2025-04-25@10:14:41 GMT
إجمالي نتائج البحث: 193
«Mayaƙan Boko Haram»:
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Assalamu alaikum masu sauraro sharhin bayan labarammu zai yi magana a kan ‘wani makircin da kasar faransa ta kullawa falasdinawa a gaza’ don su amfana da kwararrunsu’ wanda ni tahir amin zan karanta. ///… Shugaba kungiyar kare hakkin bil’adama masi suna [the Euro-Mediterranean Human Rights Monitor] ta fallasa wani shiri tsakanin gwamnatin kasar faransa da...
Kasar faransa ta jaddada anniyar na ci gaba da tattaunawa kan shirin nukiliyar iran. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Faransa ya bayyana a ranar Alhamis cewa, Faransa na ci gaba da jajircewa wajen ganin an warware matsalar nukiliyar Iran ta hanyar diflomasiyya, kuma a shirye take ta ci gaba da tattaunawa da Tehran. A yayin taron...
Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) Bauchi ta sallami ɗaya daga cikin malamanta, Dokta Usman Mohammed Aliyu daga jami’ar bisa zargin neman yin lalata da wata ɗaliba matar aure da ke karatun digiri na biyu. Idan dai ba a manta ba, Kamila Rufa’i Aliyu, ɗalibar Sashen koyon aikin injiniya ce, a shekarar bara ta roƙi mahukuntan...

Gwamnatin Siriya Tana Daukan Matakan Matsin Lamba Kan Gwagwarmaya Domin Samun Yardan ‘Yan Sahayoniyya
Sabuwar gwamnatin Siriya tana kara matsa lamba kan bangarorin ‘yan gwagwarmaya domin Isra’ila ta janye daga wasu yankunan kasarta Sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da tura kayayyakin soji zuwa tsaunukan Dutsen Harmon, yayin da suke hanzarta gina abin da suka kira “Katangar tsaro.” Har ila yau, sun karfafa wuraren tsaro da suka kafa a...
Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo, ya dakatar da basaraken yankin Masarautar Uwano Kingdom, Dakta George Oshiapi Egabor, nan take saboda matsalar yi garkuwa da mutane a yankin. Dakta George Oshiapi Egabor shi ne Okumagbe na Masarautar Uwano da ke Agenebode a Karamar Hukumar Etsako ta jihar. Kakakin gwamnan, Fred Itua, a cikin wata sanarwa, ya...

Darajar Cinikin Sarin Kaya Da Sayen Kayan Masarufin Sin Ta Karu Da Dala Biliyan 452.5 a Rubu’In Farkon Bana
Ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ta tabbatar da tsare-tsaren da kwamitin tsakiyar jam’iyyar kwaminis ta Sin da majalisar gudanarwar kasar suka tsayar don gaggauta kyautata tsarin tafiyar da ciniki daidai da zamani, da ingiza ingantaciyar bunkasuwar cinikin sarin kaya da sayen kayan masarufi bisa matakai daban-daban. Bisa alkaluman da hukumar kididdigar Sin ta fitar a...
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka, sharhin bayan labarammu na yau za yi magana dangane da “Rage kisasfin kudan ma’aikatar harkokin wajen Amurla da kimani kasha 50% da kuma tasirinsa ga matsayin Amurka a duniya da kuma cikin gida. Wanda ni tahir amin zan karanta. A makon da ya gabata ne shugaban kasar Amurka...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A daidai lokacin da ake tunanin samun sauƙi daga tarin matsalolin tsaro da na tada ƙayar baya a Najeriya, sai ga wasu sabbin matsalolin na ƙara kunno kai. Yayin da a wannan lokaci ake fuskantar hare-haren da ake zargin na ƙungiyar Boko Haram ne a Arewa maso Gabas,...
Tsohon mashawarcin Shugaba Bola Tinubu kan harkokin siyasa, Dokta Hakeem Baba-Ahmed, ya bayyana cewa babu wani ɗan siyasa da zai iya lashe kujerar shugabancin Nijeriya a Zaɓen 2027 ba tare da goyon bayan yankin Arewacin ƙasar ba. Hakeem Baba-Ahmed ya bayyana hakan a wata hira ta bidiyo tare da tsohon Babban Sakataren Hukumar Kula da...
A faransa ana ci gaba da tsare wata ‘yar Iran mai goyan bayan Falasdinu, bis azarginta da iza ta’addanci. Mahdieh Esfandiari (mai shekaru 35) ana tsare da ita tun ranar 28 ga watan Fabrairu, bayan kama ta a binrin Lyon, inda ta ke da zama. Iran ta bakin kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar, Esmail Baghai,...
Shugaban ya kuma bai wa masu ruwa da tsaki a fannin cewa, ako da yaushe, kofar Hukumar ta NPA, bode take domin hadaka wacce ta zarce ta gudanar da baje koli. Dakta Dantsoho ya kara da cewa, an samar da tsarin na EPT domin a tabbatar da cewa, ana fitar da kaya zuwa waje, ta...
Ilimi na da muhimmanci wajen gina al’umma, amma ga daliban Makarantar Firamare ta Bare a karamar Hukumar billiri, Jihar Gombe, wannan lamari ya zama kamar mafarki mai wahalar tabbatuwa. Duk da ikirarin da Gwamnatin Jihar Gombe ke yi na cewa, tana fifita ilimi ta hanyar manyan ayyuka kamar gine-ginen makarantu masu hawa biyu a kowace...
Waɗanda suka take wa Ministan sawu a tafiyar su ne jagororin hukumomin yaɗa labarai da wayar da kai da ke ƙarƙashin ma’aikatar sa. Ya yi zama daban-daban tare da ƙwararru inda suka tattauna kan yadda za a inganta ƙwarewa da kuma kayan aiki na zamani na kafafen yaɗa labarai na gwamnatin Nijeriya. Ya ce:...
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Pakisatan ta kara jaddada matsayinta na rashin amince da HKI a matsayin kasa tana kuma goyon bayan Falasdinawa a gwagwarmayan da suke yi na kwatar yencinsu da kuma kasarsu daga hannun HKI da kuma kasashen yamma musamman Amurka masu goya mata. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran wannan sanarwan tazo...
Mako guda bayan rage farashin fetur da Naira 45, matatar mai ta Dangote ta sake karya farashin man ga ‘yan sari da ragin Naira 30 duk lita. Aminiya ta rawaito cewa matatar na sayar da man ne a ranar Laraba akan ₦835, saɓanin makon da ya gabata da ta sayar da shi akan ₦865 bayan...
Ya kara da cewa, CMG ta dade tana kasancewa ingantacciyar gada dake inganta fahimtar juna tsakanin kasashen biyu, kuma ya yi imanin cewa, hadin gwiwarsu a wannan karo zai kara karfafa daddaden dankon zumunci a tsakanin kasashen biyu. (Amina Xu) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun...
Gwamnan Filato, Caleb Mutfwang, ya sanar da haramta kiwo da daddare tare da taƙaita amfani da babura a faɗin jihar sakamakon yawaitar hare-haren da ake kai wa a wasu sassan jihar. A cikin wani jawabi da ya yi a jihar a ranar Laraba, Mutfwang ya bayyana hare-haren a matsayin “ayyukan ta’addanci” da ke da nufin...
Paris St Germain ta kai zagayen daf da na ƙarshe a Gasar Zakarun Turai duk da rashin nasara da ta yi a hannun Aston Villa ranar Talata a Villa Park. Aston Villa ta yi nasarar cin PSG 3-2, inda Tielemans da McGinn da kuma Konsa suka ci mata ƙwallayen a wasa falle na biyu a...
A yayin ziyarar aiki da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai kasar Malaysia, daga yanzu manyan kafofin sadarwa kamar kafar yada labarai ta kasar Malaysia za su fara nuna shirin bidiyon “Bayanan magabata dake jan hankalin Xi Jinping” na harshen Malay wanda CMG ya shirya. Shirin ya mai da hankali ne kan...

Lauyoyin London Suna Tattara Bayanai Kan ‘Yan Birtaniya Da Suka Yi Yaki Cikin Sahun Yahudawan Sahayoniyya A Gaza
Lauyoyin Landan suna tattara bayanai kan ‘yan Birtaniya da suka yi aiki a cikin rundunar sojojin mamayar Isra’ila Kwararru kan harkokin shari’a na kasar Biritaniya sun ce gurfanar da wasu ‘yan kasar masu takardar ‘yan kasa biyu da ke aiki a cikin sojojin mamayar Isra’ila a gaban kuliya bisa zargin hannu a tafka laifukan yaki...
Gwamnatin Amurka ta sanar da janye sabon harajin da ta ƙaƙaba wa kayayyakin laturoni irin su wayoyin salula, kwamfutoci da sauran na’urorin da ake shigo mata daga ƙetare. Ana sa ran matakin ya rage raɗaɗin tashin farashin kayayyakin da zai faru a Amurka bayan da a kwanaki Shugaba Donald Trump ya lafta wa ƙasashe ciki...
A nata martani kuwa, Okonjo-Iweala ta ce, karuwar takun saka ta fuskar cinikayya ya haifar da babban kalubale ga tsarin bunkasar cinikayya da tattalin arzikin duniya. Don haka ta jaddada muhimmancin rungumar budadden salo na bin ka’idar cudanyar mabambantan sassa, kana ta jaddada wajibcin warware dukkanin takaddama ta hanyar tattaunawa mai ma’ana karkashin dandalin...
Daga karshe ta ce da farko ta samu turjiya daga wajen wasu mutane a kan kudurinta na fara harkar fim amma kuma ta yi biris dasu ta fara, amma kuma yanzu wadanda a baya ke hanata shiga fim su ne yanzu ke yi mata murnar samun nasara hakan ya matukar bata mamaki, duba da cewar...
Ministan harkokin wajen kasar Saudiya ya bayyana cewa shigo da kayakin agaji zuwa cikin zirin Gaza bai da wata dangantka da tsagaita bude wuta. Shafin yanar Gizo na labarai Arab News na kasar Saudiya ya nakalto Yerima Faisal bin Farhan yana fadar haka a jiya Jumma’a.. Ya kuma kara da cewa dole ne kasashen duniya...
Ministan Ma’aikatar Aikin Gona da Samar da Wadaccen Abinci, Sanata Abubakar Kayri ne ya bayyana a haka, a cikin sanarwar da ma’aikatar ta fitar. “Mun samar da tsarin samar da wadataccen abinci a kasar nan, wanda kowanne dan kasar zai amfana da shi”, in ji Kyari. Daga cikin manyan abubuwan da suka hada da bashin...
A cewarsa, wadannan kudaden sun hada da biyan kudaden samar da kariya da na inshore da kuma sauran kudaden da ake biyan kamfanonin na waje. Ya sanar da cewa, wadanan kudaden da ake biya, na shafar ci gaban tattalun arzikin kasar, inda ya yi nuni da cewa, duk Jirgin ruwa daya da ya yi dakon...
Kazalika, a wani binciken kwanan baya na gama gari kan yawan alummar kasar, ya gano cewa, kaso 53 na wasu matasan kasar, a kullum suna rungumar wannan dabi’ar. Sai dai, muna sane da cewa, wasu ‘yan Nijeriya, na kallon yin cacar tamkar wata aba ce, ta nishadi kawai, amma wasu bincike sun bayyana cewa, wani...
Kasashen China da Tarayyar Turai sun maida martani kan kudaden fiton da Amurka ta kara masu. Kamfanin dillancin labaran Rauter ya bayyana cewa kasashen Turai 27 sun kara kashi 25% ga wasu zababbun kayakin kasar Amurka masu shigowa kasashen su. Wannan dais hi ne maida martani na farko wanda kasashen turan suka yi tun bayan...
Akalla malaman makarantun firamare 1,800, a fadin kananan hukumomi goma sha shida na jihar Kwara, aaka horar da su kan kara kuzari kan ilimin zamani, hanyoyin amfani da kayan zamani wajen koyarwa. Da yake bayyana taron bitar na kwanaki goma da aka bude a makarantar sakandire ta Queen Elizabeth da ke Ilorin wanda KwaraLEARN...
Assalamu alaikum masu sauraro barakammu da war haka, sharhin bayan labarummu zai yi magana dangane da ‘Siyasar Amurka ta fara yakin kudaden fito tsakaninta da China da kasashen Turai da sauransu. Wanda ni tahir amin zan karanta. ///.. A ranar laraba 2 ga watan Afrilun da muke ciki ne shugaban kasar Amurka Donal Trump ya...
Gwamnatin kasar China ta bada sanarwan kara kodaden fito kan kayakin Amurka wadanda suke shigowa kasa har na kasha 80% sannan a shirye take ta ci gaba da yakin kasuwanci da gwamnatin shugaba Trump har zuwa karshe. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jami’an gwamnatin kasar China na fadar haka a yau...
Ta kuma ce har yanzu ƙasashe sama da 70 daga sassa daban-daban na duniya sun tuntuɓi Amurka domin a yi tattaunawa kan yadda sabbin harajin ke shafar kasuwanci a duniya. Mene ne Ma’anar Wannan Haraji? Wannan haraji na nufin idan ana shiga da kaya daga China zuwa Amurka, za a ƙara musu kuɗi sosai kafin...
Ya ce karin wa’adin na baya-bayan nan ya biyo bayan cikar wa’adin farko na ranar 1 ga Afrilu, 2025, wanda aka sanya tun da farko a ranar 24 ga watan Janairu. Umar ya kara da cewa, duk da wannan karin wa’adin, amma an ci gaba da samun karancin fitowar masu filaye domin sabunta takardunsu....

Trump Yayi Barazanar Karawa China Kashi 50% Na Kudaden Fito A Dai-Dai Lokacinda Suka Shiga Tsakiyar Yakin Tattalin Arziki
Shugaban kasar Amurka Donal Trump yayi barazanar karwa kasar China kasha 50% na kudaden fiton da zata karba daga kayakin kasar China da zasu shiga kasar, idan har bata janye maida martanin da tayi na kasha 34% dai dai karin kudin fito da Amurka ta kara mat aba. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran...
Jamhuriyar musulinci ta Iran, ta bayyana cewa za ta fata tattaunawa wacce ba ta kai tsaye ba da Amurka a ranar Asabar mai zuwa a kasar Oman. Ministan harkokin wajen Iran din ne Abbas Araghchi ya bayyana hakan a shafinsa na ‘’X’’ a safiyar Talata. “Iran da Amurka za su gana a Oman ranar Asabar...
Jamhuriyar Nijar ta ayyana harshen Hausa a matsayin na kasa, yayin da Faransanci ya zama harshen aiki mai sauki, don haka, Faransanci ba yaren hukuma ne ba. Matakin dai ya dogara ne da shawarwarin da babban taron kasar ya gabatart a watan Fabrairu, wanda kuma shugaban kasar Janar Abdourahamane Tiani ya amince da shi a...
Assalamu alaikujml/m masu sauraro, sharhin bayan labarummu zai yi magana danagne da zanga-zanga masu yawa wadanda ake yi a kasashen larabawa a dai dai lokacinda HKI take kara tsananta kisan kiyashi a yankin Zirin gaza, wanda ni tahir amin zan karanta. ////.. Madalla, a dai-dai lokacin da sojojin HKI suke kara yawan hare-haren da suke...
Fulham ta kawo ƙarshen wasanni 26 da Liverpool ta yi a jere ba tare da rashin nasara ba a gasar Firimiyar Ingila ta wannan kakar. Fulham ta yi nasarar doke Liverpool da 3-2 a Craven Cottage ranar Lahadi a wasan mako na 31. Liverpool ce ta fara zura ƙwallo a ragar Fulham ta hannun Mac...
Assalamu alaikum masu sauraro, sharhin bayan labarammu nay au zai yi magana kan cewa “Amurka ba zata taba zama mai sulhuntawa tsakanin HKI da Falasdinawa ba” wanda ni tahir amin zan karanta. A dai dai lokacinda rikicin gaza ya zama matsalar ta duniya a halin yanzu, da dama daga cikin masana suna ganin gwamnatin Amurka...
Direba da kwandastan motar bas sun tsere domin tsira da rayukansu, inda suka bar fasinjoji a ciki yayin da wata motar bas ta BRT ta kama wuta a Maryland da ke Jihar Legas da safiyar ranar Asabar. Majiyar Channels TV da ke wajen da lamarin ya faru, ta ce motar ta taso ne daga yankin...
Jamhuriyar Musulinci ta Iran ta yi kira ga kasashe mambobi kungiyar hadin guiwa ta Shanghai da ta yi Allah wadai da barazanar Trump ta baya baya nan kan kasar. A taron ministocin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai da aka gudanar a birnin Moscow a ranar Alhamis, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran Majid Takht Ravanchi,...
Masu ababen hawa da dama sun maƙale a gadar Namne da ta rufta daura da hanyar Jalingo zuwa Wukari a Ƙaramar hukumar Gassol ta Jihar Taraba sakamakon ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a da aka yi ranar Laraba. Ruwan sama ya kawar da gadar da aka gina ta wucin gadi a hanyar da aka...
Wani makusancin dangin Janar tsiga, ya shaida wa Daily trust cewa, bayan sun karbi kudin, masu garkuwa da mutanen sun ajiye Tsiga har tsawon mako guda kafin su tuntubi iyalan shi, inda daga bisani suka hada Janar din da ‘yan uwanshi a waya domin tattaunawa da su. Ya kara da cewa, masu garkuwa da...
Sanata mai wakiltar mazabar Kogi ta tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, da aka dakatar, ta bayyana cewa “ita ba mahaukaciya ba ce”, kuma “ba ta tsoron kowa” a yayin da take jawabi ga dimbin magoya bayanta a lokacin da ta dawo gida a Ihima, karamar hukumar Okehi ta jihar Kogi a ranar Talata da yamma. Dawowarta ta...
Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara kuma Sanata mai wakiltar mazabar Zamfara ta Yamma, Dakta Abdul’aziz Yari, ya yi kira ga ‘yan siyasa da masu hannu da shuni da su kara kaimi wajen gudanar da ayyukansu na alheri fiye da watan Ramadan. Da yake zantawa da manema labarai a mahaifarsa Talatan Mafara, a wani bangare na...
Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa ya taya al’ummar Musulmi murna bisa kammala azumin watan Ramadan lafiya, tare da kira garesu da su rungumi koyarwar Annabi Muhammadu (S.A.W) a cikin rayuwarsu ta yau da kullum. Ya bayyana hakan ne a sakon sa na Sallah ga al’ummar jihar. Malam Umar Namadi ya yi addu’a...
Masarautar Kauru da ke jihar Kaduna ta jaddada kudirinta na tabbatar da tsaro, inda ta bukaci mazauna yankin da su kasance masu taka-tsan-tsan duk da ci gaban da gwamnati ta samu a baya-bayan nan wajen magance matsalar ‘yan fashi da garkuwa da mutane da kuma munanan hare-hare. Mai martaba Sarkin Kauru, Alhaji Zakari Ya’u Usman...
Shugaban gwamnatin soja na kasar Guinea Janar Mamadi Doumbouya ne ya yi wa tsohon shugaban sojan kasar Camara afuwa bayan da aka yanke masa zaman gidan kurkuku bisa laifin kisan kiyashin da ya faru a 2009 a birnin Conakry. Kafafen watsa labarun kasar ta Guinea ne su ka sanar da afuwar da shugaba Mamadi ya...
Sheikh Na’im Qasim babban sakatarin kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ya bayyana cewa JMI ce ginshikin goyon bayan al-ummar Falasdinu, kuma itace gaba-gaban a duk wani yunkuri na yentar da falasdinawa da Falasdinu daga hannun HKI da masu goya mata baya. A wani jawabin da ya gabatar a jiya Asabar, shugaban kungiyar ta Hizbullah, ya...