2025-03-28@12:30:59 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2586

«Hasken Lantarki»:

    Ina mika sakon gaisuwata ga iyayena da yayyena da kannena, ‘yan uwana maza da mata wadanda muka yi makaranta tare da su, al’ummar Musulmi baki daya, duk ina yi muku fatan alkhairi tare da fatan an yi Juma’a lafiya. Allah ya maimaita mana, ina gaida mijina tare da yi masa fatan alkhairi da fatan an...
    Ana ci gaba da gudanar da jerin gwamnon ranar Kudus ta duniya a birane daban-daban na kasashen duniya. Tashar Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, yanzu haka ana ci gaba da gudanar da jerin gwamnon ranar Kudus ta duniya a birane daban-daban na kasashen duniya. Marigayi Imam Khomeni ne ya ayyana ranar karshe ta kowane...
    “Jami’an ‘yansanda da ke ofishin ‘yansanda, Mayo Belwa, sun isa wurin, inda nan take suka garzaya da wanda abin ya shafa zuwa asibitin Cottage, Mayo-Belwa, domin  kokarin ceton ransa, amma abin takaici, an tabbatar da mutuwarsa a lokacin da ya ke karvar magani.” Kakakin rundunar ‘yansandan ya ce, ya yi saurin shiga tsakanin wanda ake...
    Wakilin kungiyar gwagwarmayar Falastinawa ta Islamic Jihad a Tehran ya bayyana cewa: Ranar Qudus wata dama ce ta samar da hadin kai. A wannan rana al’ummar musulmi suna sabunta alkawarin da suka yi da Allah dangane da batun Palastinu. Ranar Kudus tana hada kai tare da karfafa gwagwarmayar Musulunci a yankin. Ya ci gaba da...
    A safiyar yau ne aka fara gudanar da jerin gwano na ranar Qudus ta duniya a duk fadin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, inda aka samu halartar jama’a da dama karkashin taken “Muna ci gaba da cika alkawarin da muka dauka.” Mahalarta taron za su yi tattaki ne daga masallatai da manyan filaye a birane da...
    Shugaba Bola Tinubu da takwaransa na Ghana, John Mahama, sun  tattauna batutuwa da dama domin  karfafa alakar da ke tsakanin kasashen yammacin Afirka. An gudanar da ganawar ne  a Abuja  bayan da Mahama ya kai wa Tinubu ziyarar ban girma domin yabawa da  halartar shugaban Najeriya a yayin bikin rantsar da shi a Accra, babban...
    Sarkin Musulmi, Mai Alfarma Muhammad Sa’ad Abubakar, ya umarci al’umma da su fara duban watan Shawwal daga gobe Asabar, 29 ga watan Ramadan 1446, wanda ya yi daidai da 29 ga watan Maris, 2025. Shugaban kwamitin harkokin addini na masarautar Sakkwato, Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaidu, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da...
    Mai Bai Wa Gwamnan Sakkwato Shawara kan Harkokin Karkara, Malami Muhammad Galadanchi (Bajare), ya bai wa magoya bayan jam’iyyar APC a jihar, kyautar Naira miliyan 22 domin gudanar da shagalin Sallah Karamar. Yayin bayar da kyautar a ranar Alhamis, Bajare ya ce ya yi hakan ne domin nuna godiyarsa ga jagoran APC a jihar, Sanata...
    Yadda Ake Ba Da Ita Ana ba da ita kafin a fita zuwa Sallar Idi ko kafin Ranar Sallah da kwana daya ko biyu. Abin da ake bayarwa shi ne Muddan Nabiyy (mudun awo ne dan madaidaici wanda za a iya auna shi da cikin tafukan hannun mutum mai matsakaicin tsawo) guda hudu a kan...
    Gwamnatin Jihar Gombe, ta tabbatar da mutuwar mutum uku daga cikin 33 da suka kamu da cutar sanƙarau a jihar. Kwamishinan Lafiya na jihar, Dakta Habu Dahiru ne, ya bayyana hakan yayin ƙarin haske game da ɓullar cutar a jihar. Majalisa ta janye ƙudirin tuɓe wa matakaimakin shugaban ƙasa da gwamnoni rigar alfarma Lakurawa sun...
    kungiyar ta koka kan cewa bai dace a yi amfani da EFCC wajen kamun Jami’an gwamnatin jihar Bauchi da nufin nuna yatsa wa Gwamna Bala Muhammad wanda ya kasance mai fitowa da hakikanin gaskiyar halin da talakawa ke ciki da nema musu hakkinsu daga wajen shugaban kasa. kungiyar ta lura da cewa in ana amfani...
    Rahoton ya bayyana rashin wadataccen abinci mai gina jiki, da wahalhalun tattalin arziki na iya zama ummul-haba’isin muhimman abubuwan da ke haifar da rashin abinci ga yara. A cikin 2024 kadai, Médecins Sans Frontières (MSF) ta ce ta yi wa yara sama da 300,000 maganin tamowa, doriyar kashi 25 cikin 100 daga 2023. Daga cikin...
    A yayin da watan Ramadan ɗin wannan shekara yake bankwana, ga abubuwan da malamai suka bayyana game da fitar da Zakkar kono, wato Zakatul Fidr ga duk wanda ke da hali. Sahabi Abdullahi Ibn Abbas ya ruwaito cewa: “Manzon Allah (SAW) wajbata fitar Zakkar kono domin kankare kurakurai da yasassun maganganun da mai azumi ya...
    Imam sayyid Aliyul Khamina’ie Jagoran juyin juya halin musulunci na kasar Iran yayi kira ga mutanen kasar su fito kwansu da kwarkwatansu don halattar zanga-zangar ranar Kududs ta duniya a yau Jumma’a. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jagoran yana fadar haka a wani jawabin da ya gabatar a jiya Alhahamis da...
    Jiragen ruwan yaki na dakarun juyin juya halin musulunci  IRGC a nan Iran, kanana da manya-manya, har’ila yau da na masu sa kai sun gudanar da faretin jiragen ruwan yaki don raya ranar Kudus ta duniya kwana guda kafin ranar. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto dubban  jiragen yaki da na masu...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa gwamnatin kasar ta Mayarwa Shugaban kasar Amurka Donal Trump amsar wasikarsa ga kasar danagne da shirinta na makashain Nulkiya ta hanyar kasar Omman. Aragchi ya bayyana haka a jiya Alhamis a lokacinda yake hira da kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran. Ya kuma kara...
    Gwamnatin kasar Amurka tana shirin dakatar da bada kudade ga hukumar GAVI wacce take samar da alluran riga kafi don tallafawa kasashe masu tasowa daga ciki har da tarayyar Najeriya. Jaridar Daily Trus ta Najeriya ta nakalto wata sanarwa daga hukumar USAID bayar inda take cewa gwamnatin shugaba Donal  Trump yana son janye tallafin da...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano,m, ta ƙwato kuɗi Naira 4,850,000 tare da mayar da su ga wani mutum da aka sace, bayan sun ceto shi. A wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar, ya bayyana cewa an yi garkuwa da mutumin ne a garin Zakirai, a Ƙaramar Hukumar Gabasawa. An kashe...
    Jihohin da wannan matsalar ta fi shafa sun hada da, Zamfara, Borno, Yobe da kuma Katsina, musamman duba da yadda aukuwar yawan rikice-rikice, ya tarwatsa rayuwar miliyoyin alumomin yakin da fadawa cikin kangin fatara da yunwa da kuma rashin samun wadataccen abinci. A ra’ayin mu, matsalar karancin abinci a kasar nan, ba voyayayen abu bane,...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Lokutan sallah su ne lokuta na farin ciki, godiya ga ni’imar Allah, da kuma ibada. A wannan lokaci, yana da muhimmanci a tabbatar da ayyukan da ake aikatawa sun kasance masu inganci da dacewa da koyarwar addini. NAJERIYA A YAU: Halin Da Matasa Suka Tsinci Kansu A Najeriya...
    Mai magana da yawun ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin ya bayyana cewa, kasar tana matukar adawa da yunkurin Amurka na kara yawan dozin-dozin na kamfanoninta a cikin jerin kamfanonin da aka takaita fitar da kayayyakinsu zuwa kasashen waje. Jami’in, wanda ya bayyana haka a ranar Larabar nan, ya ce, matakin na Amurka ba komai ba...
    Kakakin ma’aikatar kasuwanci ta Sin He Yadong, ya bayyana a yau Alhamis cewa, kasar Sin za ta ci gaba da samar da kyakkyawan yanayin kasuwanci da ya dace da kasuwa, da doka da kuma mizanin kasa da kasa. He Yadong ya bayyana haka ne a gun taron manema labarai na yau da kullum, inda ya...
    Masu fashin baki da dama na da ra’ayin cewa, tabbas illar wannan mataki na Amurka zai koma kanta, inda wasu daga sassan raya tattalin arzikin kasar kamar na albarkatun gona, da makamashi za su iya fuskantar matsin lamba mai tsanani. Yayin da wasu sassan kamfanonin kasar kuma ka iya fuskantar raguwar ribar da suke samu...
    Ɗaya daga cikin ƙasurguman ’yan ta’addan da suka addabi al’umma a Jihar Zamfara da kewaye, Kachalla Isuhu Yellow ya kwanta dama. BBC ya ruwaito cewa an kashe ƙasurgumin ɗan bindigar ne a yayin wani rikicin cikin gida da ya kaure tsakanin ƙungiyoyin ’yan bindiga. Bayanai sun ce lamarin ya faru da yammacin yau Alhamis, bayan...
    Majalisar Wakilai ta janye ƙudurin dokar da ke neman cire rigar kariya ga mataimakin shugaban ƙasa da gwamnoni da mataimakansu. Hakazalika majalisar ta janye amincewa da ƙudurin da ke neman a soke hukuncin kisa ga masu aikata laifi a ƙasar. Sallah: Yadda ake shirin caɓa ado duk da tsadar kaya Majalisa ta buƙaci a rage...
    Babu wata ɗaliba da ke cikin ginin a lokacin da gobarar ta tashi, domin tuni aka sauya wa ɗaliban masauki bisa umarnin jami’ar.   Har yanzu dai hukumomi ba su bayar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai...
    Yau Alhamis, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya gana da ministan kasar Faransa mai kula da harkokin Turai da sauran kasashen waje, Jean Noel Barrot a birnin Beijing. Yayin ganawar, Wang Yi ya ce a lokacin da duniya take fama da yanayi mai cike da sauye-sauye da hargitsi, ya kamata kasashen biyu su...
    A karon farko, karfin lantarkin da tashoshin samar da lantarki da ba sa amfani da man fetur da kwal da Sin ta kafa suka samar, ya zarce kilowatt biliyan 2 zuwa karshen watan Fabrairu. Wannan na kunshe ne cikin sabon rahoton da majalisar kula da lantarki ta kasar Sin ta fitar, wanda ya ce adadin...
    Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya sanar da soke bukukuwan Sallah na bana, saboda bukatar tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar. A wata sanarwa da aka fitar, Sarkin ya bayyana takaicinsa kan matakin amma ya jaddada cewa, tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi shi ne babban abin da ya sa a...
    Majalisar Wakilai ta janye ƙudurin dokar da ke neman cire rigar kariya ga mataimakin shugaban ƙasa da gwamnoni da mataimakansu. Hakazalika majalisar ta janye amincewa da ƙudurin da ke neman a soke hukuncin kisa ga masu aikata laifi a ƙasar. Sallah: Yadda ake shirin caɓa ado duk da tsadar kaya Majalisa ta buƙaci a rage...
    Majalisar Wakilai ta janye ƙudurin dokar da ke neman cire rigar kariya ga mataimakin shugaban ƙasa da gwamnoni da mataimakansu. Hakazalika majalisar ta janye amincewa da ƙudurin da ke neman a soke hukuncin kisa ga masu aikata laifi a ƙasar. Ƙudurorin biyu na cikin ƙudurori 42 da suka tsallake karatu na biyu a jiya Laraba....
    A yau Alhamis sojojin na kasar Sudan sun sanar da abinda su ka kira; Yin shara a cikin birnin Khartum, domin gano inda gyauron mayakan dakarun rundunar sa-kai suka buya. Haka nan kuma sojojin na Sudan sun sanar da sakin farsunoni masu yawa da rundunar kai daukin gaggawa din suka tsare su, a lokacin da...
    A yayin da ake tunkarar bikin ƙaramar sallah, hankalin Musulmi a ko ina a duniya, ya karkata zuwa ga hidimar wannan rana ta musamman, musamman a fannin ado da sabbin kaya. A wata ziyarar da Aminiya ta kai babbar kasuwar tufafi da kayan ado ta Kwari da ke Kano, ta tarar da kasuwa cike maƙil...
    Sojojin Iran sun fitar da bayani a daidai lokacin da ake shirin  raya ranar Kudus ta duniya, suna masu bayyana cewa; Hanyar da za ta warware matsalar Falasdinu ita ce yin gwgawarmaya da kuma samun goyon baya daga al’ummun duniya. Bayanin ya kuma kara da cewa; A daidai lokacin da al’ummar Falasdinu suke fuskantar zalunci,ta’addanci,...
     Jiniyar gargadi ta kada a cikin sassa masu yawa na Falasdinu dake karkashin mamaya  bayan harbo makami mai linzami da mutanen Yemen su ka yi. Kafafen watsa labarun HKI sun ce, jiniyar gargadin ta kada a cikin garuruwa 255 a HKI daga cikin har da birnin Kudus. Jaridar “Yediot Ahronot” ta buga labarin dake cewa,...
    Manzon musamman na ministan harkokin wajen Iran a kan Syria, Muhammad Ridha Ra’uf Shaibani ya gana da karamin minista a gwamnatin kasar Katar inda su ka tattauna halin da ake ciki a kasar Syria, haka nan kuma sun jaddada wajabcin shigar da dukkanin bangarorin al’ummar kasar a cikin sha’anin tafiyar da gwamnati. A jiya Laraba...
    Wakilin dindindin na kasar Sin a ofishin MDD dake Geneva da sauran kungiyoyin kasa da kasa dake Switzerland Chen Xu, ya gabatar da jawabi a jiya Laraba, yayin taro na 58 na kwamiti mai kula da harkokin kare hakkin bil Adama na MDD, don bayyana ra’ayin kasar Sin kan halin da Palasdinu da Isra’ila ke...
    A yayin da muka kammala watan azumin Ramadan, muna gabatar da wannan fadakarwa kan abubuwan da suka kamata mu yi da wadanda za mu guje musu a wannan rana ta farin ciki ta Sallah kamar haka: Zakkar Fidir: Zakatul-Fitr ko Zakkar Fid-da-Kai, ita ce sadakar da ake fitarwa a karshen azumin watan Ramadan. Sunnah ce...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Majalisar Dattawa, ta buƙaci Ma’aikatar Sadarwa da ta yi aiki tare da kamfanonin sadarwa domin rage kuɗin data, ta yadda kowa zai iya samun Intanet mai sauƙi a Najeriya. A zaman majalisar na ranar Laraba, Sanata Asuquo Ekpenyong (APC – Kuros Riba), ya nuna damuwa kan yadda farashin data ya ƙaru da kusan kashi 200....
    Ya kuma yi kira ga iyaye su kula da ’ya’yansu tare da hana su shiga ayyukan da ka iya haddasa tashin hankali. Ya tunatar da al’umma cewa Sallah lokaci ne na zaman lafiya, haɗin kai, da farin ciki, don haka dole ne kowa ya fifita zaman lafiya fiye da bambance-bambancen da ke tsakaninsu. Rundunar ta...
    Kasashen Iran, Lebanon, Iraki, da kuma Yemen sun kaddamar da wani atisayen hadin gwiwa na sojojin ruwa domin nuna goyan baya ga  Falasdinawa a zirin Gaza, wadanda ke ci gaba da fuskantar zalinci  na gwamnatin Isra’ila. An fara faretin hadin gwiwa a tekun Fasha, da yankin gabar tekun Makran, da kuma tekun Caspian da ke...
    Majalisar Dinkin Duniya ta nuna fargaba kan yadda ake ci gaba da samun karuwar matsalar jin kai a zirin Gaza, inda ta bayar da rahoton cewa akalla Falasdinawa 142,000 ne suka rasa matsugunansu a cikin mako guda kacal saboda tsanantar hare-haren bama-bamai na Isra’ila. Kakakin MDD Stephane Dujarric, ya bayyana a wani taron manema labarai...
    Bayanai daga falasdinu na cewa an kashe Hamas Abdul-Latif al-Qanou wani kakakin kungiyar Hamas a wani harin da Isra’ila ta kai a arewacin Gaza. Kamfanin dillancin labaran Quds na Falasdinu ya bayar da rahoton  cewa, jami’in ya yi shahada ne a wani harin da Isra’ila ta kai ta sama a kan tantinsa a garin Jabalia...
    A Isra’ila dubban masu zanga-zanga ne suka taru a Tel Aviv domin nuna adawa da mulkin firaministan kasar Benjamin Netanyahu. Masu zanga zangar sun kuma bukaci a tsagaita bude wuta da kuma sako fursunonin da ake tsare da su a Gaza. Sun rike alluna masu dauke da hotunan wadanda  ake tsare da su a Gaza...
    Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun Litinin 31 ga watan Maris da Talata 1 ga watan Afrilu a matsayin ranakun hutun karamar Sallah. Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin cikin gida wadda babbar sakatariyar ma’aikatar Magdalene Ajani ta sanya wa hannu. A cikin sanarwar, ministan harkokin cikin gida na Najeriya Olubunmi Tunji-Ojo...
    An kama mataimakin shugaban ƙasa na farko a Sudan ta Kudu Riek Machar a babban birnin ƙasar Juba, a yayin da ake ci gaba da samun ƙaruwar zaman tankiya tsakaninsa da Shugaba Salva Kiir. Faɗa tsakanin dakarun da ke goya wa shugabannin biyu baya ya tsananta a yankunan Rejaf da ke kudancin Juba da Wunaliet...
    Gwamnatin jihar Kano ta bayyana kudirinta na tallafawa shirin inganta ilimi na bunkasa Afirka (BEAR) III, wani shiri na hadin gwiwa da hukumar kula da ilimi da kimiya da al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya (UNESCO) da Jamhuriyar Koriya suka yi.   A wata sanarwa mai dauke da sa hannun daraktan wayar da kan jama’a ma’aikatar...
    FRSC, ta miƙa lamarin ga ‘yansanda don bincike, tare da yin kira ga direbobi su kiyaye dokokin hanya domin guje wa irin wannan hatsari. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da...
    Ministan Tsaro, Mohammed Badaru Abubakar ya yi alkawarin inganta sansanin horas da kuratan sojoji dake Zaria wato Depot domin baiwa hukumar Soji damar ci gaba da aikin horaswa a wajen.   Ministan ya yi wannan alkawarin ne a lokacin da ya kai ziyarar tantance sojojin Najeriya da ke Chindit Cantonment a Zariya.   Ministan ya...