, ya ce...
    Mako guda bayan rage farashin fetur da Naira 45, matatar mai ta Dangote ta sake karya farashin man ga ‘yan sari da ragin Naira 30 duk lita. Aminiya ta rawaito cewa matatar na sayar da man ne a ranar Laraba akan ₦835, saɓanin makon da ya gabata da ta sayar da shi akan ₦865 bayan...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wani matashi, Umar Auwal, mai shekaru 20 da ya yi iƙirarin kashe mutane ya miƙa kansa ga rundunar ’yan sanda a Jihar Kano. Matashin mai inkiyar ‘Abba Dujal’ ya ce ya miƙa kansa ga mahukunta ne sakamakon rashin samun kwanciyar hankali tun bayan ta’addancin da ya aikata a bayan nan. Kotu ta yanke wa tsohon...
    Haka kuma a ƙaramar hukumar Ringim ta Jihar Jigawa, ya amsa cewa ya kashe wani mutum sannan ya sayar da babur ɗinsa wanda ya sace a kan kuɗi Naira 300,000. Rundunar ‘yansanda ta ce yanzu haka suna ci gaba da bincike a kansa a Sashen Binciken Manyan Laifuka (CID), don tabbatar da gaskiyar iƙirarin da...
    Muhammad Atiku wanda ɗan tsohon mataimakin shugaban ƙasa ne, ya ce, gwamnna Bauchi, Bala Mohammed, bai taɓa mara wa mahaifinsa baya ba a zaɓukan 2019 da 2023 da aka yi. Ɗan Atiku na wannan kalamai ne a matsayin martani ga ɗan gwamnan Bauchi, Shamsu Bala wanda ya zargi ɗan tsohon mataimakin shugaban ƙasa da yi...
    Lauyoyin Landan suna tattara bayanai kan ‘yan Birtaniya da suka yi aiki a cikin rundunar sojojin mamayar Isra’ila Kwararru kan harkokin shari’a na kasar Biritaniya sun ce gurfanar da wasu ‘yan kasar masu takardar ‘yan kasa biyu da ke aiki a cikin sojojin mamayar Isra’ila a gaban kuliya bisa zargin hannu a tafka laifukan yaki...
    Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta sanar da sharudan sakin dukkan fursunonin Isra’ila da take tsare da su Wani jami’in Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ya ce: Kungiyar a shirye take ta sako daukacin fursunonin Isra’ila domin tsagaita bude wuta da ficewa daga Gaza, kamar yadda wani rahoto da tashar talabijin ta Alkahira ta fitar....
    Gabanin ziyarar aiki da shugaban kasar Sin Xi Jinping zai yi a Malaysia, firaministan kasar Datuk Seri Anwar Ibrahim, ya zanta da manema labarai na CMG a jiya Litinin, inda ya darajanta bunkasar huldar kasashen biyu.   Anwar Ibrahim ya kuma bayyana matukar amincewa da tunanin Xi Jinping na ingiza al’adu da wayewar kan...
    Wata budurwa ’yar kasar China ta janyo muhawara a shafukan sada zumunta bayan ta nuna masaukinta da ba a saba gani ba — banɗaki mai faɗin ƙafa 6 a wurin aikinta, wanda ta biya kuɗin China Yuan 50 kacal, kwatankwacin Naira dubu 10 da dari 533. Kowa yana ƙoƙari ya tara kudi, amma mutum nawa...
    Kotu ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 23 ga watan Yuni, 2025, domin samun rahoto kan sulhun, tare da bayar da umarnin a ci gaba da tsare shi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp...
    Wani ƙazamin rikici da ya janyo salwantar rayukan fiye da mutum 50 a Jihar Filato ya tayar da ƙura a faɗin Nijeriya. Aƙalla mutane 51 ne aka kashe a wasu hare-hare biyu da aka kai a yammacin Lahadi a Jihar Filato da ke Arewa maso tsakiyar Nijeriya. Mahukunta a Filato sun ce an kai harin...
    Tsangayar Ilimi na Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK) ya shirya wani taron bikin cika shekaru 50 da kafuwa tare da gudanar da taron kasa karo na uku. Taron wanda aka yi wa take da “Ilimi Mai Sauya Rayuwa Don Gaba: Fuskantar Sabbin Kalubale da Buɗe Damar Samun Ci gaba” ya samu halartar manyan masu...
    Jiragen saman yakin mamayar Isra’ila sun kai farmaki kan asibitin Baptist da ke birnin Gaza, lamarin da ya janyo dakatar da aiki a cikinsa Wakilin gidan talabijin na Al-Alam Mohammed Al-Balbisi ya ruwaito cewa: Jiragen saman yakin sojojin mamayar Isra’ila sun yi ruwan bama-bamai a wasu gine-gine na asibitin Baptist, da suka hada da ginin...
    Sakamakon gazawar shugabanci, bayar da tallafi na neman zama wani bangare a tarihin dimokoradiyyar Nijeriya, inda gwamnatocin jihohi da ’yan majalisu da sauran ’yan siyasa suke amfani da shi wajen cusa wa ’yan kasa ra’ayinsu na siyasa. A duk lokacin da al’umma suka koka a kan wani mummunann yanayi da ya hada da matsin tattalin...
    Ba kamar kayayyakin manyan kamfanoni irin su Ajinomoto, Bedan wadanda aka zuba su a cikin kwali, ana sayar da su cikin lafiyayyen mazubi kuma NAFDAC ta amince da su ba, wadannan danyun kaya ne da ba su da wata alama. Babban abin ban tsoro shi ne ba za a iya gano masana’antunsu don bincikar sahihancinsu...
    Gwamnatin Yobe ta bayyana shirinta na mayar da tubabbun mayaƙan Boko Haram cikin al’ummarsu da aka yi wa shirin kawar da tsattsauran ra’ayi, gyara da sake haɗewa da iyalansu ƙarƙashin rundunar Operation Safe Corridor (OPSC). Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ne ya bayyana haka a ranar Alhamis a Damaturu lokacin da ya karɓi baƙuncin...
    Wadda aka tsara a cikin babi shida, takardar matsayar ta gwamnati ta sake tabbatar da yanayin moriyar juna ta cinikayya tsakanin Sin da Amurka.   Ta kara da bayyana cewa, kasar Sin ba ta neman cin bulus a harkar kasuwanci, kuma bangarorin biyu sun samu riba mai yawa daga hadin gwiwar tattalin arziki da suke...
    Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da sayar da ɗanyen mai da man da aka tace farashin Naira, maimakon amfani da dalar Amurka. Wannan mataki na daga cikin manufofin gwamnati na bunƙasa tattalin arziƙin cikin gida, rage matsin lamba kan kasuwar musayar kuɗi, da kuma bunƙasa makamashi. ’Yan bindiga sun mamaye...
    Gwamnatin Saudiyya ta ayyana 1 ga watan Dhul Qada, wadda za ta yi daidai da 29 ga watan Afrilu, a matsayin ranar karshe da duk wani bako da ke kasar da zummar aikin Umarah da ya fice daga ƙasar. Sanarwar da ma’aikatar aikin Hajji da Umarah ta Saudiyya ta fitar ta ce ta dauki matakin...
    Gwamnatin jihar Jigawa ta ce za ta bullo da shirin bada magani kyauta ga masu cutar siga da hawan jini da kuma sikila. Kwamishinan lafiya na jihar, Dr Abdullahi Muhammad Kainuwa ya bayyana haka ga manema labarai a Dutse. Yace tuni gwamna Umar Namadi ya bada umarnin gabatar masa da wannan kudiri domin aiwatar da...
    Kwanan nan wani mai kiwon karnuka a Indiya ya biya Rupee miliyan 500 — kwatankwacin Naira biliyan 8 da miliyan 949 da dubu 481 da 589 domin sayen wani karen kerkeci na jinsin karen Shephard Caucasian, wanda hakan ya sa karen ya zama mafi tsada a duniya. Karen mai suna Cadabomb Okami, an bayar da...
    Mista Abel Olumuyiwa Enitan, Sakataren dindindin na ma’aikatar Ilimi, ya tabbatar da cewa ma’aikatar tana shirye don ƙara yin haɗin gwuiwa tare da NYSC domin inganta tsarin ilimi a Nijeriya.   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga...
    Madugun kungiyar Ansarallah ta kasar Yeman ya yi ikirarin cewa, zafafan hare-haren wuce gona da iri da Amurka ke kaiwa kasar Yemen, ya kasa dakatar da ayyukan gwagwarmayar Yeman na goyon bayan al’ummar Gaza ko kuma kare jiragen Isra’ila a tekun Bahar Rum. A wani jawabi da ya yi a ranar Juma’a, Abdul-Malik al-Houthi ya...
    Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyid Abdulmalik al-Husi ya bayyana cewa; Al’ummar musulmi suna fuskantar manyan hatsari guda biyu,  da su ka hada laifukan da HKI take tafkawa a Gaza, da kuma kokarin shafe hakkokin falasdinawa baki daya. Shugaban kungiyar ta Ansarullah ya kuma tabo batun keta tsagaita wutar yaki da HKI take yi...
    Da yake tofa albarkacin bakinsa kan sayar da danyen mai da naira, wani babban jami’in gwamnati wanda ke da masaniya sosai kan lamarin da ke aiki da kwamitin da aka kafa don shirin ya bayyana cewa gwamnati ba wai ta dakatar da tsarin bane gaba daya. “Shirin cinikayyar danyen mai a kan naira zai ci...
    Harbin dai ya samu Comfort ne a kai, inda nan take ta mutu, yayin da wasu harsasai suka samu mijinta a mukamuki da kafadarsa dama. Yayin da ‘ya’yansu ke kururuwar firgici, rahotanni sun ce jami’an sun gudu daga wurin. An kori Musiliu daga aikin ‘yansanda ne a ranar 17 ga watan Satumba, 2015, daga bisani...
    Ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi, ya bayyana a yau Talata cewa, al’ummar Sinawa da ’yan kasar Rasha sun ba da gudummawa gaya wajen samun nasarar yakin duniya na biyu. A wata hira da ya yi da rukunin gidajen rediyo da talabijin mallakin kasar Rasha wato Russia Today a yau a birnin Moscow, Wang...
    Jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya yi kakkausan gargaɗi kan barazanar Amurka da ƙawayenta na kai wa ƙasarsa hari. Khamenei ya sha alwashin maida mummunar martani idan har Amurka da ƙaddamar da hare-hare a ƙasar ta Iran. Gargaɗin nasa martani ne kan barazanar da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi wa ƙasar cewa...
    Jagunlabi ya ce za a gudanar da shirin ne tare da hadin gwiwar gwamnatocin jihohi domin mayar da wuraren tarihi zuwa wuraren shakatawa domin samar da kudin shiga wanda hakan zai haifar bunkasar tattalin arziki da samar da ayyukan yi a fannin fasaha da nishadi.   Ya bayyana cewa, aikin zai mayar da hankali ne...
    Sabon tsarin sayar da man fetur a Najeriya ya haifar da ƙarin farashi, inda ake sayar da kowace lita a kan Naira 930 a Legas da kuma Naira 960 a Arewa. A ranar 28 ga watan Maris, 2025, sabon tsarin ya fara aiki bayan da aka dakatar da sayar wa matatar Dangote mai a farashin...