2025-03-19@06:40:16 GMT
إجمالي نتائج البحث: 471
«Gidauniyar Dangote»:
Motocin dai, an bai rundunar soji Uku, yayin da rundunar ‘yansanda ta Mopol ta karbi daya. Kwamandan Barikin Soji na Birnin Kebbi, Manjo A. P. Azubuine, ya bayyana godiyarsa na goyon baya da gwamnatin ke basu wajen yaki da ‘yan ta’adda a fadin jihar. Shi ma a nasa bangaren, ACP Aliyu Jega, kwamanda Mopol...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Masu Goyon Bayan Falasdinu Sun Gudanar Da Zanga-Zanga Don Bukatar Sakin Mahmoud Khalil A Tsakiyar Birnin New York
Amurkawa masu goyon bayan Falasdinu sun gudanar da gangami a unguwar manhatan na birnin Nuyork don neman sakin Mahmoud Khalil daya daga cikin masu gwagwarmaya kan tafarkin samun yencin Falasdinawa. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa kama Mahmoud Khalila da kuma tsareshi ya ingiza matasa da dama a Amurka suka nuna...
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyar mu a yau , shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata, wadanda suka shafi siyasa tattalin arziki zamantakewa tsaro da sauransu, inda muke masu karin bayani sannan mu ji ra’ayin masana dangane da...
Babban Rajistara na Sashen kula da lafiyar Koda a Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Gombe (FTHG), Dr. Fidelis Linga, ya yi kira ga jama’a da su kula da lafiyarsu domin kaucewa kamuwa da cututtukan koda. Ya bayyana hakan ga manema labarai a Gombe yayin bikin Ranar Koda ta Duniya. Dr. Fidelis Linga ya jaddada...
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour (LP) a 2023 kuma tsohon gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi, ya kai ziyara Jihar Bauchi a ranar Alhamis don wata ganawa ta musamman. Da isarsa filin jirgin sama na Sir Abubakar Tafawa Balewa, Mataimakin Gwamnan Jihar Bauchi, Rt. Hon. Mohammed Auwal Jatau, ne ya tarɓe shi. Obi ya...
Gidauniyar Attahiru Bafarawa ta fara rabon tallafin kudi naira miliyan goma sha uku da dubu dari takwas ga iyaye mata marayu dari biyu da saba’in da bakwai da masu bukata ta musamman a jihar Sokoto domin tallafawa kananan sana’o’i. Da yake jawabi a wajen kaddamar da shirin, Shugaban shirin, Malam Lawal Maidoki ya bayyana...
Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗi a baya-bayan nan dangane da ƙaruwar yanayin zafi a sassan ƙasar, yayin da jihohi da dama suke fuskantar ƙarin matsanancin zafi. Gargaɗin ya kuma nuna cewa, tsananin zafin da za a yi fama da shi cikin kwanaki uku ko huɗu masu zuwa wanda zai haddasa damuwar...
Hukumar kula da tituna ta tarayya (FERMA) ta jaddada kudirinta na kula da titunan gwamnatin tarayya da inganta ababen more rayuwa a fadin kasar nan. Daraktan hukumar ta FERMA, Injiniya Kabiru Iliyasu Dan-Mulki ne ya bayyana haka a lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin kungiyar ‘yan jarida ta kasa (NUJ) daga gidan rediyon tarayya...
Jami’an tsaro da ke rakiyar tawagar Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, sun daƙile wani harin Boko Haram a kusa da garin Gujba a Jihar Yobe. Gwamnan da tawagarsa na kan hanyarsu ta komawa Maiduguri daga Biu lokacin da suka haɗu da ’yan ta’addan, wanda hakan ya tilasta musu tserewa bayan musayar wuta. Majalisar wakilai...
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi maraba da matakin da kasar Yemen ta dauka na haramtawa jiragen ruwan Isra’ila shiga tekun Bahar Maliya Bayan sanarwar da kungiyar Ansarallah ta kasar Yemen ta fitar na cewa za ta dawo da haramcin da ta yi wa jiragen ruwan Isra’ila na tsallakawa tekun Bahar Rum, Hamas ta...
Ministan harklokin wajen Rasha, Sergei Lavrov ya ce kasarsa na goyon bayan sake farfado da yarjejeniyar farko ta Iran da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da shi. Mista Lavrov ya jaddada goyon bayan Moscow ga sake farfado da muhimmiyar yarjejeniya da Iran da manyan kasashen duniya suka rattabawa hannu a shekarar 2015....
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Matsalar tsaro a Arewacin Najeriya na ci gaba da tsananta, lamarin da ya sa wasu al’umma ke neman hanyoyin kare kansu. Ɗaya daga cikin hanyoyin da wasu yankuna suka ɗauka shi ne yin yarjejeniya da ’yan bindiga da ke addabar su, domin samun zaman lafiya. NAJERIYA A YAU:...
Idan ka dauki bangaren tsofaffi da kananan yara, za ka iya cewa su ne mafi rauni a cikin al’umma. Tsofaffi sun gajiya don haka suna bukatar taimako, yara kanana kuma ba su kawo karfi ba, bisa haka dole suna bukatar madafa. A nan, sai mu ce gwamnatin Sin ta yi tunani mai kyau. Kundin rahoton...
Mohammad Reza Aref mataimakin shugaban kasa na farko a nan JMI ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iran ba zata karbi umurni daga wata kasa dangane da shirin makamashin nukliya ta zaman lafiya na kasar ba. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Reza Aref yana fadar haka a jiya Talata, ya kuma kara...
“Bayan samun rahoton, jami’in ‘yansanda reshen Faskari ya yi gaggawar tara tawagar jami’an tsaro zuwa wurin. “Rundunar ta hanyar amfani da dabaru, ta yi kwanton bauna, inda ta rikita ‘yan bindigar da ruwan harsashi wanda ya hakan ya ta tilasta musu guduwa da raunuka daban-daban, an yi nasarar ceto dukkan mutanen 30 da aka...
Shugaban kwamatin duba rabon abincin azumi na majalisar dokokin jihar Jigawa a shiyyar Dutse kuma mataimakin Shugaban Majalisar, Alhaji Sani Isiyaku Abubakar ya bukaci masu aikin dafa abincin a karamar hukumar Gwaram da su dauki wannan aiki a matsayin turbar samun lada daga Allah Madaukakin Sarki ba wai hanyar neman riba kadai ba. Alhaji Sani...
Da jijjifin safiyar yau Laraba ne aka harba rukunin taurarin dan’adam masu karamin zango daga doron kasa guda 18 a cikin roka kirar Long March-8 Y6, daga cibiyar harba kumbo ta kasuwanci ta lardin Hainan da ke kudancin kasar Sin. Taurarin na dan’adam da aka harba, wanda rukuninsu shi ne na biyar a cikin nau’o’insa,...
Hakika yadda kasar Amurka ta dakatar da tallafi a wannan karo ya nuna ra’ayin shugaba Donald Trump dangane da kasashen Afirka. Wanda za a iya fahimta bisa ganin yadda ya bayyana kasar Lesotho a matsayin “kasar da ba a san ta ba”, wacce ba ta cancanci tallafin da ake ba ta ba, a kwanakin baya,...
Jami’ar kula da manufofin ketare ta Tarayyar Turai, Kaya Kalas, ta tabbatar da cewa, EU za ta iya sake kakaba takunkumi kan kasar Syria, idan aka samu tabarbarewar lamurra, tana mai nuni da yadda ake cin zarafin fararen hula a gabar tekun Syria. Kaya Kalas ta shaidawa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya cewa, “Muna...
Shugaban ofishin yada labarai a Gaza Salama Marouf, ya yi Allah wadai da ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi, saboda kin janyewa daga yankin Salahul Din a kudancin Gaza da kuma ci gaba da kutsawa da da kai hare-hare a cikin Rafah. Marouf ya yi gargadin...
Kasar Ukraine ta bayyana aniyarta ta amincewa da shawarar da Amurka ta gabatar, game da dakatar da bude wuta nan take tsakaninta da Rasha har tsawon kwanaki 30, biyowa bayan fara tattaunawa da tawagar Amurka a birnin Jeddah na kasar Saudiyya. Wata sanarwar hadin gwiwa tsakanin wakilan Ukraine da na Amurka da aka fitar a...
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta ce matakin da Isra’ila ta dauka na hana shigar da kayayyakin jin kai da bukatun yau da kullum a zirin Gaza da aka yi wa kawanya ya zama “laifi na yaki da kuma hukuncin gama-gari.” A cikin wata sanarwa da ta fitar, Hamas ta ce matakin rufewar ya saba...
Kungiyar tarayyar turai ta jaddada bukatar warware batun Iran ta hanyar diflomatsiyya. Da taek sanar da hakan babbar Jami’ar kula da harkokin ketare ta kungiyar ta ce babu wata hanyar da za’a bi wajen warware matsalar Iran in ba ta diflomasiyya ba. ‘’ta hanyar diflomatsiyya ne za’a warware takaddamar da ake game da batun yarjejeniyar...
Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da daruruwan fasinjoji a ranar Talata a wani yunkurin ci gaba da ta da hankali da wata kungiyar ’yan aware ke yi a Kudu maso yammacin Pakistan. ’Yan bindigar sun raunata direban jirgin kasan a kokarinsu na kwace iko da jirgin a yankin Balochistan mai duwatsu da ke iyaka...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban Kwamitin Tallafa wa Marayu na Riyadissalihin Funtua, Alhaji Lawal Mekaji (Madugun Kasuwar Funtua), ya yi kira ga al’umma, musamman iyaye da masu hannu da shuni, da su bada gudunmawa wajen tallafa wa marayu da inganta rayuwarsu. Ya yi wannan kira ne yayin da yake raba kayan sutura da abinci ga marayu a Funtua a...
An kora Kungiyar Kwallon Kafa ta Manchester United gida a Gasar cin Kofin FA na bana, bayan Fulham ta doke ta da ci 2-1 har gida a filin wasanta na Old Trafford a makon da ya wuce. Manchester United ta yi bankwana da gasar ne alhali ita ce ke mai riƙe da Kofin FA da...
A nata ɓangaren, Amurka ta ce za ta yi amfani da wannan dama don fahimtar matsayin Ukraine kan kawo ƙarshen rikicin da ke tsakanin ta da Rasha. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don...
Kamfanin Man Fetur na Najeriya NNPC ya ce yarjejeniyar da ya ƙulla da Matatar Dangote domin sayar mata da ɗanyen man fetur a farashin naira za ta ƙare a wannan wata na Maris. Sai dai kamfanin ce yana tattaunawa da Matatar Dangote domin tsawaita yarjejeniyar sayar mata da ɗanyen mai a naira. An hana tashe...
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi imanin cewa barazanar da Isra’ila ke yi na sake dawo da yaki a zirin Gaza ba ta da amfani, tana mai cewa tattaunawar tsagaita bude wuta ce hanya daya tilo da Isra’ila za ta iya ceto rayukan ‘yan kasarta da take garkuwa ranar Litinin 10 ga watan Maris,...
Shugaban kasar Ghana, John Darmani Mahama ya nemi kungiyar Ecowas da ta amince da kungiyar kawancen kasashen Sahel din nan guda uku da suka balle daga cikinta. Mista Mahama, ya bayyana hakan a kafofin sada zumunta a ranar Litini jim kadan gabanin ya ziyarci kasar Burkina faso, bayan ya kai irin wanan ziyara kasashen Mali...
Jakadan kasar Rasha na din din din a cibiyoyin MDD da suke Vienna, ya bayyana cewa dakatar da aiwatar da yarjeniyar shirin Nukliya na kasar Iran wanda ake kira JCPOA, wacce kuma aka samar da shi a shekara ta 2015, da kasashen yamma suka yi, shi ne ya haddasa dukkan matsalolin da suka biyo baya....
Rundunar ‘Yan sanda a jihar Kwara ta ce ta fara bincike kan kisan da aka yi wa Alhaji Idris Abubakar, shugaban kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) na jihar. A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Adetoun Ejire-Adeyemi ya fitar, ya ce an harbe shugaban...
Ƙungiyar SERAP, mai fafutukar haƙƙin ɗan Adam da yaƙi da cin hanci da rashawa a Nijeriya, ta buƙaci Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio da ya gaggauta janye dakatarwar da majalisar ta yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan. SERAP ta ce dakatarwar da aka yi wa Sanata Natasha ba komai ba ne illa tauye mata ’yancinta...
Shugabana kasar Ghana John Dramani Mahama, ya ziyarci kasashen Mali da Nijar a wani bangare na ran gadin diflomatsiyya da ya fara a kasashen sahel din nan uku da suka balle daga kungiyar Ecowas. Bayan birnin Bamako a ranar Asabar, shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama ya je birnin Yamai a ranar Lahadi, inda wasu...
Kasar Qatar ta bukaci hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa da ta sanya ido kan cibiyoyin nukiliyar Isra’ila. A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Qatar ta fitar ta bayyana cewa, Doha ta bukaci hukumar ta (IAEA) da ta sanya damar gudanar da bincike da ka’ida daga hukumar ta MDD, kan...
Bayanai da kungiyar dake sa ido kan kare hakkin bil adama ta Syria ta bayar, sun ce rikicin baya-bayan nan tsakanin bangarorin da ke dauke da makamai da suka hada da kungiyar Hayat Tahrir al-Sham (HTC) da kungiyoyin dake da alaka da tsohon shugaban kasar Bashar al-Assad, ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 1,000...
Babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Naim Qassem ya bayyana cewa, gwagwarmayar al’ummar kasar Lebanon na nan da karfinta, duk da asarorin da ta yi da kuma sadaukarwa. A wata hira da yayi da tashar talabijin ta Al Manar, Sheikh Qassem ya bayyana cewa, ‘yan gwagwarmaya a kasar Lebanon sun yi nasarar cimma yarjejeniyar tsagaita bude...
Fiye da fursunoni 40 na Isra’ila da ke hannun kungiyoyin gwagwarmayar Falastinawa ne suka mutu a hare-haren da sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila suka yi ta kaddamarwa kan al’ummar yankin tun daga ranar 7 ga Oktoba, 2023, kamar yadda wani rahoton baya-bayan nan na jaridar New York Times ya bayyana. Binciken, wanda jaridar ta New York...
Rahotanni daga kasar Syria na cewa wata tawagar Majalisar Dinkin Duniya ta shiga birnin Jableh da ke yankin Latakia na kasar Siriya a karon farko a daren jiya Lahadi, kamar yadda wata majiya ta kasar ta shaida wa Al Mayadeen. Tawagar ta Majalisar Dinkin Duniya sun zagaya a unguwannin Jableh, inda suka duba shaguna da...
Ofishin jakadancin kasar Sin dake Nijeriya, ya shirya taro domin bikin ranar mata ta duniya da ake gudanarwa a ranar 8 na watan Maris din kowacce shekara. Taron mai taken “Labarinta, Makomarta” wanda ya gudana ranar Juma’a a cibiyar raya al’adu ta kasar Sin dake birnin Abujan Nijeriya, ya hada mata daga dukkan bangarorin rayuwa,...
Gwamnatin jamhuriyar demokradiyyar congo ta ware kudi da sun kai dalar Amurka miliyan 5 akan duk wanda ya kamo mata shugabannin kungiyar ‘yan tawaye ta M 23 da su ka hada Corneelle Nangaa, Sultani Makenga da kuma Betrand Bisimwa. Sai dai duk da kudade masu tsokar da DRC din ta sanya akan shugabannin kungiyar su...
Abin haka yake, akwai kasashe sama da 190 a duniyarmu, idan kowace kasa na bin manufar ba kanta fifiko, to nuna fin karfi zai zama a ko ina a duniyarmu, kuma kasashe masu karamin karfi su ne za su fi fuskantar matsalar. Amma abin farin ciki shi ne, har yanzu akasarin kasashen duniyarmu na rungumar...
Kungiyar da ke sa ido kan kare hakkin bil adama ta Syria ta bayar da rahoton cewa, adadin fararen hula da aka yi kisan kiyashin na baya-bayan nan daga tsiraru ‘yan Alawite ya kai mutane 1,018 tun daga ranar alhamis zuwa wannan Lahadi. Kungiyar sa ido ta ce jami’an tsaron sabuwar gwamnatin Syria da kuma...
Wasu ’yan bindiga sun harbe shugaban ƙungiyar makiyaya Fulani ta Miyetti Allah reshen Jihar Kwara, Alhaji Idris Abubakar Sakaina. Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10 na daren ranar Asabar yayin da maharan suka biyo sawunsa suka harbe shi a ƙofar gidansa da ke yankin Oke Ose na birnin Ilorin. Malaman Tsangaya Sun Bai...
Ƙungiyar Malaman Tsangaya a Jihar Gombe ta karrama Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya lambar yabo ta ‘Khadimul Qur’an’ a matsayin girmamawa ga goyon bayansa maras misaltuwa ga ilimin Alƙur’ani da kuma matakan da ya ɗauka wajen kyautata tsarin Almajiranci. Ƙungiyar Malaman Tsangaya ta miƙa wannan girmamawa ga Gwamnan yayin wani taron buɗa-baki na musamman da aka...
Ƙungiyar Malaman Tsangaya a Jihar Gombe ta naɗa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya sarautar ‘Khadimul Qur’an’ a matsayin girmamawa ga goyon bayansa maras misaltuwa ga ilimin Alƙur’ani da kuma matakan da ya ɗauka wajen kyautata tsarin Almajiranci. Ƙungiyar Malaman Tsangaya ta miƙa wannan girmamawa ga Gwamnan yayin wani taron buɗa-baki na musamman da aka shirya musu...
Minnaro kafin mutuwarshi shi ne babban likitan kungiyar ta Barcelona, kungiyar ta fitar da sanarwar mutuwarshi ana dab da fara wasan, hakan ne ya sa aka dakatar da wasan domin nuna girmamawa gareshi da kuma jajantawa yan uwa da abokan arziki. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun...
A karon farko alkaluman ta’addaci a yankin Sahel da ke nahiyar Afirka ya zarce na jimillar sauran sassan duniya, a cewar rahoton cibiyar GTI mai bincike kan ta’addanci a matakin duniya. Rahoton ya nuna yawan kashe-kashe masu alaka da ta’addanci a Sahel, “ya zarce rabin jimillar adadin a duniya.” Kotu ta saki tsohon shugaban Koriya...