2025-03-19@06:59:33 GMT
إجمالي نتائج البحث: 471
«Gidauniyar Dangote»:
Hamas ta tabbatar cewa “Shawarar da Netanyahu ya yanke na dakatar da shigar da kayan agajin da jin kai na kasashen duniya zuwa zirin Gaza, hakan na a matsayin laifin yaki da kuma keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta da musayar fursunoni.” Kungiyar ta yi kira ga masu shiga tsakani da kasashen duniya da su matsa...
Rahotanni da suke fitowa daga Nijar sun bayyana cewa; Wata kungiyar mai alaka da al-ka’ida ta dauki alhakin kashe sojojin kasar 11 a kan iyaka da Aljeriya. A ranar Juma’ar da ta gabata ne dai lamarin ya faru,kuma a jiya Asabar ne aka yi jana’izarsu a garin Agadez, kamar yadda wata majiyar watsa labara ta...
Kungiyar Hamas ta yi kira ga masu shiga tsakani na kasa da kasa da su yi matsin lamba akan ‘yan mamaya su dakatar da azabatar da fiye da mutane miliyan daya da suke yi ta hanyar hana shigar da kayan agaji. Kungiyar ta Hamas wacce ta fitar da sanarwa a yau Lahadi ta ce, matakin...
Hanyar da ƙungiyar mayakan Hizbulla ta Lebanon ke samun kuɗaɗenta na sake fuskantar sabbin nazari, bayan wani harin sama da Israi’la ta kai a ƙarshen shekarar da ta gabata kan wata ƙungiyar hada-hadar kuɗi da ke da alaƙa da ƙungiyar. Ƙungiyar Hizbulla ita ce runduna mafi karfi a Lebanon, kuma jam’iyyar siyasa ce na musulmai...
Salah ya kasance danwasa na farko a gasar Premier da ya ci ya kuma bayar aka ci a wasanni daban-daban har goma a kaka daya. Sannan shi ne danwasa na farko da ya yi haka a daya daga cikin manyan gasar Turai biyar tun bayan Lionel Messi da ya yi wannan bajinta a kakar 2014-15,...
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi watsi da shawarar da Isra’ila ta gabatar na tsawaita matakin farko na yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza, inda ta yi kira ga kasashen duniya da su matsa wa gwamnatin mamayar lamba don ci gaba da mataki na biyu na yarjejeniyar kamar yadda aka tsara tun farko. Yau...
Shugaban kungiyar Ansarallah ta kasar Yemen Sayyed Abdul-Malik Al-Houthi, ya bayyana cewa Isra’ila na fakewa da goyan bayan Amurka tana keta yarjeejniyar tsagaita wuta a Gaza. Al-Houthi ya bayyana cewar: Kin janyewar makiya daga yankin Rafah, ya zamanto karara karya yarjejeniyar da aka kulla tsakanin Masar da makiya yahudawan sahyoniya. » Ya kara da cewa:...
Babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada kokarin sa kaimi ga ciyar da shirin kasar Sin mai kwanciyar zuwa matsayi mai girma. Xi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jagorantar taron nazari na ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS a jiya Juma’a. Inda ya yi kira da...
Kasashen Iran da Hadaddiyar Daular Larabawa sun gudanar da taron kwamitin Siyasa da al-adun na kasashen biyu a karon farko a birnin Abu Dhabi wanda ya kara tabbatar da irin ci gaban da suke samu a dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa kyautata dangantaka tsakanin...
Shugaban kungiyar Ansarullah Sayyid Abdulmalik Badruddeen Huthi ya bayyana cewa kasar Yemen a shirye take ta sake shiga yaki idan yarjeniyar tsagaita wuta tsakanin bangarorin biyu ta wargaje. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Sayyid Huthi yana fadar haka a wani jawabin da ya gabatar ta hotunan bidiyo a jiya 28 ga...
Hukumar abinci ta duniya ( FAO) ta sanar da cewa bisa la’akari da yadda adadin mutanen Afirka yake karuwa da kaso 2.3% a kowace shekara, hakan yana nufin cewa amfani da alkama zai karu. Bugu da kari hukumar abincin ta duniya ta ce da akwai wasu dalilan da za su sa Rashan ta kara yawan...
1.1 Abinci sahur yana da albarka; yin sahur albarka ne, haka ma abincin sahur abinci ne mai albarka. Ana karɓo hadisi daga Miƙdãm ɗan Ma’adikarib Allah ya ƙara yarda a gare shi, daga Annabi (S.A.W) ya ce: “Ina horonku da cin abincin sahur, domin abinci ne mai albarka” Nasã’i (Almujtabã 4/149 da Sunanul Kubrã 2/115)...
Kazalika, wannan kimiyya abar maraba ce ga masu kiwon Shanu, musamman ga wadanda ke bukatar fadada samar da ingantacciya kuma wadatacciyar Madara a guraren kiwonsu. Kirkirar kimiyyar, ta zo kan gaba duba da kokarin niyyar da Ma’aikatar Bunkasa Kiwon Dabbobi ta sanya a gaba, ta zamanantar da kiwon dabbobi da kuma habaka samar da wadatacciyar...
Hukumar bada lamuni ta Duniya IMF da kuma bankin duniya, manya-manyan cibiyoyin kudade a duniya sun ce ba zasu bada kudade don sake gina kasar Lebanon ba, sai sun cika wasu sharudda zuwa wani lokaci. Kuma sune samar da huldar jakadanci da HKI da kuma kwance damarar kungiyar Hizbullah. Jaridar Al-Akhbar ta kasar Lebanon ta...

Kungiyar Kare Hakkin Bil’adama ta ‘Euro-Med Monitor’ Ta Ce Ta Sami Shaidu Wadanda Suka Tabbatar Da Cewa HKI Tana Azabtar Da Fulasdinwa
Wata kungiyar kare hakkin bil’adama mai zaman kanta wacce take da cibiya a birnin Geneva na kasar Swizlanta ta bada sanarwan cewa ta sami cikekken shaidu wadanda suke tabbatar da cewa gwamnatin HKI tana azabtar da falasdinawa wadanda take tsare da su. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kungiyar tana bada wannan...
Shadidan Hizbullah kimabi 130 ne aka yi jana’izarsu a yau jumma’a a kudancin kasar Lebanon. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran tanakalto kungiyar Hizbullah na fadar haka, ya kuma kara da cewa kungiyar ta gabatar da shihidar da dama saboda kare kasarsu, saboda kare kasar Lebanon daga mamayar HKI. Labarin ya kara da cewa...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
“PDP jam’iyyar siyasa ce, kuma muddin kuka ci gaba da kai mata hari, ba za ku samu ci gaba ba. Ba za ku iya daukar nauyin ‘yan baranda na siyasa da farfaganda don lalata mana kima ba don kawai burge Shugaba Bola Tinubu saboda ajandar ku ta 2027. “Ba wani dan Arewa mai hakali da...
Cibiyar Bunƙasa Ayyukan Bincike za ta gudanar da gangami domin nazarin dokokin da suka shafi zamantakewar Musulmi a jihohin da ta ke aiki, domin inganta haƙƙoƙin mata da ƙananan yara. Shugaban tawagar cibiyar, Dokts Taofik Abubakar daga Jami’ar Bayero Kano ne, ya bayyana hakan yayin wata ziyarar girmamawa da suka kai wa Mai Martaba Sarkin...
Rundunar sojin Isra’ila ta amince da “cikakkiyar gazawarta” dangane da harin da kungiyar Hamas ta kai a kudancin kasar a ranar 7 ga watan Oktoba, 2023, wanda ya haifar da yaki a zirin Gaza, bisa sakamakon wani binciken da aka gudanar. A binciken da sojojin Isra’ila suka yi na cikin gida kan abubuwan da suka...
A ranar Litinin ne Jam’iyyar NNPP ɓangaren Kwankwasiyya a Kano, ta fitar da sanarwar dakatar da jiga-jigan ’yan siyasarta huɗu. An dakatar da Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila, da sauran ’yan majalisar wakilai uku, da suka haɗa da Aliyu Sani Madakin Gini da Kabiru Alhassan Rurum da kuma Abdullahi Sani Rogo. Sai dai ba kowa ne...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Al’ummar Musulmi na yin azumi ne bisa dalilan addini kamar yadda Allah Ya yi umarni don samun lada. Sai dai daga baya binciken masana kimiyya ya gano cewa bayan lada da ake samu daga yin azumi, akwai wasu alfanu da mai azumi ke samu ga lafiyar jikin shi...
An bude cibiyar tattarawa da yada labarai game da manyan taruka biyu na kasar Sin na shekara-shekara, a otel na Media Center dake birnin Beijing a jiya Alhamis. Za a kaddamar da taro karo na 3 na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin ta 14 ne a ranar 5 ga watan Maris, yayin da za a...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ya bayyana a yau ranar 27 ga wannan wata cewa, kasar Sin za ta ci gaba da maida batun samun bunkasuwa a matsayin batu mafi muhimmanci a cikin ajendar kasa da kasa, da bin tunanin raya al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil Adama, da zama babbar...

Bankin Raya Afirka ( AFDB) Ya Bayyana Kasashen Da Tattalin Arzikinsu Yake Bunkasa Da Sauri A Cikin Nahiyar
Bankin Raya Afirka ya sanar da wasu kasashe 10 da ya ce, su ne tattalin arzikinsu yake bunkasa da sauri a cikin nahiyar, tare da yin hashashen cewa gabashin Afirka zai zama sama da sauran yankunan nahiyar a cigaba. Ana hasashen cewa a cikin rabin kasashen nahiyar za a sami habakar jumillar kudaden shiga (...
Helikwaftan farko da aka haɗa a Najeriya ya kusa kammaluwa, kuma shirye-shiryen gwajin tashinsa sun yi nisa. Hukumar NASENI, mai kula da binciken inganta aikin injiniya da kimiyya da ƙere-ƙere ce ta bayyana haka. Ta sanar da wannan nasara ce a yayin wani taron kwararru da ta gudanar a Kaduna ranar Laraba. Manajan Ayyuka a...
Gidauniyar Sarki Salman ta Saudi Arabiya ta bayar da tallafin kayan abinci ga marasa ƙarfi 2,450 a Jihar Kebbi ta hannun hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA). An gudanar da rabon ne a Birnin Kebbi, inda aka raba buhuhunan shinkafa da wake mai nauyin kilo 25, garin masara kilo 2, da man gyada....
Shugaban Hafsan Sojan Sama, Air Marshal Hasan Abubakar ya zama Shugaban Kungiyar Sojojin Sama na Afrika-AAAF. Da yake jawabi a wajen taron shugabannin sojojin saman Afrika da aka gudanar a kasar Zambiya, Air Marshal Hasan Abubakar, ya jadadda bukatar samar da hanyoyin warware kalubalen tsaro da kasashen Afirka ke fuskanta. A cikin wata...
Isra’ila ta saki fursunonin Falasdinawa da dama a daidai lokacin da kungiyar Hamas ta mika gawarwakin ‘yan Isra’ila hudu ga kungiyar agaji ta Red Cross. Fursunonin sun isa birnin Ramallah da ke gabar yammacin kogin Jordan ne a kan motocin kungiyar agaji ta Red Cross bayan sun tashi daga gidan yarin Ofer da ke yankin...
Ukraine ta amince da wata yarjejeniya da Amurka kan haƙar ma’adinai da cinikayyar albarkatun ƙasa. Ana sa ran sanar da yarjejeniyar a hukumance a yau Laraba, inda za a ba wa kamfanonin Amurka dama su shiga harkar haƙar ma’adinai a Ukraine, ciki har da man fetur da iskar gas. Dangote ya rage farashin man fetur...
Babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Na’im Kasim ya gana da ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Arigchi da kuma shugaban majalisar dokokin kasar Iran Muhammad Bakir Qalibof a birnin Beirut babban birnin kasar Lebanon. Tashar talabijan ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta bayyana cewa Jami’an gwomnatin 2 sun je kasar Lebanon ne don halattan taron...
Kungiyar Hamas wacce take iko da Zirin Gaza ta bada sanarwan cewa an kawo karshen takaddama da HKI dangane da jinkirin da tayi wajen sakin fursinonin Falasdinawa 620 a ranar Asabar da ta gabata bayan da ta saki fursinoni yahudawa har 6. Tashar talabijin ta Prersstv a nan Tehran ta nakalto kakakin kungiyar Hazem Qassem...
A ranar 25 ga wata ne zaunannen wakilin kasar Sin a majalisar dinkin duniya Fu Cong, ya bayyana a taron kwamitin sulhu na MDD game da batun Isra’ila da Falasdinu cewa, tilas ne a aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a zirin Gaza baki dayanta, don tabbatar da tsagaita wuta mai dorewa. Ya kuma yi...
Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da sama da Naira Biliyan daya da miliyan dari biyar domin biyan diyya ga wadanda aikin gina tituna a cikin gari ya shafa. Kwamishinan yada labarai da matasa da wasanni da al’adu na jiha Alhaji Sagir Musa Ahmed ya bayyana hakan ga manema labarai bayan taron majalisar zartarwa ta jiha...
Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da sama da Naira Biliyan Biyar domin biyan diyya ga wadanda aikin gina tituna a cikin gari ya shafa. Kwamishinan yada labarai da matasa da wasanni da al’adu na jiha Alhaji Sagir Musa Ahmed ya bayyana hakan ga manema labarai bayan taron majalisar zartarwa ta jiha da aka gudanar a...
An cimma matsaya tsakanin Isra’ila da Hamas kan sakin fursunomin Falasdianwan nan 206 da Isra’ila ta jinkira, bayan da Hamas ta saki ‘yan Isra’ila shida. An dai tsara sakin fursunonin a ranar Asabar data gabata, saidai Isra’ila ta jinkirta sakin falasdinawan bisa abinda ta kira rashin gamsuwa da cin wulakanta ‘yan kasarta gabanin sakin da...

Amurka : Kungiyar DAWN Ta Bukaci ICC Ta Binciki Biden Kan Laifin Hada Kai Da Isra’ila A Laifukan Gaza
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta DAWN mai hedkwata a birnin Washington ta yi kira ga kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ICC da ta binciki rawar da tsohon shugaban Amurka Joe Biden da wasu jami’an Amurka suka taka wajen taimakawa Isra’ila ta aikata laifukan yaki a Gaza. A bukatar da aka mika wa...
Kungiyar Hamas ta yi Allah wadai da matakin da Isra’ila ta dauka na sanya takunkumin hana masu ibada shiga masallacin Al-Aqsa a cikin watan Ramadan. A cikin wata sanarwa da ta fitar, Hamas ta yi ishara da umarnin da ‘yan sandan Isra’ila suka bayar na ba wa masu ibada 10,000 kawai damar gudanar da sallar...
An naɗa wasu dattawan Afirka da suka yi mulki a kasashen yankin a matsayin masu shiga tsakani domin warware takaddamar da ta barke a tsakanin ’yan tawayen M23 da gwamnatin Dimokuraɗiyyar Congo. Kungiyoyin raya kasashen gabashi (EAC) da kudancin nahiyar Afirka (SADC) ne suka naɗa tsoffin shugabannin Habasha da Kenya da Nijeriya domin sanya idanu...
Ministar harkokin wajen Madagascar Rasata Rafaravavitafika ta bayyana a Tananarive, hedkwatar kasar jiya Litinin cewa, ana godiya ga Sin da ta dade take tura tawagogin likitanci zuwa kasar cikin shekaru 50 da suka gabata, don ba da tallafin jinya na zamani a yankuna masu nisa na Madagascar, da ceton rayuka na miliyoyin mutane dake wuraren....
An tabbatar da mutuwar mutum 10 a sakamakon wani haɗari da ya auku a babbar hanyar Damaturu zuwa Maiduguri a Jihar Yobe. Haɗarin wanda ya jikkata mutum uku ya auku ne shingen binciken ababen hawa da jami’an tsaro suka kafa a daidai garin Warsala. Babu hannun Naira Marley a mutuwar Mohbad — Kotu Tattalin arzikin...
Wani dan kwallon Najeriya mai suna Abubakar Lawal daga Jihar Sakkwato ya rasu bayan fadowa daga bane a kasar Uganda, inda yake taka leda. Rahotanni sun bayyana cewa Abubakar Lawal mai shekaru 29 ya gamu da ajalinsa ne bayan ya fado daga hawa na uku na wanin babban kantin sayar da kayayyaki a Kampala, babban...
Mutanen unguwa sun kama wani magidanci mai shekara 45 kan zargin sa da lalata wani yaro ɗan makarantar firamare ta hanyar luwadi a yankin Zariya ta Jihar Kaduna. Al’ummar yankin sun ce dama ana zargin mutumin da yi wa yara maza fyade, don haka suke ta bibiyar motsinsa, kuma yaron ya faɗa da bakinsa cewa...
’Yan sanda sun cika hannu da wani magidanci bayan da ya sari matarsa da adda a kai, ta ce ga garinku nan. ’Yan sanda sun kama magidancin ne bayan samun rahoton aika-aikan da ya yi wa mai dakin tasa a sakamakon takaddamar da suka samu a tsakaninsu. Lamarin ya faru ne a sabuwar unguwar Upper...
Rundinar kare juyin juya halin musulinci ta Iran, ta bayyana bikin jana’izar sakataren kungiyar Hezbollah ta Lebanon mai rasuwa Sayyed Hassan Nasrallah da kuma Sayyed Safiedinne da aka gudanar a matsayin wani babban sako na ‘yan gwagwarmaya ga duniya baki daya. Wannan babban taron da akayi a Beirut abun tarihi ne ga duniyar musulmi, ya...
Kasashen nan guda uku mambobin kungiyar kawancen Sahel (AES) da suka balle daga kungiyar ECOWAS, sun kaddamar da tutarsu ta bai daya. An kadaddamar da tutar ne a yayin haduwar ministocin harkokin wajen kasashen jiya Asabar a Bamako babban birnin kasar Mali mai rike da shugabancin kungiyar na farko. Firaministan Mali, Janar Abdoulaye Maïga ya...
Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya bukaci wadanda suka ci gajiyar shirin bayar da tallafi a mazabun jihar da su yi amfani da damar da suka samu domin dogaro da kai. Ya bayyana hakan ne a wajen kaddamar da shirin da majalisar da ke wakiltar mazabar Kaugama ya yi. Malam Umar Namadi wanda...
Kungiyar Hamas ta bada sanarwan dakatar da tattaunawa da HKI har zuwa lokacin da ta saki fursinoni Falasdinawa wadanda yakamata ta sakesu bayan da Hamas ta saki yahudawa 6 a karo na 7 na musayar fursinoni. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto daya daga cikin shuwagabannin kungiyar Mahmoud Mardawi yana fadar haka...
Kungiyar Tarayyar Makiyaya ta CORET ta ce zata tallafawa yara makiyaya 1,600 a makarantun makiyaya guda shida a Jihohin Kaduna da Jigawa a wani yunƙuri na rage ƙarancin abinci da rashin ingantaccen abinci. Sakataren Janar na CORET, Mohammed Bello Tukur ne ya bayyana hakan a lokacin ƙaddamar da shirin ciyar da ɗalibai na...