2025-03-02@22:08:34 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1265
«Gwamna Nasir»:
’Yan bindiga sun kai hari ƙauyukan Bagiza da Rausa Kade a Ƙaramar Hukumar Arewa, Jihar Kebbi, inda suka kashe mutum shida a makon da ya gabata. Maharan sun kashe mutum biyar a Rausa Kade, sannan suka hallaka ɗaya a Bagiza yayin harin da suka kai domin satar shanu. Matata ta taɓa kawo min ƙarar Akpabio...
’Yan bindiga sun kai hari ƙauyukan Bagiza da Rausa Kade a Ƙaramar Hukumar Arewa, Jihar Kebbi, inda suka kashe mutum shida a makon da ya gabata. Maharan sun kashe mutum biyar a Rausa Kade, sannan suka hallaka ɗaya a Bagiza yayin harin da suka kai domin satar shanu. Matata ta taɓa kawo min ƙarar Akpabio...
Jakadan kasar Sin a Amurka Xie Feng ya bayyana a cikin wani jawabi ta bidiyo da ya gabatar ga taron kolin jagorancin Sin na Duke-UNC a ranar 28 ga watan Fabrairu cewa, kasancewar zaman lafiya mai dorewa tsakanin Sin da Amurka a duniya, abu ne da ya zama wajibi kuma nauyi ne dake kan wuyansu....
Hukumar wayar da kan jama’a ta kasa NOA, ta yi kira ga al’ummar Musulmi da su yi amfani da wannan lokaci na watan Ramadan wajen tunanin abubuwan da za su amfani kasa baki daya. Kodinetan hukumar na jihar Jigawa Mallam Ahmed Tijjani Ibrahim ya yi wannan kiran a wata sanarwa da ya raba wa manema...
Hamas ta tabbatar cewa “Shawarar da Netanyahu ya yanke na dakatar da shigar da kayan agajin da jin kai na kasashen duniya zuwa zirin Gaza, hakan na a matsayin laifin yaki da kuma keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta da musayar fursunoni.” Kungiyar ta yi kira ga masu shiga tsakani da kasashen duniya da su matsa...
Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres na mika sakon gaisuwa a yayin da al’ummar Musulmi a fadin duniya suka fara gudanar da azumin watan Ramadan. Ramadan yana kunshe da dabi’u na tausayi, tausayawa da karamci. Sannan dama ce ta sake haduwa da dangi da sauran al’umma. Kazalika dama ce ta tuna wadanda ba...
Masar ta jaddada matsayinta kan duk wani yunkuri na kawo barazana ga hadin kan Sudan da ‘yancin kanta da kuma yankinta, tare da yin gargadin cewa kafa gwamnatin rikon kwarya na iya kawo rudani a kasar. A cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya Lahadi, Ma’aikatar harkokin wajen Masar ta sanar da cewa “Jamhuriyar...
Wasu ’yan bindiga sun yi basaja a matsayin jami’an Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), tare da sace mutum 10 a Otal ɗin White Hill da ke kan titin Shiroro a Ƙaramar Hukumar Chanchaga a Jihar Neja. Wani masani kan harkokin tsaro, Zagazola Makama, ya ce harin ya faru da misalin ƙarfe 4:58...
Hukumar Hisba ta Jihar Kano, ta kama wasu matasa da ba su yi azumi a ranar farko ta watan Ramadan ba. Mataimakin Kwamanda Janar na Hukumar, Dokta Mujahideen Abubakar ne, ya tabbatar da kama matasan. Sojoji sun ƙwato makamai a dajin Sambisa Miji ya kashe matarsa saboda abincin buɗa-baki a Bauchi Hakazalika, ya tabbatar da...
Dakarun Sojin Najeriya tare da haɗin gwiwar JTF na Operation Hadin Kai, sun kai farmaki dajin Sambisa, inda suka ƙwato makamai da alburusai masu yawa. Wata majiya ta bayyana cewa sojojin, sun kai samame yankin Ukuba tare da bataliya ta musamman ta 199 da kuma ‘yan sandan JTF domin bincike da ƙwato makaman da ‘yan...
Wadannan ayyuka suna tunatar da duniya hakikanin fuskar Musulunci. Kuma ko da yaushe na kan zama mafi samun kwarin gwiwa da kwanciyar hankali a wannan lokaci. A cikin wannan wata mai alfarma, dukkkanmu muna samun daukaka ta hanyar dabbaka wadannan dabi’u kuma muna rungumar ‘yan uwantaka don gina duniya mai adalci da zaman lafiya ga...
Wadannan ayyuka suna tunatar da duniya hakikanin fuskar Musulunci. Kuma ko da yaushe na kan zama mafi samun kwarin gwiwa da kwanciyar hankali a wannan lokaci. A cikin wannan wata mai alfarma, dukkkanmu muna samun daukaka ta hanyar dabbaka wadannan dabi’u kuma muna rungumar ‘yan uwantaka don gina duniya mai adalci da zaman lafiya ga...
Aƙalla fasinjoji 12 ne suka ƙone ƙurmus har lahira a wani mummunan hatsari da ya auku a kan titin Benin zuwa Auchi a Jihar Edo. Kakakin Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC) a Edo, Cyril Mathew, ya tabbatar da aukuwar hatsarin. Miji ya kashe matarsa saboda abincin buɗa-baki a Bauchi Abubuwan da ya kamata a...
’Yan sanda sun cafke wani magidanci mai shekaru 50, Alhaji Nuru Isah kan zargin lakaɗa wa matarsa dukan da ya yi ajalinta a dalilin abincin buɗa-baki. Bayanai sun ce taƙaddamar wadda aka soma gudanar da bincike a kanta ta auku ne a ranar Asabar a yankin Fadaman Mada da ke Jihar Bauchi. Burina in yi...
Maryam Abubakar sabuwar jaruma ce a Masana’antar Kannywood ’yar Hajiya Hauwa Garba da aka fi sani da ’Yar Auta ko Sabirar Gidan Badamasi. A zantawarta da Aminiya ta ce babban burinta shi ne ta yi fice da suna kamar yadda mahaifiyarta Hajiya Hauwa Garba ta yi: Mene ne takaitaccen tarihinki? Sunana Maryam Abubakar wadda aka...
Ministan harkokin wajen kasar Ali Muhammad Umar ya bayyana cewa; Somaliya za ta iya rattaba hannu akan takardun fahimtar juna da za su bai wa Habasha izinin amfani da tashar ruwa da take a gabar tekun Indiya daga nan zuwa watan Yuni. A ranar Alhamis din da ta gabata ne dai Fira ministan kasar Habasha...
Bismillahir Rahmanir Rahim Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Wanda Ya isar da komai. Tsira da amincin Allah su tabbata bisa ga Annabi (S.A.W) da kuma bayinsa zababbu. Bayan haka. Wannan wani dan takaitaccen sako ne nake so na isar da shi ga ’yan uwa Musulmi, na ciro hujjojinta daga littafin Allah (S.W.T) da kuma...
Rundunar Basij a yankin kudu maso gabacin kasar Iran ta bada sanarwan shahadar dakarunta guda biyu a jiya Asabar. Kamfanin dillancin labaran tasnim na kasar Iran, ya nakalto rundunar IRGC na yankin ya na bada sanarwan shahadar Hojjatoleslam Sadeq Mahmoudi da kuma Milad Damankesh a lokacinda suke komawa gida daga wurin aiki a cikin wata...
A wani bidiyo mai ban mamaki da Hukumar Kashe Gobara ta yankin Tulsa da ke kasar Amurka ta fitar ya nuna yadda wani kare ya yi sanadin tashin wuta a wani gida ta hanyar tauna fakitin batirin Lithium. Hukuma ta kama karen bayan gano hakan a bidiyon mai ban mamaki, wanda ya nuna shi yana...
Mikel Arteta ya ce, Arsenal ce za ta lashe kofin Premier League na kakar bana, ba kamar yadda ake hasashen Liverpool ba. A ranar Laraba Gunners, wadda take da tazarar maki 11 tsakaninta da Liverpool za ta fafata da Nottingham Forest a wasan mako na 27 a Premier League. Ta ina Kungiyar Hizbullah ke samun...

Hamas Ta Bukaci Falasdinawa A Birnin Qudus Su Sabawa Dokar Takaita Yawan Masu Shiga Masallacin Al-Aksa A Kudus
Wata kungiyar kare hakkin bil’adama ta kasa da kasa ta bada rahoton cewa sojojin HKI sun kashe akalla yara 16 tun farkon wannan shekara ta 2025 a yankin yamma da kogin Jordan. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Ayed Abu Eqtaish, daraktan kungiyar ‘ The Defense for Children International’ a yankin yamma...
Kungiyar Hamas ta bada sanarwan cewa gwamnatin HKI a yankin yamma da Kogin Jordan tana rusa gidajen Falasdinawa a sansanin yan gudun hijira na Nur- Ashamsh, a ranar farko ta watan Ramadan mai alfarma. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar Nihad Ashawish shugaban kwamitin mai kula da sansanin yan gudun hijirar...
Gwamnatin kasar masar ta tabbatarwa gwamnatin Falasdinawa kan cewa tana goyon bayan falasdinawa a cikin dawo da hakkinsu, na kafa kasarsu mai cikekken yanci wacce take da gabacin birnin Qudus a matsayin babban birnin Kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Mostafa Madbouly ministan harkokin wajen kasar Masar yana fadar haka a...
An kaddamar da taro na 10 na zaunannen kwamitin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin wato CPPCC karo na 14 a yau 1 ga watan Maris a nan birnin Beijing, inda memban hukumar siyasa na kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta Sin kuma shugaban majalisar CPPCC Wang Huning ya halarci taron....
Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta gamu da cikas a kokarinta na darewa kan teburin gasar Laliga ta kasar Sifaniya, bayan rashin nasarar da ta yi a hannun Real Betis a filin wasa na Benito Villamarin da ke Seville. Tsohon dan wasan Real Madrid, Isco Alacon ne ya lashe kyautar gwarzon dan wasa a...
Rundunar ’yan sandan Kano ta cafke wasu matasa biyu kan zargin satar wayoyin hannu a kasuwar waya ta Beirut da ke birnin na Dabo. Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ta ce an cafke ɗaya daga cikin ababen zargin ne yana yunƙurin satar waya a wani shago....
Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Hansi Flick, ya bayyana cewa kungiyarsa za ta je har gidan Atletico Madrid ta doke ta a wasan kusa da na karshe na gasar cin kofin Coppa Del Rey, bayan da Barcelona da Atletico Madrid suka tashi 4-4 a wasan farko zagayen daf da karshe a Copa del Rey...

Shugabar Tanzaniya Ta Yaba Da Yadda Ake Ci Gaba Da Samun Karuwar Jigilar Kayayyaki A Tashar Tanga Da Sin Ta Inganta
Shugabar kasar Tanzaniya Samia Suluhu Hassan ta bayyana a jiya Juma’a cewa, tashar jirgin ruwa ta Tanga da kasar Sin ta inganta yanzu tana jigilar sama da tan miliyan 1.2 na kaya a duk shekara, adadin da ya karu daga jigilar tan 400,000 a kowace shekara. “Habaka tashar ta Tanga ya inganta ayyukanta.” a cewa...
Salah ya kasance danwasa na farko a gasar Premier da ya ci ya kuma bayar aka ci a wasanni daban-daban har goma a kaka daya. Sannan shi ne danwasa na farko da ya yi haka a daya daga cikin manyan gasar Turai biyar tun bayan Lionel Messi da ya yi wannan bajinta a kakar 2014-15,...
Shugaban Ƙasar Ukraine, Volodymyr Zelensky ya ce bai ga laifin da ya yi wa Shugaban Amurka Donald Trump, ballantana ya nemi afuwa. Zelensky ya bayyana haka ne bayan zazzafar cacar-baki da ya kaure a tsakaninsa da Trump a ofishin shugaban ƙasar Amurka. A cewarsa, “ina godiya ga Amurka da gudunmuwar da take ba mu,” in...
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi watsi da shawarar da Isra’ila ta gabatar na tsawaita matakin farko na yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza, inda ta yi kira ga kasashen duniya da su matsa wa gwamnatin mamayar lamba don ci gaba da mataki na biyu na yarjejeniyar kamar yadda aka tsara tun farko. Yau...
Shugaban kungiyar Ansarallah ta kasar Yemen Sayyed Abdul-Malik Al-Houthi, ya bayyana cewa Isra’ila na fakewa da goyan bayan Amurka tana keta yarjeejniyar tsagaita wuta a Gaza. Al-Houthi ya bayyana cewar: Kin janyewar makiya daga yankin Rafah, ya zamanto karara karya yarjejeniyar da aka kulla tsakanin Masar da makiya yahudawan sahyoniya. » Ya kara da cewa:...

Kasashen Afirka ta Kudu da Malaysia da Colombiya za su hana jiragen ruwa da ke dauke da makamai zuwa Isra’ila
Shugabannin kasashen Afirka ta Kudu da Malaysia da Colombia sun jaddada aniyarsu ta hana jiragen ruwa da ke dauke da makamai zuwa Isra’ila amfani da tashar jiragen ruwansu, a daidai lokacin da gwamnatin kasar ke ci gaba da aiwatar da kisan kare dangi a zirin Gaza. “Za mu hana jiragen ruwa da ke dauke da...
Allah Ya yi wa Sarkin Sasa, Alhaji Haruna Maiyasin rasuwa bayan shafe shekaru 125 a duniya. Fadar Sarkin Sasa da ke Ibadan, babban birnin Jihar Oyo, ce ta bayar da sanarwar rasuwar Sarkin wanda ke riƙe da muƙamin Sardaunan Yamma. HOTUNA: Gobara ta laƙume shaguna 100 a Kasuwar Sakkwato An raba wa ma’aikatan gona babura...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taba jaddada cewa, kasar Sin ta girmama ikon mallakar kasa da cikakken yanki na kasashen tsibirai na yankin tekun Pasifik, da girmama bukatunsu da al’adun kabilunsu da kuma hadin gwiwarsu wajen samun ci gaba da kansu. A kwanakin baya, yayin da firaministan kasar tsibiran Cook Mark Brown yake hira...
Ana fargabar cewa wata gobara ta laƙume aƙalla shaguna 100 a Kasuwar Kara da ke Jihar Sakkwato. Gobarar wadda ta tashi tun da Asubahin wannan Asabar ɗin ta shafe sa’o’i 9 tana ta’adi. An raba wa ma’aikatan gona babura 200 a Yobe Yadda farashin kayan abinci ya sauka a kasuwannin Arewa Wani ɗan kasuwar da...
Babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada kokarin sa kaimi ga ciyar da shirin kasar Sin mai kwanciyar zuwa matsayi mai girma. Xi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jagorantar taron nazari na ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS a jiya Juma’a. Inda ya yi kira da...
Amma duk da haka, hatta wake-wake da raye-raye da kuma abinda ya shafi sinima, tsofaffin jarumai ne su ka kawo su a masana’antar Kannywood, saboda haka ya kasance wani lokaci mai ban sha’awa a tarihi lokacin da Hamisu Lamido Iyan-Tama ya hadu da Hindatu Bashir a kan dandamali don ba shi lambar yabo. Dukkanmu sai...
Gwamnatin Yobe ta raba wa ma’aikatan gona babura guda 200 domin gudanar da ayyukan kula da harkokin noma a jihar. Kwamishinan ma’aikatar gona da albarkatun kasa, Ali Mustapha Goniri ne ya bayyana haka a lokacin da yake miƙa baburan ga waɗanda suka rabauta. Yadda farashin kayan abinci ya sauka a kasuwannin Arewa Yadda ake ‘Spring...
Sunana Aisha T. Bello daga Jihar Kaduna: Rashi ramadan basket nasa a kore saurayi saboda ‘yan mata sun maida ramadan basket dole. Shawara ta ga al’ummar musulmi duniya shi ne; mu yi amfani da wannan dama gun rokon Allah, saboda in Allah ya nuna mana wanan mu gani ba lallai bane mu ga wani watan...
Farashin kayayyakin abinci kamar masara da shinkafa da gero da dawa da wake da gari da waken soya da dai sauransu sun ragu, musamman a manyan jihohin da ake nomawa, kamar yadda wani bincike da Aminiya ta gudanar ya nuna. Wannan na faruwa ne gabanin watan Ramadan, wanda aka fara yau Asabar. Yadda ake ‘Spring...
Mene ne ruwan kanwa? Ruwan kanwa wani ruwa ne da akeyiwa mai azumi yanada dadi sosai sannan idan mai azumi ya sha bayasa kasala yana warware cikin ko hanji cikin mutum zance, idan mai azumi yasaba da shan ruwan kanwa duk randa baisha ba bazai taba jin dadi ba. Ya ake ruwan kanwa? Da...
C- A nan ganyen zogalen da kika tafasa sai ki zuba a faranti ki yanka tumatir manya guda uku, ki yanka gurji (cocumber) babba guda daya, ki saka magi, gishiri kadan, mai kadan. Kar ki sa wulikuli. Zai yi miki maganin basir da cikowar gaba. Zai kara mi ki ni’ima da dandano sosai. 5) Ruwan...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno, ta sanar da ƙarin matakan tsaro yayin da al’ummar Musulmi suka shiga watan azumin Ramadan. Haka kuma, rundunar ta taya Musulmi murnar shigowar wannan wata mai alfarma. Gobara ta hallaka mutum 2 a sansanin ’yan gudun hijira a Borno Ramadan: Ga arahar kayan abinci ga rashin kuɗin saya Kakakin rundunar,...
Dabi’un Da Suke Sa Malamin Makaranta Ya Ke Zama Nagartacce Ko dai su kasance suna koyar da manyan dalibai ne ko kuma lamarin ya zama suna koyar da kirga ce daga daya zuwa goma Azakakuran Malamai suna da wadansu dabi’u da suka yi kama da juna. Alal misali sanin kowa ne duk dai masu ilimi...
A yau daya ga watan Maris ne dokar haramta amfani da tankunan dakon man fetur masu daukar lita 60,000 saboda yawan hatsarin da suke yi, wanda kuma yake lakume rayukan daruruwan mutane a ko wace shekara a duk fadin kasar. Jaridar Weeken Trust ya bayyana cewa hukumar ‘ The Nigerian Midstream and Downstream Petroleum Regulatory...
Wata gobara da ta tashi cikin ta lalata wani ɓangare na Asibitin Ago da ke kan titin Ago Palace, Okota, a Jihar Legas. Gobarar ta fara ne da misalin ƙarfe 8:30 na daren ranar Juma’a, inda ta shafi wani sashe na ginin mai bene hawa ɗaya, inda asibitin yake. Gobara ta hallaka mutum 2 a...
Tawagar yan wasan Damben Gargariya ta kasar Iran sun zama zakara a wasan damben da ya gudana a birnin Tirana babban birnin kasar Albaniya a makon da ya gabata, inda suka tashi da lambobin yabo 6 wadanda suka hada da zinari 4 azurfa da tagulla. Wannan nasara da ta maida kasar a matsayin zakara a...
Kasashen Iran da Hadaddiyar Daular Larabawa sun gudanar da taron kwamitin Siyasa da al-adun na kasashen biyu a karon farko a birnin Abu Dhabi wanda ya kara tabbatar da irin ci gaban da suke samu a dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa kyautata dangantaka tsakanin...
Shugaban kungiyar Ansarullah Sayyid Abdulmalik Badruddeen Huthi ya bayyana cewa kasar Yemen a shirye take ta sake shiga yaki idan yarjeniyar tsagaita wuta tsakanin bangarorin biyu ta wargaje. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Sayyid Huthi yana fadar haka a wani jawabin da ya gabatar ta hotunan bidiyo a jiya 28 ga...