2025-03-22@10:31:35 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1601
«Kiwon Lafiya»:
Rahotanni daga sansanin ‘yan hijira na Nablus a yammacin kogin Jordan sun ambaci cewa sojojin mamayar HKI sun tilasta wa iyalai 10 ficewa daga gidajensu. Sojojin na HKI suna shirin kaddamar da wani gagarumin hari na tsawon kwanaki uku a cikin sansanin “Ayn.” Dake Nabilus. A gefe daya, kafafen watsa labarun Amurka sun ambaci cewa;...
Ma’aikatar tsaron kasar Rasha ta sanar da kakkabo jiragen sama marasa matuki 57 da kasar Ukiraniya ta harba zuwa yankuna mabanbanta na kasar. A yau Laraba ne ma’aikatar tsaron kasar ta Rasha ta sanar da cewa; An harbo jiragen marasa matuki 35 da aka harba wa yankin Kursk dake yammacin Syria a jiya da dare. Sai...
Majiyar ‘yan aware ta kasar Mali ta sanar da cewa wani hari da sojojin gwamnati su ka kai a arewacin kasar ya yi sanadiyyar kashe mutane 18 a arewacin kasar Yemen, sai dai sojojin gwamnatin ta ce, ‘yan aware ta kai wa hari. Kungiyar Azbinawa ‘yan aware ta ce sojojin gwamnatin kasar sun kai hari...
Fubara ya ƙara da cewa, duk da rikicin siyasar da ake fama da shi, gwamnatinsa tana ci gaba da aiki yadda ya kamata, kuma ana biyan ma’aikata albashinsu tare da ƙaddamar da muhimman ayyuka a jihar. Ya buƙaci al’ummar jihar su ci gaba da bin doka da oda, yana mai cewa za su ci gaba...
Haka kuma, a ranar 3 ga Fabrairu, jami’an ‘yansanda sun kama wasu mutum uku da bindigogi 10 ƙirar AK-47, inda suka amsa cewa suna sayar da su ga masu aikata laifuka. Rundunar ‘yansanda ta ce za ta ci gaba da yaƙi da fasa-ƙwauri da safarar makamai da miyagun ƙwayoyi, tare da kira ga ‘yan ƙasa...
Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya buƙaci al’ummar jihar da su zauna lafiya sannan su kasance masu kiyaye doka da oda. Fubara ya yi kiran ne safiyar wannan Larabar bayan da yammacin Talatar jiya Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da shi da mataimakiyarsa da duk ’yan majalisar dokoki sannan ya ayyana dokar ta ɓaci a...
Wata gobara da ta auku safiyar wannan Larabar ta laƙume kasuwar ’yan gwan-gwan da ke unguwar Dakata a Ƙaramar Hukumar Nassarawa ta Jihar Kano. Kasuwar wadda ake kira da Kwalema tana nan a kan titin Zango, daura da gidajen man Dominion da kuma Mobil da ke makwabtaka da ofishin Hukumar WAEC. Cire Gwamna Fubara ya...
Shugaban na kurdawa a Syira Hikmat al-Hijri ya soki halayyar gwamnatin rikon kwarya ta kasar Syria, tare da nuna kin amincewa da sabon tsarin mulkin kasar da aka sanar kwanaki kadan da su ka gabata. Hikmata al-Hijri ya yi kira da gyara yadda ake tafiya a yanzu da kuma rubuta sabon tsarin mulki wanda zai...
A ci gaba da taya Falasdinawa fada da sojojin Yemen suke yi, sun kai wa sansanin jiragen sama na HKI dake saharar “Nakab” hari da makami mai linzami samfurin “Ballistic’ wanda ya fi sauti sauri. A wata sanarwa da sojojin Yemen su ka yi da marecen jiya Talata sun bayyana cewa; a karkashin taimakawa Falasdinawa...

Kungiyar Jihadul-Islami Ta Falasdinu Ta Sanar Da Shahadar Abu Hamza Kakakin Dakarunta Na Sarayal-Kudus”
A jiya Talata ne dai kungiyar ta Jihadul-Islami ta kaddamarwa da al’ummar Musulmi shahadar Naji Abu Saif, wanda ake yi wa lakbi da Abu Hamza, da ya kasance kakakin dakarun “Sarayal-Kudus” bayan da ‘yan sahayoniya su ka yi masa kisan gilla tare da iyalansa da iyalan dan’uwansa. A bayanin da ta fitar, kungiyar ta Jihadul-Islami...
Ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya (NBA) ta soki matakin da Shugaba Bola Tinubu ya ɗauka na ayyana dokar ta ɓaci da kuma cire Gwamna Similanayi Fubara na Jihar Ribas. Cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, shugaban NBA, Mazi Afam Osigwe (SAN), ya ce a ƙarƙashin Kundin Tsarin Mulki, shugaban ƙasar ba shi da ikon tsige...
Ibnu Juzai Allah Ya yi masa rahama, ya yi bayanin kushu’i a matsayin wani yanayi na zuciya wanda yake cike da tsoron Allah, da girmamawa, da ƙasƙantar da kai saboda girman Allah Ta’ala. Wannan yana ɗaya daga cikin manyan halayen da ake buƙata a cikin ibada, musamman salla, domin ya zamanto salla ta yi tasiri...
Alkaluma daga ma’aikatar masana’antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin ko MIIT, sun nuna irin ci gaba bisa daidaito da sashen masana’antun dijital na kasar Sin ya samu a shekarar 2024 da ta gabata, inda a shekarar ta bara sashen ya samu karin kudin shiga da riba. Alkaluman da MIIT ta fitar a jiya Litinin,...
Dalilin wannan doka shi ne rikice-rikicen addini tsakanin Musulmai da Kiristoci a watan Satumba 2001, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 2,000. A Jihar Borno Ma An Taɓa Sanya Dokar, Amma Ba A Jihar Baki Ɗaya Ba A shekarar 2011, Shugaba Goodluck Jonathan ya ayyana dokar ta-ɓaci a wasu ƙananan hukumomin...
A baya-bayan nan yayin hira da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, ministan kula da harkokin gona na kasar Gambiya Demba Sabally, ya bayyana goyon baya da taimakon fasaha na kasar Sin, a matsayin wadanda suka taka muhimmiyar rawa wajen samar da gagarumin ci gaba a fannin aikin gona a kasarsa a ’yan shekarun nan. Idan...
Shugaban Majalisar Dattawan Arewa (NEF), Farfesa Dahiru Ango Abdullahi Yakawada, ya yi murabus daga sarautar Magajin Rafin Zazzau. Farfesa Dahiru Ango Abdullahi ya yi murabus ne daga sarautar Magajin Rafin Zazzau saboda shekarunsa da suka ja. Hamas ta ɗora alhakin harin da Isra’ila ta kai a kan Amurka Majalisar Wakilai ta amince da ƙudirin dokar...
Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da Gwamna da mataimakinsa da daukacin ’yan Majalisar Dokokin Jihar Ribas, tare da ayyana dokar ta-baci a Jihar. Tinubu ya kuma ayyana Ete Ibas a matsayin Gwamnan Rikon Jihar Ribas, a yayin jawabinsa ga ’yan Najeriya
Jaridar Financial Times ta Burtaniya ta bayyana cewa, masu zuba jari na kasashen waje suna kara “gano kasar Sin”, kuma sun yi imanin cewa, kasar Sin za ta iya samar da “kirkire-kirkire da damammaki” masu yawa a wasu fannoni. (Safiyah Ma) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun...
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana yau Talata cewa, bisa gayyatar da gwamnatin kasar Namibiya ta yi masa, wakilin musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, kana mataimakin shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin Peng Qinghua, zai halarci bikin rantsar da shugabar kasar Netumbo Nandi-Ndaitwah a birnin Windhoek,...
A yunkurin da gwamnatin jihar Jigawa ke yi na sauya fasalin harkar noma, majalisar zartaswa ta jihar ta amince da ware sama da naira biliyan daya da miliyan dari biyar domin fara aiki da sabon Kamfanin injinan noma na jihar. Kwamishinan Yada Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ne ya...
Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ƙwace wani fili mallakar sakatariyar Jam’iyyar PDP da ke Abuja. Hakan na ƙunshe ne cikin wata wasiƙa mai ɗauke da sa hannun shugaban sashen kula da filaye na Abuja, Chijioke Nwankwoeze. Nwankwoeze ya ce an yanke hukuncin ƙwace filin ne sakamakon gazawar babbar jam’iyyar adawar na biyan kudin gini na...
Bayan shafe kwanaki 40 har yanzu waɗanda suka yi garkuwa da tsohon Shugaban Hukumar Kula da Masu Yi wa Ƙasa Hidima ta Najeriy a(NYSC), Birgediya Janar Maharazu Tsiga mai ritaya ba su sako shi ba duk da cewa an biya kuɗin fansa. Rahotanni sun nuna cewar an biya maƙudan kuɗaɗe don ganin an sako Janar...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Majiyar gwamnatin kasar Yemen ta basa sanarwan kai hare-hare har sau biyu kan kataparen jirgin ruwa mai daukar jiragen yaki na kasar Amurka dake cikin Tekun Red sea, wato USS Harry Truman. Inda suka cilla makami mai linzami guda da kuma jiragen yake wadanda ake sarrafasu daga nesa kan jirgin. Har’ila yau sojojin yamen sun...
Gwamnatin HKI ta bayyana damuwarta da jibge sojojin da gwamnatin kasar masar take yi a yankin Sinaa kusa da kan iyakar kasar da HKI. Tun bayan da gwamnatin HKI ta gama lalata makaman gwamnatin kasar Siriya bayan ta taimaka ta kawo dan Daesh kan kujerar shugabancin kasar ta Siriya, kuma ta bayyana cewa yankunan da...
HKI ta keta yarjeniyar tsagaita wuta a Gaza, a jiya inda ta kai hare-hare masu yawa, wadanda suka yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 300 ya zuwa safiyar yau. Tashar talanijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, jiragen yakin HKI sun kai hare-haren a kan yankunan zirin Gaza da dama, kuma yawan mutanen...
A ranar Juma’a, fadar Kremlin ta ce Shugaba Putin ya aike saƙo zuwa ga Trump ta hannun manzon Amurka na musamman, Steve Witkoff, yana bayyana cewa Rasha tana nazarin batun tsagaita wuta amma tana taka-tsantsan. Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya ce yana fatan wannan tattaunawa za ta kai ga samun mafita, amma ya jaddada cewa...
Tawagar Kwallon Kafa ta Super Eagles ta Nijeriya ta gayyaci sababbin ’yan kwallo takwas da za su wakilci kasar domin buga mata wasannin neman gurbin shiga Gasar Kofin Duniya na 2026. Tuni Super Eagles karkashin jagorancin sabon mai horaswa Eric Chelle, ta fitar da jadawalin ’yan wasa na farko da za su taka mata...
Tun bayan juyin mulkin da ya kifar da tsohon shugaban ƙasar, Mohammed Bazoum, Nijar na ci gaba da janye jikinta daga ƙungiyoyin yammacin duniya. A baya-bayan nan ma, tare da Mali da Burkin Faso, ƙasar ta fice daga ƙungiyar ECOWAS. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin...
Tun bayan juyin mulkin da ya kifar da tsohon shugaban ƙasar, Mohammed Bazoum, Nijar na ci gaba da janye jikinta daga ƙungiyoyin yammacin duniya. A baya-bayan nan ma, tare da Mali da Burkin Faso, ƙasar ta fice daga ƙungiyar ECOWAS. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin...
Shugaban kungiyar Ansarullah na kasar Yemen Sayyid Abdulmalik Husi ya bayyana cewa; Matukar Amurka ta ci gaba da kai wa Yemen hare-hare, to suna da hanyoyi da za su iya gasa mata aya a hannu masu yawa. Sayyid Abdulmalik al-Husi ya yi ishara da yadda dubun dubatar mutanen Yemen su ka fito a cikin birnin...
Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya bayyana cewa; Dukkanin batutuwan da Musulunci da kuma al’kur’ani maigirma suke bijiro da su, sun ginu ne akan ginshikin gaskiya da kuma adalci. Shugaban kasar ta Iran ya kara da cewa; Idan har wadannan ginshikan biyu su ka zama ana aiki da su a cikin al’umma, to za a...

Munanan Hare-hare Sojojin HKI A Gaza Da Safiyar Yau Talata Sun Yi Sanadiyyar Shahadar Fiye Da Falasdinawa 200
Rahotanni Daga Gaza sun ce adadin Falasdinawan da su ka yi shahada da safiyar yau sun haura 200 Wata sanarwar da ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza ta fitar a yau Talata ta ce; Adadin shahidan sanadiyyar sabbin hare-haren HKI sun kai 244. Sai dai har yanzu ba a kammala tantance adadin adadin shahidan ba, da...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Mallakar Muhalli na ɗaya daga cikin burin kowanne ɗan Najeriya. Sai dai wannan buri a mafi yawan lokacin baya cika musamman ga masu matsakaitan samu. Ƙananan ma’aikata da mafi ƙarancin albashin su yake naira dubu saba’in ba zai ciyar da su, ko tufatar da su ba, ballantana har...
Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [9] Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [8] Neman taimako daga Allah yana da nau’i biyu: 1. Taimako na Gaba ɗaya: Wannan yana nufin cewa dukkan halittu suna buƙatar Allah wajen gudanar da rayuwa, kamar samun arziki, da lafiya, da tsira da kulawa, da sauran su. 2....
Kakakin hukumar raya hadin gwiwar neman ci gaban kasa da kasa ta kasar Sin (CIDCA), Li Ming, ya bayyana a gun taron manema labaru na yau Litinin cewa, rage yawan tallafin kasashen waje da Amurka ta yi, da rage fiye da kashi 90 cikin 100 na ayyukan da take yi, sun sabawa alkawuran da ta...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a yau Litinin cewa, atisayen da sojojin kasar Sin suka yi a mashigin tekun Taiwan wani muhimmin martani ne ga goyon bayan da kasashen waje ke nunawa kan yunkurin neman “’yancin kan Taiwan,” kuma babban gargadi ne ga ‘yan awaren Taiwan. Kakakin ta ce, matakin...
“Dole ne mu ci gaba da bunkasa jiharmu, kuma an gina wadannan gidajen ne don habaka jiharmu. “Ga dukkan masu gidaje da ke wadannan jerin gidaje, ina sanar da su a fili, ko dai su koma wuraren da zama ko kuma a kwace,” in ji Gwamna Yusuf. Ya kuma bukaci wadanda ba za...
Seyi Tinubu, ɗan Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa, mahaifinsa ne kaɗai shugaban ƙasar da ba shi da burin azurta kansa da kuɗin talakawa. Har wa yau ya ƙara da cewa shi kaɗai ne shugaban da ke bai wa matasa damammaki a gwamnatinsa. Abba ya rantsar da sabon Kwamishinan Gidaje na Kano Ana zargin...
A ranar Larabar da ta gabata ne, harajin kashi 25 na shugaban Amurka Donald Trump kan duk wasu kayayyakin karafa da goron ruwa ya fara aiki. Inda Kanada ta mayar da martani kai tsaye da harajin kashi 25 kan kayayyakin Amurka na sama da dala biliyan 20, wadanda suka hada da karafa, kwamfutoci da kayan...
Yau Litinin da safe, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwa ta Sin ya kira wani taron manema labarai, inda kakakin hukumar kididdiga ta Sin, Fu Linghui ya yi bayani kan yadda tattalin arzikin kasar ke gudana a cikin farkon watanni biyu na bana da suka gabata. Kididdiga na nuna cewa, daga watan Janairu zuwa Fabrairu...
Gwamna Abba Kabir Yusuf a wannan Litinin ɗin ya rantsar da sabon Kwamishinan Ma’aikatar Tsarawa da Bunƙasa Gidaje ta Kano, Ibrahim Yakubu Adamu. Wannan dai shi ne karo na huɗu cikin ƙasa da shekaru biyu ke nan da gwamnan yake faɗaɗa majalisar zartarwa jihar ta Kano. Ana zargin wa da ƙani da yi wa almajiri...
Wasu manyan jami’an kasar Habasha sun bayyana cewa, layin dogon da ya sada tsakanin kasar Habasha da Djibouti da kasar Sin ta gina, yana kara inganta bangaren hada-hadar kayayyaki na kasar Habasha, kana ya zama wani muhimmin ginshiki da ke taimaka wa cinikayyar shigo da kaya da fitar da su zuwa kasashen waje a kasar....
Iran ta ce za ta fifita diflomatisyya ta tsakaninta da kasashe makobtanta na yankin. Ministan harkokin wajen kasar ne Abbas Araghchi ya jaddada aniyar kasar kan harkokin diflomasiyya a yankin, yana mai bayyana cewa kasashen da ke makwabtaka da kasar na cikin tsarin Jamhuriyar Musulunci. “Makwabtanmu sune fifikonmu,” in ji ministan harkokin wajen Iran a...
Ofishin kwamitin kolin JKS da na majalisar gudanarwar kasar Sin, sun sanar da kaddamar da sabon shiri game da tsare-tsaren musamman na bunkasa sayayya a kasar Sin, a gabar da kasar wadda ita ce ta biyu a karfin tattalin arziki a duniya ke kara karkata ga mayar da kasuwannin gida ginshiki, kuma babban karfi na...
Babban sakantaren MDD António Guterres, ya yi kira ga mabambantan bangarori masu ruwa da tsaki a Yemen da su yi iyakacin kokarin yin hakuri da juna, su kuma dakatar da kowane irin matakin soja, inji kakakinsa a wata sanarwa. Sanarwar ta ce, “Mun lura da cewa, Amurka ta kai hare-hare da dama kan wasu wurare...
“Za a lika sunayen tare da albashin ma’aikata a wurare masu mahimmanci a cikin harabar ma’aikatu, ofisoshin gwamnati da sakatariyar kananan hukumomi 44 na jihar don sauƙaƙe aikin,” in ji Faruk. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga...
Rundunar ’yan sandan Adamawa ta cafke wani ƙani da yayansa — Aliyu Abdulmalik da Ibrahim Abdulmalik — kan zargin yanke kan wani almajiri ɗan shekara 10, Abdallah Lawali. Bayanai sun ce ’yan uwan junan biyu sun aikata wannan ta’asa ce a ranar 7 ga watan Maris a unguwar Sarkin Yamma da ke Ƙaramar Hukumar Jada....
Sai dai hukumar yankin Taiwan na ci gaba da kokarin yada karairayi, tare da tunasar da kowa kasancewarta. In ba haka ba, wadannan bayanai masu kunshe da kurakurai da muka ambata ba za su bayyana a kan wata jaridar Najeriya ba. Hakika, a shekarun nan, hukumar Taiwan ta yi ta kokarin takala da batun neman...
Seyi Tinubu, ɗan shugaban kasa Bola Tinubu, ya bayyana cewa mahaifinsa shi ne shugaban Nijeriya mafi girma a tarihi, yana yaba wa shugabancinsa da himmarsa wajen bunkasa rayuwar matasa. A cikin wani faifan bidiyo da ya bayyana ranar Litinin, Seyi ya furta wannan magana yayin da yake jawabi ga taron matasa a jihar Adamawa. Ya...