2025-04-12@21:06:52 GMT
إجمالي نتائج البحث: 665

«Falasdinawa»:

    Lamarin ya faru ne a lokacin da matashin mawakin yake kan dandamali ya na rera daya daya daga cikin fitattun wakokinsa, har zuwa lokacin wannan rahoto, Bilal Billa bai fitar da wata sanarwa a kafafen sadarwar ba, amma kuma faruwar lamarin ya janyo cece kuce inda wasu a bangare guda ke ganin abin da aka...
    An kammala zagayen farko na tattaunawa tsakanin Iran da Amurka a babban birnin Muscat a shiga tsakanin kasar Oman. Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi da Steve Witkoff, manzon musamman na shugaban Amurka kan harkokin yankin gabas ta tsakiya ne suka jagoranci shawarwarin yau Asabar. A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Iran ta...
    Gwamnatin jihar Jigawa ta ce za ta samar da ababen hawa ga shugabannin makarantun babbar  sakandare a fadin jihar. Kwamishinan ilimi na jihar, Farfesa Isa Yusuf Chamo, ne ya bayyana hakan yayin wani taro da ya gudanar da shugabannin makarantu a garin Dutse. A cewarsa, za a gyara gidajen ma’aikatan makarantun sakandare domin saukaka matsalar...
    Tun da safiyar yau Asabar ne dai ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci ya isa birnin Mascut na kasar Oman da can ne za a yi tattaunawar da ba ta gaba da gaba ba a tsakanin jamhuriyar musulunci da Amurka. Jim kadan bayan isar tasa birnin Mascut ministan harkokin wajen na jamhuriyar musulunci ta Iran...
    Wanda ya jagoranci sallar juma’a a Tehran ya bayyana cewa; Tun cin nasarar juyin musulunci, Iran ta zabi hanyar tattaunawa, saboda ta tabbatar da kyakkyawar niyyarta da kuma aiki da hankali a mu’amalrta da duniya. Limamin na Tehran Ayatullah Saiddiki ya ce, a yayin tattaunawar da za a yi a tsakanin Iran da Amurka wacce...
    Ministan harkokin wajen kasar Saudiya ya bayyana cewa shigo da kayakin agaji zuwa cikin zirin Gaza bai da wata dangantka da tsagaita bude wuta. Shafin yanar Gizo na labarai Arab News na kasar Saudiya ya nakalto Yerima Faisal bin Farhan yana fadar haka a jiya Jumma’a.. Ya kuma kara da cewa dole ne kasashen duniya...
    Sojojin kasar Yemen sun yi amfani da jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa kan cibiyoyin makamai na HKI wadanda suka Yaffa (tel aviv) saboda daukar fansa kan kashe-kashen da take yi a Gaza. Tashar talabijin Presstv a nan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labaran YAF na kasar Yemen yana fadar haka a jiya Jumma’a,...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriya kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a 2023, Alhaji Atiku Abubakar ya ziyarci tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari a Kaduna. Atiku ya samu rakiyar tsofaffin gwamnoni da suka haɗa da tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai da tsohon Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal da wasu jiga-jigan ’yan siyasa. An gano gawar makiyayi...
    Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku ya kasance mai fafutukar tabbatar da hadin kan ‘yan adawa, yana mai jaddada muhimmancin hadin gwiwa wajen kayar da Tinubu a zaben 2027. A ranar 8 ga watan Maris ne ya bayyana kokarinsa na hada kan ‘yan adawa da kafa kawancen korar jam’iyyar APC. Bayan sauya shekar El-Rufa’i daga jam’iyyar...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumar ilimin bai daya ta kasa wato UBEC ta yabawa Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa bisa jajircewar sa wajen inganta ilimi a matakin farko a Jihar. Shugabar Hukumar, Hajiya Aisha Garba, ta bayyana hakan a yayin ziyarar gwamnan zuwa hedikwatar UBEC a Abuja. Hajiya Aisha Garba ta bayyana jihar Jigawa a matsayin abin...
    Jami’an Kongo da masu shiga tsakani na M23 sun isa Qatar domin tattaunawa don cimma yarjejeniyar tsagaita wuta. Jami’an Kongo da masu shiga tsakani na kungiyar M23 sun isa Doha babban birnin kasar Qatar domin tattaunawa da nufin cimma tsagaita bude wuta da kuma kawo karshen fadan da aka shafe watanni ana gwabzawa a yankin,...
    Asusun ba da lamuni na ilimi na Najeriya ya yi barazanar daukar matakin shari’a a kan cibiyoyin da ke boye bayanai kan yadda ake biyan dalibai rancen kudi yayin da suke neman biyan kudaden makarantun daga hannun daliban.   Sanarwar da Manajin Darakta na NELFUND, Mista Akintunde Sawyerr ya fitar ta bayyana cewa, sakamakon binciken...
    Sojojin HKI suna ci gaba da yin kiyashi a sassa mabanbata na Gaza, da a bayan nan su ka yi wa mutane 30 kisan kiyashi a unguwar Shuja’iyya dake birnin Gaza.  Majiyar asibitin Falasdinawa ta ambaci cewa; Harin da sojojin HKI su ka kai da manyan bindigogi sun yi sanadiyyar shahadar mutane 17 a unguwar...
    Kasar Sudan ta kai kukan HDL a gaban kotun MDD cewa ta keta dokar hana kisan kiyashi ta hanyar taimakawa dakarun kai daukin gaggawa. A jiya Alhamis kasar ta Sudan din ta bukaci kotun ta kasa da kasa dake karkashin MDD da  ta ta fitar da hukunci na gaggawa na bayar da umarni ga HDL...
    Wadannan ayyuka domin inganta harkar ilimi da kuma nuna gaskiya, sun sa Jigawa ta zama abin koyi ga sauran jihohi.   Tunda farko, Gwamna Malam Umar Namadi, a nasa jawabin, ya ce gwamnati ta dauki kwakkwaran matakai na magance matsalar rashin ilimi bayan wani bincike da wani masani mai zaman kansa ya fitar cewa, yawancin...
    Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya jagoranci wata tawaga zuwa Jihar Edo domin binciko gaskiyar abin da ya faru game da kisan mafarauta ’yan asalin jihar a ƙauyen Uromi. Gwamna Abba Kabir Yusuf ne, ya umarci a kafa wannan tawaga, wacce ta ƙunshi manyan shugabanni irin su Sarkin Rano, Kwamishinonin ma’aikatu da...
    Jakadan Sudan a Tehran, Abdul Aziz Hassan Saleh, ya tabbatar da cewa, za a gudanar da zaman farko na kotun kasa da kasa da ke birnin Hague a yau Alhamis, domin duba korafin da Sudan ta shigar kan kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, kan rawar da take takawa a yakin da ake ci gaba da yi...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa Jagoran juyin juya halin Musulunci na kasar Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ba shi da wata adawa da Amurkawa masu zuba jari a kasar. “Muna maraba da masu zuba jari.” amma ba tare da tauye mutunci ko tsaron kasa ba. Har ila yau kalaman nasa sun sake tabbatar...
    Gwamnatin Washington ta sanar da kakabawa Iran sabbin takunkumai kan shirinta na nukiliya an zaman lafiya, a matakin da Amurka ke ganin shi ne kawai hanyar matsin lamba kan Iran domin ta mika wuya game da shirint ana nukiliya. Takunkumin, wanda ma’aikatar baitul malin Amurka ta sanar a jiya Laraba, ya shafi hukumomi biyar da...
    Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron, ya ce kasarsa na shirin amincewa da yankin Falasdinawa a matsayin kasa nan da watanni masu zuwa. Ya ce hakan na iya faruwa a farkon watan Yuni nan wannan shekarar a taron Majalisar Dinkin Duniya da za a gudanar a New York. kawo yanzu, Kasashe 147 ne suka amince da...
    Shugaban Amurka Donald Trump ya dakatar da haraje-harajen da ya lafta kan kayayyakin da ke shiga kasar daga kasashen duniya, sai dai ya kara harajin da kashi 125 ga kasar China. A wani bayani da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Shugaba Trump ya ce za a rage haraje-harajen zuwa kashi 10%, sai dai...
    Mazauna karamar hukumar Gezawa ta Kano sun shiga cikin tashin hankali da makoki sakamakon nutsewar wasu mata biyu a cikin wani tafki.   Rahotanni sun nuna cewa matan (an sakaya sunansu) sun gamu da ajalinsu ne a lokacin da suke wanka a kogi bayan sun dawo daga aiki a wata masana’antar sarrafa hibiscus.   A...
    “Ina rokon Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta masa, ya sa ya huta har abada.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) za ta hada gwiwa da kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ) a yaki da hako ma’adinai da kuma ayyukan ta’addanci a kasar nan.   Mukaddashin Daraktan shiyyar Kaduna mai kula da shiyyar Kaduna, Mista Bawa Usman Kaltungo ne ya bayyana hakan a lokacin da ya...
    Al’ummar Karamar Hukumar Maigatari sun yi kira ga gwamnatin jihar Jigawa da ta taimaka wajen gina hanyoyin da za su hada garuruwansu. Wani mazaunin yankin, Malam Ali A. Bulama Turbus, wanda ya wakilci al’ummomin yayin da yake magana da Rediyon Najeriya a Maigatari, ya jaddada muhimmancin aikin gina hanyar. Ya bayyana cewa samar da hanya...
    Kungiyar tarayyar Turai ta yi maraba da tattaunawa tsakanin Amurka da JMI dangane da shirinta na makamashin Nukliya, tare da kara jaddada cewa hanyar diblomasiyya kadai ta rage don warware wannan matsalar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa a halin yanzu dai kungiyar tarayyar ta Turai ta na ci gaba da...
    Jiragen yakin HKI sun kashe akalla mutane 38 a wurare daban-daban a zirin Gaza, kuma mafi yawan wadanda ta kashen yara kanana ne. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar Falasdinawa a Gaza na cewa da sassafe jiragen yakin sun kaiwa wani gidan Bene a unguwar shujaiyya na wajen garin Gaza inda...
    A ci gaba da kokarinsa na kawo sabon tsari domin inganta harkokin noma a jihar Jigawa, Gwamna Malam Umar Namadi ya jagoranci tawagar gwamnatin jihar zuwa wani babban taro da manyan masu zuba jari na duniya da masu ruwa da tsaki a harkar noma. Taron wanda ya gudana jiya Talata a otal din Hilton da...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya yi martani ga kalaman shugaban Amurka Donald Trump na baya-bayan nan game da yiwuwar tattaunawa da Iran kai tsaye, inda ya yi karin haske kan matsayar Tehran, kamar yadda jaridar Washington Post ta kawo. Araghchi ya bayyana imaninsa cewa irin matakan da Iran ta dauka a baya-bayan nan...
    Wasu ‘yan kasar Amurka uku da aka daure bisa laifin yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango, yanzu haka suna hannun Amurka bayan yanke hukuncin da aka yi a kansu a makon jiya, kamar yadda wasu jami’an Amurka da na  fadar shugaban kasar Kongo suka bayyana ga kamfanin dillancin labarai...
    Ya ce karin wa’adin na baya-bayan nan ya biyo bayan cikar wa’adin farko na ranar 1 ga Afrilu, 2025, wanda aka sanya tun da farko a ranar 24 ga watan Janairu.   Umar ya kara da cewa, duk da wannan karin wa’adin, amma an ci gaba da samun karancin fitowar masu filaye domin sabunta takardunsu....
    Ya jaddada cewa, taken taron ya dace kuma yazo a kan lokaci “wanda na yi imanin cewa, dandalin zai taimaka wajen gabatar da jawabai a bangarori daban-daban na gyare-gyaren kasafin kudi da shugaba Bola Tinubu ke aiwatarwa a karkashin shirin renewed hope.”   Ya ce, jawabin da ake gabatarwa a dandalin zai ba da gudummawa...
    Kungiyar Hamas wacce take iko da zirin Gaza, ta yi tir da gwamnatin Falasdinawa a yankin yamma da kogin Jordan da aka mamaye, saboda dirar mikiyan da ta yi kan Falasdinawa a yankin wadanda suke zanga-zangar beman HKI ta kawo karshen kissan kiyashin da ta yi a gaza. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran...
    Akalla Falasdinawa 58 ne aka kashe tare da jikkata wasu 213 a cikin awa 24 da suka wuce a hare-haren da Isra’ila ta kai a Zirin Gaza. Ma’aikatar lafiya ta yankin ta sanar cewa wasu daga cikin wadanda abin ya shafa sun makale a karkashin baraguzai da kuma kan tituna, ba za a iya isa...
    Akalla Falasdinawa 58 ne aka kashe tare da jikkata wasu 213 a cikin awa 24 da suka wuce a hare-haren da Isra’ila ta kai a Zirin Gaza. Ma’aikatar lafiya ta yankin ta sanar cewa wasu daga cikin wadanda abin ya shafa sun makale a karkashin baraguzai da kuma kan tituna, ba za a iya isa...
    Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya ce kasarsa ta yi imani da tattaunawa, amma ba a karkashin wulakanci da kaskanci ba.” Ya jaddada cewa Iran ba ta neman yaki, ko tada zaune tsaye, ko kuma mallakar makamin nukiliya, yana mai kira ga kasashen duniya da su amince da hakan. Pezeshkian ya bayyana hakan ne a yammacin...
    Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ci gaba da gudanar da  tarurrukan bita ga maniyyata aikin Hajjin bana, bayan  kammala azumin watan Ramadan. Daraktan Hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya bayyana hakan ga Rediyon Najeriya a Dutse, babban birnin jihar. A cewarsa, hukumar za ta tabbatar da cewa maniyyata sun sami...
    An gudanar da zanga-zangar adawa da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu wada ta barke a wasu manyan biranen Nijeriya da suka haɗa da Abuja da Legas da kuma Fatakwal. Zanga-zangar wadda wata kungiyar gwagwarmaya ta Take It Back ta shirya na gudana ne duk da gargadin da ’yan sanda suka yi na neman a jingine ta....
    Jamhuriyar musulinci ta Iran, ta bayyana cewa za ta fata tattaunawa wacce ba ta kai tsaye ba da Amurka a ranar Asabar mai zuwa a kasar Oman. Ministan harkokin wajen Iran din ne Abbas Araghchi ya bayyana hakan a shafinsa na ‘’X’’ a safiyar Talata. “Iran da Amurka za su gana a Oman ranar Asabar...
    A wani mataki na mayar da martani da nuna fishi, kasar Aljeriya ta yi wa jakadunta a kasashen Mali, da Nijar kiranye, tare da jinkirta aikewa da jakadanta a Burkina faso, bayan da kasashen guda uku na kawacen sahel suka dau irin wannan matakin domin goyan bayan Mali, bisa takadamar dake tsakaninta da Aljeriya biyo...
    Shugabannin kasashen Faransa da Masar da kuma Jordan sun fitar da wata sanarwa ta hadin gwiwa inda suka bukaci a tsagaita bude wuta cikin gaggawa a Gaza, tare da sukar Isra’ila kan gazawarta wajen tabbatar da ayyukan jin kai a zirin. Kiran tsagaita wuta ya nuna bukatar samar da agajin jin kai cikin gaggawa a...
    Assalamu alaikujml/m masu sauraro, sharhin bayan labarummu zai yi magana danagne da zanga-zanga masu yawa wadanda ake yi a kasashen larabawa a dai dai lokacinda HKI take kara tsananta kisan kiyashi a yankin Zirin gaza, wanda ni tahir amin zan karanta. ////.. Madalla, a dai-dai lokacin da sojojin HKI suke kara yawan hare-haren da suke...
    A wannan Litinin ɗin ce anga-zangar adawa da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta ɓarke a wasu manyan biranen Nijeriya da suka haɗa da Abuja da Legas da kuma Fatakwal. Zanga-zangar wadda wata ƙungiyar gwagwarmaya ta Take It Back ta shirya na gudana ne duk da gargaɗin da ’yan sanda suka yi na neman a jingine...
    Ministan harkokin wajen Iran Sayyid Abbas Arakci ya bayyana cewa, Iran ba ta kin zama teburin tattaunawa, amma ba za ta zauna gaba da gaba da Amurka ba, yana mai kara da cewa; Har ya zuwa yanzu ba a yi wata tattaunawa gaba da gaba a tsakanin Iran da Amurka ba. Ministan harkokin wajen na...
    Jami’an ‘yansanda a gundumar Maitama da ke Abuja sun yi amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa masu zanga-zangar adawa da gwamnati, inda suka yi kira ga gwamnatin da ta dauki matakan gaggawa kan tabarbarewar tattalin arziki da kuma zargin ‘yansanda na cin zarafin al’umma a kan ikirarin dokar hana aikata laifuka ta yanar gizo. Zanga-zangar...
    Gwamnatin jihar Jigawa ta ce za ta bullo da shirin bada magani kyauta ga masu cutar siga da hawan jini da kuma sikila. Kwamishinan lafiya na jihar, Dr Abdullahi Muhammad Kainuwa ya bayyana haka ga manema labarai a Dutse. Yace tuni gwamna Umar Namadi ya bada umarnin gabatar masa da wannan kudiri domin aiwatar da...
    Jami’an rundunar ‘yansandan jihar Ribas a ranar Litinin sun harba tiyagas (barkonon tsohuwa) kan masu zanga-zangar lumana don nuna adawa da abin da suka kira rashin shugabanci nagari a kasar. Masu zanga-zangar karkashin kungiyar ‘Take It Back’ sun kuma gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewa da ayyana dokar ta-baci a jihar Ribas da kuma yadda...
    Zanga-zangar adawa da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta ɓarke a wasu manyan biranen Nijeriya da suka haɗa da Abuja da Legas da kuma Fatakwal. Zanga-zangar wadda wata ƙungiyar gwagwarmaya ta Take It Back ta shirya na gudana ne duk da gargaɗin da ’yan sanda suka yi. Mutanen da Sanƙarau ta kashe sun kai 151 —...