2025-04-12@06:36:11 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2195
«yan TikTok»:
Ta kara da cewa, “Ta hanyar hada tsarin horaswa na ayyukan masana’antu a cikin tsarinmu na TVET, muna rage gibin rashin kwarewar da bude kofa ga sana’o’i masu kyau a fannin fasahar sadarwa na zamani na Kenya,” (Mai fassara: Mohammed Yahaya) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun...
Rundunar ’yan sandan Jihar Yobe ta samu gagarumar nasara a ƙoƙarinta na yaƙi da miyagun laifuka, inda ta cafke wasu fitattun mutane biyu da ake zargi da garkuwa da mutane. Waɗanda aka kama sun haɗa da: Babaro Baushe mai kimanin shekara 40 da Umaru Dau’a, mai kimanin shekara 25 da suka fito daga ƙauyen Askuwari...
Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya jagoranci wata tawaga zuwa Jihar Edo domin binciko gaskiyar abin da ya faru game da kisan mafarauta ’yan asalin jihar a ƙauyen Uromi. Gwamna Abba Kabir Yusuf ne, ya umarci a kafa wannan tawaga, wacce ta ƙunshi manyan shugabanni irin su Sarkin Rano, Kwamishinonin ma’aikatu da...
Shugaban na kasar Sin ya kuma yi fatan alheri ga kasashe da jama’ar yankin na Latin Amurka da Caribbean wajen samun manyan nasarori a fannin ci gaba, da farfado da tattalin arziki, ta yadda za su ba da gagarumar gudummawa ga hadin kai da kuma hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa a duniya....
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka Tommy Bruce a cikin wata sanarwa da ya fitar ya bayyana cewa: Ministocin harkokin wajen Amurka da na Saudiyya sun tattauna kan yunkurin diflomasiyya a Gaza na sakin mutanen da aka yi garkuwa da su da kuma samar da tsagaita bude wuta mai dorewa a Gaza inda Hamas ta samu...
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakchi ya tattauna ta wayar tarho da takwaransa na Masar Badr Abdelatty, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi yankin. Manyan jami’an diflomasiyyar Iran da Masar sun yi magana ta wayar tarho da yammacin ranar Laraba, a cewar shafin Telegram na kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran. Araqchi ya jaddada muhimmancin...
Guguwar ruwan sama ya lalata gidaje da dama a ƙaramar hukumar Shanga ta Jihar Kebbi. Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris ya jajanta wa al’ummar Garin Kestu da ke unguwar Atuwo a Ƙaramar hukumar Shanga, ya kuma buƙaci iyalan waɗanda abin ya shafa da su ɗauki lamarin a matsayin wata ƙaddara. Yadda Tinubu ya taimaka wa...
Jigo a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya bayyana yadda Shugaba Bola Tinubu, ya taimaki ’yarsa ta samu aiki a Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Ƙasa (NUPRC). Galadima, ya bayyana haka ne yayin wani shiri a gidan talabijin na AIT. Matatar Ɗangote ta rage farashin fetur zuwa N865 Yadda masu safarar ɗan Adam ke...
Jigo a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya bayyana yadda Shugaba Bola Tinubu, ya taimaki ’yarsa ta samu aiki a Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Ƙasa (NUPRC). Galadima, ya bayyana haka ne yayin wani shiri a gidan talabijin na AIT. Matatar Ɗangote ta rage farashin fetur zuwa N865 Yadda masu safarar ɗan Adam ke...
Ya ce a siyasa akwai nau’ukan mutane uku – masu gaskiya, maƙaryata, da masu son tada zaune tsaye. Ya ce su a matsayinsu na ‘ya’yan jam’iyyar APC na gaskiya, suna goyon bayan Tinubu da Shettima, kuma idan akwai kura-kurai, suna ganin ya kamata a gyara ne, ba a lalata komai ba. Dangane da raɗe-raɗin cewa...
Al’ummomin Jihar Kastina sun shiga sabon tashin hankali bayan da ’yan bindiga suka kai wasu munanan hare-hare a wasu yankuna biyu a Jihar Katsina a ƙarshen makon jiya, inda suka kashe mutane shida tare da yin garkuwa da wasu 59. A daren Lahadi, kusan ƙarfe 10:30, ’yan bindiga ɗauke da makamai suka kai farmaki ƙauyen...
A cewar mai magana da yawun Ma’aikatar Cikin Gida ta Amurka, Tammy Bruce, akwai damuwa kan taimakon da ke iya faɗa wa hannun ƙungiyoyin Taliban da Houthi, waɗanda ke iko da mafi yawan yankunan waɗannan ƙasashe. A baya-bayan nan, Hukumar Yaƙi da Yunwa ta Duniya (WFP) ta bayyana cewa katse tallafin Amurka tamkar “hukuncin kisa...
Gwamnatin Najeriya ta nuna damuwarta kan yadda masu safarar mutane ke ƙara amfani da kafafen sadarwa na zamani wajen yaudarar mutane da kuma yi musu cin zarafi, inda ta bayyana hakan a matsayin barazana wadda ba ta da iyaka kuma mai saurin yaɗuwa wadda ke buƙatar ɗaukar mataki cikin gaggawa. Da yake jawabi a taron...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Irin alaƙar da ke tsakanin wasu abokai na da matuƙar kusanci da kyau, ta yadda a wasu lokutan ma ba a iya banbance dangantakar tsakaninsu ta ’yan uwan na jini ko kuma abota. Irin wannan dangantaka ya kamata ne a ce ana samun ta a tsakanin ’yan uwa...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa Jagoran juyin juya halin Musulunci na kasar Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ba shi da wata adawa da Amurkawa masu zuba jari a kasar. “Muna maraba da masu zuba jari.” amma ba tare da tauye mutunci ko tsaron kasa ba. Har ila yau kalaman nasa sun sake tabbatar...
Gwamnatin Washington ta sanar da kakabawa Iran sabbin takunkumai kan shirinta na nukiliya an zaman lafiya, a matakin da Amurka ke ganin shi ne kawai hanyar matsin lamba kan Iran domin ta mika wuya game da shirint ana nukiliya. Takunkumin, wanda ma’aikatar baitul malin Amurka ta sanar a jiya Laraba, ya shafi hukumomi biyar da...
Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron, ya ce kasarsa na shirin amincewa da yankin Falasdinawa a matsayin kasa nan da watanni masu zuwa. Ya ce hakan na iya faruwa a farkon watan Yuni nan wannan shekarar a taron Majalisar Dinkin Duniya da za a gudanar a New York. kawo yanzu, Kasashe 147 ne suka amince da...
Shugaban Amurka Donald Trump ya dakatar da haraje-harajen da ya lafta kan kayayyakin da ke shiga kasar daga kasashen duniya, sai dai ya kara harajin da kashi 125 ga kasar China. A wani bayani da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Shugaba Trump ya ce za a rage haraje-harajen zuwa kashi 10%, sai dai...
Kungiyar ci gaban kasashen yammacin Afirka, ECOWAS ta nuna damuwa kan takun-tsakar da ya kunno kai tsakanin kasar Mali da makwafciyarta Aljeriya, lamarin da ya kai ga kasashen biyu janye jakadu a tsakaninsu. A cikin wata sanarwa da ta fitar, Ecowas ta ce “Tana bibiyar abin da ke faruwa wanda ya shafi dangantakar da ke...
Manchester City na nace kan buƙatar ɗanwasan tsakiya na Newcastle da Brazil Bruno Guimaraes, mai shekara 27, yayin da take shirin rabuwa da ɗanwasanta na Belgium Kevin de Bruyne, mai shekara 33. (UOL esporte – in Portuguese) Chelsea a shirye take ta biya fam miliyan 102 kan ɗanwasan Real Madrid da Brazil Rodrygo, mai shekara 24. (Fichajes...
Wannan rikicin haraji ya faro ne tun shekarar 2018, lokacin da Trump ya fara ƙaƙaaba wa China da wasu ƙasashe haraji mai tsanani kan kayayyakin da ake shiga da su Amurka, a wani yunƙuri na kare masana’antu da ayyukan yi a cikin gida. Sai dai masana tattalin arziƙi sun ce wannan mataki zai iya kawo...
Buhari ya gode wa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu bisa gyaran da aka yi masa a gidansa na Kaduna. Ya gode wa gwamnonin APC da suka kai masa ziyara domin taya shi murnar Sallah, inda ya ce wasu daga cikinsu ya yi aiki tare da su, yayin da wasu kuwa sabbi ne. Shugaban gwamnonin kuma Gwamnan...
Runduna ta 8 ta sojojin Najeriya ta fara gasar wasanni ta kasa da ake gudanarwa duk shekara a jihar Sokoto da nufin karfafa sojojin Najeriya don shiryawa tsaron kasa. Babban Jami’in Kwamandan runduna ta takwas Manjo Janar Ibikunle Ajose ya ce gasar tana nuni ne kai tsaye ga hafsan hafsoshin sojin kasar na ganin...
Lauyan kare hakkin bil’adama Femi Falana SAN ya yabawa jihar Kano bisa yadda take tafiyar da harkokin shari’a. Falana ya bayyana hakan ne a yayin wani taron karawa juna sani ga masu gabatar da kara kan ingancin gudanar da shari’ar laifuka da Kurawa Hussein And Associates tare da hadin giwar Ma’aikatar Shari’a ta Kano...
Rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi, ta tabbatar da sace wani dalibi dan aji 4 na Jami’ar Tarayya ta Birnin Kebbi, mai suna Augustine Madubiya, mai shekaru 23 da haihuwa, wanda ke Sashen Tattalin Arziki zuwa inda ba a san inda aka nufa ba. Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Nafiu Abubakar, ya shaida wa...
Buhari ya gode wa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu bisa gyaran da aka yi masa a gidansa na Kaduna. Ya gode wa gwamnonin APC da suka kai masa ziyara domin taya shi murnar Sallah, inda ya ce wasu daga cikinsu ya yi aiki tare da su, yayin da wasu kuwa sabbi ne. Shugaban gwamnonin kuma Gwamnan...
Ya jinjina wa haɗin kai tsakanin jami’an tsaro da al’umma, yana mai cewa hakan ya taka muhimmiyar rawa wajen nasarar aikin. Gwamnati ta yaba da ƙwazon jami’an da suka halarci aikin kuma ta sha alwashin ci gaba da yaƙi da ‘yan ta’adda a faɗin jihar. “Za mu ci gaba da fatattakar waɗanda ke barazana ga...

Sin Ta Kara Wasu Kamfanonin Amurka 12 Cikin Jerin Wadanda Ta Dakatar Da Fitar Musu Da Wasu Kayayyaki Daga Kasar Sin
Bisa umarnin haramcin, za a dakatar da duk wasu huldodin fitar da hajoji daga kasar Sin zuwa wadannan kamfanoni nan take. Kazalika, a cewar ma’aikatar cinikayyar ta Sin, idan akwai wata bukata ta wajibi, dole ne sassan da za su gudanar da wata hulda mai alaka da hakan su tabbatar sun nemi izni. Ban...
Al’ummar Karamar Hukumar Maigatari sun yi kira ga gwamnatin jihar Jigawa da ta taimaka wajen gina hanyoyin da za su hada garuruwansu. Wani mazaunin yankin, Malam Ali A. Bulama Turbus, wanda ya wakilci al’ummomin yayin da yake magana da Rediyon Najeriya a Maigatari, ya jaddada muhimmancin aikin gina hanyar. Ya bayyana cewa samar da hanya...
Wasu ’yan bindiga sun nemi a ba su Naira miliyan 100 kafin su sako wani fasto da suka yi garkuwa da shi a Jihar Kaduna. Faston, mai suna Samson Ndah Ali, mai shekaru 30, yana aiki da cocin Evangelical Church Winning All (ECWA) da ke Mararaba Aboro, a Ƙaramar Hukumar Sanga. Mutanen da suka saba...
Dokar bunkasa ci gaban Afirka da samar da dama ga yankin (AGOA), wacce ta bai wa kasashen yankin damar fitar da kayayyaki zuwa Amurka ba tare da haraji ba, ta shiga gararamba bisa yadda karin harajin zai kassara masana’antu kamar su masaku, da na karafa, da kuma noma. Nijeriya da Afirka ta Kudu da...
Assalamu alaikum masu sauraro barakammu da war haka, sharhin bayan labarummu zai yi magana dangane da ‘Siyasar Amurka ta fara yakin kudaden fito tsakaninta da China da kasashen Turai da sauransu. Wanda ni tahir amin zan karanta. ///.. A ranar laraba 2 ga watan Afrilun da muke ciki ne shugaban kasar Amurka Donal Trump ya...
Rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara ta tabbatar da wani mummunan hari da ‘yan bindiga suka kai a garin Banga, da ke cikin karamar hukumar Kauran Namoda, inda aka kashe mutane biyu tare da sace wasu da dama. Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda ta jihar, DSP Yazid Abubakar, ne ya bayyana hakan cikin...
Ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, Peter Obi, ya ce talauci a Najeriya ya tsananta matuƙa har ta kai mutanen da suka saba ba shi abinci a baya yanzu suna neman taimako daga wajensa. Obi, ya bayyana hakan ne a lokacin taron kwamitin zartarwa na ƙasa na jam’iyyar LP da aka gudanar a otal...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa JMI ba zata taba jada baya a kan shirinta na makamashin Nukliya ba, kuma yayi allawadai da duka wani shiri na kaiwa cibiyoyin nukliyar kasar Hare-hare. Tashar talabijin ta Presstv ta nakalto shugaban yana fadar haka a taron raya ranar Nukliya ta karo karo na 19 a...

Tarayyar Turai Ta Yi Maraba Da Tattaunawa Tsakanin IRAN da Amurka Kan Shirinta Na Makamashin Nukliya
Kungiyar tarayyar Turai ta yi maraba da tattaunawa tsakanin Amurka da JMI dangane da shirinta na makamashin Nukliya, tare da kara jaddada cewa hanyar diblomasiyya kadai ta rage don warware wannan matsalar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa a halin yanzu dai kungiyar tarayyar ta Turai ta na ci gaba da...
Sojojin kasar Yamen sun bada sanarwan maida martani ga hare-haren jiragen yakin kasar Amurka a kan kasar na baya-bayan nan, kuma zasu ci gaba da kai hare-haren kan wadannan wurare har zuwa lokacinda za’a kawo karshen yaki a Gaza. Tashar talabijin ta presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin sojojin kasar Yemen Burgediya Janar Yahyah...
Gwamnatin kasar China ta bada sanarwan kara kodaden fito kan kayakin Amurka wadanda suke shigowa kasa har na kasha 80% sannan a shirye take ta ci gaba da yakin kasuwanci da gwamnatin shugaba Trump har zuwa karshe. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jami’an gwamnatin kasar China na fadar haka a yau...

Jiragen Yaki Da Sojojin Kasa Na HKI Sun Kashe Falasdinawa 38 A Yankin Gaza Daga Safiyar Yau Zuwa Yanzu
Jiragen yakin HKI sun kashe akalla mutane 38 a wurare daban-daban a zirin Gaza, kuma mafi yawan wadanda ta kashen yara kanana ne. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar Falasdinawa a Gaza na cewa da sassafe jiragen yakin sun kaiwa wani gidan Bene a unguwar shujaiyya na wajen garin Gaza inda...
Manajan daraktan cibiyar CGIAR Ismahane Elouafi, ta jaddada cewa idan ana son rage tsadar shigar da abinci nahiyar, wanda a yanzu ya kai kimanin dala biliyan 100 a kowacce shekara, zuba jari wajen inganta kyawun kasa da samar da ruwa da rainon ingantattun irrai masu samar da kyakkyawar yabanya, na da matukar amfani. Ta...
Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Sha’anin Tsaro, Nuhu Ribadu, ya roƙi ’yan Najeriya da su daina biyan ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane kuɗin fansa. Ribadu, ya ce biyan kuɗin fansa ba ya sa ana sakin waɗanda aka sace, kuma hakan na ƙara dagula al’amuran tsaro. Harajin China da Amurka: Mece ce...

Tattalin Arzikin Sin Na Bunkasa Yadda Ya Kamata Duk Da Kakkaba Mata Karin Harajin Kwastam Daga Amurka
A ran 7 ga watan nan da muke ciki bisa agogon gabashin kasar Amurka, kasar ta Amurka ta kara barazanar kakkaba wa Sin karin haraji na kashi 50%, kasar Sin a nata bangaren ta bayyana aniyarta ta daukar matakan da suka dace don kare muradunta. Tattalin arzikin Sin na samun bunkasa yadda ya kamata...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira da a gina al’umma mai kyakkyawar makomar bai daya tare da kasashe makwabta, da kuma kokarin bude sabon babi na ayyukan da suka shafi kasashe makwabtan kasar Sin. Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kwamitin kolin...
Sabon rikici ya sake kunno kai tsakanin ƙasashen China da Amurka, yayin da shugaba Donald Trump, ya ƙara wa kayayyakin da ake shiga da su ƙasar daga China haraji zuwa kashi 104. Wannan matakin ya shafi kayayyaki kamar wayoyin hannu, batir, kayan wasan yara da na’urorin wasanni. Za a ci gaba da sayar da ɗanyen...
Sabon rikici ya sake kunno kai tsakanin ƙasashen China da Amurka, yayin da shugaba Donald Trump, ya ƙara wa kayayyakin da ake shiga da su ƙasar daga China haraji zuwa kashi 104. Wannan matakin ya shafi kayayyaki kamar wayoyin hannu, batir, kayan wasan yara da na’urorin wasanni. Za a ci gaba da sayar da ɗanyen...
Ta kuma ce har yanzu ƙasashe sama da 70 daga sassa daban-daban na duniya sun tuntuɓi Amurka domin a yi tattaunawa kan yadda sabbin harajin ke shafar kasuwanci a duniya. Mene ne Ma’anar Wannan Haraji? Wannan haraji na nufin idan ana shiga da kaya daga China zuwa Amurka, za a ƙara musu kuɗi sosai kafin...
An yi kira ga Gwamna Mohammed Umar Bago na jihar Neja da ya sanya baki kan rikicin fili mai fadin sama da hektar saba’in da biyar da ake zargin Hakimin Tegina da ke karamar hukumar Rafi ya kwace daga hannun mamallakinsa a Pangu Gari. Babban Limamin Pangu Gari, Alhaji Umar Musa Danladi ne ya...
Rundunar Sojin Nijeriya ta ce ba a biya kuɗin fansa ba kafin a ceto tsohon shugaban NYSC, Janar Mahrazu Tsiga (mai ritaya), daga hannun ‘yan bindiga. A wata sanarwa da Birgediya Janar Tukur Gusau ya fitar, ya bayyana cewa an yi amfani da bayanan sirri da kuma dabarun soji wajen ceto Janar Tsiga. Dole Dukkanin...
Amurka za ta iya janye sojoji 10,000 daga Gabashin Turai, kamar yadda rahoton NBC News ya bayyana. A shekarar 2022, tsohon shugaban Amurka Joe Biden ya tura karin sojoji 20,000 zuwa yankin bayan Rasha ta kai hari Ukraine. A ranar Talata, NBC ta ruwaito cewa jami’ai shida daga Amurka da Turai sun tabbatar da tattaunawa...
Kantoman Ribas, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas, ya amince da naɗin sabbin kantomomi na ƙananan hukumomi 23 da ke faɗin jihar. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Ribas, Farfesa Ibibia Lucky Worika ya fitar a safiyar wannan Larabar a birnin Fatakwal. ’Yan bindiga sun kashe masunta 3 a Sakkwato Likitocin Nijeriya dubu 16...