2025-02-22@21:54:40 GMT
إجمالي نتائج البحث: 419
«Masara»:
Shugaban kungiyar dalibai ta makarantar (SUG), Comrade Haruna Umar, ya bayyana cewa marigayiya tana cikin shirye-shiryen kammala rajistar ta a makaranta ne ma kafin rasuwarta, kana ya roƙi ɗalibai da su kasance cikin hakuri da lumana, yana mai tabbatar da cewa hukumar makaranta da ta tsaro suna iya ƙoƙarinsu na ɗaukar matakan da suka dace...
NAFDAC Ta Rufe Shaguna Da Wuraren Ajiyar Magunguna Marasa Inganci A Legas
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Filato, ta kama wani matashi tare da wasu mutum uku kan zargin safarar harsasai daga Jos zuwa Abuja. Matashin ya bayyana cewa ’yan ta’adda sun biya shi Naira 50,000 domin ya karɓo harsasai daga Jos zuwa Abuja. Majalisa na neman rushe ƙudirin ƙara kuɗin kira da data Noman rani ne zai...
Ma’aikatar ilimi ta jihar Kano ta fara rangadin tantancewa a kauyukan jihar, gabanin shirin wayar da kan al’umma game da yaran da ba su zuwa makaranta. Ziyarar na da nufin gano musabbabin wannan matsala tare da nemo mafita ta hanyar hada kai tsakanin al’umma. Kididdigar da Asusun yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya...
Majalisar Wakilai ta buƙaci Hukumar Kula da Sadarwa (NCC) ta janye ƙarin kashi 50 na kuɗin waya da data da ta amincewa kamfanonin sadarwa su yi. Wannan dai na zuwa ne a yayin da ɗan majalisar daga Jihar Bayelsa, Oboku Oforji ya gabatar da ƙudirin kan lamarin. Majalisar ta ce ƙarin bai kamata ba a...
Iran ta yi kakkausar suka kan barazanar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi na yin amfani da karfi a kan kasar, inda ta bayyana hakan a matsayin barazana da rashin da’a. A cikin wata wasika da ya aike a wannan Talata zuwa ga shugaban Majalisar Dinkin Duniya da shugaban kwamitin sulhu na dindindin jakadan...
Kasar Aljeriya ta yi marhabin da shirin Iran na gudanar da taron kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC a zirin Gaza, wanda shugaban na Amurka ya ce yana son karbe iko tare da raba al’ummar kasar baki daya. Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya gabatar da shawarar gudanar da wani zama na...
Wakilin LEADERSHIP Hausa Ya Zama Shugaban Wakilan Kafafen Yaɗa Labarai A Kebbi

Jaridar Telegraph Ta Ce; Shugabannin Sojojin Iran Sun Bukaci Jagora Da Ya Soke Fatawar Haramci Kera Makamin Nukiliya
Jaridar Daily Telegraph ta watsa labarin cewa: Shugabannin Iran sun bukaci Jagoran juyin juya halin Musulunci Sayyid Khamenei da ya janye fatawarsa kan haramcin mallakar makamin nukiliya Jaridar Daily Telegraph ta kasar Birtaniya ta watsa rahoton cewa: Shugabannin sojojin Iran sun bukaci Jagoran juyin juya halin Musulunci Sayyid Ali Khamenei ya yi watsi da haramcin...
Kasar Saudiyya ta jaddada matsayinta na yin watsi da kalaman masu tsattsauran ra’ayin sahayoniyyanci game da korar Falasdinawa daga muhallinsu Saudiyya ta jaddada cewa: Tana yi watsi da kalaman masu tsattsauran ra’ayin sahayoniyyanci game da neman tilastawa al’ummar Falasdinu yin hijira daga yankunansu, kuma ta nuna cewa ba za a samu dawwamammen zaman lafiya ba...
Ya ce: “A baya, muna da wasu hukumomi da ke ƙayyade farashin kayan abinci, amma domin kasuwanci na ’yanci da bunƙasa harkokin noma, gwamnati ba ta ga dacewar ci gaba da hakan ba. “Yanzu abin da gwamnati ke yi shi ne ta tabbatar da cewa ana samar da isassun kayan abinci, domin idan abu...
An cafke wani saurayi mai kimanin shekaru 13 bayan ya je rajistar layin wayar salula a yankin ’Yan Katako da ke Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa. Rundunar ’yan sandan Filato ce ta yi wa manema labarai holen saurayin mai suna Umar Hashim tare da wasu mutum shida da ake zargi da garkuwa da kuma kisan...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Zanen fuska na da dadadden tarihi a Arewacin Najeriya musamman a kasar Hausa. Sai dai wannan dadaddiyar al’ada tana kan hanyar gushewa domin kuwa ba kasafai ake samun wadanda suke yin ta a wannan zamani ba. NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ke Hana Matan Arewa Karantar Ilimin Kimiyya?...
“Wannan shi ne dalilin da ya sa Gwamna Dauda Lawal ya bayyana a cikin takardar yaƙin neman zabensa gabanin zaben 2023 cewa batun tsaro ne zai sa a gaba, inda ya yi alƙawarin aiwatar da matakan shawo kan lamarin. “A halin yanzu an shaida cewa Gwamna Lawal ya cika alƙawarin. “Gwamnatin Gwamna Dauda Lawal ta...

’Yan Wasan Motsa Jiki Na Asiya Sun Yi Murnar Bikin Sabuwar Shekara Bisa Kalandar Gargajiya Ta Sin A Harbin
An gabatar da bikin mu’ammalar al’adu a jiya Litinin a birnin Harbin da ake wa lakabin “Birnin kankara”, yayin da ake gudanar da gasar wasannin motsa jiki na lokacin hunturu ta Asiya karo na 9 a birnin. An yi wannan gaggarumin biki ne bisa jigon “bikin sabuwar shekara ta kalandar gargajiya ta kasar Sin, wato...
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka. Sharhin bayan labarammu zai yi magana ne dangane da barazanar shugaban kasar Amurka ga JMI “Ko ta yarda da ta zauna kan teburin tattaunawa da ita kan shirinta na makamashin nukliya ko kuma ya tura HKI ta fermata da yaki’. Wanda ni tahir amin zan karanta. ///… A...
Masu zanga-zangar wadanda ke dauke da alluna da rubuce-rubuce daban-daban sun ce, dole ne kamfanin ya samar da mafita mai dorewa tare da maido da wutar lantarki a tashar wutar lantarki ta ‘Kwara Poly feeder’ da ke rarraba wutar ga al’ummomin yankin.
Kungiyar masu samar da motoci ta kasar Sin CPCA, ta ce bangaren fitar da motoci daga kasar Sin zuwa kasashen ketare, ya ci gaba da samun tagomashi a shekarar 2024. A cewar CPCA, kasar Sin ta fitar da jimilar motoci miliyan 6.41 zuwa kasashen waje a bara, adadin da ya karu da kaso 23 bisa...
Gwamnatin Jihar Jigawa ta kara jaddada kudurinta na yin hadin gwiwa da wani kamfanin sarrafa dabino da kayan marmari domin inganta noman dabino da alkama a jihar. Gwamna Umar Namadi ya bada wannan tabbaci a lokacin da tawagar Babban Daraktan kamfanin, Dakta Abubakar Musa Bamai ta ziyarci shi a gidan Gwamnati dake Dutse, Babban...
Kafafen watsa labarun HKI sun ce; Barazanar da ake yi wa kungiyar Hamas ba ta wani tasiri a gare ta. Kafafen watsa labarun na HKI suna yin tambaya akan yadda Hamas din take isar da sakwanni a fakaice ga Isra’ila a yayin bikin mika fursunoni da take shiryawa. Tashar talabijin din ta 12: ta ambaci...
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi barazanar cewa matukar Falasdinawa ba su saki fursunonin Isra’ila ba daga nan zuwa Asabar, to za a kawo karshen tsagaita wutar yakin da aka yi, da komawa yaki. Shugaban kasar ta Amurka ya shata wa’adin 12: 00 Na ranar Asabar a matsayin lokacin karshe na mika fursunonin. Shugaban...
Dalibai 179 za su samu shaidar Digiri Mai Daraja ta Ɗaya a yayin bikin yaye ɗalibai na Jami’ar Bayero ta Kano (BUK). Shugaban Jami’ar Bayero, Farfesa Sagir Abba, ya bayyana cewa dalibai 4,402 ne za a yi bikin yaye su a ranar farkon, inda a za a ba su shaidar kammala Digirin farko da Difloma...
Dalibai 179 za su samu shaidar Digiri Mai Daraja ta Ɗaya a yayin bikin yaye ɗalibai na Jami’ar Bayero ta Kano (BUK). Shugaban Jami’ar Bayero, Farfesa Sagir Abba, ya bayyana cewa dalibai 4,402 ne za a yi bikin yaye su a ranar farkon, inda a za a ba su shaidar kammala Digirin farko da Difloma...

Sojojin Mamayar Isra’ila Suna Ci Gaba Da Murkushe Falasdinawa A Birnin Tulkaram Da Ke Gabar Yammacin Kogin Jordan
Sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da rusa ababen more rayuwa a birnin Tul-karam da sansanoninsa na Falasdinu tare da kama Falasdinawa da tilasta wa jama’a yin gudun hijira Sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da kai hare-hare kan birnin Tul-Karam da sansanoninsa guda biyu Tul-karam da Nourul- Shams a rana ta 16 a jere,...
Wani sanatan Amurka yana barazana ga shugaban kasar Tunisiya da neman rusa nasarar dimokuradiyyar kasar Sanatan Amurka Joe Wilson, dan majalisar wakilai daga shiyar kudancin jihar Carolina, ya kaddamar da hari kan shugaban kasar Tunusiya Qais Sa’id, inda ya dauke shi a matsayin “dan mulkin kama karya” tare da yin kira da a kakabawa Tunisiya...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Dakta Zainab Muhammad na daga cikin matan Arewacin Najeriya da ta jajirce tare da ƙudirin cika burinta na karantar kimiyya duk da ƙalubalen da wasu matan yankin ke bayyana cewa suna fuskanta wurin karantar fannin. Dakta Zainab ba kimiyya kawai ta karanta ba, ta karanci ɗaya daga cikin...
Kungiyar kula da harkokin jigilar kayayyaki da sayen kayayyaki ta kasar Sin ta samar da adadin sana’o’in adana kayayyaki na Sin a watan Janairun da ya gabata cewa, wanda ya nuna cewa, yawan bukatun ajiye kaya a Sin ya bunkasa cikin sauri duba da karuwar bukatun sayayya a lokacin bikin sabuwar shekara, kuma sana’o’in adana...
Wani sabon babi na takaddamar cinikayya a duniya na kunno kai biyo bayan sabon matakin da shugaban Amurka Donald Trump ya dauka na karin harajin kashi 10 cikin dari kan kayayyakin da Sin ke shigowa da su kasarsa, lamarin da ke ci gaba da rura takun sakar kasuwanci a duniya. Tabbas wannan ba maganar haraji...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa, kasar Iran ba zata taba zama don tattaunawa da kasar Amurka ba a dai-dai lokacin take kara takurawa kasar da takunkuman tattalin arziki ba. Tashar talabijin ta Presstva nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka bikin ciki shekaru 46 da samun nasarar juyin juya...
Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal Dare, ya bayyana cewa sharaɗinsa na sulhu da ’yan bindiga shi ne kawai su daina kashe-kashe su zubar da makamai sannan su miƙa wuya. A baya dai Gwamna Dare ya sha nanata cewa ba zai yi sulhu da ’yan fashin daji ba. Gwamna Sule ya naɗa Kwamishinoni 16 a Nasarawa Atiku...

Shugaban Kungiyar Hamas Yace: Iran Bata Gusheba Tana Taimaka Mana, Kuma Shirin Trump Na Kwace Gaza Zai Ya Lalace
Khalilul Hay, shugaban kungiyar Hamas a Gaza, wanda ya halarci gangamin bikin cika shekaru 46 da nasarar juyin juya halin musulunci a kasar Iran, ya bayyana cewa yakin Tufanul Aksa ya na matsayin mataki na farko ne na kwatar kasar Falasdinu daga hannun wadanda suka mamayeta. Ya kuma kara da cewa JMI ta taimakawa kungiyar...
Sam Nujoma, dan gwagwarmaya neman yencin kasar Namibiya karkashin gwamnatin wariyar launin fata ta Afrika ta kudu, ya rasu a jiya Lahadi kamar yanda gwamnatin kasar ta Namibi a ta bada sanarwa. Shugaban kasar ta Namibia mai ci, Nangola Mbumba ya ce tsohon shugaban kasar ya na jinya a as wani asbiti a babban birnin...
An yi wa dubban mutane gwajin lafiya kyauta a Indonesiya don kauce wa mutuwa da wuri. Za a yi gwajin ga ɗaukacin ‘ƴan kasar ne a ranar murnar bikin haihuwarsu, domin cika alkawarin da shugaba Prabowo Subianto ya yi lokacin yaƙin neman zaɓe. Jarirai da ƙananan yara da kuma tsofaffi na cikin waɗanda za a...
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA ta gabatar da kayan agaji ga gwamnatin jihar Zamfara domin tallafawa wadanda gobara ta shafa a wata makarantar Islamiyya da ke Kaura Namoda. A lokacin da take mika kayayyakin, Darakta Janar na Hukumar Hajia Zubaida Umar, ta ce matakin ya nuna damuwar gwamnatin tarayya kan halin...
Sojojin Najeriya sun tarwatsa babbar maɓoyar ƙasurgumin ɗan Bello Turji da ke ƙauyen Garin Fakai a Jihar Zamfara. Wanann nasarar zai gurgunta harkokin ƙasurgumin ɗan ta’addan, wanda a halin yanzu ke wasan ɓuya da jami’an tsaro. Ƙauyen Fakai shi ne babbar mafakar Bello Turji, ɗan ta’addan da ke addabar yankin Zamfara da sassan Jihar Sakkwato....
Sanarwar ta kuma bayyana cewa wannan ziyara ta gwamnan, za ta ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar Zamfara da Bankin na Duniya. Cikin jawabin sa a wurin, Gwamna Dauda Lawal ya jaddada ƙudirin gwamnatin sa na ƙarfafa dangantakar ta Bankin Duniyar. “Ina so in fara da nuna godiya ta ga Bankin Duniya game...
Wani ɗalibi a Kwalejin Kimiyya da Ƙere-kere ta Tarayya da ke Jihar Nasarawa ya yi wa abokin karatunsa kisan gilla ta hanyar amfani da wuƙa da gatari. Rundunar ’Yan Sanda Jihar Nasarawa ta ce ɗalibin da ya yi kisan gillar ɗan ajin ND2 a Fannin Aikin Banki da Hadahadar Kuɗaɗe ne a Kwalejin kuma yana...
Sojojin Najeriya sun tarwatsa babbar maɓoyar ƙasurgumin ɗan Bello Turji da ke ƙauyen Garin Fakai a Jihar Zamfara. Wanann nasarar zai gurgunta harkokin ƙasurgumin ɗan ta’addan, wanda a halin yanzu ke wasan ɓuya da jami’an tsaro. Ƙauyen Fakai shi ne babbar mafakar Bello Turji, ɗan ta’addan da ke addabar yankin Zamfara da sassan Jihar Sakkwato....
Wasu ’yan daba sun gine-ginen makaranta a yankin Okpoga da ke Karamar Hukumar Okpogwu da ke Jihar. Ɓata-garin sun ƙona gine-ginen ne a Makarantar Sakandaren Central UBE da ke Ogwu-Okpoga da kuma Makarantar Ƙaramar Sakandare s ake Obossa. Wani shaida ya bayyana wa wakilinmu cewa a makon da ya gabata ne ’yan daban suka yi...
Ma’aikatar harkokin wajen Masar ta sanar cewa, kasar za ta karbi bakuncin taron gaggawa na kasashen Larabawa a ranar 27 ga watan Fabrairun nan, domin tunkarar al’amura na baya-bayan nan da suka shafi batun Falasdinu da zirin Gaza. Sanarwar ta ce, an yanke shawarar gudanar da taron ne bayan muhimman shawarwarin da Masar ta yi...
“Zaben Alhaji Ibrahim Ibn Umar El-Kanemi, a matsayin sabon Shehun Dikwa, an gudanar da shi cikin lumana da hadin kai wanda sarakunan masarautar suka taka rawar gani wajen zakulo wanda ya dace,” in ji Zulum. Ya bukaci sarkin da ya yi ba da jagoranci daidai da irin kalubalen zamani, yana mai jaddada rawar da...
’Yan sanda a Babban Birnin Tarayya Abuja sun buƙaci al’umma su kawo musu rahoton duk wanda aka ga yana sana’ar bola-jari a cikin gari. Kwamishinan ’Yan Sanda na Abuja, Disu Olatunji, ne ya sanar da haka bayan taron Majalisar Tsaro ta Babban Birnin Tarayya wanda Minista Ezenwo Nyesom Wike ya jagoranta. Idan ba a manta...
Yanzu haka, an kara tura manyan injuna domin gudanar da aikin ceto a wurin da zaftarewar kasa ta auku a lardin Sichaun na kasar Sin. Da farko za su kwashe duwatsu da kasa da suka lullube wurin, kuma da zarar an ga alamun gini, za a sanar da ma’aikatan dake wurin domin kara bincike. Zuwa...
Alkaluman farashin kayayyakin masarufi na kasar Sin (CPI), wanda ke auna matakin hauhawar farashin kayayyakin, sun daga da kaso 0.5 bisa dari a watan Janairu. Adadin ya karu ne kan kaso 0.1 bisa dari da ya kasance a baya, galibi saboda hutun bikin bazara na sabuwar shekarar gargajiya ta kasar Sin, a cewar hukumar kididdigar...

Sharhin Bayan Labarai “Yadda JMI Ta bunkasa Bangaren Gine-Gine Da Masana’antu Da Kamfanonin Tare Da Fasahar Cikin Gida”
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na sharhin bayan labarai, wanda zai yi magana a kan “Yadda JMI Ta Bunkasa Sana’argine-gine da da kamfanoni tare da amfani da fasahar cikin gida’ wanda ni tahir amin zan karanta. Tun bayan nasarar juyin juya halin musulunci a nan kasar...
A rana Juma’a da ta gabata, aka kaddamar da gasar wasannin kankara ta nahiyar Asiya karo na 9, a birnin Harbin na lardin Heilongjiang na kasar Sin. Wannan gasa ta kasance babbar gasar wasannin kankara ta kasa da kasa karo na 2 da Sin ta karbi bakuncinta, biyo bayan gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi...
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Masar ta sanar da kiran taron kasahen larabawa a karshen wannan watan na Febrairu da ake ciki domin tattauna batun tilasta wa Falasdinawa yin hijira daga Gaza a karkashin shirin Amurka da Isra’ila. Da safiyar yau Lahadi ne dai ma’aikatar harkokin wajen ta Masar ta bayyana cewa za ta karbi bakuncin...
Wata gobara da ta tashi a wajen sayar da gas a Sabon Wuse da ke Ƙaramar Hukumar Tafa a Jihar Neja, ta yi sanadin ƙonewar motoci da shaguna da kuma kayan abinci. Lamarin ya faru ne a daren ranar Asabar lokacin da wata tanka ke sauke gas a wajen sayar da gas. Gwamnatin Kano ta...
Sojojin mamayar Isra’ila sun fara janyewa daga yankin Netzarim da ke tsakiyar Zirin Gaza Kafofin yada labaran haramtacciyar kasar Isra’ila sun tabbatar da cewa: Sojojin mamayar Isra’ila za su fara ficewa daga yankin Netzarim da ke tsakiyar Zirin Gaza a daren jiya. Jaridar Yedioth Ahronoth ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta watsa rahoton cewa: Rundunar sojin...
Sojojin Sudan suna kokarin canza ma’aunin yaƙin kasar bayan da suka sun tunkari birnin Khartoum fadar mulkin kasar domin yantar da shi gaba daya Babban birnin kasar Sudan, Khartoum, shi ne tushen rikicin kasar da a halin yanzu aka shafe makonni ana gwabza fada tsakanin sojoji da mayakan dakarun kai daukin gaggawa, amma fadan ya...