2025-04-15@22:40:06 GMT
إجمالي نتائج البحث: 612

«Mashariq Al Dhahabiah Al Mutawazi»:

    Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da amfani da Hijabi ga jami’an tsaro mata a fadin jihar. Kwamishinan Yada Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu, Alhaji Sagir Musa Ahmed ne ya bayyana haka jim kadan bayan kammala taron majalisar zartarwa da aka gudanar a fadar gwamnatin  jihar da ke Dutse. A cewarsa, majalisar ta bayar da umarni...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Ba su kallon tattaunawa tsakanin Iran da Amurka na kasar Oman da kyakkyawan fata ko ganin rashin amfaninsa kwata-kwata Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya karbi bakwancin wakilan gwamnati da dama, da wakilan majalisar shawarar Musulunci, da manyan jami’an shari’a, da jami’ai daga...
    Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta sanar da cewa: Za a gudanar da zaman tattaunawa kan Shirin makamashin nukuliyar Iran zagaye na biyu ne a birnin Muscat na kasar Oman Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya sanar da cewa: Zaman tattaunawa zageye na biyu wanda ba na kai tsaye ba, tsakanin Iran da Amurka...
    Lauyoyin Landan suna tattara bayanai kan ‘yan Birtaniya da suka yi aiki a cikin rundunar sojojin mamayar Isra’ila Kwararru kan harkokin shari’a na kasar Biritaniya sun ce gurfanar da wasu ‘yan kasar masu takardar ‘yan kasa biyu da ke aiki a cikin sojojin mamayar Isra’ila a gaban kuliya bisa zargin hannu a tafka laifukan yaki...
    Ban da haka, Wang ya ce matakan kasar Amurka sun karya ka’idojin kungiyar WTO na rashin nuna bambanci, da takaita karbar haraji, kana suna girgiza tsarin tattalin arzikin duniya, da tushen tsarin cinikayya da ya shafi bangarori daban daban. Ganin haka ya sa kasar Sin daukar matakan ramuwar gayya kan kasar Amurka, don kare halaltacciyar...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Bagaei ya bayyana cewa kokari da JMI a tattaunawarta da kasar Amurka kan shirin Nukliyar kasar shi ne ganin an dauke  mata takunkuman tattalin arzikin da aka dora mata,  ko amurka da dora mata.. Tashar talabjin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar...
    A zantawarsa ta wayar tarho da tokwaransa na kasar Kuwait, ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya ce tattaunawarsa da Abdullah Ali Al-Yahya ya fi bada karfi kan al-amuran yankin Asiya ta kudu musamman tattaunawa tsakanin Iran da Amurka kan shirinta na makamshin nukliya da kuma dagewa kasar takunkuman tattalin arzikin da aka dora...
    A jiya Litinin daruruwan yahudawa ‘yan share wuri zauna sun kutsa cikin masallacin kudus, suna masu bayar da take na tsokana ga Musulmi. Har ila yau ‘yan share wuri zauna din sun kuma gudanar da na’u’oin ibadu na addinin yahudanci a cikin farfajiyar masallacin na Kudus. Ma’aikatar  da take kula da wuraren ‘wakafi’ na musulunci,...
    Rundunar ‘Yansandan Jihar Adamawa ta kama Umar Shaibu bisa zargin cin zarafin wata mata a yankin Jimeta a jihar. An kama Shaibu ne bayan wani bidiyo mai tayar da hankali ya yadu a kafafen sada zumunta, kamar yadda Jami’in hulda da Jama’a na ‘Yansandan Jihar Adamawa, SP Suleiman Nguroje, ya bayyana. Salamatu Yakubu, matar...
    Hukumar kula da agaji ta MDD (OCHA) ta bada sanarwan cewa, gwamnatin HKI a yankin yamma da kogin Jordan ta kori Falasdinawa a gidaje 5 a yankin bayan sun rusa gidajensu. Hukumar ta kara da cewa wadanda HKI ta rusa gidajensu a yankin sun hada da yara 19 da da iyayensu 33 maza da mata...
    ’Yan sanda sun kama shahararren mawaƙin zamani a Najeriya Habeeb Okikiola Badmus, wanda aka fi sani da Portable, bayan ƙazancewar rikicinsa da fitaccen ƙwararren mawakin Fuji, Okunola Saheed “Osupa.” A ranar Lahadi da dare ne ’yan sanda daga Jihar Kwara suka yi takakkiya suka kamo Portable mai waƙar “Zazu Zeh” a garin Abeokuta, Jihar...
    Babban sakataren kungiyar kasashen Larabawa na yankin tekun Farisa (PGCC) ya yi fatan alkhairi ga kasashen Iran da Amurka a tattaunawa ba kai tsaye ba a tsakaninsu dangane da shirin Nukliya ta kasar Iran na zaman lafiya wanda suka fara, a birnin Mascat na kasar Omman a ranar Asabar da ta gabata. Kamfanin dillancin labaran...
    Gwamnatin Jihar Jigawa ta siyo tan tan guda 360 domin tallafawa manoma don ci gaba da habbaka harkokin noma a Jihar. Gwamna Umar Namadi ya bayyana haka a lokacin kaddamar da shirin noman rani na shinkafa a kauyen Jura dake Karamar Hukumar Auyo. Ya yi bayanin cewar, gwamnatin ta kuma siyo injin girbin shinkafa...
    Al’ummar Mauritaniya sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da yakin da ake yi a Gaza A karkashin taken “An rusa Gaza” kuma goyon bayan al’umma ga Falasdinawa abu ne da ya zama wajibi, ba zabi ba, mazauna birnin Nouakchott fadar mulkin kasar Mauritaniya sun gudanar da zanga-zanga domin jaddada bukatar musulmi a ko’ina a duniya...
    Sanarwar ta ƙara da cewa, ƙungiyar ta karrama gwamna Lawal tare da gwamnonin Akwa Ibom, Kaduna, da kuma jihar Legas.   “A jiya a Legas, ƙungiyar ‘yan kasuwa ta Nijeriya da Amurka (NACC) ta gudanar da bikin cika shekaru 65 da ƙaddamar da Alhaji Sheriff Balogun a matsayin shugaban ƙungiyar na 20.   “Taron mai...
    Nan da wata biyu Majalisar Dokoki ta Kasa ta 10 za ta cika shekara biyu, rabin wa’adinta, da fara aiki a matsayin ɓangaren da ke kafa dokoki da kuma saita ɓangaren zartarwa domin yin daidai a bisa tsarin dimokuradiyyar Nijeriya. ’Yan kasar da dama na ganin wannan muhimmin ɓangare ya zama dan amshin shata ga...
    Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce shirye-shirye sun yi nisa game da aikin Hajjin shekarar 2025 a jihar. Daraktan Hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ne ya bayyana hakan ga Radio Nigeria a hedikwatar hukumar da ke Dutse. A cewarsa, zuwa yanzu hukumar ta mika sunayen maniyyata fiye da dubu ɗaya da suka...
    Matainakin shugaban kasar kasar Iran na farko Mohammad Reza Aref ya bayyana cewa, daukewa Iran takunkuman zalunci wadanda kasashen yamma suka dora mata na daga cikin asalin hakkin kasar da aka tauye. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Aref yana fadar haka a jiya Asabar, ya kuma kara da cewa, kasar Iran...
    Fadar mulkin Amurka ta “White Hosue” ta bayyana cewa tattaunawar da aka yi a tsakanin ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci  da wakilin Donald Trump akan gabas ta tsakiya Steve Witkoff, ta hanyar shiga tsakanin kasar Oman, ta yi armashi. Da marecen jiya Steve Witkoff ya bayyana cewa; shugaba Donald Trump ya ba shi umarnin...
    Sharhin zai yi dubi ne game da tattaunawar da aka fara gudanarwa zagaye na na farko tsakanin Iran da Amurka a birnin Mascut fadar mulkin kasar Oman, inda gwamnatin kasar Oman din take shiga tsakani a wannan tattaunawa wadda aka fara gudanarwa. Tun da safiyar Asabar ne dai ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci ya...
    Ya soki masu ra’ayin cewa dimukradiyya wani sharadi ne na ci gaba, yana mai cewa “karya ne” shi akwai wata kasa da ta ci gaba a karkashin tsarin dimukradiyya?. Burkina24 ta nakalto cewa “Babu wata kasa da za a iya bayyanawa da ta ci gaba a dimukradiyya. Ya ci gaba da cewa gwamnatinsa za ta...
    An kammala zagayen farko na tattaunawa tsakanin Iran da Amurka a babban birnin Muscat a shiga tsakanin kasar Oman. Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi da Steve Witkoff, manzon musamman na shugaban Amurka kan harkokin yankin gabas ta tsakiya ne suka jagoranci shawarwarin yau Asabar. A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Iran ta...
    Gwamnatin jihar Jigawa ta ce za ta samar da ababen hawa ga shugabannin makarantun babbar  sakandare a fadin jihar. Kwamishinan ilimi na jihar, Farfesa Isa Yusuf Chamo, ne ya bayyana hakan yayin wani taro da ya gudanar da shugabannin makarantu a garin Dutse. A cewarsa, za a gyara gidajen ma’aikatan makarantun sakandare domin saukaka matsalar...
    Tun da safiyar yau Asabar ne dai ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci ya isa birnin Mascut na kasar Oman da can ne za a yi tattaunawar da ba ta gaba da gaba ba a tsakanin jamhuriyar musulunci da Amurka. Jim kadan bayan isar tasa birnin Mascut ministan harkokin wajen na jamhuriyar musulunci ta Iran...
    Sojojin kasar Yemen sun yi amfani da jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa kan cibiyoyin makamai na HKI wadanda suka Yaffa (tel aviv) saboda daukar fansa kan kashe-kashen da take yi a Gaza. Tashar talabijin Presstv a nan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labaran YAF na kasar Yemen yana fadar haka a jiya Jumma’a,...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriya kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a 2023, Alhaji Atiku Abubakar ya ziyarci tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari a Kaduna. Atiku ya samu rakiyar tsofaffin gwamnoni da suka haɗa da tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai da tsohon Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal da wasu jiga-jigan ’yan siyasa. An gano gawar makiyayi...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumar ilimin bai daya ta kasa wato UBEC ta yabawa Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa bisa jajircewar sa wajen inganta ilimi a matakin farko a Jihar. Shugabar Hukumar, Hajiya Aisha Garba, ta bayyana hakan a yayin ziyarar gwamnan zuwa hedikwatar UBEC a Abuja. Hajiya Aisha Garba ta bayyana jihar Jigawa a matsayin abin...
    Jami’an Kongo da masu shiga tsakani na M23 sun isa Qatar domin tattaunawa don cimma yarjejeniyar tsagaita wuta. Jami’an Kongo da masu shiga tsakani na kungiyar M23 sun isa Doha babban birnin kasar Qatar domin tattaunawa da nufin cimma tsagaita bude wuta da kuma kawo karshen fadan da aka shafe watanni ana gwabzawa a yankin,...
    Asusun ba da lamuni na ilimi na Najeriya ya yi barazanar daukar matakin shari’a a kan cibiyoyin da ke boye bayanai kan yadda ake biyan dalibai rancen kudi yayin da suke neman biyan kudaden makarantun daga hannun daliban.   Sanarwar da Manajin Darakta na NELFUND, Mista Akintunde Sawyerr ya fitar ta bayyana cewa, sakamakon binciken...
    Kasar Sudan ta kai kukan HDL a gaban kotun MDD cewa ta keta dokar hana kisan kiyashi ta hanyar taimakawa dakarun kai daukin gaggawa. A jiya Alhamis kasar ta Sudan din ta bukaci kotun ta kasa da kasa dake karkashin MDD da  ta ta fitar da hukunci na gaggawa na bayar da umarni ga HDL...
    Wadannan ayyuka domin inganta harkar ilimi da kuma nuna gaskiya, sun sa Jigawa ta zama abin koyi ga sauran jihohi.   Tunda farko, Gwamna Malam Umar Namadi, a nasa jawabin, ya ce gwamnati ta dauki kwakkwaran matakai na magance matsalar rashin ilimi bayan wani bincike da wani masani mai zaman kansa ya fitar cewa, yawancin...
    Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya jagoranci wata tawaga zuwa Jihar Edo domin binciko gaskiyar abin da ya faru game da kisan mafarauta ’yan asalin jihar a ƙauyen Uromi. Gwamna Abba Kabir Yusuf ne, ya umarci a kafa wannan tawaga, wacce ta ƙunshi manyan shugabanni irin su Sarkin Rano, Kwamishinonin ma’aikatu da...
    Jakadan Sudan a Tehran, Abdul Aziz Hassan Saleh, ya tabbatar da cewa, za a gudanar da zaman farko na kotun kasa da kasa da ke birnin Hague a yau Alhamis, domin duba korafin da Sudan ta shigar kan kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, kan rawar da take takawa a yakin da ake ci gaba da yi...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa Jagoran juyin juya halin Musulunci na kasar Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ba shi da wata adawa da Amurkawa masu zuba jari a kasar. “Muna maraba da masu zuba jari.” amma ba tare da tauye mutunci ko tsaron kasa ba. Har ila yau kalaman nasa sun sake tabbatar...
    Gwamnatin Washington ta sanar da kakabawa Iran sabbin takunkumai kan shirinta na nukiliya an zaman lafiya, a matakin da Amurka ke ganin shi ne kawai hanyar matsin lamba kan Iran domin ta mika wuya game da shirint ana nukiliya. Takunkumin, wanda ma’aikatar baitul malin Amurka ta sanar a jiya Laraba, ya shafi hukumomi biyar da...
    Mazauna karamar hukumar Gezawa ta Kano sun shiga cikin tashin hankali da makoki sakamakon nutsewar wasu mata biyu a cikin wani tafki.   Rahotanni sun nuna cewa matan (an sakaya sunansu) sun gamu da ajalinsu ne a lokacin da suke wanka a kogi bayan sun dawo daga aiki a wata masana’antar sarrafa hibiscus.   A...
    “Ina rokon Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta masa, ya sa ya huta har abada.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) za ta hada gwiwa da kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ) a yaki da hako ma’adinai da kuma ayyukan ta’addanci a kasar nan.   Mukaddashin Daraktan shiyyar Kaduna mai kula da shiyyar Kaduna, Mista Bawa Usman Kaltungo ne ya bayyana hakan a lokacin da ya...
    Al’ummar Karamar Hukumar Maigatari sun yi kira ga gwamnatin jihar Jigawa da ta taimaka wajen gina hanyoyin da za su hada garuruwansu. Wani mazaunin yankin, Malam Ali A. Bulama Turbus, wanda ya wakilci al’ummomin yayin da yake magana da Rediyon Najeriya a Maigatari, ya jaddada muhimmancin aikin gina hanyar. Ya bayyana cewa samar da hanya...
    Kungiyar tarayyar Turai ta yi maraba da tattaunawa tsakanin Amurka da JMI dangane da shirinta na makamashin Nukliya, tare da kara jaddada cewa hanyar diblomasiyya kadai ta rage don warware wannan matsalar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa a halin yanzu dai kungiyar tarayyar ta Turai ta na ci gaba da...
    A ci gaba da kokarinsa na kawo sabon tsari domin inganta harkokin noma a jihar Jigawa, Gwamna Malam Umar Namadi ya jagoranci tawagar gwamnatin jihar zuwa wani babban taro da manyan masu zuba jari na duniya da masu ruwa da tsaki a harkar noma. Taron wanda ya gudana jiya Talata a otal din Hilton da...
    Wasu ‘yan kasar Amurka uku da aka daure bisa laifin yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango, yanzu haka suna hannun Amurka bayan yanke hukuncin da aka yi a kansu a makon jiya, kamar yadda wasu jami’an Amurka da na  fadar shugaban kasar Kongo suka bayyana ga kamfanin dillancin labarai...
    Ya ce karin wa’adin na baya-bayan nan ya biyo bayan cikar wa’adin farko na ranar 1 ga Afrilu, 2025, wanda aka sanya tun da farko a ranar 24 ga watan Janairu.   Umar ya kara da cewa, duk da wannan karin wa’adin, amma an ci gaba da samun karancin fitowar masu filaye domin sabunta takardunsu....
    Ya jaddada cewa, taken taron ya dace kuma yazo a kan lokaci “wanda na yi imanin cewa, dandalin zai taimaka wajen gabatar da jawabai a bangarori daban-daban na gyare-gyaren kasafin kudi da shugaba Bola Tinubu ke aiwatarwa a karkashin shirin renewed hope.”   Ya ce, jawabin da ake gabatarwa a dandalin zai ba da gudummawa...
    Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya ce kasarsa ta yi imani da tattaunawa, amma ba a karkashin wulakanci da kaskanci ba.” Ya jaddada cewa Iran ba ta neman yaki, ko tada zaune tsaye, ko kuma mallakar makamin nukiliya, yana mai kira ga kasashen duniya da su amince da hakan. Pezeshkian ya bayyana hakan ne a yammacin...
    Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ci gaba da gudanar da  tarurrukan bita ga maniyyata aikin Hajjin bana, bayan  kammala azumin watan Ramadan. Daraktan Hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya bayyana hakan ga Rediyon Najeriya a Dutse, babban birnin jihar. A cewarsa, hukumar za ta tabbatar da cewa maniyyata sun sami...
    An gudanar da zanga-zangar adawa da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu wada ta barke a wasu manyan biranen Nijeriya da suka haɗa da Abuja da Legas da kuma Fatakwal. Zanga-zangar wadda wata kungiyar gwagwarmaya ta Take It Back ta shirya na gudana ne duk da gargadin da ’yan sanda suka yi na neman a jingine ta....
    Jamhuriyar musulinci ta Iran, ta bayyana cewa za ta fata tattaunawa wacce ba ta kai tsaye ba da Amurka a ranar Asabar mai zuwa a kasar Oman. Ministan harkokin wajen Iran din ne Abbas Araghchi ya bayyana hakan a shafinsa na ‘’X’’ a safiyar Talata. “Iran da Amurka za su gana a Oman ranar Asabar...