2025-02-21@14:22:10 GMT
إجمالي نتائج البحث: 356
«Makarantar Allo»:
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kara kudirin kasafin kudin shekarar 2025 daga naira tiriliyan 49.7 zuwa naira tiriliyan 54.2, yayin da majalisar dokokin kasar ke kokarin ganin an zartar da shi kafin karshen wata. Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya sanar da karin kasafin ta hanyar wasiku daban-daban da shugaba Tinubu ya aikewa majalisar...
Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kauyen Tsiga da ke karamar hukumar Bakori a jihar Katsina inda suka yi garkuwa da tsohon Darakta Janar na Hukumar Kula da Matasa masu yi wa kasa hidima NYSC, Birgediya Janar Maharazu Tsiga mai ritaya da wasu mutum takwas. Majiya mai tushe ta bayyana hakan ga gidan rediyon Najeriya...
Shugaba Bola Tinubu, ya buƙaci hukumomin ilimi su tabbatar da cewa makarantun gwamnati da masu zaman kansu sun ɗauki matakan kare ɗalibai daga haɗura. Wannan kira na zuwa ne bayan da wata gobara ta yi ajalin almajirai 17 a wata makarantar tsangaya da ke garin Ƙauran Namoda, a Jihar Zamfara. Allah Ya yi wa Sheikh...
Rundunar ƴansanda ta jihar Kwara ta daƙile yunƙurin sace mutane biyu tare da cafke mutum huɗu da ake zargi da hannu a lamarin a ƙananan hukumomin Ifelodun da Baruten. Kakakin rundunar, Toun Ejire-Adeyemi, ya bayyana cewa jami’an tsaro sun cafke su ne bayan bin diddigin kiran wayar barazana da wasu mutane suka samu a Ifelodun...
Wata gobara da ta tashi a Ƙauyen Zago da ke Ƙaramar Hukumar Danbatta a Jihar Kano, ta ƙone gidaje, amfanin gona, da dabbobi, lamarin da ya janyo wa mazauna ƙauyen asara mai tarin yawa. Gobarar, ta fara ne da safiyar ranar Laraba, inda ta ƙone gidaje da dama tare da lalata hatsi da sauran amfanin...
’Yan bindiga su yi garkuwa da tsohon Shugaban Hukumar Masu Yi Wa Kasa Hidima (NYSC), Manjo-Janar Maharazu Tsiga (ritaya). Rahotanni daga mahaifarsa Jihar Katsina na cewa maharan sun yi garkuwa da Janar Tsiga ne a ranar Laraba da dare. Bayanan sun bayyana cewa ƙauyensu Tisga da ke ƙaramar hukumar Ƙanƙara ta Jihar Katsina ne maharan...
An kama wani ɗalibin firamare mai shekara 13 ɗauke da bindiga a makaranta, inda yake barazanar harbe abokan karatunsa da ita. Bayan nan ne jami’an tsaro suka yi nasarar kama shi a Makarantar Firamare ta St. Paul da ke ƙauyen Ikot Ibiok a Ƙaramar Hukumar Eket a Jihar Akwa Ibom. A safiyar Alhamis ne kakakin...
Rundunar ƴansanda ta jihar Kwara ta daƙile yunƙurin sace mutane biyu tare da cafke mutum huɗu da ake zargi da hannu a lamarin a ƙananan hukumomin Ifelodun da Baruten. Kakakin rundunar, Toun Ejire-Adeyemi, ya bayyana cewa jami’an tsaro sun cafke su ne bayan bin diddigin kiran wayar barazana da wasu mutane suka samu a Ifelodun...
Mai martaba Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya yi kira da a zaman lafiya da hakuri a tsakanin al’ummar garin Rimin Zakara sakamakon rikicin filaye da ya barke tsakanin al’umma da Jami’ar Bayero ta Kano (BUK). Sarkin ya yi wannan roko ne a ziyarar da ya kai yankin bayan dawowarsa daga aikin...
Kwanan baya, kasar Amurka ta sanar da kara harajin kashi 10 cikin dari a kan daukacin kayayyakin kasar Sin da ake kaiwa kasar, tare da kafa hujja da wasu batutuwa irin su maganin Fentanyl. Bayan haka, nan take kasar Sin ta sanar da daukar matakan mayar da martani a kan karin harajin Amurka domin kare...
Wata Babbar Kotu a Jihar Akwa Ibom, ta yanke wa Farfesa Ignatius Uduk hukuncin ɗaurin shekaru uku a gidan yari kan laifin sauya sakamakon zaɓe. An gurfanar da Farfesan kan tuhume-tuhume uku da suka haɗa da gazawa wajen aiwatar da aikinsa, sauya sakamakon zaɓe, da kuma yin rantsuwar ƙarya a gaban kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓe....
“Canada, Mexico da Sin su ne suke sayen rabin duk kayayyakin amfanin gona da Amurka ke fitarwa. Kasuwanni ne da muke bukata babu makawa don raya tattalin arzikin Amurka. Sanya haraji kan manyan kasuwannin fitar da kayayyakin guda uku na noma da kiwo na Amurka, musamman na dogon lokaci zai haifar da mummunan sakamako,” in...
Sakamakon yadda kasar Sin take ci gaba da zurfafa yin gyare-gyare a gida daga dukkan fannoni, da kyautata bude kofa ga ketare bisa matakin koli, ya sa kasar ta Sin za ta ci gaba da kara azama kan bunkasar tattalin arziki. Za kuma ta ci gaba da nuna kuzari kan raya kanta tare da amfanar...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Iran za ta mayar da martani ga duk wata barazana ko matsin lamba gwargwadon tsayin dakarta Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya bayyana cewa: Iran ta sha tabbatar da cewa a shirye take ta gudanar da huldar siyasa da diflomasiyya don tabbatar da moriyar...
Sojojin Sudan sun kwace iko da birnin Al-Kamlin da ke jihar Aljazira a tsakiyar kasar Rundunar sojin Sudan ta sanar a yau jiya Talata cewa: Sojojinta da mayakan da suke goya musu baya sun kwace iko da birnin Al-Kamlin da ke jihar Aljazira a tsakiyar kasar, kuma babban hafsan hafsoshin rundunar sojin kasar Janar Abdul-Fattah...

An Samu Yuan Biliyan 9.51 Daga Sayen Tikitin Kallon Fina-Finai A Lokacin Hutun Bikin Bazara A Kasar Sin
An Samu Yuan Biliyan 9.51 Daga Sayen Tikitin Kallon Fina-Finai A Lokacin Hutun Bikin Bazara A Kasar Sin
Da yake magana ta wayar tarho game da mummunar gobarar, Shugaban ƙaramar hukumar Kaura-Namoda, Comrade Mannir Muazu Haidara, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce yana kan hanyarsa domin duba halin da ake ciki kuma zai bayar da karin bayani daga baya.
Ministan Tsaro, Muhammad Badaru Abubakar, ya bayyana cewa sun kusa da kama ƙasurgumin ɗan ta’addan nan da ya addabi yankin Arewa Maso Yamma, Bello Turji. Ministan ya ƙara da cewa Gwamnatin Tarayya tana da tabbacin cewa matsalar tsaro za ta zama tarihi kafin ƙarshen shekarar 2025. Sarkin Jiwa a Abuja ya yi rashin mahaifiya Tinubu...
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya buƙaci a ƙara adadin kasafin kuɗin shekarar 2025 daga Naira tiriliyan 49.7 zuwa Naira tiriliyan 54.2. Wannan buƙata na ckkin wata wasiƙa da ya aike wa Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, wadda aka karanta a zaman majalisar na ranar Laraba. Tinubu zai tafi Faransa daga nan ya zarce...
A yau ne shugaba Bola Ahmed Tinubu zai tashi daga Abuja zuwa birnin Paris na kasar Faransa a wata ziyarar kashu kai, inda daga nan zai wuce Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha. A cikin wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga ya fitar, ya ce...
Ancelotti ya shaidawa manema labarai ranar Talata cewa “Bellingham ya samu rauni yayin atisaye amma kuma Vinicius Jr zai buga wasan gobe duk da cewar har yanzu ya na kan murmurewa daga raunin da ya ji a watan jiya Ya kuma ce Mbappe ya yi atisaye kamar yadda aka saba a yau, amma gobe...
Shugaba Bola Tinubu a wannan Larabar zai bar Nijeriya zuwa ƙasar Faransa domin kai wata ziyara ta ƙashin kai. Daga nan kuma Shugaba Tinubu zai wuce ƙasar Habasha inda zai halarci taron gamayyar ƙungiyar ƙasashen Afirka ta AU. NAHCON ta tsawaita wa’adin biyan kuɗin Hajjin bana Dalilin da farashin citta ya yi tashin gwauron zabo...
Shugaba Bola Tinubu a wannan Larabar ya bar Nijeriya zuwa ƙasar Faransa domin kai wata ziyara ta ƙashin kai. Daga nan kuma Shugaba Tinubu zai wuce ƙasar Habasha inda zai halarci taron gamayyar ƙungiyar ƙasashen Afirka ta AU. NAHCON ta tsawaita wa’adin biyan kuɗin Hajjin bana Dalilin da farashin citta ya yi tashin gwauron zabo...
Sojojin sama na JMI sun sami nasarar kakkabo jiragen yaki na makiyan da aka sawwara, tare da amfani da makami mai suna Majid a cikin atisayen sojojin sama da suke gudanarwa a kudu masu yammacin kasar. Jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa dai, suna da masu muhimmanci a yakin zamani a halin yanzu, don...
An kuma samu labarin cewa ɗalibin ya rasa mahaifinsa a wasu shekarun baya, lamarin da ya mahaifiyarsa wadda tsohuwar malamar makaranta ce ta ci gaba da ɗaukar nauyin karatunsa tun daga lokacin. Rahotanni sun nuna cewa matsalarsa ta ƙara tsananta tun bayan dawowarsa makaranta a bara, inda abokan karatunsa suka tara kuɗi domin biya...
A bayan nan ne Amurka ta sanya harajin kashi 25 a kan kayayyakin da ake shigar wa ƙasar daga Canada da Mexico da kuma kashi 10 kan kayayyakin makamashi na Canada, yayin da kayayyakin China za su fuskanci harajin kashi 10. Sakatariyar yaɗa labaran Fadar White House, Karoline Leavitt, ce ta bayyana hakan a yayin...
A yayin da farashin buhu daya na danyar citta da ke a matsayin iri ya yi tashin gwauron zabon da ba a taɓa ganin irin sa ba, inda ake sayar da shi a kan Naira 210,000 kowane buhu, shi kuwa busasshen buhun citta ana sayar da shi ne daga Naira dubu 500,000 zuwa Naira 550,000...
A kwanakin baya Hausawa mazauna Jahar Imo suka yi bikin cika shekara 153 da zama a garin Owerri Fadar Gwamnatin Jihar Imo da ke yankin Kudu maso Gabas yankin da ake kira da Ibo. Hausawa mazauna Jihar Imo da ke Owerri babban birnin jahar a kwanan baya sun yi bikin cika shekara 153 da zuwa...
Jaridar Politico ta buga wani rahoton dake cewa sojojin kasar Ukiraniya suna fuskantar matsin lamba mai yawa, da kuma rashin kwararrun mayaka. Wannan matsin lambar da sojojin kasar suke fuskanta ya sa ana tunanin mayar da sojojin sama zuwa na kasa da tura su filin daga. Har ila yau jaridar ta ambaci yadda sojojin da...
Rahotanni sun ambaci cewa bayan ficewar sojan Faransa na karshe daga sansanin Abaci dake gabacin kasar Chadi,kasar Turkiya tana shirin maye gurbinta. Wata majiyar kasar Turkiya ta shaidawa wata kafar labaru ta Afirka cewa, Ankara tana shirin girke jiragen yaki marasa matuki a cikin sansanin dake kan iyaka da kasar Libya akokarin da take yi...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A da akan kwashe kwanaki ana bukukuwan aure a ƙasar Hausa, kama daga kamu, zuwa sa lalle, yinin biki da zaman ajo zuwa buɗar kai da sayen baki. Sai dai waɗannan al’adu sannu a hankali suna ta gushewa. Ko mene ne dalilin wannan sauyin? NAJERIYA A YAU: Hanyoyin...
Hukumar kula da aikin Hajji ta kasa NAHCON ta sanar da a ci gaba da yi wa maniyyata rajista har zuwa ranar Litinin 10 ga watan Fabrairu, 2025. A daren Talata 4 ga watan ne hukumar ta amince da kara lokacin a taron da ta yi da shugabannin hukumomin alhazai na jihohi. Wata sanarwa da...
Ministan ya kara da cewa, za a kaddamar da kashin farko na gyaran madatsar ruwan a tsakanin watan Fabrairu zuwa Yulin 2025. Ya kuma kara jaddada muhimmancin wannan aiki na tabbatar da cewa ba a samu ambaliyar ruwa a jihar Borno a shekarar 2025 ba.
Haruna, mazaunin Unguwar Kanawa Dutse Abba, an rahoto cewa, ya jagoranci ‘yan bindiga uku – Shago Yaro, Tanimu Ayuba, da kuma Lamido Dantajiri zuwa gidan dansa, Alhaji Anas da misalin karfe 1 na dare, inda suka tarar ba ya gida, amma suka yi awon gaba da matansa biyu, ‘ya’yansa uku, kaninsa, da matar kaninsa. ...
Sakamakon sanarwar da Amurka ta fitar kwanan baya a kan kara haraji na kashi 10 cikin dari a kan daukacin kayayyakin kasar Sin da ake kaiwa kasar tare da kafa hujja da wasu batutuwa irin su maganin Fentanyl, a yau Talata, ma’aikatar cinikayya da takwararta ta kudi ta kasar Sin sun fitar da wata sanarwa...
A Talatar nan Majalisar Dokoki ta kasa ta ci gaba zama don hanzarta kammala aiki kan ƙudirin sabuwar dokar haraji mai cike da ruɗani da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gabatar mata. Bayan zaman farko a ranar 14 da watan nan na Janairu, ta dage zama zuwa ranar 28 domin kwamitoci su kammala aikin tantance...
Ministocin harkokin wajen 5 na kasashen larabawa tare da hadin gwiwar jami’an Falasdinawa sun rubuta wa ministan harkokin wajen Amurka Marco Antonio Rubio wasiki da a ciki suke nuna kin amincewa da shirin korar Falasdinawa zuwa wajen Falasdinu. Kasashen da su ka rubuta wasikar sun kunshi Saudiyya, HDL, Katar, Masar da Jordan, sai kuma mai...
Shugaban kasar Amurka donal Trum ya bayyana anniyarsa na aiki tare da kungiyar kasashen masu arzikin man fetur don rage farashin man fetur a duniya. Shugaban ya bayyana cewa zai yi aiki da kasar Saudiya UAE da sauransu don rage farashin man man fetur a duniya. Kuma daga nan yana ganin aka iya kawo karshen...

Kungiyar Hamas Ta Bayyana Cewa A Shirye Take Ta Fara Tattaunawa, Marhala Ta Biyu Na Tsagaita Wuta A Gaza
Kungiyar Hamas wacce take iko da yanin zirin gaza ta bada sanarwan cewa a shirye take, masu shiga tsakanin, wato kasar Masar ta fara tattaunawa marhala ta biyu na tattaunawar tsagaita wuta a Gaza. Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto kamfanin dillancin laran AFP na kasar Faransa yana fadar haka. Ya kuma...

Sojojin Iran Sun Fara Atisayen Soje Karu Na Biyu Mafi Yawa A Bangaren Garkuwan Sararin Samaniyar Kasar
Sojojin JMI sun bada sanarwan fara isayen soje karo na biyu a yankun tsakiya da kuma kudancin kasarTashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa za’a fara wannan atisayen ne a yau Talata 04 ga watan Fabrairu, kuma atisayen zai fi maida hankali ne a kan garkuwan tsaron kasar , wanda kuma ya...
An yi kiyasin adadin tafiye-tafiyen fasinjoji tsakanin yankuna zai kai biliyan 4.8 a duk fadin kasar Sin daga ranar 14 ga watan Janairu zuwa ta 2 ga watan Febrairu, wato rabin farko na kwanaki 40 na zirga-zirgar bikin bazara. Adadin ya nuna karuwar kashi 7.2 cikin dari bisa makamancin lokaci na bara, a cewar tawagar...
Kwamandan makarantar horas da sojoji dake Zaria, Manjo Janar Ahmadu Bello Mohammed ya yi alkawarin inganta dangantakar da ke tsakanin makarantar da majalisar masarautar Zazzau. Ya bayyana haka ne lokacin da ya kai wa mai martaba Sarkin zazzau Malam Ahmed Nuhu Bamalli ziyarar ban girma a fadar sa dake Zaria. Manjo Janar Ahmadu Bello, wanda...
Majalisar dokokin jihar Kano ta zartar da wani kudirin doka da za ta ci tarar naira N25, 000 ga duk wanda aka samu ya yi fitsari, bahaya, zubar da shara ko kuma zubar da majina a kan titi ko kuma a ƙarkashin gada a jihar. Hakan ya biyo bayan dokar da majalisar ta zartar wanda...
Gwamnatin mamayar Isra’ila ta tantance hanya ta musamman da jirgin da ya dauki fira ministan mamayar Isra’ila zuwa Amurka saboda tsoron kama shi! A wani mataki da ke nuni da yadda gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke kara nuna damuwa, jaridar Ma’ariv ta haramtacciyar kasar ta watsa rahoton cewa: Jirgin da ke dauke da fira ministan...
Masu zanga-zanga a birnin Kinshasa fadar mulkin kasar Dimokaradiyyar Kongo sun kai hare-hare kan ofisoshin jakadancin kasashe da suka hada da Amurka da Faransa Masu zanga-zangar sun kai hare-hare a wasu ofisoshin jakadanci a birnin Kinshasa, fadar mulkin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango, a lokacin da suke gudanar da zanga-zangar a makon da ya gabata, don nuna...
Guinea-Bissau Na Neman Karfafa Hadin Gwiwar Kafofin Yada Labarai Da Sin
Masarautar Fika da ke Jihar Yobe ta buɗe gasar ƙwallon ƙafa karo na uku a filin wasa na Dabo Aliyu da ke garin Potiskum. An buɗe gasar ƙarƙashin jagorancin mai Martaba Sarkin Fika, Alhaji Dr. Muhammad Ibn Abali Muhammad Idris wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Yobe. Ya je Maiduguri daga Legas a...
Ko da yake har yanzu kotun ba ta bayar da cikakken bayani kan hukuncin ba, amma an gano cewa, shari’ar mai lamba HCO/05C/2024, Dakta Barnabas Adeku Ojiah da wasu mutane biyu ne suka shigar da ita, inda suke kalubalentar hukuncin tsohon gwamnan jihar na Kogi. Sai dai, jin ta bakin Ohinoyi, Alhaji Ahmed Muhammed...
A kwanan nan, kasar Amurka ta sanar da sanya karin harajin kwastam da ya kai kaso 10% kan kayayyakin da kasar Sin ke fitar da su zuwa kasuwannin Amurka. Wannan mataki ya keta ka’idojin kungiyar cinikayya ta duniya WTO, wanda kuma zai lalata huldar dake tsakanin Sin da Amurka a fannin cinikayya. Yanzu haka, kasar...
Uwargidan Gwamnan Jihar Jigawa, Hajiya Hadiza Umar Namadi ta kaddamar da wani katafaren wurin shan shayi da taliya na zamani a karamar hukumar Maigatari ta jihar. Hajiya Hadiza Namadi ta ce, wurin sayar da shayin da taliyar da aka zamanantar da shi wani yunkuri ne na karamar hukumar ta Maigatari. Ta kara da...