2025-03-06@19:16:20 GMT
إجمالي نتائج البحث: 20
«Yarjejeniyar»:
Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya jaddada kudurin Najeriya na aiwatar da cikakken yarjejeniyar biyu da aka kulla tsakanin China Media Group da manyan gidajen watsa labarai na gwamnati a Najeriya – Hukumar Talabijin ta Najeriya (NTA) da Hukumar Rediyon Tarayyar Najeriya (FRCN) a taron hadin gwiwa tsakanin Sin...

Hamas Ta Ce Yarjeniyar Tsagaita Wuta Ne Kadai Za Ta Kubutar Da Fursinonin Yahudawa Daga Hannun Kungiyar
Wani babban Jami’in kungiyar Hamas Osama Hamdan ya bayyana cewa hanya daya tilo ta kubutar da ragowar Fursinonin yahudawan HKI daga hannun kungiyar, kuma ita ce dabbaka bangare na 2 na yarjeniya tsagaita wuta tsakanin kungiyar da kuma HKI. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Osama Hamdan yana fadar haka a jiya...
Kungiyar Hamas wacce take iko da zirin Gaza ta bayyana cewa ba za ta amince da duk wa ta sabon tattaunawa da kuma sauya yarjeniyar tsagaita wuta da aka cimma da HKI dangane da yaki a Gaza ba. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Mahmoud al-Mardawi wani babban jami’in kungiyar yana fadar...
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars wacce ake wa laƙabi da Masu Gida ta doke abokiyar karawarta Enugu Rangers da ci 2-1 a filin wasa na Sani Abacha dake Kano. Wasan wanda aka fara da karfe 4 na yammacin ranar Lahadi, ya na daga cikin manyan wasanni masu zafi da ke ɗaukar hankalin masu sha’awar...
Kungiyar Hamas ta yi kira ga masu shiga tsakani na kasa da kasa da su yi matsin lamba akan ‘yan mamaya su dakatar da azabatar da fiye da mutane miliyan daya da suke yi ta hanyar hana shigar da kayan agaji. Kungiyar ta Hamas wacce ta fitar da sanarwa a yau Lahadi ta ce, matakin...
Shugaban kungiyar Ansarallah ta kasar Yemen Sayyed Abdul-Malik Al-Houthi, ya bayyana cewa Isra’ila na fakewa da goyan bayan Amurka tana keta yarjeejniyar tsagaita wuta a Gaza. Al-Houthi ya bayyana cewar: Kin janyewar makiya daga yankin Rafah, ya zamanto karara karya yarjejeniyar da aka kulla tsakanin Masar da makiya yahudawan sahyoniya. » Ya kara da cewa:...
A ranar 25 ga wata ne zaunannen wakilin kasar Sin a majalisar dinkin duniya Fu Cong, ya bayyana a taron kwamitin sulhu na MDD game da batun Isra’ila da Falasdinu cewa, tilas ne a aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a zirin Gaza baki dayanta, don tabbatar da tsagaita wuta mai dorewa. Ya kuma yi...
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, ta ca zata saki ‘yan Isra’ila shida yau Asabar a matakin karshe na yarjejeniyar tsagaita wuta ta farko da ta cimma da Isar’ila. An kuma tsara Isra’ila za ta saki fursunonin falasdinawa Falasdinawa 602 a wannan Asabar a musayar wacce ita ce ta bakwai tun cimma yarjejeniyar a ranar 19...

Kungiyoyin Hamas Da Jihadul Islami Da Hamas Sun Yi Tirsa Da HKI Kan Azabtar Da Falasdinawa A Gidan Yarin Ofer
Kungiyoyin Hamas, Jihad Isalami da kuma sauransu a kasar Falasdinu da aka mamaye sun bayyana yi allawadi da HKI saboda yadda suke zazabtar da fursinonin Falasdinawa a gidan yarin Ofer, kamar yadda labari ya ke isa daga ca. Tashar talabijin ta Presstv na takalto cewa gidan yarin ofer ya na yammacin birnin Ramallah, a...
Jiragen Yakin HKI Sun kai hare-hare kan wasu muhimman wurare a kudancin kasar Lebanon, wanda hakan keta yarjeniyar tsagaita wuta a tsakanin kasashen biyu. Kamafanin dillancin labaran IP na kasar Iran, ya bayyana cewa jiragen yakin HKI sun kai hare-hare a kusa da kogin Litan, Yohmor Al-shaqif da kuma Zoutr Al-sharqiyya, da kuma Deir Siryan,...
Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya tabbatar da naɗin Sarkin Yarbawan Funtuwa, Oba Alhaji Murtala Sani Adeleke a matsayin sabon Sarkin Yarbawan Jihohin Arewa 19 har da Abuja. Mataimakin Gwamnan JIhar Katsina, Malam Faruk Lawal Jobe ne ya tabbatar da naɗin a madadin gwamnan a lokacin da yake karɓar baƙuncin tawagar Sarakunan Yarbawan Arewa...
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta bayyana cewa yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakaninta da Isra’ila “tana cikin hadari” kuma “zata iya rugujewa,” Bassem Naïm, ne wani mamba a ofishin siyasa na kungiyar, ya bayyana hakan ga kamfanin AFP, yayin da tattaunawar da ake yi kan mataki na biyu na tsagaita bude wuta, da ya kamata...

“Yar Sakon Amurka A Kasar Lebanon Morgan Ortagus Tana Shan Mayar Da Martani Daga Bangarori Mabanbanta
Bangarori mabanbanta na kasar Lebanon suna mayarwa da ‘yar sakon Amurka martani saboda tsoma baki da ta yi a kan yadda za a kafa gwamnati a kasar. Morgan Ortagus wacce ta gana da jami’an kasar Lebanon ta bayyana cewa, bai kamata a kafa gwamnati a kasar ta wakilan kungiyar Hizbullah a ciki ba. Kungiyar malaman...
Sakatare Janar na kungiyar Hizbullah ta Lebanon Sheikh Naim Qasem ya ce gwamnatin Lebanon ce ke da alhakin tabbatar da cewa Isra’ila ta mutunta yarjejeniyar tsagaita bude wuta a kasar ta Lebanon. “Gwamnatin Lebanon, bayan tsawaita yarjejeniyar tsagaita bude wuta, ita ce ke da alhakin bibiyar lamarin da kuma matsa lamba kan kasashe masu sa...
A na sa jawabin Ministan Bunkasa Hakar Ma’adanai Dakta Dele Alake, ya godewa Gallezot, kan yin aikin da ya yi dashi, wajen tabbatar da rattaba hannun wannan yarjejeniyar, duk da karancin lokacin da ake dashi na lokacin da yake da shi, a lokacin da Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya ziyarci Shugaban kasa Bola Tinubu....
Isra’ila ta dakatar da sakin fursunonin Palasɗinawa ba zato ba tsammani yayin da ake ci gaba da musayar fursunoni da waɗanda aka kama ƙarƙashin yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, a cewar rahoton Army Radio. Hukumomi ba su bayyana dalilin dakatarwar ba, kuma babu tabbas kan lokacin da za a ci gaba da tsarin. Wani Ɗan...
Ofishin yada labarai na gwamnati a zirin Gaza ya sanar da cewa Falasdinawa kusan 300,000 da suka rasa matsugunansu ne suka koma gida a gabar tekun a ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma da kungiyar Hamas. “Wannan ya zo ne bayan kwanaki 470 na kisan kiyashi da sojojin mamaya na...
An tsawaita yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin Isra’ila da Lebanon na tsawon kimanin makonni uku bayan da gwamnatin kasar ta ki janye dakarunta kamar yadda aka kulla da farko. An bayyana cewa yarjejeniyar tsakanin kasashen biyu za ta ci gaba da aiki har zuwa ranar 18 ga Fabrairu, 2025. Shi ma firaministan kasar Labanon Najib...
Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta bayyana cewa: Tun a shekara ta 2000 al’ummar Lebanon suka tabbatar da cewa su ne jagororin gaskiya a kan tafarkin nasara Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta fitar da wata sanarwa a jiya Lahadi, inda ta jaddada cewa: Daidaiton sojoji da al’umma da kuma ‘yan gwagwarmaya da suke kare...
Bayan tsawon shekaru 40 a tsare, shugaban fursunonin Falasdinawa, Mohammed Al-Tous, ya samu ‘yancinsa Kungiyar kula fursunonin Falasdinawa da suke tsare a gidan yarin haramtacciyar kasar Isra’ila ta bayyana cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila ta saki Muhammad al-Tous, wanda shi ne fursuna mafi tsufa a hannunta, tare da tasa keyar shi tare da wasu fursunoni 69...