2025-04-26@11:01:23 GMT
إجمالي نتائج البحث: 454
«yarjejeniya»:
Kungiyar kasuwanci ta duniya ta bayyana cewa, za a sami raguwar hajar da za a yi kasuwancinta a duniya da kaso 0.2% saboda Karin kudin fito da Amurka ta yi. Rahoton kungiyar kasuwancin ta duniya wanda aka fitar da shi a ranar Litinin din da ta gabata ta gina shi ne akan yadda tafiyar kasuwanci...
Hukumar Hisbah a Jihar Kano ta cika hannu da wani matashi da aka gani a wani yanayi mai kamanceceniya da baɗala da wata Akuya, lamarin da ya janyo cece-kuce a dandalin sada zumunta. Matashin, Shamsu Yakubu mai shekaru 24 da ke zaune a Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa ta Kano, ya shiga hannu ne bayan ɓullar...
“Waɗannan cibiyoyi ba iya Jigawa za su yi wa amfani ba, har ma da maƙwabta. “Tare da sabbin na’urorin gwaje-gwaje irin su MRI da mammography, ba sai an je wasu jihohi domin samun irin waɗannan ayyuka ba,” in ji shi. Gwamnan ya jaddada ƙudirinsa na ci gaba da inganta harkar kiwon lafiya a jihar, ta...
Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta fitar da bayani da ya kunshi yin Allawadai da keta hurumin masallacin kudus da ‘yan sahayoniya su ka yi a cikin kwanaki uku a jere. “Yan sahayoniyar dai sun rika shiga cikin harabar masallacin na Kudus, suna yin ibadunsu na yahudanci, tare da kariyar ‘yan sandan HKI. Kungiyar ta...

Hamas Ta Fadawa Iyalan Yahudawan Da Take Tsare Dasu A Gaza Kan Cewa ‘Ya’yansu Zasu Koma A Cikin Akwatunan Gawaki
Reshen soja na kungiyar Hamas wato rundunar Izzuddin Qassam, ya gargadi iyalan fursinonin yahudawan Sahyoniyya wadanda take tsare da su a Gaza kan cewa yayansu zasu koma hannunsu gawaki, saboda irin yadda HKI take kara yawaita Jefa boma-boman a kan Falasdinawa a Gaza. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto wani mai magana...
Hukumar Bunƙasa Noman Sukari a Najeriya (NSDC) ta sanya hannu kan yarjejeniyar Dala biliyan guda da kamfanin SINOMACH na ƙasar China kan bunƙasa noman rake da sarrafa shi da nufin samar da sukari da kudina ya kai metrik ton miliyan guda. Kulla yarjejeniyar wani ɓangare ne na shirin Kawancen Najeriya da China, na Gwmanatin Shugaba...
Ministan harkokin noma na JMI Ghulan Reza Noori Ghezelji ya jagoranci wata tawagar jami’an gwamnatin kasar zuwa kasar Brazil don halattan taron ministocin noma na kungiyar BRICS da kuma tattauna al-amura masu muhimmanci wadanda suka shafi ayyukan noma a duniya. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa gwamnatin JMI ta fara aiki...
Wasu masu dauke da makamai sun kai hari a wasu kauyuka biyu dake jihar Filato inda su ka kashe mutane 52. Rahotannin da suke fitowa daga jihar ta Filato sun ambaci cewa wasu makiyaya ne su ka kai harin na ranar Litinin din da ta gabata an kai shi ne a kan yankin Bassa. Kamfanin...
Kasashen turan nan guda uku da ake wa lakabi da E3, sun nuna goyon bayansu ga tattaunawar da ake tsakanin Iran da Amurka. Ministan Birtaniya mai kula da yammacin Asiya Hamish Falconer ne ya bayyana hakan inda ya ce Birtaniya tare da Faransa da Jamus na goyon bayan sasanta batun nukiliyar Iran ta hanyar diflomasiyya....
Wani babban jami’in Hamas ya ce kungiyar a shirye take ta sako dukkan fursunonin Isra’ila da suka rage a zirin Gaza da aka yi wa kawanya, domin musanya abin da ya bayyana da ” fursunoni” da kuma tabbatar da kawo karshen yakin kisan kare dangi da ake ci gaba da yi. Kamfanin dillancin labaran AFP...
Da yake jawabi a madadin shugaban kasa, Gwamna Uba Sani ya bayyana mahimmancin hanyar wadda ta hada babban birnin tarayya da jihohi sama da 12 dake fadin shiyyar Arewa ta tsakiya, Arewa maso Yamma, da Arewa maso Gabas. A yayin taron da aka yi a Jere a karamar hukumar Kagarko a ranar Lahadin da...

Kasashen Larabawa Na Yankin Tekun Farisa Sun Yi Fatan Al-Khairi Ga Iran Da Amurka A Tattaunawar Shirin Nukliyar Kasar
Babban sakataren kungiyar kasashen Larabawa na yankin tekun Farisa (PGCC) ya yi fatan alkhairi ga kasashen Iran da Amurka a tattaunawa ba kai tsaye ba a tsakaninsu dangane da shirin Nukliya ta kasar Iran na zaman lafiya wanda suka fara, a birnin Mascat na kasar Omman a ranar Asabar da ta gabata. Kamfanin dillancin labaran...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A yanzu haka al’ummar Borno na cikin zullumi sakamakon wasu hare-haren da ake zargin ƙungiyar Boko Haram ce ta kai a wasu sassan jihar. Waɗannan hare-hare dai suna faruwa ne bayan shekaru da dama da iƙirarin hwamnati cewa an yi nasarar nakasa ƙungiyar. Ko mene ne dalilin sake...
Shugaban Kasa Bola Tinubu ya kaddamar da aikin sake gyaran babban titin Abuja-Kaduna-Zariya-Kano, wadda ke da matukar muhimmanci ga tattalin arzikin Arewacin Najeriya. Da yake jawabi a taron kaddamarwar a Kagarko, Jihar Kaduna, Gwamna Uba Sani, ya bayyana yadda aka yi watsi da hanyar da kuma irin mummunan tasirin da hakan ya yi ga rayuka...
Sakamakon gazawar shugabanci, bayar da tallafi na neman zama wani bangare a tarihin dimokoradiyyar Nijeriya, inda gwamnatocin jihohi da ’yan majalisu da sauran ’yan siyasa suke amfani da shi wajen cusa wa ’yan kasa ra’ayinsu na siyasa. A duk lokacin da al’umma suka koka a kan wani mummunann yanayi da ya hada da matsin tattalin...
Sanarwar ta ƙara da cewa, ƙungiyar ta karrama gwamna Lawal tare da gwamnonin Akwa Ibom, Kaduna, da kuma jihar Legas. “A jiya a Legas, ƙungiyar ‘yan kasuwa ta Nijeriya da Amurka (NACC) ta gudanar da bikin cika shekaru 65 da ƙaddamar da Alhaji Sheriff Balogun a matsayin shugaban ƙungiyar na 20. “Taron mai...
Wani matashi ɗan shekara 18 mai suna Bakura Muhammed, ya gamu da ajalinsa a wani rikici da ya ɓarke tsakanin ƙungiyoyin matasa masu gaba da juna da ake wa laƙabi da Malians a Maiduguri. Majiyoyin leken asiri sun shaida wa Zaga-zola Makama cewa, rikicin ya faru ne da misalin karfe 4:30 na yammacin ranar...
Yin garkuwa da mutane domin don karbar kudin fansa ya zama ruwan dare a Jihar Katsina har ta kai ga ana shiga cikin manyan birane ana daukar manyan mutane ko makusantansu. Daga manyan sojoji zuwa sarakuna da malaman addini da ’yan siyasa da attajirai da ma dalibai, babu wanda ya tsira daga wannan matsalar...
Rahotanni sun ce an kashe wani uba da ‘ya’yansa biyu a ƙauyen Zogu da ke Gundumar Miango a Ƙaramar hukumar Bassa ta jihar Filato. Kakakin Ƙungiyar ci gaban Irigwe (IDA), Sam Jugo, wanda ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a Jos, ya bayyana sunayen waɗanda harin ya rutsa da su kamar haka, Weyi Gebeh...
Ga kuma yadda ake sarrafawa: Da farko, a zuba ruwa a tukunya a sa a wuta domin ya tafasa. A rage wuta kadan, sannan a zuba garin alabo a hankali cikin ruwan da ke tafasa, ana juyawa da muciya ko cokali ko leda mai kauri don kada ya yi kolalla. A ci gaba da juyawa...
Manyan Ayyukan Malamin makaranta Malaman makaranta suna da ayyuka wadanda sun fi karfin ayi su a cikin aji saboda wurin ba huruminsu ba ne,abubuwan sun hada da irin kwarewar da suke da ita,wadda za su yi amfani da ita wajen renon/ koyar da daliban da kuma yadda rayuwarsu a matsayin ‘yan makaranatrasu za ta kasance....
’Yan sanda sun kama wani magidanci bisa zargin ya ɗirka wa ’yar cikinsa mai shekara 17 ciki a yankin Kariya da ke Ƙaramar Hukumar Ganjiwa a Jihar Bauchi. Kakakin ’yan sandan jihar, Ahmed Wakil ya ce an kama mutumin mai shekaru 50 ne bayan samun ƙara cewa ya yi wa ’yar tasa fyaɗe fiye da...
Hanyoyi Biyar Da Mai Kiwon Kajin Gidan Gona Zai Kare Kajinsa Daga Tsananin Zafin Rana. 1- A Tabbatar An Sama Musu Wadacciyar Iska A Dakin Kwanansu: Ana bukatar mai kiwon kajin ya tabbatar ya sama musu wadatacciyar iska a dakin kwanansu, ana kuma bukatar a yi wa shigifar dakinsu fenti yadda za ta rika rage...
Kazalika, mahalarta taron sun jaddada muhimmancin inganta samar da ayyukan yi, da karfafa tattalin arziki, da kyautata zaman rayuwar ’yan Najeriya, ta hanyar kulla huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare da kasar Sin. (Mohammed Yahaya) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura...
Tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriya kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a 2023, Alhaji Atiku Abubakar ya ziyarci tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari a Kaduna. Atiku ya samu rakiyar tsofaffin gwamnoni da suka haɗa da tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai da tsohon Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal da wasu jiga-jigan ’yan siyasa. An gano gawar makiyayi...
Kazalika, a wani binciken kwanan baya na gama gari kan yawan alummar kasar, ya gano cewa, kaso 53 na wasu matasan kasar, a kullum suna rungumar wannan dabi’ar. Sai dai, muna sane da cewa, wasu ‘yan Nijeriya, na kallon yin cacar tamkar wata aba ce, ta nishadi kawai, amma wasu bincike sun bayyana cewa, wani...
Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta yi hasashen za a yi ruwan sama mai ƙarfi da ambaliya a jihohi 30 da kuma babban birnin tarayya Abuja. Jihohin da ake fargabar fama da ambaliyar ruwan sun haɗa da: Abia, Adamawa, Akwa Ibom, Anambra, Bauchi, Bayelsa, Benue, Borno, Cross-Riɓer, Delta, Ebonyi, Edo, Gombe, Imo, Jigawa, Kebbi, Kogi, Kwara, Lagos,...
Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bada sanarwan cewa yana kokarin cimma matsaya da kasar Chaina dangane da kamfanin sadarwa da kuma yanar gizo na TIK Tok. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto shugaban yana fadar haka a shafinsa na ‘Trump Social, Labarin ya kara da cewa shugaban yana fadar haka a...
Al’ummomin Jihar Kastina sun shiga sabon tashin hankali bayan da ’yan bindiga suka kai wasu munanan hare-hare a wasu yankuna biyu a Jihar Katsina a ƙarshen makon jiya, inda suka kashe mutane shida tare da yin garkuwa da wasu 59. A daren Lahadi, kusan ƙarfe 10:30, ’yan bindiga ɗauke da makamai suka kai farmaki ƙauyen...
Al’ummar Karamar Hukumar Maigatari sun yi kira ga gwamnatin jihar Jigawa da ta taimaka wajen gina hanyoyin da za su hada garuruwansu. Wani mazaunin yankin, Malam Ali A. Bulama Turbus, wanda ya wakilci al’ummomin yayin da yake magana da Rediyon Najeriya a Maigatari, ya jaddada muhimmancin aikin gina hanyar. Ya bayyana cewa samar da hanya...

Tarayyar Turai Ta Yi Maraba Da Tattaunawa Tsakanin IRAN da Amurka Kan Shirinta Na Makamashin Nukliya
Kungiyar tarayyar Turai ta yi maraba da tattaunawa tsakanin Amurka da JMI dangane da shirinta na makamashin Nukliya, tare da kara jaddada cewa hanyar diblomasiyya kadai ta rage don warware wannan matsalar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa a halin yanzu dai kungiyar tarayyar ta Turai ta na ci gaba da...

Jiragen Yaki Da Sojojin Kasa Na HKI Sun Kashe Falasdinawa 38 A Yankin Gaza Daga Safiyar Yau Zuwa Yanzu
Jiragen yakin HKI sun kashe akalla mutane 38 a wurare daban-daban a zirin Gaza, kuma mafi yawan wadanda ta kashen yara kanana ne. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar Falasdinawa a Gaza na cewa da sassafe jiragen yakin sun kaiwa wani gidan Bene a unguwar shujaiyya na wajen garin Gaza inda...
Manajan daraktan cibiyar CGIAR Ismahane Elouafi, ta jaddada cewa idan ana son rage tsadar shigar da abinci nahiyar, wanda a yanzu ya kai kimanin dala biliyan 100 a kowacce shekara, zuba jari wajen inganta kyawun kasa da samar da ruwa da rainon ingantattun irrai masu samar da kyakkyawar yabanya, na da matukar amfani. Ta...
Amurka za ta iya janye sojoji 10,000 daga Gabashin Turai, kamar yadda rahoton NBC News ya bayyana. A shekarar 2022, tsohon shugaban Amurka Joe Biden ya tura karin sojoji 20,000 zuwa yankin bayan Rasha ta kai hari Ukraine. A ranar Talata, NBC ta ruwaito cewa jami’ai shida daga Amurka da Turai sun tabbatar da tattaunawa...
Duk da wannan zullumi da ake ciki, a kwanakin baya, kasar Sin ta tattauna da wasu kamfanonin Amurka sama da 20 cikinsu har da Tesla, inda ta kara ba su tabbacin cewa, za ta ci gaba da bude kofarta ga kamfanonin kasashen waje da aiwatar da gyare-gyare a gida. Wannan shi ake nufi da babbar...

Hamas Ta Yi Allawadai Da Gwamnatin Falasdinawa Kan Masu Goyon Bayanta A Yankin Yamma Da Kogin Jordan
Kungiyar Hamas wacce take iko da zirin Gaza, ta yi tir da gwamnatin Falasdinawa a yankin yamma da kogin Jordan da aka mamaye, saboda dirar mikiyan da ta yi kan Falasdinawa a yankin wadanda suke zanga-zangar beman HKI ta kawo karshen kissan kiyashin da ta yi a gaza. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran...
Wani magidanci ya shiga hannun hukuma bayan da ya lakada wa ’yarsa mai shekaru 27 duka har lahira a yankin Ojo da ke Jihar Legas. Kakakin ’yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin, ya bayyana cewa rundunar ta cika hannu da magidncin ne bayan ya yi aika-aikan a ranar 3 ga watan nan na Afrilu. Hundeyin ya...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A zamanin yau, ba kira da tura saƙo kawai ake yi da wayar hannu ba; baya ga haka, muhimmiyar hanya ce ta samun kuɗi da bunƙasa sana’o’i. Ko kun san dabarun amfani da wayoyinku don samun kuɗaɗen shiga? NAJERIYA A YAU: Mene ne Tasirin Shirin NYSC Bayan Shekaru...

Kudaden Musanyar Kasashen Waje Da Sin Ta Adana Sun Kai Fiye Da Dala Tiriliyan 3.2 A Watanni 16 A Jere
Alkaluman da hukumar kididdiga ta kasar Sin ta samar sun shaida cewa, ya zuwa karshen watan Maris na bana, yawan kudaden musanyar kasashen waje da Sin ta adana ya kai dala tiriliyan 3.2407, adadin da ya karu da kashi 0.42%, wato da dala biliyan 13.4 bisa na makamancin watan Fabrairu. Hakan ya sa yawan kudaden...

Matakin Sin Na Karfafa Takaita Fitar Da Abubuwa Masu Alaka Da Ma’adanan “Rare Rarth” Na Nuni Ga Aniyarta Ta Kare Tsaron Kasa
Kazalika, a cewar kungiyar, matakin takaita fitar da nau’o’in sinadaran ba zai shafi kamfanoni masu bukatarsu ba, muddin ba sa gudanar da wasu ayyuka daka iya zama illa ga tsaron kasar Sin, da ikon mulkin kan kasar, ko moriyar ci gabanta. Har ila yau, matakan ba za su haifar da cikas ga daidaito da wanzuwar...
Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a Kinshasa, babban birnin Jamhuriyar Dimokaraɗiyyar Congo ya kashe aƙalla mutane 30 tare da haddasa ɓarna mai tarin yawa. Ruwan saman ya janyo tsaiko wajen gudanar da al’amura a babban birnin tare da katse zirga-zirgan ababen hawa a kan titin Kinshasa, wanda ya taso daga tsakiyar birnin zuwa...
Jami’an rundunar ‘yansandan jihar Ribas a ranar Litinin sun harba tiyagas (barkonon tsohuwa) kan masu zanga-zangar lumana don nuna adawa da abin da suka kira rashin shugabanci nagari a kasar. Masu zanga-zangar karkashin kungiyar ‘Take It Back’ sun kuma gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewa da ayyana dokar ta-baci a jihar Ribas da kuma yadda...
Iran ta bakin kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar, Esmail Baghai, ta ce nahiyar turai sun tafka kure na tarihi, ta hanyar goyon bayan Isra’ila ta hanyar yin watsi da sammacin kama Benjamin Netanyahu. Esmail Baghai ya bayyana haka ne a cikin wani sako a asusunsa na X, bayan ziyarar aiki da Netanyahu ya kai kasar...
Kungiyar Tuntuba ta Arewacin Najeriya (ACF) ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta dauki matakin gaggawa wajen kawo karshen hare-haren da ake kai wa al’umma a Jihar Filato. Kungiyar ta bayyana bakin cikinta matuƙa kan harin da aka kai yankin Bokkos da Mangu a ranar 28 ga watan Maris, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da...
Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa (ACF) ta buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta ɗauki matakin gaggawa wajen kawo ƙarshen hare-haren da ake kai wa al’umma a Jihar Filato. Ƙungiyar ta bayyana baƙin cikinta matuƙa kan harin da aka kai yankin Bokkos da Mangu a ranar 28 ga watan Maris, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama...
Hamas Ta Yaba Da Ma’aikaciyar Kamfanin Microsoft Wacce Ta Fallasa Yadda Kamfanin Yake Taimakawa HKI Kungiyar Hamas wacce take iko da zirin Gaza, ta yabawa ma’aikaciyar kamfanin kayakin lantarki da kuma sadawar ta Microsof mai suna Ibtihal Abussad wacce ta fallasa kamfanin a bikin cika shekaru 50 da kafa shi, a dai dai lokacinda daractan...
Gwamnan ya taya al’ummar Musulmi murna bisa kammala azumin watan Ramadan tare da addu’ar Allah ya karvi ibadu. “Ina addu’ar Allah ya ci gaba da ba mu zaman lafiya da kwanciyar hankali tare da hadin kai a tsakani. Za mu ci gaba da shaidar bukukuwan Sallar. “Ina kuma gode wa shugabannn addininmu bisa koyar da...
Yayin ziyararsa kasar Sin kwanan nan, babban mashawarcin gwammatin wucin-gadi ta kasar Bangladesh, Muhammad Yunus, ya tattauna da wakiliyar CMG, wato babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin, inda a cewarsa, a matsayin kasa ta farko a kudancin nahiyar Asiya, wadda ta rattaba hannu tare da kasar Sin kan takardar bayanin hadin-gwiwa game...
Wakiliyar musamman ta MDD akan Falasdinu Francesca Albanze ta sanar da cewa; Bayanan da jaridar ” New York Times” masu kunshe da hotuna na laifin kashe masu aikin ceto a Rafah, suna dakile riwayar Isra’ila.” Wakiliyar ta MDD ta fada wa tashar talabijin din Aljazeera cewa, abindaya faru kisan kiyashi ne’ sannan ta kara da...
A wata sanarwa da kungiyar ta malaman addinin musulunci ta duniya ta ce wajibi ne akan kowane musulmi wanda yake da iko a fadin duniyar musulunci da ya taimakawa mutanen Gaza da makamai da kayan yaki domin dakile ta’addancin Isra’ila da yake cigaba. A jiya Juma’a ne kungiyar malaman addinin musuluncin ta duniya ta fitar...