2025-02-20@09:04:33 GMT
إجمالي نتائج البحث: 92

«gamayya»:

    Shugaban majalisar dokokin kasar Iran Muhammad Bakir Qalibof ya bayyana cewa falasdinawa masu kasa ne zasu fayyace makomar kasarsu, don haka shirin da wasu manya-manyan kasashen duniya suke dashi a kan makomar Falasdinu da Falasdinawa ba dai-dai bane kuma zamu yi yaki da shi. Tashar talabijan ta Presstv a nan Teran ta nakalto shugaban majalisar...
    Jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullah sayyid Ali Khamnei wanda ya gana da sarkin Katar  a jiya Laraba ya bayyana cewa; Siyasar Iran ta ginu ne akan kyautata alaka da kasashen makwabta, kuma tuni an cimma sabbin matakai a wannan fagen. Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya kuma fada wa sarkin na Katar Tamim Bin Hamad...
    A karshe dai, ya nanata muhimancin raya karfin kasa da kasa ta hanyar aiwatar da ayyuka masu alaka da hakan. Wang Yi ya jaddada cewa, kasar Sin tana fatan yin hadin gwiwa da sassa daban daban, domin bude sabon babin raya huldar cude-ni-in-cude-ka, tare da kafa tsarin gudanar da harkokin kasa da kasa mai inganci....
    Wani rahoto da kwamitin bincike da Gwamnatin Jihar Kano ta kafa kan zanga-zangar yunwa, ya gano cewa mutum 10 sun rasa rayukansu, yayin da wasu mutum bakwai suka samu munanan raunuka. Rahoton ya kuma bayyana cewa an yi asarar dukiya da ta kai Naira biliyan 11, sakamakon ƙone-ƙone, sace-sace, da lalata kadarorin gwamnati da na...
    Wani rahoto da kwamitin bincike da Gwamnatin Jihar Kano ta kafa kan zanga-zangar yunwa, ya gano cewa mutum 10 sun rasa rayukansu, yayin da wasu mutum bakwai suka samu munanan raunuka. Rahoton ya kuma bayyana cewa an yi asarar dukiya da ta kai Naira biliyan 11, sakamakon ƙone-ƙone, sace-sace, da lalata kadarorin gwamnati da na...
    Aƙalla mutum 11 sun shaƙi iskar ’yanci bayan kuɓuta daga hannun ƙungiyar mayaƙan Boko Haram masu iƙirarin jihadi a Jihar Borno. Waɗanda suka shaƙi iskar ’yancin na daga cikin mutanen da ƙungiyar Boko Haram ta sace a wani wurin kamun kifi a Doron Baga. Majalisar Edo ta tanadi hukuncin kisa kan masu garkuwa da mutane...
    Kakakin ma’aikatan shari’a a kasar Iran ya bayyana cewa jami’an tsaro na kasar Iran sun kama mutane biyu yan kasar Burtaniya tare da tuhumar aikin liken asiri a lardin Kerman na kasa. Kamfanin dillancin labaran (IP) na kasar Iran ya bayyana cewa mutanen biyu suna tafiye-tafiye zuwa lardunan kasar Iran suna tattara bayanai a cikin...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci A nan Iran Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya gana da shuwagabannin kungiyar Jihadul Islami na kasar Falasdinu da aka mamaye a jiya Talata. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ya bayyana cewa Ziyad Nakhalah shugaban kungiyar ne ya jagoranci tawagar kungiyar zuwa ganawa da jagoran. Labarin ya nakalto Jagoran...
    Gwamnatin tarayya ta ce ta bai wa gwamnatin jihar Jigawa tallafin kayayyakin noma na sama da naira biliyan 5 domin bunkasa noman abinci a fadin jihar.     Ministan noma da samar da abinci Sanata Abubakar Kyari ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a garin Dabi da ke karamar hukumar Ringim a...
    Kasar Sin na maraba da duk kokarin da ake yi cikin lumana don warware rikicin kasar Ukraine, ciki har da tattaunawa tsakanin Amurka da Rasha, kuma Sin na fatan dukkan bangarori da masu ruwa da tsaki za su shiga cikin shawarwarin samar da zaman lafiya in lokaci yayi. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewa: Barazanar makiya a kan kasar Iran da al’ummarta ba ta yi nasara ba Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa: Gagarumar zanga-zamga da al’ummar Iran suka gudanar a ranar 22 ga watan Bahman ta tabbatar da cewa barazanar makiya a...
    Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa; Iran tana taka rawa ta musamman wajen wanzar da kwanciyar hankali da tsaron yankin Tekun Pasha Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta hanyar mallakar mafi yawan layukan kan iyaka da tekun Pasha da kuma iko da mashigar Hormuz, ta...
    Jaridar Ma’ariv ta Isra’ila ta bayyana adadin wadanda suka jikkata a cikin sojojin mamayar Isra’ila da kuma miliyoyin yahudawan sahayoniyya da suka samu matsalar tabin hankali a lokacin yakin Gaza Jaridar “Ma’ariv” ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta bayyana a jiya litinin, adadin wadanda suka mutu a cikin jerin sojojin mamayar Isra’ila a yayin mummunan ayyukan...
    Ana fargabar cewa gobara ta yi ajalin wata uwa da ’ya’yanta biyu a yankin Onipakala da ke Ƙaramar Hukumar Ondo West a Jihar Ondo. Bayanai sun ce musibar ta auku ne da tsakar daren Lahadi yayin da jama’a ke sharar barci, lamarin da ya jefa makwabta cikin zullumi. Saudiyya ta bai wa Kano da Abuja...
    Gwamnatin Katsina ta kashe kimanin Naira biliyan 5.4 domin bai wa mata 3,610 tallafin kiwon awakai. Gwamna Dikko Umar Radda ne ya bayyana hakan a yayin ƙaddamar da shirin raba tallafin awakan a gundumar Dan-Nakolo da ke Ƙaramar Hukumar Daura ta jihar. Gwamnati ta kashe N5bn domin bai wa mata tallafin kiwon awakai a Katsina...
    Kungiyoyin Hamas, Jihad Isalami da kuma sauransu a kasar Falasdinu da aka mamaye sun bayyana yi allawadi da HKI saboda yadda suke zazabtar da fursinonin Falasdinawa a gidan yarin Ofer, kamar yadda labari ya ke isa daga ca. Tashar talabijin ta Presstv  na takalto cewa gidan yarin ofer ya na yammacin birnin Ramallah, a...
    Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana cewa kasashen Turai basa cikin tattaunawar tsagaita wuta a Ukraine. Jaridar Daily Mail ya bayyana cewa hankalin shuwagabannin kasashen turai ya tashi a lokacin da JD Vance mataimakin shugaba Trump ya fada masu cewa ba wani shugaba daga cikin shuwagabannin kasashen Turai da zasu halarci taron tsagaita wuta...
    Gwamnatin Katsina ta kashe kimanin Naira biliyan 5.4 domin bai wa mata 3,610 tallafin kiwon awakai. Gwamna Dikko Umar Radda ne ya bayyana hakan a yayin ƙaddamar da shirin raba tallafin awakan a gundumar Dan-Nakolo da ke Ƙaramar Hukumar Daura ta jihar. Ya bayyana cewa, a ƙarƙashin shirin, an raba wa mata 3,610 awakai huɗu-huɗu...
    Gwamnatin Amurka ta fara aiwatar da matakan korar ‘yan Nijeriya daga ƙasar, inda ake sa ran mutane 85 za su iso Lagos, yayin da wasu 116 ke tsare. Jakadan Amurka a Nijeriya, Richard Mills, ya bayyana haka yayin wata ziyarar ban girma da ya kai wa Ministan harkokin wajen Nijeriya, Ambasada Bianca Odumegwu-Ojukwu, a Tafawa...
    Wani matashi da aka kama kan yin gunduwa-gunduwa da budurwarsa da suka haɗu a Facebook bayan ta je ɗakinsa ya bayyana dalilinsa na aikata hakan. Matashin mai shekaru 29 da ke iƙirarin malumtar addini ya amsa a wurin ’yan sanda masu bincike cewa shi ne ya yi wa gawar budurwar tasa gunduwa-gunduwa. Ya shaida musu...
    Bishop na Cocin Katolika da ke  Kontagora, Babban Rabaran Bulus Yohanna ya gudanar da bikin aure ga ma’aurata ashirin da daya a jihar Neja. A lokacin da yake jawabi yayin bikin daurin aurea cocin St. Mark Catholic da ke Nsanji Nkoso a karamar hukumar Magama ta jihar Neja,  Bishop din ya bayyana cewa, bai kamata...
    Gwamnatin jihar Kano, KNSG, ta ce ta tanadi hanyoyin dakile mace-macen mata masu juna biyu maimakon rage yawan mace-macen.   Kwamishinan lafiya na jihar Dr Abubakar Labaran Yusuf ne ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a wajen taron hadin gwiwa na Partners Coordination Forum (PCF) da aka gudanar a Kano.   A wata...
    Kungiyoyin farar hula masu yaki da zazzabin cizon sauro, rigakafi da abinci mai gina jiki (ACOMIN), reshen jihar Taraba, ta koka kan matsalar karancin kayan gwajin cutar kanjamau a jihar.   Shugaban kungiyar na jiha, Alhaji Muhammad ​​Danburam ya bayyana haka a lokacin da ya kai ziyarar wayar da kan hukumar yaki da cutar kanjamau...
    An shiga ruɗani bayan da wasu sojoji sun lakaɗa wa wasu ’yan sanda da ke bakin aiki duka a Ƙaramar Hukumar Okpe da ke Jihar Delta. Rikicin jami’an tsaron ya samo asali ne bayan ’yan sanda sun yi kamen wasu matasa da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi. ’Yan sanda sun tsare motar matasan ne...
    Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta jaddada cewa: Al’ummar Iran ba zata taba amincewa da gudanar da duk wani zaman tattaunawa karkashin matsin lamba ba Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta mayar da martani ga yarjejeniyar tsaron kasa ta shugaban kasar Amurka, tana mai jaddada cewa: Iran ta yi watsi da duk wata tattaunawa karkashin matsin lamba,...
    Hukumar kula da ‘yan sama jannati na kasar Sin (CMSA), a yau Laraba, ta bayyana sunayen tufafin ‘yan sama jannati da motar zirga-zirga a duniyar wata na aikin binciken wata na kasar. CMSA ta ce, an sa ma tufafin na ‘yan sama jannati suna Wangyu, wanda ke nufin kallon duniyar sama, kuma ya yi daidai...
    Iran ta yi kakkausar suka kan barazanar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi na yin amfani da karfi a kan kasar, inda ta bayyana hakan a matsayin barazana da rashin da’a. A cikin wata wasika da ya aike a wannan Talata zuwa ga shugaban Majalisar Dinkin Duniya da shugaban kwamitin sulhu na dindindin jakadan...
    Kungiyar Tarayyar Afirka ta bayyana cewa: Sudan ce kasar da aka fi fama da matsalar jin kai a duniya A zaman tattaunawa da Kungiyar Tarayyar Afirka ta gudanar ta bayyana yakin basasar Sudan a matsayin “mafi girman matsalar jin kai a duniya,” inda ta yi gargadin irin mummunar illar da yake yi kan fararen hula,...
    “Wannan shi ne dalilin da ya sa Gwamna Dauda Lawal ya bayyana a cikin takardar yaƙin neman zabensa gabanin zaben 2023 cewa batun tsaro ne zai sa a gaba, inda ya yi alƙawarin aiwatar da matakan shawo kan lamarin. “A halin yanzu an shaida cewa Gwamna Lawal ya cika alƙawarin. “Gwamnatin Gwamna Dauda Lawal ta...
    A ci gaba da kokarinta na samun tagomashi a fannin tattalin arziki da ci gaban jihar ta hanyar kawo sauyi a harkar noma, gwamnatin jihar Jigawa na shirin hada gwiwa da wani kamfani da ke samar da dabino  da bayar da shawarwari a harkar noma, wanda ke da ofishi a Najeriya a kasar Saudiyya domin...
    Dan Majalisar Tarayya mai Wakiltar Zangon Kataf/Jaba daga Jihar Kaduna, Honorabul Amos Gwamna Magaji ya sauya sheka daga jam’iyyar adawa ta PDP zuwa APC mai mulki. A safiyar Talata Shugaban Majalisar, Abbas Tajuddeen ya sanar da sauya shekar, yana mai bayyana rikicin cikin gidan PDP a mastayin dalilin ficewar dan majalisar daga jam’iyyar. Dan majalisar ya ...
    Dalibai 179 za su samu shaidar Digiri Mai Daraja ta Ɗaya a yayin bikin yaye ɗalibai na Jami’ar Bayero ta Kano (BUK). Shugaban Jami’ar Bayero, Farfesa Sagir Abba, ya bayyana cewa dalibai 4,402 ne za a yi bikin yaye su a ranar farkon, inda a za a ba su shaidar kammala Digirin farko da Difloma...
    Dalibai 179 za su samu shaidar Digiri Mai Daraja ta Ɗaya a yayin bikin yaye ɗalibai na Jami’ar Bayero ta Kano (BUK). Shugaban Jami’ar Bayero, Farfesa Sagir Abba, ya bayyana cewa dalibai 4,402 ne za a yi bikin yaye su a ranar farkon, inda a za a ba su shaidar kammala Digirin farko da Difloma...
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Sirrin nasarar da Iran ta samu shine haɗin kai da kasancewar mutane a cikin kowane fagen neman ci gaba Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa juyin juya halin Iran ya samu nasarar korar azzalumai daga kasar Iran ce, kuma sirrin ire-iren nasarorin da aka samu bayan nasarar...
    Sai dai yadda gwamnatin Trump ta sanar da rufe USAID ya ba da damar tona asirinta, kuma tabbas tarihi zai tabbatar da cewa, gaskiya na hannun wadanda ke kokarin samar da ci gaba da kiyaye hadin gwiwar cin moriyar juna da ma wadanda ke kokarin tabbatar da makomar dan Adam ta bai daya.    
    Babban hafsan hafsishin sojojin Iran Manjo Janar Muhammad Bakri ya bayyana cewa sojojin Iran a shirye suke fiye da ko wani lokaci don kare JMI daga makiyanta. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ya bayyana cewa Bakiri ya bayyana haka ne a lokacinda yake tattaki na bukukuwan cika shekaru 46 da nasarar juyin juya...
    Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal Dare, ya bayyana cewa sharaɗinsa na sulhu da ’yan bindiga shi ne kawai su daina kashe-kashe su zubar da makamai sannan su miƙa wuya. A baya dai Gwamna Dare ya sha nanata cewa ba zai yi sulhu da ’yan fashin daji ba. Gwamna Sule ya naɗa Kwamishinoni 16 a Nasarawa Atiku...
    Wasu ’yan daba sun gine-ginen makaranta a yankin Okpoga da ke Karamar Hukumar Okpogwu da ke Jihar. Ɓata-garin sun ƙona gine-ginen ne a Makarantar Sakandaren Central UBE da ke Ogwu-Okpoga da kuma Makarantar Ƙaramar Sakandare s ake Obossa. Wani shaida ya bayyana wa wakilinmu cewa a makon da ya gabata ne ’yan daban suka yi...
    Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya nada Umar Farouk Ibrahim a matsayin sabon Sakataren Gwamnatin Kano. Nadin na kunshe cikin wata sanarwar da Kakakin Gwamnatin Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya wallafa a shafukansa na sada zumunta a yammacin ranar Asabar 08, ga Febarairun 2025. Dalilan Da Suka Sa Gwamnan Kano Sallamar SSG Da Wasu...
    Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya nada Umar Farouk Ibrahim a matsayin sabon Sakataren Gwamnatin Kano. Nadin na kunshe cikin wata sanarwar da Kakakin Gwamnatin Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya wallafa a shafukansa na sada zumunta a yammacin ranar Asabar 08, ga Febarairun 2025. Dalilan Da Suka Sa Gwamnan Kano Sallamar SSG Da Wasu...
    A gasar Serie A 14:03 – Joao Felix (Chelsea – AC Milan) aro   Premier League 01:00 – Adel Disasi (Chelsea – Aston Billa) aro- 00:25 – Marshall Munetsi (Reims – Wolbes) ba a fayyace kudin ba. 00:15 – Carlos Alcaraz (Flamengo – Eberton) aro- 00:00 – Nasser Djiga (Red Star Belgrade – Wolbes) ba...
     Wanda ya jagoranci sallar juma’a a yau anan birnin Tehran, Hajjatul-Islam Kazim Saddiki, ya bayyana cewa: Trump yana yin baraza da tsoratarwa da cewa zai rage karfin da Iran take da shi a fagen fasahar Nukiliya da kuma matsayin da take da shi a cikin wannan yankin na yammacin Asiya, sai dai kuma ya kamata...
    Kwamishiniyar Mata, Yara da Nakasassu ta Jihar Kano, Hajiya Amina Abdullahi, ta gargadi ma’aikatan Cibiyar Reformatory Institute ta Kiru da su guji karkatar da kayayyakin da aka ware domin gina cibiyar.   A yayin ziyarar duba aikin gyare-gyaren, kwamishina Amina ta jaddada muhimmancin yin amfani da kudaden da aka ware wajen abubuwa masu inganci a...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiya ya bayyana cewa juyin juya halin musulunci  a nan Iran ya zo ne da sakon zaman lafiya ga dukkan kasashen duniuya, don haka ne ta haramtawa kanta mallakan makaman nukliya wanda yake kissan kare dangi. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a jiya...
    Hukumar Jin Dadin Alhazai ta jihar Jigawa ta ce ta mikawa hukumar alhazai ta kasa NAHCON kudaden aikin hajjin maniyyatan jihar  na shekarar 2025 kimanin naira biliyan 4.5. Babban Daraktan hukumar Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya bayyana haka ga manema labarai a Dutse babban birnin jihar. Ya ce hukumar ta aika wa NAHCON...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa : Gabadayen Falastinu tun daga kogi har zuwa teku ta al’ummar Falasdinawa ce. Jagoran ya jaddada goyon bayan Iran ne ga gwagwarmayar Falasdinawa kan kasarsu mai dimbin tarihi, tun daga kogin Jordan zuwa tekun Bahar Rum, kamar shafin offishin jagoran ya...
    An kama wani ɗalibin firamare mai shekara 13 ɗauke da bindiga a makaranta, inda yake barazanar harbe abokan karatunsa da ita. Bayan nan ne jami’an tsaro suka yi nasarar kama shi a Makarantar Firamare ta St. Paul da ke ƙauyen Ikot Ibiok a Ƙaramar Hukumar Eket a Jihar Akwa Ibom. A safiyar Alhamis ne kakakin...
    Kasashen larabawa masu kawance da Amurka sun kasance a sahun gaba wajen mayarwa da shugaban kasar Amurkan martani, bayan da ya bayyana cewa kasarsa za ta shimfida ikonta a Gaza, bayan fitar da Falasdinawa da Gaza. Gabanin wannan sanarwar ta  Shugaba Donald Trump ya bayyana cewa ya tuntubi kasashen Jordan da Masar masu makwabtaka da...
    Gwamnatin jihar Neja ta karbi yara ashirin da daya da aka kama a kan iyakar Najeriya da jamhuriyar Nijar yayin da ake safarar su zuwa Sudan.   Mataimakin gwamnan jihar, Kwamared Yakubu Garba wanda ya bayyana haka a lokacin da yake karbar yaran a madadin gwamnatin jihar Neja a Minna, ya ce an kama yaran...
    Mataimakin shugaban kasar Iran kan al-amuran na Musamman Muhammad Javad Zareef  ya bayyana cewa tattaunawa kadai da Amurka, ba zai warware matsalolin Iran ba. Kamfanin dillancin labarum IP na kasar Iran ya nakalto Zareef ya na fadar haka a taron majalisar ministocin da aka gudanar a jiya Laraba  a nan Tehran. Kamfanin dillancin labaran IP...