2025-04-25@06:14:49 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1661
«Manyan Sakatarorin Gwamnati»:
Gwamnatin Najeriya ta amince kuma ta sanar cewa za a bai wa mahajjatan ƙasar kuɗin guzirinsu a hannu maimakon amfani da kati ko kuma asusun banki. Hakan ya biyo bayan tsoma bakin mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya yi wanda ya roƙi shugaba Bola Tinubu a madadin maniyyatan ta hannun Hukumar Alhazai ta Ƙasa NAHCON....
Sabbin ‘yan sama-jannatin da aka tura, za su gudanar da gwaje-gwaje da bincike game da yanayin rayuwa a sararin samaniya, da kimiyyar karamar fizgar kasa ko jazibiyya (micro-gravity physics) da sabbin fasahohin sararin samaniya. Kazalika, za su kuma yi tafiye-tafiye mabambanta a sararin samaniya don kakkafa shingayen kariya daga baraguzai da tarkacen sararin samaniya,...
Bugu da kari, masharhanta da dama na ganin karin harajin fito ba zai warware matsalar da Amurkan ke ciki ba. Ko shakka babu idan Amurka na son ta tunkari wannan kalubale bisa gaskiya, sai ta sauya tsarin ilimi, ta kuma bunkasa fannin kirkire-kirkirenta, da daga martabar masana’antu, da zuba jari na dogon lokaci a fannin,...
Jiragen yakin Amurka sun kai jerin hare-haren a kan biranen San,a,Sa’adah da kuma Hudaidah na kasar Yemen. Kamfanin dillancin labarun “Saba’a” na kasar Yemen ya nakalto cewa sojojin na Amurka sun kai hare-hare har sau uku a dutsen Naqam, wanda yake gabashin birnin San’aa. Kamfanin dillancin labarun na “Saba’a” ya kuma ce, jiragen yakin Amurka...
Ban da haka, yadda gwamnatin Trump ba ta da tabbas a kan manufofinta na haraji yana kuma ba kasashen duniya mamaki. Ba a jima ba da gwamnatin Amurka ta sanar da matakinta na harajin ramuwar gayya a kan kasashen da ke ciniki da ita, sai kuma ga shugaba Trump ya sanar da dage harajin a...
Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya ce a yanzu jihar na ɗaya daga cikin jihohin da suka fi zaman lafiya a Najeriya. Ya ce, a matsayinsa na babban jami’in shari’a da tsaro a Jihar Yobe, yana da haƙƙin ganin an bi doka don tabbatar da cewa jihar ta samu zaman lafiya. An kama mata...
Rundunar ’yan sandan Jihar Imo ta kama wasu mata biyu a lokacin da suke yunƙurin sayar da wani yaro ɗan shekara huɗu da aka yi garkuwa da shi a Owerri kan kuɗi Naira miliyan 2.7. An yi garkuwa da yaron ne a Abuja a lokacin da yake tallan kayan miya, sannan aka kawo shi Owerri...
Hukumar lura da gidajen bashin ma’aikatan gwamnatin tarayya (FGSHLB) ta sanar da cewa ta fara tattara jerin sunayen ma’aikatan gwamnati da suka yi ritaya amma ba su biya bashin gidajen da suka karɓa ba. Shugabar sashin sadarwa da hulɗa da jama’a na FGSHLB, Ngozi Obiechina, ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar...

Kasar Iran Ta Bayyana Cewa Kakaba Takunkumi Kan Kasarta Ya Sabawa Hikimar Gudanar Da Zaman Tattaunawa Da Ita
Jamhuriyar Musulunci ta Iran Ta bayyana cewa; Kakaba takunkumi kan kasarta ya sabawa ikirarin Amurka na yin shawarwari da ita Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi kakkausar suka kan matakin da Amurka ta dauka na kakabawa wasu gungun mutane masu alaka da bangaren makamashi, man fetur da iskar gas da kuma...
Jami’in kasar Yemen ya jaddada cewa: Kwanaki masu zuwa za su aiwatar da abubuwan mamaki da za su ba abokan gabanmu mamaki! Daraktan sashin yada labarai na fadar shugaban kasar Yemen Zaid Al-Gharsi ya jaddada samun gagarumin ci gaba a karfin sojojin kasar Yemen musamman a fannin fasaha da makamai. Ya yi nuni da cewa,...
Munanan azabtarwa kan fursunonin Falasdinawa a gidajen kurkukun haramtacciyar kasar Isra’ila da suka hada da fyade da dangogin azaba Rahoton da Hukumar Kula da Fursunoni Falasdinawa dakungiyar Fursunonin Falasdinawa da aka saka daga gidan kurkukun haramtacciyar kasar Isra’ila sun fiyar da rahoton hadin gwiwa a yau Alhamis, 24 ga watan Afrilun shekara ta 2025, da...

Gwamnatin Siriya Tana Daukan Matakan Matsin Lamba Kan Gwagwarmaya Domin Samun Yardan ‘Yan Sahayoniyya
Sabuwar gwamnatin Siriya tana kara matsa lamba kan bangarorin ‘yan gwagwarmaya domin Isra’ila ta janye daga wasu yankunan kasarta Sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da tura kayayyakin soji zuwa tsaunukan Dutsen Harmon, yayin da suke hanzarta gina abin da suka kira “Katangar tsaro.” Har ila yau, sun karfafa wuraren tsaro da suka kafa a...
Ma’aikatar yada labarai ta jihar Kano tare da hadin gwiwar hukumar kula da gidajen Radiyo da Talabijin ta kasa NBC sun shirya taron yini biyu ga masu fafutukar siyasa da masu sharhi kan harkokin yada labarai. Taron na da nufin tsaftace harkar siyasa da inganta fahimtar juna tsakanin ‘yan siyasa a jihar....
Babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya ba da umarnin ga rundunar sojin Najeriya da ta fatattaki ‘yan bindigar da ke addabar al’ummar kananan hukumomin Baruten da Kaiama na jihar kwara da Borgu da ke dajin Kainji a jihar Neja cikin wata guda. A jawabin da ya yi wa dakarun rundunar soji...
Muƙaddashin Shugaban Jam’iyyar PDP na Ƙasa, Ambasada Umar Damagum, ya umarci jami’an jam’iyyar da su yi karɓi Arch. Setonji Koshoedo a matsayin mukaddashin sakataren jam’iyya na ƙasa. Gwamnonin PDP, a taron da suka yi a Ibadan, Jihar Oyo, sun amince da Koshoedo a matsayin mukaddashin sakatare har sai lokacin da shugabannin shiyyar Kudu maso Gabas...
Amurka ta kai wasu sabbin hare-hare ta sama a Yaman, a daidai lokacin da kasar Larabawar ke ci gaba da nuna goyon baya ga Falasdinawa a Gaza. Gwamnonin Sana’a da Sa’ada su ne wuraren da Amurka ta kaddamar da sabbin hare-hare a safiyar Alhamis. A birnin San’a, jiragen yakin Amurka sun kai hare-hare 6 a...
Aljeriya sun kori fiye da bakin haure 1,100 zuwa Nijar a rana guda, al’amarin da ba a taba ganin irinsa ba. Bakin hauren da hukumomin Aljeriyar suka bayyana da basa bisa ka’ida, an kora su a cikin hamadar sahara a ranar Asabar din da ta gabata, Inda sukayi tattaki zuwa kan iyakar kasar Nijar, kasar...
Jamhuriyar Musulinci ta Iran, za ta karbi bakuncin taron farko na kasa da kasa kan kare hakkin bil adama a Gabas ta Tsakiya. Shugaban Hukumar Al’adu da Sadarwa ta Musulunci Mohammad Mehdi Imanipour ya bayyana cewa, za a gudanar da taron farko na kasa da kasa kan batun kare hakkin bil’adama kan Gabas ta Tsakiya...
Sanarwar ta kara da cewa, Shugaban tawagar ‘yan fashin, Baba-Beru ya samu munanan raunuka, wanda daga baya ya rasu a Asibiti. “An garzaya da dukkan wadanda suka samu raunuka zuwa Asibitin kwararru na Murtala Mohammed da ke Kano, inda Baba-beru ya rasu a lokacin da ake jinyarsa, amma jami’an ‘yansanda an sallame su bayan...
Jami’in ya kara da cewa, kasar Sin ba ta son gwabza yakin kasuwanci da karin harajin kwastam, amma kuma ba za ta rungume hannu ta zuba ido ba idan yakin ya kaure, yana mai nuni da cewa, idan har Amurka ta zabi fafata yakin kasuwanci, Sin za ta sha damarar yakin har sai ta ga...

Shawarar Tabbatar Da Tsaro A Duniya Ta Samar Da “Kyakkyawan Fata” Ga Duniya Mai Fama Da Tashin Hankali
Na uku, ba da ra’ayin samun tsaro kafada da kafada, inda aka jaddada cewa, ya dace kasa da kasa su yi fatali da ra’ayin nuna wa juna fito-na-fito, kana, su fuskanci dimbin kalubalen tsaro cikin hadin-gwiwa. Na hudu wato na karshe, tallata ra’ayin tabbatar da tsaro mai dorewa, wato a maida hankali kan dorewar tsaro...
Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu a Majalisar Dattawa, Abdurrahman Kawu Sumaila ya tabbatar da ficewarsa daga jam’iyyar NNPP zuwa APC. Sumaila ya tabbatar wa Aminiya ficewarsa a wani saƙon kar ta kwana, bayan wallafa wa a shafinsa na Facebook. Majalisun jihohi sun buƙaci a kawo ƙarshen matsalar tsaro Gwamna da jiga-jigan siyasa a Delta...

Gwamna Inuwa Ya Bayar Da Gudunmawar Naira Miliyan 10 Ga Iyalan Wadanda Hatsarin Ista Ya Rutsa Da Su A Gombe
Da yake jawabi a fadar Mai Tangele (Sarkin Billiri), Danladi Sanusi Maiyamba, ya bayyana lamarin da matukar bakin ciki tare da fatan samun makoma mai kyau ga wadanda suka rasu, ya kuma warkar da wadanda suka samu raunuka da gaggawa. Daga nan sai Gwamna Inuwa ya sanar da bayar da gudummawar Naira miliyan 2...
A yau Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, yake-yaken karin haraji da kasuwanci ba su haifar da komai illa tauye halastattun hakkoki da muradun dukkan kasashe, tare da kawo cikas ga tsarin ciniki tsakanin bangarori daban-daban, da kuma yin tasiri mara kyau ga tsarin tattalin arzikin duniya. Yayin ganawarsa da...
Asusun bayar da lamuni na duniya ( IMF) ya yi gargadin cewa rashin tabbataci da Karin kudin harajin Amurka ya haddasa zai iya kawo tsaiko a cikin harkokin cinikiyya ta duniya. Sanarwar wacce babban jami’in ttatalin arziki na Asusun bayar da lamunin na duniya Pierre -Oliver-Gourinchas, ya bayyana ta kara da cewa; Za a iya...
Kungiyar da take wakiltar Iran a wasannin Taekwondo na duniya a kasar Sin, ta sami lambobin yabo 8 a ranar farko da bude gasar ta kasa da kasa. An fara wasannin na Tikondu a garin Tayan dake kasar China wanda shi ne karo na 7 da kuma ‘yan wasa 491 daga duniya suke gasa. Daga...
Ministan harkokin wajen Iran wanda ya ziyarci kasar China, ya bayyana cewa, tattaunawa da mahukunta wannan kasa ta yi kyau, kuma ba da jimawa ba, shugaban kasar Iran zai kai Ziyara can kasar. Ministan harkokin wajen na Iran Abbas Arakci bayan ganawa da takwaransa na China ya ce; Na yi doguwar ganawa da ministan harkokin...
Hukumar lafiya ta duniya (W.H.O ) ta sanar da cewa rashin magani da na’urorin wanke koda a Gaza, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 400 masu fama da wannan cutar. Hukumar lafiyar ta duniya ( w.h.o) ta kuma yi ishara da yadda ‘yan mamaya su ka lalata bangarorin da suke kula da cutuka na musamman a...
Ƙungiyar shugabannin majalisun jihohin Nijeriya ta yi tur da matsalolin tsaron da suka addabi jihohin Filato, Borno, Binuwai, Neja, da kuma Kwara a baya-bayan nan. Ƙungiyar ta buƙaci gwamnatocin jihohi da na tarayya da su ɗauki matakan gaggawa domin daƙile bala’in da jihohin a kwanan nan suka tsinci kansu a ciki. Abin da ya sa...
Gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori da wasu jiga-jigan ‘yan siyasa na jihar sun sun sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa APC. Daga cikin jiga-jigan da suka sauya sheƙa har da tsohon gwamna Ifeanyi Okowa, shugaban jam’iyya, da sauran masu ruwa da tsakin jam’iyyar reshen jihar. Abin da ya sa na bi sahun mahaifiyata a Kannywood —...
Bugu da kari, kasar ta samar da cibiyoyin kula da lafiyar mata da kananan yara 3,081, baya ga likitocin yara da na mata a fadin kasar da yawansu ya kai 373,000. Kana fiye da kashi 90 cikin dari na cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko a yanzu sun mallaki kayan aiki da sassan kula da...
Ba wannan ne karon farko da ake zargin wasu ‘yan ƙasashen waje da kai hare-hare a Nijeriya ba. A baya an yi zargin cewa ƙungiyoyi kamar Lakurawa da ke kai hare-hare a jihohin Sakkwato da Zamfara, sun samo asali ne daga ƙasashen waje. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu...
Maryam Abubakar, ɗaya ce daga cikin jaruman masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood ’yan ƙalilan da suka yi nasarar bin sahun iyayensu a harkar fim. Matashiyar jarumar, wadda aka fi sanin ta da Maryam Intete a masana’antar, ta yi bayani a kan matsayinta na wadda iyayenta suka suka a cikin cikin harkar fim. Mahmuda: Sabuwar ƙungiyar...

Rohoton Kwamitin Kare Hakkin Dan Adam Ya Tabbatar Da Tafka Manyan Laifukan Cin Zarafin Bil-Adama A Siriya
Wani rahoton kare hakkin bil adama ya tabbatar da aikata manyan laifuka a gabar tekun Siriya tare da yin kira da a kare fararen hula Kwamitin da ke bin diddigin kare hakkin bil adama a kasar Siriya karkashin jagorancin dan gwagwarmaya Haitham Al-Manna, ya fitar da wani cikakken rahoton take hakkin dan Adam mai shafuka...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Wutar lantarki ta zama tamkar gwal a wasu sassan Arewacin Najeriya, inda a wasu yankuna aka ba da rahoton samun ta sa’o’i biyu kawai a rana, wasu kuma ba sa samun ko daidai da dakika ɗaya. Masu ƙananan sana’o’i suna kallon rayuwarsu da kasuwancinsu suna durƙushewa yayin da...
‘Yan majalisar dokokin Aljeriya, sun yi kira da a haramta daidaita alaka da Isra’ila. ‘Yan majalisar dokokin Aljeriya da wakilan jama’a na kasar a zaman majalisar dokokin kasar, sun yi Allah wadai da laifukan da Isra’ila ke aikatawa akan al’ummar Gaza, tare da nuna cikakken goyan bayansu ga falasdinawa. Mahalarta taron sun yi kira ga...
Guo Jiakun ya kara da cewa, kasar Sin ta kiyaye amfani da tsarin kimiyya da babu rufa-rufa a ciki mai baje komai a faifai, tare da nuna goyon baya da kuma shiga cikin kokarin da kasashen duniya ke yi na gano ainihin inda cutar ta samo asali. Ya bukaci Amurka da ta daina siyasantar...
A safiyar jiya Litinin ce Fafaroma Francis mai shekaru 88 ya koma ga mahaliccinsa, bayan da ya yi fama da mutuwar ɓarin jiki da kuma bugun zuciya, kamar yadda Fadar Vatican ta sanar. Shugaban na mabiya ɗariƙar Katolika ya shafe makonni 5 a asibiti a farkon wannan shekara, sakamakon harbuwa da cutar limoniya, amma ya...
Brigadier General Ali Mohammad Naeini, kakakin dakarun dakarun kare juyin juya halin musulunci na kasar ya bayyana cewa dakarunsa a shirye suke fiye da ko wani lokaci wajen kara kan iyakokin JMI daga makami. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran Naeini yana fadar haka a yau Talata a wani taro da kafafen yada labarai...
Iyalan Alhaji Surajo Ilyasu Malumfashi (RADIO NIGERIA KADUNA) dana Alhaji Idris Ahmed Accama na farin cikin sanar da bikin aure na ‘ya’yansu, Muhammad Auwal Idris da Zainab Surajo Malumfashi. Za’a gudanar da bikin auren ranar Asabar, 3 ga Mayu, 2025, a Masallacin Juma’a na Dan Fodio, Dake Anguwan Sunusi, Jihar Kaduna. Za a daura...
Gwamna Umar Mohammed Bago, ya sanya dokar hana fita ta tsawon sa’o’i 12 a birnin Minna na Jihar Neja. Wannan dai na zuwa ne sakamakon hare-haren da ya janyo salwantar rayuka da aka samu a bayan nan a babban birnin. Hanyoyin da za a magance rikicin Filato — Masana HOTUNA: Yadda Pantami ya kai wa...
Kamfanoni da masana’antun America da dama sun dakatar da harkokinsu, dubban mutane sun rasa aikin yi. Don haka wannan mataki bai haifar da sakamakon da Mr. Trump ke bukata ba, musamman idan aka yi la’akari da yadda kasuwar hannayen jari ta shiga cikin rudani, gami da hali na rashin tabbas da manoman America suka samu...
Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: A shirye suke su cimma yarjejeniya yayin da suke kiyaye muradun kasarsu Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Iran a shirye take ta cimma matsaya bisa kayyade tsare-tsare tare da kiyaye moriyar kasarta, amma idan ba ta son yin shawarwari da ta daga kan matsayinta, tare da...
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Ba su da niyyar gudanar da tattaunawa da Amurka a fili Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana ta shafinsa na Twitter a takaitaccen jawabin da aka shirya yi a taron manufofin nukiliya na kasa da kasa na Carnegie, yana mai jaddada cewa, “Iran sam ba...
Munanan abubuwan da suka faru na zubar da jini bayan wasa tsakanin Al-Ahly Tripoli da Al-Suwaihli a Libya A kusa da filin wasa na birnin Tripoli an ga abubuwan na zubar da jini bayan wasan da aka yi tsakanin Al-Ahly Tripoli da Al-Suwaihli, lokacin da wasu motocin ma’aikatar harkokin cikin gida ta gwamnatin hadin kan...
Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo, ya dakatar da basaraken yankin Masarautar Uwano Kingdom, Dakta George Oshiapi Egabor, nan take saboda matsalar yi garkuwa da mutane a yankin. Dakta George Oshiapi Egabor shi ne Okumagbe na Masarautar Uwano da ke Agenebode a Karamar Hukumar Etsako ta jihar. Kakakin gwamnan, Fred Itua, a cikin wata sanarwa, ya...
Adadin mutanen da suka mutu a hare-haren da aka kai a Jihar Binuwai ya ƙaru zuwa 72. Adadin ya ƙaru ne bayan gano ƙarin gawarwaki 13 a ranar Litinin a ƙananan hukumomin Ukum da Logo.Adadin ya ƙaru ne bayan gano ƙarin gawarwaki 13 a ranar Litinin a ƙananan hukumomin Ukum da Logo. Da farko a...
A yayin harin, mutane da dama sun gudu zuwa dazuka, amma sun fara dawowa yayin da zaman lafiya ya fara samuwa. “Yanzu mutane sun fara dawowa garin kuma abubuwa sun fara dawowa dai-dai,” inji wani mazaunin yankin. Wani dagacin ƙauyen, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce an samu zaman lafiya kuma al’umma sun...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya mika ta’aziyya game da rasuwar shugaban ‘yan darikar katolika na duniya Paparoma Francis. A wani sako da ya aike a jiya Litinin, Pezeshkian ya ce Paparoma Francis a matsayinsa na shugaban darikar Roman Katolika ya sadaukar da rayuwarsa gaba daya wajen yada koyarwar Yesu Almasihu. Shugaban ya ce Paparoma...
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya rattaba hannu kan wata yarjejeniya ta hadin gwiwa daga dukkan fannoni bisa manyan tsare-tsare da Iran a hukumance, a cewar wata takardar aiki da aka wallafa a yanar gizo a jiya Litinin. Shugaban kasar Rasha da takwaransa na Iran Masoud Pezeshkian sun rattaba hannu kan yarjejeniyar a ranar 17...