2025-02-23@21:46:28 GMT
إجمالي نتائج البحث: 14

«Sayyid Hassan Nasrallah»:

    Lokacin kadan da ya gabata ne dai aka rufe shahid Sayyid Hassan Nasrallah a makwancinsa na kare dake kusa da filin saukar jiragen sama na Beirut,bayan da aka dauki tsawon yau ana gudanar da jana’izarsa. Dubun dubatar mutanen Lebanon da kuma wasu daga wajen kasar ne su ka halarci taron jana’izar Sayyid Shahid Hassan Nasrallah da kuma ta Sayyid Hashim Safiyuddin da  aka gudanar a cikin birnin Beirtu. Tashar talabijin din al’mayadin ta bayyana cewa bisa kirdado adadin mutanen da su ka halarci jana’izar sun kai mutane miliyan daya da 400,000. Mahalarta jana’izar sun cika filin wasa na birnin Beirut da kuma manyan tituna ta yadda babu masaka cinke, da hakan ya sa motar da take dauke da makararsa da...
    Babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrallah Sheikh Na’im Kassim ya bayyana Shahidin al’umma Sayyid Hassan Nasrallah da cewa, jagora ne na musamman na al’ummun larabawa da musulmi kuma shugaban gwgawarmaya. A cikin jawabin da ya gabatar a lokacin jana’izar Shahid Sayyid Hassan Nasrallah, da Shahid Hashim Safiyuddin, inda ya bayyan cewa: A wannan rana muna yin ban kwana da jagora na tarihi na musamman wanda kuma yake a matsayin alkiblar ‘yantattun na duniya. Sheik Na’im Kassim ya kuma ce; Sayyid Hassan Nasrallah ya kasance wanda ‘yan gwgawarmaya suke kauna, wanda Falasdinu da birnin Kudus ne manufarsa, ya kuma taka rawa wajen farfado da batun kare hakkokin Falasdinawa. Babban sakataren kungiyar ta Hizbullah Sheikh Na’im Kassim ya kuma ce; Sayyid...
    Wanda ya wakilci jagoran juyin juya halin musulunci na Iran a wajen jana’izar Babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrallah da kuma Shahid Safiyuddin Hashim, ya gabatar da jawabi da a ciki ya bayyana cewa: Jagoran jihadi mai girma, kuma shugaban gwgawarmaya a cikin wannan yankin, Sayyid Hassan Nasrallah ( Allah ya daukaka matsayinsa)  ya kai matsayi na koli na daukaka da izza. Sayyid Mujtaba al-Husainy ya kuma ce; A wannan lokacin za a binne gangar jikin Sayyid a cikin kasar da ya yi jihadi saboda Allah akanta, amma ruhinsa da kuma tafarkinsa na gwgararmaya zai kara daukaka fiye da kowane lokaci a baya. Sayyid Mujtaba al-Husaini ya kuma ce:Makiya su kwana da sanin cewa, gwgawarmaya za ta cigaba da...
    Tawagogi na ci gaba da isa Beirut, domin halartar jana’izar tsohon sakataren kungiyar Hezbollah ta Lebanon mirigayi Sayyid Hassan Narsrallah. Iran, ma ta sanar da aikewa da wata babbar tawaga zuwa kasar ta Lebanon domin halartar jana’izar shahiddan Sayyid Hasan Nasrallah da Sayyed Hashem Safieddine. A gobe Lahadi ne za a gudanar da jana’izar wadannan shahidai biyu a birnin Beirut, inda ake sa ran tawagogin daga kasashe 78 za su halarta. Shugaban kwamitin da ke sa ido a jana’izar, Sheikh Ali Daher, ya sanar a ranar Juma’a cewa za a fara jana’izar a hukumance a ranar Lahadi daga karfe 1 na rana (agogon kasar). Jami’ai da dama da suka hada da shugaban kasar Lebanon da kakakin majalisar dokokin kasar za...
    Hukumar bayar da gudunmawar fansho ta Jihar Jigawa da Kananan Hukumomin jihar ta kulla yarjejeniyoyi da wasu mashahuran Hukumomin Asusun Fansho guda shida (PFA) da nufin tabbatar da tafiyar da kudaden fansho na jihar yadda ya kamata. Shugaban ma’aikata na jiha Alhaji Muhammad K Dagaceri wanda ya jagoranci rattaba hannu kan yarjejeniyar a madadin gwamnatin jihar Jigawa a gidan fensho na Dutse ya ce taron yana kara jaddada kudirin gwamnati na  tabbatar da gaskiya da inganci a tsarin tafiyar da fansho. Ya kuma jaddada mahimmancin kula da harkokin kudi da kuma bukatar samar wa wadanda suka yi ritaya kudaden fansho domin ci gaba da gudanar da rayuwarsu. “Wannan yarjejeniya ta nuna wani gagarumin ci gaba a kokarin da...
    Tashar jiragen sama ta birnin Beirut tana cike da masu shiga kasar daga kasashen daban-daban don halattar jana’izar Shahidai kuma shuwagabannin kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasarallah da kuma Magajinsa Shahid Sayyid Hashimi Safiyyuddeen wanda za’a gudanar a ranar 23 ga watan Fabarairu da muke ciki. Kamfanin tafiye-tafiye na “Ajuz Travillin Agency’ ya fadawa tashar talabijin ta Almanar kan cewa tun yawan jiragen sama masu zuwa daga kasashen waje suka nin nink tafiye-tafiyensu zuwa Beiru, daga cikinsu, akwai Iraq Air wanda yake zuwa Beiru  har sau biyu. Amma daga yau ya kara shi zuwa har sau ukku. Kamama Egypt Air ya ninka zuwasa Beirut har sai yu. Da kuma Tarksih Air shi ya ninninka ta fiyasa zuwa kasar. Labarin ya kara...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’el Baghae ya ce gwamnatin kasar Iran zata aika tawaga mai karfi zuwa kasar Lebanon don halattar Jana’izar Sayyid Hassan Nasarallah wanda za’a gudanar a cikin yan kwanaki masu zuwa. Bakha’I ya kara da cewa,  zamu halarci Jana’izar a kasar Lebanon, kuma zamu aika da tawaka wacce zata kunshi manya-manyan jami’an gwamnati da kuma malaman addini. A ranar Talatan da ta gabata ce wani jami’an kungiyar ta Hizbullah, ya bada sanarwan cewa baki daga kasashe 79 ne zasu halarci jana’izar. Sheikh Ali Daher shugaba kwamitin gudnar da jana’izar ya kara da cewa, ranar zata kasashen ranar sabonta bai’a da marigayin da kuma wanda ya gaje shi. A ranar 27 ga watan Satumba shekara ta...
    Binciken shiyya-shiyya na ayyukan ya nuna cewa shiyyar Kudu-maso-Kudu ta geo-siyasa ce ta kan gaba a jadawalin ayyuka 114 da aka yi watsi da su, inda Jihar Akwa Ibom ke kan gaba da ayyuka 87. An nakalto cewa kawo yanzu gwamnan Jihar Akwa Ibom, Umo Eno ya zuba Naira biliyan 47.93 cikin ayyuka 36 na kwamitin kudi da manufofin gwamnatin tarayya (FGPC) da ya gada, da kuma Naira biliyan 4.04 cikin 51 na ayyukan gaggawa (EIPs) da ya gada daga gwamnatin da ta shude, adadin da ya kai Naira biliyan 51.96. Shiyyar Arewa maso yamma ta biyo bayansu da ayyuka 44 da aka yi watsi da su, wanda jihar Zamfara kadai ke da ayyuka 33 da ba a kammala ba....
    Babban jami’in jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin Cai Qi, ya yi kira a ranar Laraba, da a ci gaba da yin kokari wajen kawar da ayyukan da ba su da ma’ana, da rage nauyin da ke wuyan jami’an kananan matakai, don tabbatar kyakkyawan salon aiki tsakanin ’yan jam’iyya da jami’ai wajen cimma burin da aka sa a gaba a cikin shirin shekaru biyar-biyar karo na 14 wato daga shekarar 2021 zuwa ta 2025. Cai, wanda kuma mamban zaunannen kwamitin kula da harkokin siyasa na kwamitin kolin JKS ne, kuma mamba a sakatariyar kwamitin kolin JKS, ya bayyana hakan ne a wani taro na matakin koli game da wannan batu. Taron ya bayyana cewa, ya kamata a mayar da hankali wajen...
    A wani umurnin da ya bayar Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran, Imam Aya. Sayyid Alilul Khami’nae ya sanya babban sakataren kungiyar Hizbullah a matsayin wakilinsa a kasar Lebanon. Bayan shahadar Sayyed Hassan Nasarallah da kuma Sayyed Hashim safiyuddeen An zabi sheikh Na’em Kasim a matsayin babban sakataren kungiyar ta Hizbullah a kasar Lebanon. Kafin haka dai Shahid Sayyed Hassan Nasarallah ne mai wakiltar jagoran a kasar ta Lebanon. Sheikh Qasim dai  ya taka rawar a zo a gani  wajen yakin da kungiyarsa ta shiga da HKI na watanni 15.. Kuma ana saran shi ne zai zama mai fitar da kungiyar zuwa tudun na tsira daga halin da ta shiga ciki ya kuma ci gaba da yakar kungiyar.
    Bbaban magatakardar kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’im Kassim wanda ya gabatar da jawabi a jiya Lahadi ya bayyana cewa; Za a yi jana’izar Shahid Sayyid Hassan Nasrallah tare da Shahid Sayyid Hashim Safiyuddin. Sheikh Na’im Kassim ya kara da cewa, za a binne Shahid Sayyid Hassan Nasrallah a wani wuri dake kusa ba filin saukar jiragen sama na birnin Beirut, yayin da shi kuma Sayyid  Hashim Safiyuddin za a binne shi a mahaifarsa ta Deir-Kanun dake kudnacin Lebanon. Wani bayanin da Sheikh Na’im Kassim ya yi, shi ne cewa bayan shahadar Sayyid Hassan Nasrallah an zabi Sayyid Safiyuddin Hashim, saidai gabanin su sanar da kwanaki shi ma ya yi shahada. Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya ce, taken...
    Tashar Talabijin din “ Almanar” ta sanar da cewa, da marecen yau Lahadi ne babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sheikh Na’im Kassim sai yi jawabi akan muhimman abubuwan da suke faruwa a Lebanon da kuma wannan yankin. Har ila yau, Almanar ta ce babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah Sheikh Na’im Kassim zai yi bayani akan lokacin da za a yi jana’izar Shahid Sayyid Hassan Nasrallah. Babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrallah ya yi shahada ne a sanadiyyar hare-haren masu muni da jiragen yakin HKI su ka kai wa unguwar Dhahiya dake birnin Beiruta. Majiyar ‘yan sahayoniya ta ce sun jefa bama-bamai da su ka nai nauyin tan 85 akan ginin da Shahid Sayyid Hassan Nasrallah yake ciki.
    Gwamnan ya kara jaddada Gwamnatinsa ta maida hankalin ta ne kan irin ayyukan da za ta yi wa al’umma, inda ya yi kira kamata ya yi koda wane lokaci Shugabanni su rika tunawa da al’umman da suka zabe su, suna yi ma su aiki. Da yake kara yin bayani Gwamna Ododo ya ba kungiyar mataimakan Shugabannin Kananan Hukumomi kan kudurin sa na ci gaba da kammala duk bada wadansu mukamai na magoya bayan sa fda suke a Karkara. Ya yi kira da mambobin kungiyar da wadanda suka amfana da taimakon kungiyar,su ci gaba da aiwatar da abubuwan da suka sa a gaban su, saboda ayyukan alkahairin da suka fara zai samar da babbar gudunmawar ci gaba a wasu shekaru ma...
    Yayin da dokar haramtawa hukumar kula da ‘yan gudun hijirar Palasdinu ta MDD (UNRWA) yin aiki a Isra’ila ke gab da fara aiki, kwamitin sulhu na majalisar ya kira wata budaddiyar muhawara dongane da batun, inda wakilin Sin da wakilan sauran kasashe suka sake bayyana goyon bayansu ga hukumar. Wakilin Sin na dindindin a MDD Fu Cong, ya yi kira ga Isra’ila da ta daina dakatarwa da kai wa hukumar hari, kana ta dakatar da zartar da dokoki masu ruwa da tsaki, yana mai kira ga kasashen duniya su ci gaba da goyon bayan hukumar wajen gudanar da ayyukanta da marawa MDD da kwamitin sulhun baya, wajen daukar matakan gaggawa domin tabbatar da hukumar ta gudanar da ayyukanta. Yankin Gabashin...
۱