2025-04-05@01:21:25 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1452
«Kwamitin Zaman Lafiya»:
A wani muhimmin mataki na karfafa zaman lafiya da sulhu, gwamnatin jihar Jigawa ta kaddamar da kwamitocin zaman lafiya da sulhu a kananan hukumomin Jahun da Miga. A lokacin bikin kaddamarwar, Sakataren Gwamnatin Jihar, Malam Bala Ibrahim, ya bayyana aikace-aikacen da aka dora wa kwamitocin. Ya jaddada bukatar kwamitocin su gano musabbabin rikice-rikicen da suka...
Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja, a ranar Juma’a, ta haramta wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio tattaunawa da manema labarai yayin da ’yar majalisar ta shigar da ƙara a gaban kotu. Mai shari’a Binta Nyako ce ta yanke hukuncin a ranar Juma’a bayan ƙorafin da lauyan da ke...
Jihohin da wannan matsalar ta fi shafa sun hada da, Zamfara, Borno, Yobe da kuma Katsina, musamman duba da yadda aukuwar yawan rikice-rikice, ya tarwatsa rayuwar miliyoyin alumomin yakin da fadawa cikin kangin fatara da yunwa da kuma rashin samun wadataccen abinci. A ra’ayin mu, matsalar karancin abinci a kasar nan, ba boyayayen abu bane,...

Kasar Sin Za Ta Kara Sanya Harajin Fito Na Kaso 34% Kan Dukkan Kayayyakin Da Take Shigowa Daga Amurka
Kasar Sin ta sanar a yau Juma’a cewa, ta shigar da kara a gaban kungiyar cinikayya ta duniya WTO, kan matakin da Amurka ta dauka na kakaba harajin kwastam kan abokan cinikayyarta. A cikin wata sanarwa da ta fitar, ma’aikatar cinikayyar kasar Sin ta ce, harajin kwastam da Amurka ta kakaba, ya matukar take halaltattun...
Shugaba Tinubu ya zanta da manema labarai bayan kammala Sallar Idi na karshen watan Ramadan a filin da aka gabatar da Sallar Idi na kasa a Abuja ranar Lahadi. Cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya fitar, shugaban ya bukaci ‘yan Nijeriya da kada su koma kan aikata abubuwan da su...
Kungiyar kasuwanci ta duniya ( WTO) da asusun bayar da lamuni ( IMF) sun yi gargadi akan sakamakon dake tattare da Karin kudaden fito na kasuwanci da gwamnatin shugaban kasar Amurka Donald Trump ta yi a jiya Alhamis. Kungiyar kasuwancin ta duniya, ta yi hasashen cewa ci gaban harkokin kasuwanci a duniya zai sami koma...
Tsohon Kwamishinan ’Yan sanda na Jihar Kano kuma tsohon Mashawarci na Musamman ga Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya, CP Muhammad Wakili (ritaya), ya jaddada cewa dole ne ’yan sanda su yi amfani da ikon da suke da shi cikin gaskiya da adalci, don tabbatar da zaman lafiya da ci gaban ƙasa. Da yake jawabi a wani...

Kasar Sin Ta Sanar Da Daukar Matakan Hana Fitar Da Kayayyaki Zuwa Kasashen Waje Kan Wasu Ma’adinan Da Ba Kasafai Ake Samun Su Ba
Ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin tare da hadin gwiwar babbar hukumar kwastam ta kasar Sin, ta sanar a yau Juma’a cewa, za ta fara aiwatar da matakan kiyaye fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje kan nau’o’in ma’adinai bakwai matsakaita da masu nauyi da ba kasafai ake samun su, wadanda suka hada da samarium, gadolinium, terbium,...
An ceto yara takwas da aka yi safarar su daga Jihar Taraba ta hanyar haɗin gwiwar ma’aikatar mata da ci gaban ƙananan yara ta Jihar Taraba da Hukumar Hana Safarar Mutane ta Ƙasa (NAPTIP). Kwamishiniyar harkokin mata da ci gaban yara ta jihar Taraba, Misis Mary Sinjen ta ce yaran da aka ceto sun fito...
Adadin waɗanda suka mutu sakamakon hare-haren baya-bayan nan a ƙaramar hukumar Bokkos da ke Jihar Filato ya kai 52 kamar yadda hukumomin yankin suka bayyana. Hakan ya biyo bayan sake gano wasu gawarwaki 40 ne a ranar Laraba da Alhamis da daddare yayin da masu aikin ceto suka ci gaba da kutsawa cikin dazuka don...
An kashe wani sufeton ɗan sanda a yayin wani kwanton ɓauna da wasu da ake kyautata zaton mayaƙan Boko Haram ne suka kai a kwalejin horar da rundunar ’yan sanda (PMFTC) Camp Limankara, Gwoza a Borno. Majiyoyin leƙen asiri sun shaidawa majiyar Zagazola Makama cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 0600 a ranar...
Da yake tofa albarkacin bakinsa kan sayar da danyen mai da naira, wani babban jami’in gwamnati wanda ke da masaniya sosai kan lamarin da ke aiki da kwamitin da aka kafa don shirin ya bayyana cewa gwamnati ba wai ta dakatar da tsarin bane gaba daya. “Shirin cinikayyar danyen mai a kan naira zai ci...
Jaridar BusinessDay tayi nazari kan manyan ayyuka biyar na Layukan Dogo da suka samar wani sauki, a zirga-zirgar Jirgin kasa a kasar nan. 1 Layin Dogo Daga Legas Zuwa Ibadan Ingantaccen aikin layin Dogo mai tsawon kilomita 157 da ya taso daga jihar Legas zuwa garin Ibadan. An faro aikin ne a watan Maris na...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan a zantawarsa tan wayar tarho da yerima mai jiran gadon sarautar kasar Saudiya sannan Firai ministan kasar Muhammad bin Salman ya taya shi murnin salla karama ya kuma yiawa dukkan kasashen musulmi fatan alkhairi. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana cewa, JMI bata neman yaki...
Jakadan kasar Iran a cibiyoyin MDD a kasashen Turai ko Geneva Ali Gahraini ya yi tir da amincewar da hukumar kare hakkin bil’adama ta MDD ta yi da zargin kasar ta take hakkin bil’adama a taronta na baya-bayan nan abirnin Geveva. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Baraini yana cewa, hukuncin da...
Jam’iyyar APC, ta musanta jita-jitar cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, na shirin sauya Mataimakinsa, Kashim Shettima, kafin zaɓen 2027. Jam’iyyar ta ce babu wata matsala tsakaninsu kuma maganar sauya Shettima ba ta da tushe. Hakeem Baba-Ahmed ya yi murabus daga gwamnatin Tinubu Fitaccen malami Dokta Idris Dutsen Tanshi ya rasu Daraktan Yaɗa Labarai na Jam’iyyar...
Dokta Hakeem Baba-Ahmed, ya yi murabus daga matsayin mai bai wa Shugaba Bola Tinubu shawara kan harkokin siyasa. Majiyoyi daga fadar shugaban ƙasa sun tabbatar da cewa ya aike da takardar murabus ɗinsa kimanin makonni biyu da suka wuce, inda ya ce dalilansa na ƙashin kai ne. Batun na yanke jiki na faɗi ƙarya ce...
Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya musanta jita-jitar da ake yaɗawa cewar ya yanke jiki ya faɗi har aka kai shi asibiti a ƙasar waje. Ya ce wannan ƙarya ce da maƙiyansa na siyasa suka ƙirƙira don kawar da hankalin mutane. NAJERIYA A YAU: Dalilan Kamuwa Da Cutar Hawan Jini Da Hanyoyin Magance Ta...
Kasashen duniya na ci gaba da mayar da martini tare da shan alwashin ramuwar gayya game da harajin da shugaban Amurka Donald Trump ya lafta musu kankan kayayyakin da ake shigowa da su kasar. Gwamnatoci da kamfanoni da dama sun sanar da matakan gaggawa na samar da matakan dakile matakin da Amurkan ta dauka kansu....
Ministocin harkokin wajen kasashen kawacen sahel na AES da ya hada Mali da Burkina Faso da Jamhuriyar Nijar, na wata ziyarar aiki a kasar Rasha. Ana sa ran ministocin za su kasance a birnin Moscow a yau Alhamis da gobe Juma’a, don tattaunawa, da zurfafa hulda tsakanin bangarorin biyu, kamar dai yadda aka bayyana cikin...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Akwai cututtuka da dama da ke yaɗuwa, kuma mafi yawan mutane da ke ɗauke da su, ba su san suna da su ba. Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce zaman lafiya, samun abinci da wadata, da rashin damuwa a ƙwaƙwalwa na daga cikin abubuwan da ke tabbatar da lafiyar...
A ranar Alhamis ɗin nan ne rundunar sojin Nijeriya ta ce ana cigaba da farautar ƙasurgumin ɗanbindiga, Kachalla Bello Turji wanda sojojin ƙasar suka daɗe suna nema ya kusa komawa ga mahalicci. Rundunar ta bayyana cewa kuma kwanakinsa sun kusa ƙarewa. Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci ta miƙa Janar Tsiga da wasu ga NSA Gobara ta...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Cibiyar yaƙi da ta’addanci ta ƙasa (NCTC) ta miƙa tsohon Darakta-Janar na masu yi wa ƙasa hidima (NYSC), Birgediya Janar Maharazu Tsiga (mai ritaya) ga mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Nuhu Ribadu. Tsiga, wanda aka kuɓutar bayan ya kwashe kwanaki 56 a tsare, a ranar Laraba an miƙa shi ne tare...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana yau Alhamis cewa, kasar Sin ta bukaci Amurka da ta gyara kuskuren da ta yi na kakaba “harajin ramuwar gayya,” kana ta magance sabanin dake tsakaninta da kasar Sin da sauran kasashen duniya dangane da tattalin arziki da cinikayya, ta hanyar yin shawarwari bisa daidaito,...
Shugaban kasar Burundi ya yi gargadin cewa Rwanda na da shirin kai wa kasarsa hari, bayan da sojojin Burundi suka taimakawa Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango (DRC) a yakin da take yi da ‘yan tawayen M23 da ke samun goyon bayan Rwanda. Shugaban kasar ta Burundi Evariste Ndayishimiye ya bayyana cewa, ya samu “sahihan bayanan sirri” da...
Dakarun Yaman sun sanar da mayar da martani kan harin baya-bayan nan da Amurka ta kai kan kasarsu, wanda ya hada da hare-hare ta sama har sau 36 a yankuna da dama a cikin gundumomin Sanaa, Sa’ada, da wasu jahohin kasar, wanda ya yi sanadin mutuwa da jikkatar mutane da dama. Kakakin Rundunar sojin Yaman...
Kungiyar malaman musulmi ta duniya ta fitar da wata sanarwa inda ta bayyana cewa laifuffukan gwamnatin sahyoniyawa a Gaza sun ketare dukkanin iyakokin kasa da kasa, tare da yin kira da a kawo karshen kashe-kashen mata da kananan yara da makamai masu guba, da yunwa, kishirwa, da cututtuka. A cewar jaridar Arabi 21, kungiyar malaman...
Aljeriya ta kira taron gaggawa na kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya domin tattauna halin da Falasdinu ke ciki. Bayan karuwar laifuffukan da yahudawan sahyoniyawa da suke aikatawa a kisan gillar da suke yiwa Palastinawa a yankin zirin Gaza da kuma ci gaba da kai hare-haren wuce gona da iri da sojojin yahudawan sahyoniya suka...
Ya ce, “Akwai rahoton cewa Turji ya shirya zai ziyarci yankin Gabashin Gatawa domin gudanar da bukukuwan Sallah, amma matakin da jama’a suka dauka na sanar da jami’an tsaro ya dakatar da shi ga hakan. “Wannan na iya zama dalilin da ya sa Bello Turji ya huce fushinsa a kan manoman da ba su...
Masu ababen hawa da dama sun maƙale a gadar Namne da ta rufta daura da hanyar Jalingo zuwa Wukari a Ƙaramar hukumar Gassol ta Jihar Taraba sakamakon ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a da aka yi ranar Laraba. Ruwan sama ya kawar da gadar da aka gina ta wucin gadi a hanyar da aka...
“A yau ne Gwamna Dauda Lawal ya fara rangaɗin wuraren haƙar ma’adanai da masana’antu, inda ya fara ziyarar aiki a wani kamfani mai zaman kansa na Comet Star Industry da ke Ƙaramar Hukumar Anka. “Ma’aikatar, mallakin Prince James Uduji OON, tana sarrafa kusan tan 1,000 a kullum. Tana da cikakkun kayan aiki da sabbin...
A jiya Laraba 2 ga wata, rundunar sojojin ‘yantar da al’umma ta kasar Sin ko PLA shiyyar gabashin kasar, ta kaddamar da wani atisayen soji mai taken “Strait Thunder-2025A”, a yankunan tsakiya da kudancin zirin Taiwan, wanda ya kasance matakin da aka dauka dangane da kalamai na shirme da jagoran yankin Taiwan, Lai Ching-te ya...
An shiga firgici da safiyar Alhamis ɗin nan, bayan wani kwale-kwale na kamfanin Lagos Ferry Services (LAGFERRY) ya kama da wuta a tashar jirgin ruwa ta Ipakodo da ke Ikorodu, a Legas inda mutane da dama suka jikkata. Majiyoyi sun ce tashin wutar ta haifar da wata babbar gobara da ta tashi daga injin jirgin...
Sama da gidaje 70 ne suka lalace da rumfuma a wata guguwa da ta yi ɓarna a unguwar Mabudi, Sabon Gida, da sauran unguwanni a ƙaramar hukumar Langtang ta Kudu a Jihar Filato. Wakilinmu ya ruwaito cewa, mamakon ruwan sama da aka yi a daren Laraba, wanda ya biyo bayan ruwan sama, ya yi ɓarna...
Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta bayyana cewa buƙatar da wasu suka shigar don yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Mazaɓar Kogi ta Tsakiya kiranye, bai cika sharuɗa ba. INEC ta ce yunƙurin bai cika sharuɗan Sashe na 69(a) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya tanadar ba. Bello Turji ya kashe manoma 11 a...
Ƙasurgumin ɗan bindiga, Bello Turji, da mayaƙansa sun kai mummunan hari garin Lugu da ke Ƙaramar Hukumar Isa a Jihar Sakkwato, inda suka kashe manoma 11. Rahotanni sun nuna cewa harin ya faru ne yayin da Turji ke dawowa daga wata ziyarar sallah da ya kai yankin. Najeriya ta yi kuskuren barin Boko Haram ta...
Gwamna Caleb Mutfwang na Jihar Filato, ya yi gargaɗin cewa Najeriya ta yi kuskure a baya wajen barin Boko Haram da sauran ƙungiyoyin ’yan bindiga har suka yi ƙarfi. Ya jaddada cewa babu wata ƙungiya da ya kamata ta mallaki makamai ko ta samu ƙarfin guiwar ƙalubalantar hukumomin tsaro. NAJERIYA A YAU: Ƙalubalen Da Iyaye...
Wani matashi mai shekaru 27, Rabiu Suleiman, ya daɓa wa abokinsa Yunusa Muazu wuƙa, tare da yi masa mummunan rauni, a kan budurwa a yankin Gwagwalada da ke Abuja. Lamarin ya faru ne a daren Talata a wani gidan kallon fina-finai a Unguwar Dodo. NAJERIYA A YAU: Ƙalubalen Da Iyaye Ke Fuskanta Wajen Tarbiyyar ‘Ya’yansu...
Asusun Bada Lamuni na Duniya (IMF), ya buƙaci Gwamnatin Najeriya da ta tabbatar da cewa manufofin tattalin arziƙin ƙasar sun kare muradun mutane masu rauni. Daraktar Hulɗa da Jama’a na IMF, Julie Kozack, ta bayyana hakan a yayin wata ganawa da manema labarai a birnin Washington, D.C. NAJERIYA A YAU: Ƙalubalen Da Iyaye Ke Fuskanta...
Rahotanni daga kasar Lebanon sun ce jiragen yakin HKI sun kai hari a garin “Naqura” dake kudancin Lebanon da safiyar yau Alhamis. Jiragen yakin na ‘yan sahayoniya sun kai harin ne har sau uku ajere akan wata tsohuwar cibiyar kiwon lafiya dake cikin garin, haka nan kuma akan wasu gudajen mutane da suke a kusa....
Yanzu da ya rasu, Hauwa ta ce ba ta da tabbas kan yadda za ta yi rayuwa da ‘ya’yanta. Lamarin mai tayar da hankali ya faru ne a ranar 27 ga watan Maris, lokacin da wasu matafiya 16 ‘yan asalin Arewacin Nijeriya suka faɗa tarkon wasu ‘yan sa-kai a Uromi, a Jihar Edo, inda suka...
Birgediya-Janar Maharazu Tsiga (mai ritaya), ya kuɓuta bayan shafe kwana 56 a hannun ’yan bindiga. An sace Janar Tsiga, wanda Tsohon Shugaban Hukumar NYSC ne, a garinsu da ke Ƙaramar Hukumar Bakori a Jihar Katsina, a ranar 5 ga watan Fabrairu, 2025. Mutum ɗaya ya rasu, 3 sun jikkata a rikicin ’yan sara-suka a Filato...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa Rafael Grossi ya sanar da shirin kai ziyara birnin Tehran nan da makwanni masu zuwa a yayin da ake ci gaba da tattaunawa don tsaida takamaimen lokacin. Ziyarar ta zo ne a wani bangare na ci gaba da huldar diflomasiyya tsakanin Iran da hukumar...
Wani rikici tsakanin matasan ƙungiyoyin Sara-Suka ya yi sanadin mutuwar mutum ɗaya tare da jikkata wasu uku a unguwar Yantifa da ke Jos ta Arewa, a Jihar Filato. Shaidu sun ce matasan sun far wa juna da makamai irin su adduna, wanda ya sa mazauna yankin tserewa don tsira da rayukansu. Tinubu ya yi ta’aziyyar...
Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa sojojin kasar na karbe iko da wasu yankunan zirin Gaza, a wani mataki na kara matsin lamba kan kungiyar Hamas domin tilasta ta sakin mutanen da ta ke garkuwa da su. “Muna karbe zirin Gaza tare da kara matsin lamba mataki-mataki domin tilasta su mayar da mutanen da...
Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) mai hedkwata a birnin Hague ta yi Allah-wadai da matakin da kasar Hungary ta dauka na kin mutunta sammacin kame firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da zai ziyarci kasar da ke tsakiyar Turai a ranar Alhamis. Mai magana da yawun kotun, Fadi El Abdallah, ya fada yayin...
Ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi ya nanata shirin Tehran na shiga tattaunawar da Amurka kan shirinta na nukiliya na zaman lafiya, yana mai gargadin cewa barazanar soji daga Amurka na dagula halin da ake ciki a yanzu. “Jamhuriyar Musulunci, kamar yadda ta kasance a baya, a shirye take don yin shawarwari na hakika,” in...
A lokacin da yake wurin, Kefas ya shaida wa masu ababen hawa da matafiya cewa, gwamnatin jihar za ta samar musu da wata hanyar da za su amfani da ita kafin a kammala gyaran gadar, alkawarin da har yanzun bai cika ba, ga kuma wani mamakon ruwan sama da aka yi a daren ranar Talata,...