2025-04-24@19:13:43 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2585
«iyali»:
110- Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na Kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin al-kur’ani mai girma ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da Littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawi na maulana Jalaluddin Rumi,...
To mun san ki a matsayin marubuciyar littafan Hausa. Shin ta ya kika tsinci kanki a duniyar rubutu? Hukuncin Ubangiji, na yi karance-karance da dama a baya, tun ina karamar secondary na fara rubuta labari a paper a shekarar 2016, idan na rubuta sai na ajiye. Lokacin da muka yi hutu da aka dawo aji...
Jami’an rundunar ’yan sandan jihar Edo sun ceto ɗalibai 10 da wasu ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Edo. An kashe ɗaya daga cikin ’yan bindigan, a yayin musayar wuta da ’yan sanda a lokacin aikin ceto, yayin da sauran suka tsere da raunukan harbi. Daily Trust ta ruwaito cewa an yi...
Bada shawara kan abinda ko abubuwan da su daliban suke bukatar zama da babban burin ko wane daga cikinsu,da yadda za su cimma burin abinda suke son zama a gaba. Bada taimakon lokacin da ake fuskantar matsalolin rayuwa da kuma karatu. Yin kwatance da Malamin makarnta wajen koyi da abubuwan da aka ga yana yi,irin...
Dakarun gwagwarmayar Yemen sun kaddamar da hare-haren daukan fansa kan yankin Jaffa da ke kusa da birnin Tel Aviv na Isra’ila Dakarun gwagwarmayar Yemen sun sanar da aiwatar da wasu matakan soji masu inganci kan yankin Jaffa da aka mamaye, da kuma kan jiragen ruwan Amurka masu dauke da jiragen saman yaki na Truman da...
Fadar Shugaban Ƙasa ta ƙaryata labarin da karaɗe kafofin sada zumunta cewa sojoji sun hana mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima shiga Fadar Shugaban Ƙasa. Labarin da ya tayar da ƙura cewa sojojin sun tare ƙofar shiga fadar shugaban ƙasa da cewa umarni ne daga sama ya koma gidansa da ke makwabtaka da fadar shugaban kasa,...
Mayakan kungiyar ta’addanci ta ISIS sun sake kunno kai a garuruwan Deir ez-Zor da Hasaka na kasar Siriya Yankunan Deir ez-Zor da Hasakah dake arewa maso gabashin kasar Siriya suna ci gaba da samun karuwar bullar ayyukan ta’addancin kungiyar ISIS tun daga farkon wannan wata. Hare-hare 13 sun kai sune kan Dakarun Syrian Democratic Foeces...
Sojojin Sudan sun sanar da kashe mayakan dakarun kai daukin gaggawa 70, ciki har da kwamandojin mayakan a birnin a El Fasher fadar mulkin jihar Darfur ta Arewa A ranar Alhamis ne rundunar sojin Sudan ta sanar da kashe mayakan da jami’an dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces fiye da 70 da suka...
Ta nanata cewa ba neman hada bam din nukiliya take yi ba, amma wasu kasashe – da kuma hukumar kula da makaman nukiliya ta duniya International Atomic Energy Agency (IAEA) – ba su yarda ba. An fara zargin Iran ne game da shirin nata bayan an gano wasu boyayyun wuraren binciken nukiliya a 2002. Hakan...
Iran da Amurka za su shiga zagaye na biyu na tattauna batun taƙaita shirin nukiliyar Tehran a yau Asabar. Masu shiga tsakani za su haɗu a birnin Roma bayan zagayen farko na tattaunawar da aka yi a makon jiya a Oman. Ministan harkokin wajen Iran ya ce za a iya cimma yarjejeniya idan Amurka ba...
Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta yi nasarar kubutar da wasu mutane shida da aka yi garkuwa da su, a wani samame da ta gudanar cikin gaggawa tare da tabbatar da ganin an dawo da zaman lafiya da tsaro a fadin jihar. A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan,...
Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya bukaci Kiristoci da su yi tunani a kan darussa, muhimmaci, da kuma kyawawan dabi’u na makon Easter. Gwamna AbdulRazaq a wani sako da ya aike a Ilorin, ya taya mabiya addinin kirista a jihar da ma fadin Najeriya murnar bikin Easter. Gwamnan ya ce nasarar da Yesu...
Kakakin majalisar dokokin jihar Neja, Barr. Abdulmalik Sarkin-Daji, ya mika sakon taya murna ga al’ummar kiristoci a jihar da ma sauran sassan jihar bisa nasarar kammala azumin Easter na kwanaki 40. A madadin shugabanni da membobin majalisar ta 10, shugaban majalisar ya yaba wa mabiya addinin kirista saboda sadaukarwar da suka yi da kuma...
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta sanar da cewa za ta gudanar da atisayen harbe-harbe ga sabbin ‘yan sanda a karamar hukumar Birnin Kudu ta jihar Jigawa. Kwamishinan ‘yan sandan jihar Jigawa, Ahmad Tijjani Abdullahi ya bayyana haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Dutse babban birnin jihar. Ya ce, atisayen...
Jami’an rundunar ’yan sandan jihar Edo sun ceto ɗalibai 10 da wasu ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Edo. An kashe ɗaya daga cikin ’yan bindigan, a yayin musayar wuta da ’yan sanda a lokacin aikin ceto, yayin da sauran suka tsere da raunukan harbi. Daily Trust ta ruwaito cewa an yi...
Kungiyar Sarakunan Afirka ta jaddada muhimmancin gudunmuwar da Sarakuna ke badawa wajen tabbatar da hadin kai da zaman lafiya a Najeriya. Da yake jawabi a wajen bikin nadin Alhaji Aliyu Dauda a matsayin Sardaunan Najeriya na farko, wanda aka gudanar a Yankari, Jihar Bauchi, Shugaban Kungiyar, Alhaji Ibrahim Haruna, ya bayyana gudunmuwar da...
Jam’iyyar adawa ta SDP buƙaci Shugaba Bola Tinubu da sauran shugabannin siyasa a Najeriya su dai shagala da batun zaɓen 2027, su mayar da hankalinsu wajen magance matsalar tsaro da ke ƙara mayar da ƙasar tamkar filin kisa. SDP ta bayyana cewa kashe-kashe ɗaruruwan mutane da ke faruwa a faɗin ƙasar nan – Arewa da...
Wannan nasarar ta nona irin namijin kokarinda Bankin ya yi na kara habaka samar wa da kansa kudaden shiga duk da matsin tattalin arzikin da kasar nan ke fuskanta. Bugu da kari, kadarorin Bankin sun karu zuwa jimmlar kaso 47 daga Naira tiriliyan 20 a shekarar 2023 zuwa Naira tiriliyan 30, a shekarar 2024. Kazalika,...
Ilimi na da muhimmanci wajen gina al’umma, amma ga daliban Makarantar Firamare ta Bare a karamar Hukumar billiri, Jihar Gombe, wannan lamari ya zama kamar mafarki mai wahalar tabbatuwa. Duk da ikirarin da Gwamnatin Jihar Gombe ke yi na cewa, tana fifita ilimi ta hanyar manyan ayyuka kamar gine-ginen makarantu masu hawa biyu a kowace...
Sakatare-janar na kungiyar Hizbullah Sheikh Naim Qassem ya yi Allah wadai da kalaman da kiraye kirayen da ake na “kwance damarar” kungiyar Hizbullah, yana mai kiransa da cewa wani yunkuri ne na raunata kasar Lebanon da kuma ci gaba da fadada manufofin Tel Aviv. Sheikh Naim Qassem ya bayyya hakan ne a wani jawani da...
Kasashen Nijar da Najeriya sun sha alwashin inganta dangantaka a tsakaninsu domin cin moriyar juna a matsayinsu na makobta. Wannan bayyanin ya fito bayan tattaunawa data wakana tsakanin ministocin harkokin wajen kasashen biyu a birnin Yamai bayan kwashe watanni ana takaddama. Yayin ziyarar da ministan harkokin wajen Najeriya ya kai Nijar an gudanar da wani...
Amurka ta sanar cewa ta rage yawan sojojinta a kasar Syria da rabi, tana mai cewa ta yi nasarar yaki da kungiyar IS, duk da cewa kungiyoyin masu da’awar jihadi na ci gaba da fafutuka a wannan kasa mai rauni. Wannan shawarar ta zo ne kusan watanni uku bayan hawan Donald Trump kan karagar mulki,...
Makera, Jihar Kaduna – Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Rt. Hon. Yusuf Dahiru Liman, ya halarci bukukuwan Easter tare da al’ummomin Kiristoci na Gundumar Makera, inda ya bukaci su yi amfani da lokacin wajen tabbatar sa saƙon bangaskiya, yabo, da sadaukarwa da ke tattare da bikin. A jawabin da ya gabatar, Hon. Liman ya...
Gao ya kara da cewa, Sin da kasashen Afirka sun zamo misali na bunkasa hadin gwiwar kasashe masu tasowa, suna kuma gina al’umma mai makomar bai daya ga daukacin bil’adama, kana sun nunawa duniya cewa kasashe masu tasowa na da ikon samar da sabon salon wayewar kan bil’adama na kashin kan su, kuma za su...
Bisa labarin da babban bankin jama’ar kasar Sin ya fitar, ya zuwa ranar 15 ga watan Afrilun shekarar 2025, jimillar cibiyoyin hada-hadar kudi na kasashen waje 1,160 ne suka shiga kasuwar hada-hadar lamuni ta kasar Sin, wadanda suka hada da cibiyoyin hada-hadar kudi masu zaman kansu da cibiyoyin hada-hadar kudi na kasuwanci a kasashe...
Kazalika, Injiniya Xie ya kara da cewa, a cikin rubu’in farko na bana, sashen masana’antu na kasar Sin ya taka rawar gani wajen samun ci gaba ba tare da tangarda ba sakamakon ingantuwar tsari da zurfafa ayyuka wajen samar da sabbin ginshikan bunkasa ci gaba mai inganci. (Abdulrazaq Yahuza Jere). Daga kanmu, magana ta...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Duk da cewa Atiku ya dage yayin tattaunawar da ya yi da manema labarai bayan ziyarar cewa ganawar ba ta batun siyasa ba ne, amma jawabin El-Rufai ya nuna karara akwai siyasa a cikin ganawar. Bayan ziyarar ‘yan adawa kwanaki kadan da na gwamnonin APC, shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya isa...
Waɗanda suka take wa Ministan sawu a tafiyar su ne jagororin hukumomin yaɗa labarai da wayar da kai da ke ƙarƙashin ma’aikatar sa. Ya yi zama daban-daban tare da ƙwararru inda suka tattauna kan yadda za a inganta ƙwarewa da kuma kayan aiki na zamani na kafafen yaɗa labarai na gwamnatin Nijeriya. Ya ce:...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa Iran zata halarci zaman tattaunawa da kasar Amurka kan shirin kasar na makamashin Nukliya tare da fatan bangaren Amurla ma tana bukatar cimma yarjeniya da ita, matukar Amurka bata kawo wani abu wand aba zai yu Iran ta amince ba. Tashar talabijin ta Presstv a...
Sojojin kasar Yemen sun bada sanarwan cilla makamai masu linzami kan birnin Telaviv da kuma kan jirgin yakin Amurka saboda tallafawa falasdinawa a Gaza, da kuma maida martani kan hare-haren Amurka kan kasar a jiya Alhamis. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin sojojin kasar na Yemen Burgediya Janar Yahayah Saree yana...
Hare-haren da jiragen yakin Amurka suka kaiwa lardin Hudaida ya karu zuwa 74. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar gwamnmatin kasar ta Yemen na fadar haka a yau Jumma’a ta kuma kara da cewa dukkan mutanen da suka mutu a hare-haren jiragen yakin Amurka a cibiyar man fetur na Ras Isa...
Kasar Chaina ta musanta zargin shugaban kasar Ukraine ga kasar, dangane da tallafawa kasar Rasha da makamai. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin ma’aikatar wajen kasar China Lin Jian yana fadar haka a safiyar yau Jumma’a ya kuma kara da cewa, kasar China bata taba daukar bangaren a yakin na Ukraine...
Gwamnatin kasar Amurka ta bada sanarwan cewa zata rufe wasu daga cikin ofisoshin jakadancinta har kimani 30 a kasashen duniya, amma mafi yawansu a kasashen Afirka. Shafin yanar gizo na labarai Afrika News ya nakalto ma’aikatar harkokin wajen kasar Amurkan na fadar cewa gwamnatin shugaban Trump tana son ta rage yawan kashe kudade a ma’aikatar...
Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya ce babbar jam’iyyar adawa ta PDP ba ta da wani kyakkyawan tsari da za ta iya kayar da jam’iyyar APC mai mulki a zaɓen 2027. Ministan ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai kai tsaye a Abuja ranar Juma’a. Benuwe: Har yanzu ba a gano...
Rundunar ’yan sandan Jihar Benuwe a ranar Alhamis ta tabbatar da cewa an samu kwanciyar hankali a unguwar Otobi da ke Ƙaramar hukumar Otukpo biyo bayan wani mummunan hari da ya tilastawa mazauna garin barin gidajensu. Kakakin rundunar ’yan sandan, CSP Catherine Anene a wata tattaunawa ta wayar tarho da wakiliyarmu, ta kuma yi watsi...
Ya yi bayanin cewa aikin hanyar mai nisan kilomita 700 da ya tashi daga Abuja ya wuce Kaduna ya nufi Zariya zuwa Kano zai yi matukar rage yawan aukuwar hatsari da cunkoson ababen hawa da zarar aka kammala shi. “Muna da sashe na 1, 2, 3. Sashi na 1 yana Abuja da Neja, sashe na...
Wasu ’yan ta’adda da ake kyautata zaton ’yan Boko Haram ne sun kai hari a sabuwar unguwar Yamtake da ke Ƙaramar hukumar Gwoza a Jihar Borno, inda suka kashe sojoji biyu tare da wasu fararen hula da ba a bayyana adadinsu ba. Majiyoyin tsaro da na cikin gida sun tabbatar da harin, inda suka ce...
Ita Jihar Yobe,rashin biyan sabon mafi krancin albashi da tsohon na Naira 30,000 ga Malaman makarantun ta na Firamare da Sakandare, hakan ta kasance ne saboda rashin amincewa tsakanin Kungiyar NUT da kuma Kungiyar ma’aikatan Kananan Hukumomi ta kasa (NULGE). A ma’aikatar ilimin bai daya ta Jihar Abia, bangaren Kungiyar Malaman makaranta NUT, da reshen...
Shugaban jam’iyyar APC na Jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas, ya fitar da wata sanarwa mai ƙarfi game da yiwuwar dawowar wasu shugabannin siyasa cikin jam’iyyar. A lokacin ganawar da manema labarai a Kano, Abbas ya bayyana cewa APC ba za ta karɓi mutane da hukumomin yaƙi da cin hanci kamar EFCC da ICPC ke...
“Maimakon ya bai wa babban jami’in nasu kudin ya raba wa mutanensa, sai ya zabi rarraba musu shi da kansa”, kamar yadda wata majiya ta shaida wa wannan jarida. Sai dai, wata majiyar ta shaida wa wakilinmu a ranar Larabar da ta gabata cewa, an gayyaci ‘yansandan ne zuwa babban birnin tarayya Abuja, domin ladabtar...

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Bayyana Cewa: Makiya Suna Adawa Da Fadada Alaka Tsakanin Iran Da Saudiyya
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Makiya suna adawa da fadada dangantakar Iran da Saudiyya Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da ministan tsaron Saudiyya Khalid bin Salman a jiya Alhamis. A yayin ganawar, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa, alakar da ke tsakanin...

Shugaban Kasar Iran Ya Ce: Iran Da Saudiyya Za Su Iya Magance Yawancin Matsalolin Yankin Gabas Ta Tsakiya
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Iran da Saudiyya za su iya magance yawancin matsalolin yankin Gabas ta tsakiya Shugaban kasar Iran Mas’ud Pezeshkian ya jaddada cewa: Iran da Saudiyya za su iya magance yawancin matsalolin yankin Gabas ta Tsakiya ta hanyar dogaro da karfinsu a hade ba tare da bukatar shiga tsakani daga kasashen...
Adadin wadanda suka mutu sakamakon luguden wuta da Amurka ta yi kan tashar jiragen ruwan Ra’as Issa ta Yemen ya kai mutane 38 Ofishin kula da kiwon lafiya na lardin Al Hudaidah ya watsa rahoton cewa: Adadin mutanen da suka yi shahaida da wadanda suka jikkata sakamakon harin da Amurka ta kai kan cibiyar man...
Sojojin mamayar Isra’ila sun sake aiwatar da wani sabon kisan kiyashi kan Falasdinawa 5 a sansanin Jabaliya da ke arewacin Gaza Fararen hula 5 da suka hada da yara biyu da mace daya ne suka yi shahada, wasu kuma suka bace sakamakon harin da rundunar sojin mamayar Isra’ila suka kai kan wani gida a sansanin...
Masu wannan fahimta sun yi imanin cewa duk lokacin da mutum ya ji baya son wani abu to a wurinshi wannan abin ba mai kyau ba ne. Haka nan kuma duk lokacin da mutum ya ji cewa ga wani abu amma shi ne ya kwanta mashi, toh wannan abin shi ne mai kyau. Babban misalin...
Gwamnatin tarayya ta jaddada kudirinta na kawo sauyi da kuma zamanantar da kafafen yada labarai na Najeriya da watsa shirye-shirye ta hanyar hadin gwiwa da inganta fasaha. Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Mohammed Idris ne ya bayar da wannan tabbacin a taron manema labarai na 2025 da aka gudanar...
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Gombe, Bello Yahaya ya bayar da umarnin tura isassun jami’ai a fadin jihar domin samar da isasshen tsaro kafin bukin Easter, da kuma bayan bikin Easter. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Buhari Abdullahi ya fitar a...
Rundunar sojin sama na Operation Hadin Kai ta yi nasarar aiwatar da wasu hare-hare ta sama guda biyu, inda ta auka wa maboyar ‘yan ta’adda a yankin Sambisa na jihar Borno da kuma Kudancin Tumbun. A wata sanarwa da Daraktan hulda da jama’a da yada labarai na NAF, Air Commodore Ehimen Ejodame ya fitar,...
Masarautar Gumel ta ce za ta bayar da dukkan goyon baya da hadin kai da ake bukata domin ci gaban yankin kasuwancin da ba shida shinge na Maigatari a jihar Jigawa. Mai Martaba Sarkin Gumel Alhaji Ahmad Mohammad Sani ya bayyana haka a lokacin da ya karbi bakuncin mambobin kwamitin Jiha mai kula da...